Sashe 25
Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yanayin yadda zuciyarta ke tsananta bugawa ne, ya sanya ta din ga karanto duk addu'ar da ta zo bakinta.
Sai dai ba ta ji za ta iya janye aikata abun da tayi niyya ba.
Nesa kaÉ—an da in ya kwatanta mata ta je ta tsaya, sai dai tun kafin duhun magariba ya gama rufawa, mutumin da aka kwatanta mata ya zo ya kafa teburinsa na sayar da katin waya, ya nemi wuri ya zauna.
Ta ɗan jima a tsaye, tana kallon sa, sannu a hankali ta fara tunkarar in da yake zaunen, tana addu'a a zuciyarta har ta ƙarasa in da yake.
Kafin ta yi magana, wani matashi ya rigata ƙarasawa, suka gaisa ya miƙa kuɗi, aka bashi wata baƙar leda.
Ta tattaro jarumtarta ta yi sallama ta ce "Sannu malam" ya É—aga kai ya kalleta, sai dai kamar ya razana da ganinta.
Ta sake cewa "Sannu malam"
"Yauwwa" ya amsa da kakkausar muryar sa, yana cigaba da ƙare mata kallo.
"Dan Allah kaya nake so" ya ƙare mata kallo daga sama har ƙasa, ya ce "Wane irin kaya?"
"Irin wanda ka ke sayarwa, amma ni direct nake son na din ga karɓa"
"Jami'ar tsaro ce ke?" Yayi maganar yana cigaba da kallonta
Nabila ta ce "Jami'an tsaron ai sun san da zamanka a nan, ina so ka haÉ—a ni da Aminu viper ne"
Waro ido yayi ya kalleta ya ce "Ke! Yayi maganar yana zazzaro mata ido"
Tayi ƙasa da murya ta ce "Kar ka ɗaga murya, ka taimaka mini, ɗan uwana ne, tun da ya fito daga prison ban sake ganinsa ba"
"Ƙarya ki ke yi wallahi! Ban da ke mace ce, da namiji ce ke, wallahi sai na ciro hanjinki waje na zubar a titi, bar wurin nan, kafin na karya ki"
Nabila ta marairaice ta ce "Ba ka da tabbacin ƙary.....
"Ki bar nan, kafin na tsarga ki biyu da makami" ta ja da baya a hankali, tana kallon sa.
"Ki bar nan na ce" ta juya da ɗan sauri, cikin tsoron yadda ya hayayyaƙo mata.
Wayarsa ya É—aukko ya kira Walid yana huci, cikin sa'a ya É—aga.
Walid ya ce "Maza ya ne?"
"Wata yarinya ta zo neman boss, wai Æ´ar uwassa ce, anya ba a fara bibiyar sa ba? Idan ba haka ba, yaya aka yi ta san na sanshi".
Cikin mamaki walid ya ce "Kar dai yarinyar da gagare ya ce mini ta je dabar madaki neman sa?"
"Ban sani ba, amma zan so ka ganta, ka ga wani abun mamaki, mai É—aure kai, dan na kusa guduwa wallahi"
Walid ya ce "Kamar yaya?"
"Ka ga, ina hangota haryanzu, zan bita na yi mata magana, zan ce ta dawo gobe da safe, zaka ga abun da na gani"
Walid ya ce "Kai liti, ka tabatta ba matsala?"
"Babu, kawai sonake ka ganta"
"Shikenan, idan ka tashi yau, ka shiga area wurin dila, ya baka balance, idan na zo zan karɓa"
"Sai da kai, an gama"
Nabila na shirin hawa É—an sahu, ta ji an yi fito a bayanta, ta waiwaya ta ga liti a tsaye.
"Zo mana" yayi maganar yana kallonta.
Kawai zuciyarta ta raya mata, ko wuƙa zai soka mata.
"Ki zo mana" yayi maganar cikin tsawa.
Cikin rauni ta ce "Dan Allah ba wuƙa zaka soka mini ba?"
Ya ce "Ke da kashe ki zan yi, kin isa na bari ki bar wurin nan, shawara na canza, ban san alaƙar ki da shi ba, dan haka zan haɗa ku"
Da sauri ta ɗan ƙarasa gabansa ta ce "Dan Allah, amma na ji daɗi na gode sosai da sosai".
"Mu haɗu a nan, gobe ƙarfe biyar na yamma, zan haɗaki da wanda ya san in da yake, amma wallahi ki ka yi wani abu na rashin gaskiya, kin san sauran"
Nabila ta ce "Babu wani abu na rashin gaskiya da zan yi, na gode yayana Allah ya saka da alkhairi"
Ya ce "Ke ki nemawa kanki tsari, da na zama yayanki, ware ki bar nan"
Hamadala ta yi, tare da jin kamar wata gagarumar nasara tana tunkarota.
Ƙwas-ƙwas takalminta yake bayar da sauti a kan tiles ɗin wurin, sai sauri-sauri take yi ta ƙarasa ofishin manager.
Da sallama ta shiga, ya ɗago ya amsa mata, ta ɗan risuna ta ce "Afuwan sir, na tsaya ƙarasa editing ɗin news ne, shiyasa ban zo kiranka da wuri ba".
"Bakomai sumayya, sannu da ƙoƙari, ina yabawa ƙoƙarin ki da himmarki".
Tayi murmushi ta ce "Na gode sir"
"Ina sisternki, young barrister ne? Nabila ko, kwana biyu ba ta kawo mana ziyara ba"
Sumayya ta yi murmushi ta ce "Ayyuka ne suka yi mata yawa, amma ko É—azu muna tare"
Ya ce "To Allah ya taimaka, yauwwa dama batun program É—in nan ne, honorable ya ce ba zai samu zuwa ba, sai dai aje can gidansa ayi recording program É—in, dan haka driver zai kai ki, a can badawa gidansa yake, za a kai ki ranar Friday, sunday zai yi tafiya ki yi recording program É—in"
Cikin mamaki da sanyin jiki, ta ce "Gidansa kuma sir? Amma ai yau murtala za su dawo, tun da su maza ne sai su je....
Ya É—aga mata hannu ya ce "Look sumayya, ya zama dole ki je, murtala ba zai dawo yau ba, honorable ba wani abun zai yi miki ba, gidan da yake zaune da iyalansa ne, recording É—in program kawai zaku yi. Idan kuma ba zaki yi ba, you know the consequences"
Wata irin nannauyar ajiyar zuciya ta yi, ta ce "Allah ya kaimu" ta juya a hankali ta fice.
₦500 ne, via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank
Special wanda ba sa son group 1k.
Wanda za su jira document, idan an kammala 1k ne.
90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa
wannan layin
Sai a tura mini shaidar biya ta
08081012143 ko 07063065680
Ayshercool
08081012143
[7/25, 1:18 PM] null: *ƘARFE A WUTA*
AREWABOOKS: ayshercool7724
Watpad: ayshercool7724
What's app: 08081012143
https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g
11
Bayanta manager ya bi da kallo, ta bashi tausayi sosai da sosai, sai dai yana addu'a Allah ya sa kar honorable ya cutar da ita.
Kamar ɓarawo, haka walid ya diro a tsakar gidan, maimakon ya biyo ta ƙofa, ɗan mama yana zaune yana shan sigari a ɗan tsakar gidan.
Bai kula shi ba, ya wuce É—akin da viper yake, sai dai ya duba baya ciki.
Walid ya dawo, ya kalli É—an mama ya ce "Ina Viper?"
ÆŠan mama yayi dariya ya ce "Har ka gama fushin, ka dawo?"
Walid ya ce "Kai ka san ba zan iya ba, ƙular da ni yayi ne, ina yi masa uzuri ne kawai na san kansa ya taɓu, yana ina?"
"Baya nan" É—an mama ya bashi amsa kai tsaye.
"Kamar yaya? Ina yaje?"
Ɗan mama ya zuƙi sigarinsa sannan ya ce "Ni na isa na hana shi fita ne? Ko kuma na ce sai ya gaya mini in da za shi? Da dai kai ne zai iya ɗaga maka ƙafa"
A fusace walid ya ce "Dan me zaka bari ya fita?"
"Au so ka ke na hana shi, ya karya ni, ko ya illata ni, kaɗaici ne ya dame shi, gidan babu kayan caji, sai na hayaƙi, shi ne ya fice. Yauwwa dama ina son gaya maka, ka daina kwashe kayan cajin nan gaba ɗaya, idan wani yayi rawa an bashi kuɗi, kai idan ka yi, na jaki zaka ci a hannunsa wallahi"
Cikin takaici Walid ya ce "Wai so ka ke sai ya kashe kansa ne? Kana kallon allurar nan ba ta ɗaukar sa, farar ƙwaya ma fa ba ta yi masa komai, sai rikita masa ƙwaƙwalwa, idan ya haukace fa?" Walid gani yayi ɗan mama yayi tsuru-tsuru, yana rarraba ido, dan haka ya waiwaya bayansa, Al'amin ya gani a tsaye a bayansa.
Bai kula su ba, ya zo ya raɓa walid ya wuce.
"Master"ya kira shi.
Al'amin ya waiwayo, fuskarsa babu annuri, idanunsa sun yi ja, jijiyoyin kansa suka miƙe ya ce "Me na ce maka a kan kirana da haka?"
Walid ya ƙarasa kusa da shi, dai-dai kunnensa, ya yi masa raɗa.
Viper ya kalli Walid ya ce "Kasheni ka ke so ka yi sannan hankalinka ya kwanta ko Walid?"
Walid ya É—age kafaÉ—a ya ce "Duk yadda ka gani"
Viper ya hankaɗe shi gefe, ya wuce ɗakinsa, ya rufe ƙofa.
Walid ya bishi ya leƙa ta taga ya ce "Me zaka yi ka rufe ƙofa?"
Leda ya ciro daga aljihunsa, ya haÉ—a allura a sirinji, zai yi wa kansa.
Walid ya ce "Al'amin, ba zaka daina yi wa kanka allurar nan ba ko? Ba za ta yi maka ba, ka haƙura mana"
Al'amin ya tashi, ya je ya ja tagar ya rufe, ya bar walid a waje yana surutu.
Sumayya kuwa tun da ta koma gida, mama ta lura da yanayinta, sai dai ta yi zaton ko gajiyar aiki ce, amma har dare ba ta walwala.
Dan haka ta magantu, ta ce "Ƴar mama, wai ko babu lafiya ne?"
Sumayya ta ce "A'a lafiyata ƙalau?".
"To faÉ—a ku ka yi da mutuniyar ne?"
"A'a bamu yi faÉ—a ba mama"
Ba ta gaza ba ta sake cewa "To ko wurin aikin ne suka yi miki wani abun?"
Sumayya ta ƙaƙalo murmushi ta ce "Hajiya mama, bamu yi faɗa da ƴar ki ba, lafiyata kuma ƙalau, kawai kin san yanayin aikin namu ne, kayi ta ganin abubuwa na ban tausayi daban-daban".
Mama ta ce "Ai baku ba sumayya, mu ma masu saurare, kusan kullum cikin zullumin kunna radiyon muke, sai dai ku Æ´an jarida ku ne idonmu, ta bakinku kawai muke jin wasu labaran da jin halin da duniya ke ciki. Allah dai ya saka muku da alkhairi ya tsare mana ku baki É—aya, daga ke har Nabilan aikin tainakon al'umma ku ke yi, Ubangiji Allah ya tsare ku ya kawo mazajen aure na gari"
Sumayya kamar ta gaya wa mama, abun da aka umarceta a wurin aiki, amma ta san hankalinta tashi zai yi, zata iya hanata aikin ma, kuma Allah ne gatansu aikin nan ne gatansu, dan haka ta ja bakinta tayi shiru.
***