Sashe 2
Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Get out, kar ki kuskura ki yi mini magiya. Duk gidan nan babu mai bani ciwon kan da ki ke bani Arfa, koma in da ki ka fito ba ki da wurin kwana a cikin gidan nan yau" da gudu ta juya ta fita saboda tsorata da ta yi.
Ta koma harabar gidan, a ƙasan zuciyarta ta ce "Na shiga uku, ni ake kora kamar wata karya, yanzu idan gidan mijina ne, ba sai dai ya gama bala'in in shige ɗaki na bar shi ba..
Ba ta gama tsinkewa da lamarin ba, sai da major ya kulle babbar ƙofar shiga cikin gidan.
Ta zube kayanta, ta tafi famfon harabar gidan, ta dinga wanke fuskarta, ta wanke kwalliyar fuskar gaba ɗaya, ta koma ta zauna jiran tsammani ko Allah zai saka Abba ya buɗe mata ƙofa.
Samarin gidan suka fara fitowa daga BQ, suna shimfiɗa a harabar gidan, za su yi kwanciyar zafi. Sai wulaƙanci suke yi mata, suna yi mata Allah ya ƙara, suna kyararta, kamar wadda ta aikata wani gagarumin abun kunya.
Ganin ba ta da mafita, ta laluba ta samo tabarma ta shimfiÉ—a, ta yi kwanciyarta dan a gajiye take sosai.
Tsakar dare, ta yi juyi, ta ji babu kowa a kan gadon sai ita kaÉ—ai, mamaki ya kamata, ta kalli agogon wayarta, biyu da rabi na dare.
Tasowa ta yi ta fito nemansa, sai dai ga mamakinta, ta tarar da shi a ventilation ɗin saman bene, ya zauna a kan kujera ya saka harabar gidan a gaba, hannunsa riƙe da ɗan ƙaramin Alqur'ani yana karantawa.
"Lafiya dai?" Tayi maganar cikin mamaki.
Ya waiwaya ya kalleta ya ce "Lafiya ƙalau"
"Amma me ka ke yi a wurin nan, a wannan uban daren? Na zata tuni ka kwanta, na fito na duba falo baka nan"
Cikin ko in kula ya ce "Kar ki damu, ki je ki yi kwanciyar ki, Arfat ke punishment"
Cikin takaici matar ta ce "To ta na punishment, sai kuma kai ka zo nan ka zauna, ka hana idonka bacci?"
Yayi murmushi ya ce "Ko na kwanta ba zan iya rintsawa ba, ki yi kwanciyar ki kawai" tamkar ta yi tsaki, haka ta wuce shi ta ƙyale shi, tama tunanin yaushe ƙarshen wannan lamarin zai zo?.
Haka ya kwana a zaune, yana gadin harabar gidan, duk wanda yayi juyi cikin mazan nan, yana kallon shi.
Yana ganin yadda Arfa ke ta juyi, sauro ya dame ta, sai da ya ji tamkar ya sauka ya samu abu ya rufe ta, amma ya ƙyale ta.
Asubar fari, ya yi alwala, ya sauka ƙasa domin tafiya masallaci.
Samarin na jin takunsa, suka din ga tashi, idan ba haka ba, ya tashi mutum da carbi.
Ya na zuwa in da take kwance tana bacci, ya tsula mata carbi a ƙafafuwanta.
A razane ta tashi tana rarraba ido.
Bai ce mata uffan ba, ya yi gaba ya fice.
Tana ganin ya fita, ta tattara komatsanta, ta shiga cikin gidan, sai soshe-soshe take yi, saboda uban sauron da ya cije ta.
Cikin É—akinta ta shiga, ta watsar da jakarta da sauran kayan a kan gadonta, ta jona wayarta a caji.
Ta tuɓe kayanta daga ita sai underwear. Wata matashiyar budurwa da aƙalla za ta ɗan girmewa Arfa ta fito daga banɗaki, ta kalle ta, ta ce "Arfa, ke kuwa a ina ki ka kwana? Har sha ɗayan dare ba ki dawo ba" banza tayi mata, ta taho fuuu ta kusa bangajeta, ta shiga banɗaki. Ta girgiza kai kawai ta shimfiɗa sallaya.
Da ƙyar ta yi sallar asuba, sai soshe-soshe take yi, tana idarwa ta ɓingire ta hau bacci a wurin.
Sosai take baccinta, dan ta gaji sosai, ga baccin jiya sam bai yi mata daÉ—i ba.
"Nabila!Nabila!!"
Tsaki tayi tare da jan "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, menene, wannan wane irin kira ne dan Allah?"
"Abba ne ya ce, ace miki yana fatan kin ajiye aiki ne, da ki ka kwanta kina bacci haryanzu ba ki fita ba"da sauri ta buÉ—e idonta, gaba É—aya ta manta yau Monday.
Kamar korarriya ta tashi, ta afka banÉ—aki, a gurguje ta wanke bakinta, tayi wanka, ta fito ta shafa mayuka, da turaruka ta shirya cikin uniform.
Ta saɓa coat ɗin ta a kafaɗa, ta ɗauki jakarta ta goyo, ta sanya takalminta, tayi waje tana kunna wayarta.
Ta shiga kitchen, ta buÉ—e fridge ta É—ebi lemuka ta zuba a jakartab, da abun da ta ajiye da wanda ba ta ajiye ba, duk ta kwasa ta zuba, ta zuge jakar ta fito falo.
A falon suka yi karo da wata matashiyar mata, matar ta kalli Nabila ta ce "Ma'aikaciya ko mahaukaciya, kalleki kamar korarriya Nabila, zaki fita aiki amma ki ka kwanta ki na kwasar bacci abinki".
Nabila ta ce "Anty, the whole barrister ki ke cewa mahaukaciya?"
"Yo banda shirme, kalleki kamar an hankaÉ—oki, ke wannan wane nutsatstsen ne ma zai ce ki tsaya masa shari'a?"
Nabila ta ce "I will fill a lawsuit against you, what you did is deformation of character, the whole barrister Anty ki ka zaga"
"Wuce ki tafi kafin na make ki ni? Idan suka kore ki daga wurin aikin, ai kya nutsu" Nabila ta sake kwasa da gudu a kan takalmanta kamar ba budurwa ba.
Mai aikinsu ta tarar a famfon harabar gidan, tana wanke-wanke.
"Shalelen Abbanta, yau kamar kin makara"
ÆŠaga mata hannu kawai Nabila ta yi, kowa ya ganta sai yayi magana, ta kalli hanyar benen Abba, kamar ta je ta gaishe shi, amma ta fasa ta san yadda ta makaran nan, sai ya zaunar da ita yayi mata faÉ—a, ga laifin jiya ga na yau, kuma ta san sai ya haÉ—a har da na waccan shekarar yayi mata, dan haka tayi wuf ta fice waje.
Duk irin vibration É—in da wayarta take yi, ba ta É—aga ba sai da ta zauna a cikin adaidaita sahu, sannan ta É—aga kai wayar kunnenta.
"Wai Nabila wani irin wulaƙanci ne, nake ta kiranki ki ka ƙi ɗagawa?"
Nabila ta ce "Ke ban son tijara, kin wuce aiki ne?"
A fusace mai maganar ta ce "Ban sani ba"
Nabila ta yi dariya ta ce "Sorry masoyiyya, ki fito titi gani nan" tafiyar mintuna sha biyar suka yi, suka iske wata matashiyar budurwar a titi, sanye cikin doguwar rigar abaya, ta kama adaidaita sahun ta shiga tana hararar Nabila.
"Sorry sumy, kar ki fashe dan Allah"
"Wallahi kin fusata ni Nabila"
"Shiyasa na ce ki yi haƙuri ai, ya gidan ya su mama?"
Sumayya ta ce "Suna lafiya ƙalau, meyasamu fuskarki? Na ga kamar ƙuraje"
Nabila ta rausayar da kai ta ce "Ke bari, the whole me, jiya Abba ya saka na kwana a haraba, sauron nan na cikin flowers suka yi idi a kaina"
Sumayya ta waro ido ta ce "Wai da gaske?"
"Zan yi miki ƙarya ne? Wallahi dattijon nan ya ce wai na koma in da na fito ya rufe ƙofa. Aikuwa na din ga tsinewa amaryar nan, na baro ta a gidanta cikin nishaɗi da farinciki, ni kuma na afka tashin hankali, kamar ni degree holder, Abba ya rufewa gida. Yanzu dan Allah da a gidan mijina ne, da ba sai dai yayi masifar ya gama ba, babu wanda ya ji ya gani? Ai Abba ya tozarta ni jiya. Sai so ake a ga fuska a tuhume ni, ko ayi mini rashin mutunci a gidan nan, kin san gidanmu Allah ya wadata mu da munafukai, ni kuwa na haɗe rai"
Sumayya ta ce "Allah ya ƙara, ke uwar gwaninta, har da kai amarya, banda uban anko da ki ka yi mata. Ina mai tabattar miki ke da ganinta ta tako gidanku, sai wani ikon Allah"
Nabila ta É—an yi shiru ta ce "Ku ma fa haka ne, kin san wani abu, ba hassada nake yi wa amira ta yi aure ba, amma kalli na fita kyau fa, na fita komai amma amira ta shige daga ciki, ohh ni Nabila, duk kyan nan da dirin nan yadda ki ka san na je na haye kan high table É—in nan ayi da ni ranar dinner. Ba ma wannan ba duk wannan gayun da kwalliyar ban yi saurayi a bikin nan ba"
Sumayya ta ce "Ki je ki ɗorawa ranki jarabar son aure, ki ƙi focusing a kan career ki, ni ko a jikina na san lokaci ne, kuma tun da ba yawon iskanci nake ba, duk wadda ta yi mini gorin aure sai na ci ubanta, shekarun namu nawa ne duka da za a addaba mana"
Nabila ta yi ajiyar zuciya ta ce "Ba haka ba ne Sumayya, we have a different backgrounds, ke kin san me nake nufi, wallahi ƴanci nake so Sumayya, ko ta halin ƙaƙa"
Sumayya ta ce "Kar neman Æ´anci ya kai ki ga halaka, duk ina samarin naki ne to?ba wanda zaki tsayar?"
Nabila ta yi tsaki ta ce "Bar matsiyata, daga ƴan wahala sai ƴan iska. Sai dai duk wanda ya zo hannuna sai na ci rabona ayi baran-baran. Na daina wahalar son mutum, daga ƙarshe yayi breaking heart ɗina, ya ci bulus. And also haryanzu ban samu spec ɗi na ba kin dai gane"
Sumayya ta ce "Au ke yanzu har wane zaɓe-zaɓe ki ke yi?"
Nabila ta ce "To ana raba mai rai da motsi ne? Iya wuya akwai abun da zuciya take so, kuma ni na fi son namiji mai kumari sosai. Irin wanda zaki ganshi ingarman namiji mai cikar zati. Beside fuskar namiji ba gemu, ai sunansa sumayya, ni kuma daga dattijai, sai marasa gemu, sai kuma Æ´an wahala, ni matashi nake so, ba kuma yaro ba"
Sumayya ta ce "Au sunana ne ma abun kwatancen iya shegenki ko, to ki je dan kanki. Mai napep zan sauka a nan, za ta baka kuÉ—in"
Nabila ta ce "Ke uban waye ya ce miki ina da kuÉ—i?" Tuni Sumayya ta sauka, ta bar Nabila.
Nabila ta yi ƙwafa ta ce "Zamu haɗu ne, zaki ga wulaƙanci".
***
A hankali yake buɗe jajayen idanunsa, a lokaci guda kuma yana lumshe su, tamkar mai shirin yin bacci. Sai mirgina kansa yake yi, yana sake lumshe manyan idanunsa da suka koma jajaye matuƙa.
Tamkar an jefo shi, haka ya faÉ—o É—akin, yana rarraba ido.