Sashe 16
Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Gaba É—aya yaran under age ne, kuma duk cikinsu babu yaran Aminu, dan tuni an sake su, sai wani wai madaki, na ce dai a ajiye mini su, da yiwuwar mu kama madakin, zai iya sanin in da Aminun yake,tun da abokin faÉ—ansa ne, amma da na yi magana da DPO É—in division É—in yankin, ya ce shi ma madakin ba ya kamuwa, kuma ya addabi yankin yana da yara sosai da sosai. Abun takaicin ma ba unguwar su É—aya da Aminun ba, amma suke cigaba da tayarwa da mutane tarzoma"
Mu'azzam ya ce "Harkar nan tamu sai fa Innalillahi wa Innalillahi raji'un, muna tufka manyanmu na warwarewa"
Nasir ya ce "Bari kawai, zan yi iya ƙoƙarin da zan yi, ni zan kama Madakin, Arfa har asibitin da aka kai waɗanda aka yi wa rauni ta je, muka yi waya kafin na je wai an kwashe su, an bar asibitin da su, na fara zargin anya ba jami'an mu ne aka samu bara gurbin da suke mara masa baya ba"
Mu'azzam ya ce "Ba abun mamaki bane ba, amma meya kawo Arfa cikin wannan lamari, ta bar aikin lawyern ne?"
Yayi murmushi ya ce "Rigima mana, yarinyar nan ta zarce tunaninka, ba ta wasa da duk abun da ya shafe ni ko cigaba na"
"Hmm Nasir kenan, wai yaushe zaka gayyacemu sabgar nan ne? Shekarun ka fa suna ja"
Nasir ya rausayar da kai ya ce "Mama ce ta hana, ta nuna ba ta so, ban taɓa gaya mata ba, saboda tun kafin na furta maman ta gargaɗe ni a kan haka, kuma haryanzu ni ban ji ina son kowace yarinya ba, ita ɗin dai nake so. Ban san adadin samarinta da na kora ba saboda kishi. Yadda take son abun da nake so da son cigabana, na san da zan furta ina sonta, ba zata ƙi ba, amma na rasa yadda zan yi da mama".
"A'a Nasir, dan Allah kar ka zalunci yarinya, haka zaku zauna shekaru na tafiya, kai baka aureta ba, kuma ba ka bari wani ya aura ba? Wannan ai mugunta ce, ka yi magana da Abba mana".
Nasir ya girgiza kai ya ce "Manta kawai, abun ya wuce yadda ka ke tunani".
***
Arfa na kitchen tana taya baba magajiya aiki, suna hira tana tambayar baba magajiya kwatancen cikin unguwar ƙofar na'isa, dan zuwa aiken barrister Habib, dan ita ba zuwa ta taɓa yi ba.
Baba magajiya na girki, ita kuma tana wanke-wanke a sink.
Siyama da take Æ´a ta uku ga mama ce ta shigo kitchen É—in, ta jefawa Nabila kwanukan hannunta maimakon ta ajiye.
Nabila ta yi shiru, ta cigaba aikinta suna hira, duk da abun ya ɓata mata rai.
Amfani ta kuma yi da kofi, ta wurgowa Nabila cikin sink, cikin zafin nama da masifa, Nabila ta É—auki kofin ta jefa mata a fuska ta ce "Ai ba baiwar ubanki ba ce ni, da zaki din ga jifana da kwanuka"
"Nabila ni ki ka daka?"
"An dake ki É—in?"
Baba magajiya ce ke ƙoƙarin basu haƙuri, amma siyama ta shaƙe Nabila, Nabila ta rarumo wani kwano ta buga mata, dambe ya kacame.
Baba uwani ta yi ƙoƙarin raba su, amma abu ya gagara.
Ta fito falo da gudu, tana neman taimako.
Dambe tun daga kitchen har falo, duk abun da Nabila ta rarumo sai ta kwaÉ—a mata, kamar wasu kuraye.
"Mahaukaciyar ina ce ke? Ke kullum haka zaki ƙare ki zagi wannan ki ci mutuncin ƴaƴan gida kina ƴar karere"
Cikin baƙin ciki Nabila take kallon mama, tana iya ƙoƙarinta wurin danne abubuwan da mama take yi mata, duk faɗanta da tashin hankalin ita da yaran gidan suke yi, amma sai mama ta shiga ta zaƙe ta shigarwa yaranta.
Anty ta ce "gaskiya maman Sauda wannan ba girmanki bane ba, maimakon ki yi musu nasiha, sai ki din ga aibata Arfa, ai ba a haka"
Siyama ta din ga zagin Nabila, zagi na cin mutunci, tsawar da Abba ya yi musu ne, ya sanya duk suka É—ago cikin tsuma.
Ya nuna nabila ya ce "Arfa, ban isa na saka doka ki bi ba ko? Siyama ba gaba take da ke ba? Nake jiyo muryarki tun daga waje kina zaginta?"
Arfa ta buÉ—e baki zata yi magana, amma ya daka mata tsawa ya ce ta yi masa shiru.
Siyama kuma ta fashe da kuka tana gaya masa har dukanta arfa tayi.
Aikuwa ta in da ya shiga ba ta nan yake fita ba, ya hana kowa magana ya yi wa arfa kaca-kaca saboda sanin ba ta ji, ga rashin haƙuri da taurin kai.
Da sauri ta tafi ɗakinsu tana wani irin kuka, ta je ta faɗa kan gadonta, jikinta har rawa yake yi saboda baƙin ciki takaici ta din ga kuka.
Cikin kuka ta ce "Ya Allah ka bani miji kowane iri ne, in dai zai zama alkhairi a gare ni, na tafi na bar gidan nan, na gaji Allah ka amsa mini dan girmanka, kowane iri ne zan iya zama da shi".
Can falo kuma, jikin Abba ne yayi sanyi, ganin arfa na kuka ya san akwai wani abu a ƙasa, dan idan tayi laifi, wataran ko kasheta zai yi ba zata yi kuka ba, duk da tana da saurin kukan.
Ya kalli Anty ya ce "Zainab je ki duba yarinyar nan, kar ciwonta ya tashi"
Anty ta jinjina kai, ta bi bayan arfa.
Mama kuwa a sashinta take yi wa Siyama mitar meyasa ba ta yi wa Nabila dukan da za ta kasa tashi ba.
"Mama kin san yarinyar nan har aljanu take yi, haka kurum su tashi ni ta kashe ni, komai ta rarumo buga mini take yi, ba ki ji kafaÉ—una ba"
Mama ta yi ƙwafa ta ce "Na rasa yadda zan yi maganin yarinyar nan, wallahi bana sonta ba na ƙaunarta, gaba ɗaya ba kwa gaban mahaifinku sai ita, in sha Allah sai ta zame masa masifar da ba zai iya shawo kanta ba, sai ta kwaso abun kunyar da za ta kunya ta shi a idon duniya".
Nabila kuwa ƙin saurar anty ta yi, ta sha uban kuka, Anty ta sanarwa Major kukan da take yi, ya basar kamar bai damu ba, amma ƙasan zuciyarsa sam babu daɗi.
Tsakar dare suke waya da sumayya, take gaya mata abun da ya faru.
Sumayya ta ce "Arfa, ke rashin haƙuri ne yake janyo miki wasu abubuwan, da kin yi haƙuri ba ki tanka mata ba, dama neman magana ta zo yi".
"Sumayya kin san ba zan iya ba, ni ina wulaƙanta mutane ne?"
Sumayya ta ce "A'a idan na ce kina da wulaƙanci Nabila na yi miki sharri, sai dai masifa da rashin haƙuri, ga jarababben taurin kai ba a gaya miki ki ji ko kaɗan"
Nabila ta ce "Sai dai ayi haƙuri da ni a yadda nake, ni ba zan yadda da wulaƙanci ba"
"Aikuwa zaki yi ta shan wahala dan ubanki"
Nabila ba ta damu da zagin da sumayya ta yi mata ba, domin idan da sabo ta saba, dan wasu lokutan sumayya playing role take yi kamar na uwa a rayuwarta, ta kan ji maganarta idan ta ga dama.
"Sumayya dan Allah ki yi mini addu'a, Allah ya bani miji kowane iri ne, in dai zai zame mini alkhairi a shekarar nan na bar gidan nan na huta"
Sumayya ta ce "Ba ki da hankali, kowane iri fa ki ka ce"
"Eh, wallahi idan ba haka ba, zan gudu na bar garin nan, na bar musu gidan, sumayya baki san me suke yi mini ba na gaji" ta ƙarasa maganar cikin shagwaɓa tana kuka.
Sumayya ta san komai, dan haka cikin rarrashi, ta kwantar da murya, ta din ga yi wa Nabila nasiha, da rarrashin ta, har ta sassauta kukan da take yi.
Da haka suka yi sallama, ta kwanta bacci.
Sai dai ta kasa baccin, saboda yadda zuciyarta take zafi, ta rasa me ta tsarewa maman su Sauda a rayuwa, da ita da yaranta suka tsaneta haka, Nasir ne kawai suke ɗasawa da shi, da ƙyar bacci ya kwashe ta.
Da safe ta shirya cikin wata abaya baƙa, tayi kyau ko karyawa ba ta tsaya yi ba, ta fito falo fuskarta babu walwala.
Kallo É—aya zaka yi mata, ka san ba ta samu isasshen bacci ba.
Da kamar ta yi fuska tayi tafiyarta, amma ta haura benan Abba ta je ta gaishe shi, sai dai fuskarta babu annuri, babu raha da ta saba yi idan ta je gaishe shi.
Ya ƙura mata ido ya ce "Kin karya kuwa?" Ta ce "Idan na tsaya karyawa zan makara, zan karya a wurin aiki"
"Dan zaki makara sai ki fita ba ki karya ba, yaushe ki ka fara tsoron makara? Menene ma ya hana ki tashi da wuri?"
Tayi shiru tana wasa da yatsun hannunta, idonta yana cika da hawaye.
Ya saka hannu a aljihunsa, ya ciro kuɗi masu yawa, ya miƙa mata ya ce "Ga wannan na san wata yayi nisa, babu lallai ki na da kuɗi a hannunki, ki sai wani abun idan kin je ki karya, saura ki sai abun da zai ɓata miki ciki, ko ya cutar da lafiyar ki"
Kamar ta ce ya bar su, amma ta saka hannu biyu ta karɓa, ta ce ta gode, yanayin yadda take tafiya kawai, zai tabattar mata da tana cikin damuwa ko rashin lafiya.
Gaba É—aya jikin Abba ya yi sanyi, a tsakiyar zuciyarsa yake jin zafi, idan ya ga Nabila a cikin damuwa, shiyasa wasu lokutan baya iya jure yi mata hukunci yake kawar da kai a kanta.
Duk iya ƙoƙarin da Nasir yake yi, a kan yaƙi da harkar daba, abu ya ci tura, dan yaran da aka kama ya koma ya tarar da wai an yi umarni daga sama a sake su, abun ya ɓata masa rai sosai da sosai.
*****
A farfajiyar wata bishiya suke zazzaune, suna ta shaye-shayen kayan maye, duk sun cika wurin da ƙaurin hayaƙi.