← Book details Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 32

Sashe 15

Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wayar sumayya ce ta shigo ƙaramar wayarta, dan haka ta ajiye ta hannunta ta ɗaga da sauri ta ce "Sunayya yaya ake ciki?"

"Kamar dai yadda na yi tsammani" ta bata amsa.

"Me ki ka yi tsammanin? Yi mini gwari-gwari"

"Ba irin labarin da suke buƙata ba kenan, hakan ka iya kawo musu naƙasu ga cigaba da kuma tasirin gidan radiyon su, kuma wai ba ni da cikakkiyar shaidar abun da na faɗa"

"Haba Sumayya, ni ina da shaida fa, ga kuma yaya Nasir ma, kuma ya zaki tsaya a wurin wannan shashashar matar da ba ta son cigabanki? Ki yi wa Manager magana mana direct, nima ina da lambarsa, sai na yi masa magana".

Sumayya ta ce "Nabila kenan, duk kanwar ja ce, shi ne ya jaddada mini hakan da kansa".

"Allah wadaran naka ya lalace, Yanzu sumayya shikenan zuba ido zamu yi? Babu wani abun yi?"

Sumayya ta ce"Idan na matsa zan iya rasa aikina, abun da ya nuna mini kenan, wai ba za su iya jayayya da hukuma ba, kuma na kawar da kaina a kan abun da ba zan iya jurewa ba, da ina da wata hanyar samun kuÉ—in, da ajiye aikin nan zan yi Arfa"

"Shikenan, zamu yi magana anjima, see you later" ta ajiye wayar ta zauna ta yi shiru.

Wani irin tsaki ta ja, tana mamakin yadda galibin private organizations suke buÉ—e wurare, for their personal interest kawai, kodayeke na gwamnatin ma menene, duk É—aya.

Ganin ɓacin ran ba zai amfanata komai ba, tana da abubuwan da yakamata ta yi, ya sanya ta fita ta tafi office ɗin Barrister Habib.

Yana ta aiki a system, ya É—ago ya amasa mata sallamarta, ya cigaba da aikinsa.

"Barka da aiki barrister".

"Yauwwa" ya amsa a taƙaice.

"Barrister wai haryanzu fushin ka ke yi, na shiryu fa na daina duk wani abu da nake yi, sonake na zama cikakkiyar lawyer abar koyi ga wasu, kamar gwanata Barrister Naja'atu Bunkure" da É—an sauri ya É—ago ido ya kalleta ya girgiza kai ya ce "No wonder, shiyasa ba zaki cigaba ba"

"Subhanallah, meyasa?" Tayi maganar tana ware ido.

Maimakon yayi magana, sai yayi mata shiru.

Wani irin kallo tayi masa, a zuciyarta ta ce 'Sai fa ka yi magana barrister'

A zahiri kuwa ta ce "Ni dai haka kurum nake sonta, ayyukan ta na jin ƙai suna burgeni, ina son zama kamar ita. Amma tun da haka ne ma, na canza kamar kai nake son zama, daga yau kai ne mudubina" tayi maganar tana murmushi.

"Ke da ba zaki iya zalunci ba, mu ne azzalumai ai"

Nabila ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, waye ya faÉ—i haka? Wallahi ba haka bane ba, ni ban ce ba"

"Idan har kina son zama shahararriya, dole ki yi iya yinki, a kan duk abun da ya zo hannunki, ko da kuwa babu tabbacin zaki yi nasara, idan ba zaki iya ba kuma, you can leave"

"No, zan iya, ai na shiryu yanzu"

Ya buɗe drower gabansa, ya ɗaukko wani file ya ajiye mata sannan ya ce "Wannan client ɗi na ce, a nan ƙofar na'isa gidanta yake, zan turo miki cikakken adress ɗin ta, ki je ku yi magana, sannan ki yi tunani a kan case ɗin nata" Cikin girmamawa ta ce "Na gode sosai, zan yi in sha Allah "

Tana fita daga office ɗin nasa, ta gyatsine baki, ta ce "Kamar ni za a aika, gidan wata ƙatuwa, ba ma ta zo office ta same mu ba, hamshaƙiya saboda ga ƴar Nabila ƴar wahala. Amma bakomai da na zama abun da nake so, na fi ƙarfin kowane irin wulaƙanci" ta koma nata ofishin tana cigaba da ƙunƙuni.

Da ta koma gida ma, ba ta bi ta kan aiken da barrister yayi mata ba, ta kwanta ta sha baccinta, bayan ta tashi ta shirya ta yi wanka, ta tafi gidansu sumayya.

Sun jima suna tattaunawa da sumayya, a kan harkar aiki, har sumayya ta din ga ja mata kunne, a kan kasadar da take yi, tare da nuna mata illar hakan a matsayin ta na Æ´a mace, ta kunnen hagu maganganun sumayya suka din ga shiga kunnenta suna fita, dan ba ta ji sun shigeta ba.

Ta bawa Sumayya labarin aiken da barrister Habib ya yi mata.

Sumayya ta ce "Kuma zaki É—in?"

"To ya zan yi?"

Sumayya ta yi dariya ta ce "Ai na zata taurin kan yana nan?"

Nabila ta yi murmushi ta ce "Na ajiye taurin kai, zan kama aikina yadda yakamata, ai sai burina ya cika sai na binciko wacece Bunkure kuma in sha Allah, sai sunana ya shafe nata a tarihin duniyar ma'abota shari'a".

"Allah wadaran naka ya lalace, Nabila, wai ke wani irin taurin kai ne da ke ne? Ke abu ba ya wucewa a wurinki ne? Ki bar ta kawai, idan Allah ya so, tana raye zata ga nasarar da zaki yi a rayuwa"

"Ina kwance nasarar za ta zo ta same ni kenan? Ke ƙyaleni, ina ga sai Allah ya kaimu friday da yamma, zan je waccan unguwar gidan matar, na ga bai turo mini contact ɗin matar ba tukuna, zaki rakani?"

Sumayya ta ce "A'a gaskiya, wannan unguwar, ana ta fama, kamar ba kya jin radiyo, yadda suke fama da faɗace-faɗacen daba. Ki gayawa barrister ya ce  kawai matar ta je office ɗin ku, ko kuma ki bari komai ya lafa, dan kullum cikin faɗan daba suke"

Nabila ta ce "So ki ke in kasa samun information ɗin da nake so daga bakinsa kenan? Ai lallaɓa shi zan tayi, sai na san wacece matar nan. Kodayake ma na saka Yaya Nasir ya rakani" sai kuma ta yi shiru, ta sake maimaita zancen Sumayya a zuciyarta.

*Wannan unguwar ana ta fama da faÉ—an daba*

Ta sake kallon sumayya ta ce "A unguwar ne aka ce yaran Aminu Viper sun yi sare-sare?"

Sumayya ta yi shiru tana kallon idon Nabila.

Nabila ta yi murmushi ta ce "Kar fa ki kawo komai a ranki, ba wani abun zan aikata ba, bari na tafi kan Abba ya dawo ya nemi ina nake" ta ɗau jakarta ta fita, tana jin kamar matsalarta ta zo ƙarshe.

*Masu nema daga farko, ku yi joining link channel É—ina na saman page, idan kun shiga zaku samu daga farko*

Arewabooks ayshercool7724
Watpad
ayshercool7724

Ayshercool
08081012143
[7/21, 2:16 PM] null: *ƘARFE A WUTA*

AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION
BRIGHT PENS SECOND BATCH

https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g

7

Katafaren falo ne, wanda girmansa ya ishi wani talakan gina gidan da zai rayu a ciki, talabijin É—in da ke falon kawai ta fi rabon bango.
Kujera set biyu ce a falon, kuma tsakanin kowane set da wani akwai tazara.

Tinkis-tinkis haka ya fito cikin wata irin dakakkiyar shadda maroon, sai ƙyalli take yi, ba sai an faɗa ba ka san akwai tazara mai nisan gaske tsakanin sa da talauci.

Ba wata ƙiba ce da shi ba, amma cikinsa yayi kurtsitsi a riga, har wani nishi yake yi.

Ya nemi wuri ya zauna a ɗaya daga kujerun falon, ya kalli matasan da suke zaune a ƙasa a kan carfet. Dukkansu babu mai suturar kirki a cikinsu, kansu duk askin banza, yanayin shigarsu da fuskarsu kawai za ta tabattar riƙaƙƙun masu laifi ne.

"Allah ya taimaki maigida" cewar É—aya daga cikin su.

"Ya aka yi madaki?"

"Akwai ƙura ne, ƙurar kuma na neman zama gagarumar guguwa"

"Ina jin ka"

"Aminu Viper, haryanzu jami'an tsaro ba su kama shi ba, ya sa an kaiwa yarana mummunan hari, an yi musu miyagun raunuka, jami'an tsaro sun kama yarana sun saki nasa, wanda aka kai asibiti ma, an kwashe su daga asibiti babu wanda ya san in da aka kai su"

Mutumin yayi tsaki ya ce "Ina mamakin yadda mutum É—aya ya gagari kamun hukuma, ni anya ba raina mini hankali ma suke yi ba a kansa? Yanzu menene abun yi?"

"Ka saka a sakar mini yarana, dan sai da su ayyukanka suke yiwuwa, kuma dole mu yi shiri sosai, idan da hali mu mu nemi in da yake mu kashe shi kowa ya huta"

Mutumin yayi shiru yana kallonsa sannan ya ce "Aikuwa da na yi maka tukucin da baka taɓa tunani ba, zan saka a saki yaran nan anjima kaɗan, sai dai duk yadda zaka yi ka yi, a samo yaron nan, dama mugu shi ya san makwantar mugu ai"

Madaki ya sauke numfashi ya ce "Zan shirya gagarumar É—aukar fansa kan mai uwa da wabi a unguwar su, jinin yarana da suka zubar ba zai tafi a banza ba, dan shammatar su ka yi, suka mamaye su ba na nan"

"Wannan ku ta shafa, ni babban burina shi ne Aminu, muddin yaron nan yana numfashi, kamar sarƙa ce a wuyana, dole a kawar da shi".

Madaki ya ce "Ba kai kaÉ—ai ba, ko kuma in ce da ni da kai kusan abu É—aya ne a wurinsa, nima ka san akwai tawa ni da shi, tsohuwar gaba ce ta tsawon shekaru, wanda a kanta unguwanninmu suka kasa zaman lafiya har yau, ga kuma wannan al'amari da ya faru. Muddin ban kashe Aminu ba, ni zai kasheni"

Ya jinjina kai ya ce "Ai Viper na fuskanci ƙarfe ne a wuta, ya fi ƙarfin ɗauka da hannu, sai dai da ɗan uwansa ƙarfe, kai kaɗai zaka iya maganinsa"

"Ka bani lokaci kawai, zan kuma ƙoƙartawa, matsalar ko yaransa ba kowa ne ya san in da yake ba, amma na san dole Walid ya san in da yake, amma shi ma Walid ba lafiya ba ne taɓa shi, ka dai bani lokaci"

"Babu isasshen lokaci, ka yi huɓɓasa kawai"

Madaki ya jinjina kai.

Mutumin ya É—ebo kuÉ—i ya bashi, ya sallame su, suka juya suka fita da shi da yaransa.

Nasir ne tsaye a office ɗin sa, ya kalli matashin da yake zaune, da aƙalla zai yi sa'ansa ya ce "Mu'azzam lamarin ƙasarmu sai Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ka san da ƙyar na gano station ɗin da yaran nan suke, ba ma ta yankin da abun ya faru ba ce?"

Mu'azzam ya yi murmushi ya ce "Haka ka ce mini"
Chapter 15 · 0% Book details