← Book details Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 32

Sashe 1

Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

[7/15, 1:18 PM] null:       ⚔️*🔥ƘARFE A WUTA🔥*⚔️

MALLAKAR AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION

*BRIGHT PENS SECOND BATCH*

Writer of
Gaba da gabanta
Ƙanwar maza
Cutarwa
Ruɗin ƙuruciya

Follow the COOL HAUSA CHANNEL channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/0029Vaxs8kyyIhWtuvh3g

*BISIMILLAHIRAHMANIRAHIM*

*Labarin ƙarfe a wuta, ƙirƙirarran labari ne, idan yayi kamanceceniya da rayuwar wani ko wata, arashi ne.*

Ban lamunci a juya mini littafi, ta kowace irin siga ba, sai da izinina❗

Page 1

Tsit ƙaton falon yayi, ba ka jin sautin komai, sai ƙarar gudun AC.
Sai mutanen falon da suke tsaye sun yi cirko-cirko, kamar masu jiran wani sakamako.

Wata matashiyar budurwa ce, durƙushe a kan gwiwoyinta, fuskarta ɗauke da wani yanayi na tsantsar damuwa, da tashin hankali, fuskarta tayi sharkaf da hawaye.

"Yanzu sakamakona kenan a wurinki? Irin wannan sakamakon shi na cancanta daga gare ki ko?"

Cikin ƙulewa wata babbar mace ta ce "Dama wani sakamako ka ke saka ran samu daga tsintaccaiyar mage? Ai ba za ta taɓa mage ba, abun da na din ga ankarar da kai kenan, tun a shekarun baya, amma ka kasa ankarewa, yanzu ta nuna maka ita ƴar kunama ce"

Budurwar ta yakice gumin da yake tsatstsafo mata, ba tare da nadamar abubuwan da suke gudana ba a ƙasan ranta, a zahiri ta ce "Ba mummunan sakamako bane ba, abun da ka tarbiyantar da ni a kai ne, gaskiya ita nake tsaye a kai, bani da niyyar cutar da kowa a gidan nan, kowa aikinsa yake yi, yakamata ayi mini adalci, ba a goyi bayansa a nuna ni ce nake kan ƙarya ba, a bari nima na yi nawa aikin"

Cikin tsawa É—aya matar ta ce "Har wata gaskiya ce da ke.....

Dattijon ya É—aga mata hannu ya ce "Ya isa haka, tashi ki je, ba na ko son ganinki, ki je ki yi abun da ki ke ganin ya dace da ke".

Cikin rauni da tashin hankali ta ce "Abba, ba ka son ganina ka ce?"

"Eh mana, idan har ki na gudun ɓacin raina da fushina, dole ki ba wa ɗan uwanki duk wani cikakken haɗin kai, domin gudanar da aikinsa yadda yakamata"

Cikin matsanancin tashin hankali ta ce "Amma Abba ni kuma menene makomata...? Yakamata a ji ta bakina Abba"
Bai tsaya sauraron mai za ta ce ba, yayi gaba zai bar falon. Cikin matsanancin tashin hankali, ta riƙe ƙafarsa ta na fashewa da kuka.

"Haba Abbana, me yayi mini saura a duniya, idan har zan rayu ka na fushi da ni, ka yi haƙuri zan yi abun da ka ce in sha Allah" tuni hawaye ya cigaba da wanke mata fuska, tsantsar nadama da damuwa suka mamayeta, ta din ga kuka da sheshsheƙa kamar ta shiɗe, amma ya fizge ƙafarsa ya yi gaba.

Yana barin falon, tamkar mutanen falon za su cinyeta É—anya, haka suka yo kanta sa surutu, kowa da abun da yake faÉ—a.

Tashi ta yi tsaye, ta goge hawayenta, cikin ko in kula, ita ma ta bi wata hanyar ta bar musu falon, cikin sigar kwa ci kanku.

ÆŠakinta, ta shiga ta buÉ—e drower, ta fito da wasu takardu ta zube su a kan gado, ta kunna system É—in ta da take caji a gefen gadon, lokaci guda kuma ta É—auki wayarta tana dannawa.

Jin motsin mutum a bayanta, ya sanya ta waiwaya da sauri.

A tsaye ta ganshi bakin ƙofa, fuskarsa babu walwala balle annuri.

Mayar da hankali ta yi, za ta cigaba da danna wayarta, ya tako zuwa gabanta, ya tsaya ya ƙare mata kallo sannan ya ce "Kin shirya aikata abun da aka umarce ki ko kuwa?"

Cikin hanzari ta tari numfashin sa ta ce "Ban ce shirya ba, kuma ba zan shirya ba, daga nan har gaban abada, ka fita ka rabu da ni".

Cikin matuƙar mamaki yake bin ta da kallo, "Yanzu duk kukan da ki ka yi, ƙarya ki ke yi kenan?"

A hasale ta ce "Ina ruwanka, idan ma kukan ƙarya ne ko na gaske, ka yi aikinka in yi nawa, kar ka sake yinƙurin shigar mini aiki, idan ba haka ba komai yana iya faruwa, wallahi ba zan fasa abun da na yi niyya ba, idan kuma ka cigaba da takura mini, zan baka mamaki"

Hannu ya saka, ya ɗagota daga kan gadon ya ce "Menene zai faru, wani irin mamaki zaki bani? Me zai faru nake son ki gaya mini. Kina da hankali kuwa? Kin san doka amma kina taka ta yadda ki ke so? Da me ki ke taƙama ne haka?"

"Doka ko? Ni  iya takata na yi, kai kuma cin zarafinta ka ke ƙoƙarin yi, ka ƙyale ni babu ruwanka da ni, ka yi naka aikin na yi nawa duk wanda yayi galaba shikenan. Idan ka ga dama ka je ka sake gayawa Abba abun da duk yayi maka a kaina, wallahi babu gudu babu ja da baya, ban fara dan ina saka ran dainawa ba, ba tare da na yi nasara ba" hankaɗata yayi kan gadon, yana wani irin huci, zuciyarsa na yi masa zafi, yayi wata irin ƙwafa yana bin ta da kallo. Cikin hanzari ya fice ya bar mata ɗakin, saboda idan ya cigaba da tsayuwa, zai iya yi mata abun da ba shikenan ba. Ta yinƙura ta tashi zaune tana haki, tana kallon ƙofar da ya fita.

****
Tsaye take a gefen wani gini, tana ƙarewa harabar kotun ido. Yadda aka cika harabar da manya da ƙananan motoci ne, ya sake tabattar mata da manyan shari'oi za a gudanar a yau.

Ta din ga kallon agogon hannunta, tana kallon gate shigowa harabar kotun.

Motar gidan yari ce ta shigo, aka yi parking ɗin ta, sai dai tsayuwar motar babu daɗewa wata danƙareriyar motar, ta shigo harabar kotun.

A ƙalla an kai mintuna goma da parking ɗin motar, sannan aka buɗe bayan motar, wata mata ta fito, sanye cikin coat.

Mutanen da ke harabar wurin, suka nufeta, wasu suka karɓi jakarta, ana ta yi mata fadanci, cikin girmamawa.

"Ya Allah kai ne Allah, kai ne buwayi gagara misali, Ubangiji da babu wani kafinsa, kuma babu wani a bayansa. Allah na san mutanen nan sun fi ƙarfina ta ko ina, amma kaine abun dogaro na, na san ba za ka bani kunya ba. Allah sun fi ƙarfina ka fi mini ƙarfinsu. Allah ka yi mini kunfayakununka a kan shari'ar nan, hasken gaskiya ya shafe duhun ƙarya, duk da ina da masu goya mini baya, amma Allah goyon bayanka nake buƙata" ta jima a tsaye tana karanto addu'a, tare da yi wa Allah kirari.

A hankali ta furta "What a hectic trial, Ubangiji ka iya mini" cikin nutsuwa, ta fara taka takalminta mai tudu, ta nufi shiga cikin kotun, da takunta mai kama da na ƙasaita, shigarta ta lawyoyi tayi matuƙar yi mata kyau, tana tunkarar ƙofar shiga, zuciyarta na tsananta bugawa,tana fatan Allah ya shiga lamarin ta.

****

Ƙofar famfo kano state.

Ƙarfe goma saura mintuna goma na dare, tuƙi yake yi cikin sauri, saboda yadda fasinjar da ya ɗaukko take azalzalar sa. Duk saurin da yake yi, mita take yi masa, a kan ya ƙara gudu.

Yanayin kwalliyar da ta yi, cikin baƙin material, fuskarta ta sha make-up, zai  tabattar maka daga wurin biki take.

Ta kalli agogon hannunta, kamar ta fashe da kuka ta ce "Mai napep, ka yi wa girman Allah ka yi sauri"

Ya ce "Wai dan Allah hajiya yaya ki ke so na yi ne? Haba babata duk saurin da nake yi, ki yi haƙuri mana mu tafi a sannu".

A ƙule ta ce "Ban gane babarka ba, wani irin wulaƙanci ne wata babarka, na yi maka kama da tsohuwa ne?"

Yayi murmushi ya ce "A'a, ai ku mata duk in da ku ke iyaye ne... Katse shi ta yi ta hanyar cewa "kuma sai aka ce na haifi kamar ka? Ai sai a bari na haifa tukuna, a yanzu na haifi kamar ka, ai tawa ta ƙare a duniya. Ko yayarka ka ce mini ka cuce ni, balle babarka. Ni dai ka ƙara sauri, yau na san kashina ya bushe, sai an yagalgalani da masifa a gida yau. Aikin banza, ƙawayen amarya ƴan wahala, mun gama wannan wahalar a ɗauke ta a mota an kai ta gidanta, mu muna fama a titi. Mu ma Allah ya kawo lokaci, ace ga miji ga mota"

Ya waiwaya ya kalleta yana murmushi, a fusace ta ce "Lafiya malam?"

"A'a Allah ya baki haƙuri".

Kafin su ƙarasa in da zata sauka, ta ciro masa kuɗinsa, su na zuwa in da za ta sauka, ta miƙa masa, ta sauka tayi cikin layinsu da gudu a kan takalminta mai shegen tsini, ko wahalar gudun ba ta ji.

Mayafinta da jakarta a hannu, ta tura gate É—in ta shiga ta na haki.

Wani matashin saurayi, yana tsaye a harabar gidan hannunsa riƙe da waya, ya kalleta ya ce "Daga ina ki ke?"

"Biki" ta bashi amsa kai tsaye.

"Za ki ci ubanki kuwa, Major yana nan ido biyu, tun ƙarfe takwas ya dawo yake tambaya ko kin dawo, gashi kin kashe waya ke ga ƙwararriya"

Cikin ta yayi wata ƙara saboda tsoro "Allahumma inni as'aluka afuwa wal afiya, yau na kaɗe" ta ƙarasa maganar tana nufar cikin gidan.

Cikin sanɗa ta shiga falon, sai dai tana shiga, ta fara tozali da dattijon zaune a kan kujera 3 seater, ya sanya ƙofar shigowa falon a gaba, da gani babu tambaya ta san ita yake jira.

Tsayawa tayi ƙyam da takalmanta a hannu, da jaka da mayafi, kamar ta juya da gudu ta koma.

"Daga ina?" Yayi mata magana cikin dakakkiyar muryarsa.

Cikin rawar murya ta ce "Abba, wurin biki"

"To juya ki koma in da ki ka fito"

"Ai an tashi" tayi maganar kamar ta fasa ihu, dan tuhumar Abba babu daÉ—i.

"Dama haka mu ka yi da ke? Ki fita ki je ki yi zamanki? Ki dawo mini gida bayan goma, sai ka ce ki na zaman kanki?, koma ki kwana a in da aka yi bikin"

"Dan Allah Abb.."
Chapter 1 · 0% Book details