Sashe 3
Juyin KwaÉ—o Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ivana ta miƙa hannu ta ɗauki apple ɗin dake cikin wani bowl a kan center table, tana shirin fara cin apple ɗin idonta ya kai kan wata magazine dake aje a kan center table ɗin. Sai ta aje apple ɗin ta ɗauki magazine ɗin da hannunta na dama, yayin da take saƙala gashinta a bayan kunnenta da hanunta na hagu.
Ba komai ya ja hankalinta zuwa kan magazine ɗin ba face hoton dake jikin bangon magazine ɗin. Gani take kamar ta san mutumin cikin hoton, shiru ta ɗan yi tana son tuno inda ta taɓa ganin mutumin. Fuskarsa a yammacin yau ta da ta ganshi ta haska a cikin kanta. Ƙwarai kuwa, shi ne mutumin da ta haɗu da shi a Cavo Espresso Bar, sai ta shiga karanta bangon magazine ɗin. 'Business week' shi ne babban maudu'in abin da magazine ɗin ta ƙunsa.
Sai ta zarce zuwa kan sunansa dake gefe guda, Sayyid UWAIS FAZIL... Ta sake kallon fuskarsa tana furta sunan a kan leɓenta.
“UWAIS!”
Ta furta sunan ba tare da ta ji komai a ranta ba, saboda ɗan adam ba shi da ikon hango abin da ke tunkararsa a gaba, ba shi da masaniyar abubuwan da za su faru da shi, sai na wanda suka riga suka faru da shi.
“Ki ci Shish taouk ɗinki”
Yumma ta faɗa tana aje mata Shish taouk da ta zuba a cikin plate, Ivana ta aje magazine ɗin tana murmushi, sannan ta kalli Yumma tana ɗaukan plate ɗin, ta soma cin abincin tana bata labarin yadda live performance ɗin da suka je suka kalla yau ya kasance.
Bayan ta gama cin abinci ta nufi upstairs, dan gaba ɗaya ta gaji bacci take ji, ƙofar ƙaramin ɗakinta ta buɗe, ta shiga ciki tana kallonsa kamar baƙonta. Ɗakin sam ba shi da girma, amma ya ɗauki duka kayanta da take ajewa a ɗakin, akwai gadonta ɗan siriri na kwanciyar mutum ɗaya.
Wanda ke ɗauke da baby pink duvet, sannan akwai pillows manya da ƙanana, sannan akwai wardrobe da ba ta cika faɗi ba, akwai kuma desk ɗinta, sannan dressing mirror. Mafiya yawan abubuwan dake ɗakin pink cokor ne, hatta da stikern dake jikin bango pink ne.
Miƙa ta yi tana rataya jakar guitar ɗinta a sama, inda ta saba ajeta, sannan ta nufi bathroom, ta ɗauro alwala ta dawo ɗakin, wardrobe ɗinta ta buɗe, ta ɗauki mayafi a ciki, ta yafa a kanta, sannan ta tada sallah a kan center carpet. Sai da ta gabatar da sallahr isha, sannan ta yi wanka ta sauya kaya zuwa night wear.
Tana hamma ta bi lafiyar gado ta kwanta, tana rayawa ranta cewa me ake da rayuwar da babu gadon bacci, ita a duniyarta babu abin da ya fi birgeta sama da lallausan gado, dan ko a kan sofa ba ta iya bacci.
_________________
_Ehem! Ehem! Ehem!_
_Salmanians! Ga wata sabuwar tafiya! Me ɗauke da abubuwan ban al'ajabi._
_Tafiyar ba me sauƙi ba ce kamar yanda za ku ɗauka!. Dan haka sai ku shirya da kyau._
_JUYIN KWAƊO zai zo a Book 1 and 2. Book 1 shi ne free, book 2 ne zai kasance paid a kan ₦400_
_Kuma za ku iya samunsa a ArewaBooks, domin akwai complete book 1 a can_
_Sai ku shirya, ku gyara zama, domin jin yanda rayuwa za ta yi juyi da waɗannan abokai uku, kuma juyin ma irin na kwaɗo, daga ruwa zuwa ruwan zafi._
#Bahaɗejia
#Candy
#SalmaAhmadIsah
#JuyinKwaɗo
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
. 🪄...JUYIN KWAƊO...🪄
©️Salma Ahmad Isah
SalmaAhmadIsah @ArewaBooks
SalmaAhmadIsah @Wattpad
Page-2
*House No. 106, Street 14, Jumeirah Bay Island, Abu Dabhi, Dubai.*
Gidan na ɗaya daga cikin manya manyan gidajen dake hamshaƙiyar unguwar ta Jumeirah. Dan ko a yanayin gininsa za ka san an kashe kuɗi, ballantana ace ka samu damar kutsa kai ciki. Motar Armaan da ta ɗauko hanya tun daga unguwarsu Adam da ya aje a gida ta faka a gaban gidan.
Ya kashe motar, sanna ya cire seat belt ya fito yana jan jakarsa dake a wurin me zaman banza, ya goya jakar a bayansa, sannan ya juya ya fuskanci hamshaƙin gidan. Glasses ɗinsa ya gyarawa zama ta hanyar saka ɗan yatsansa manuniya ya tura bridge ɗin glasses ɗin, sannan ya nufi kyakkyawar ƙaramar ƙofar shiga gidan. Dan gidan ba shi da wani compound, wanna ƙofar ita ce da ka buɗeta za ta sadaka da gidan, hatta da garejin aje motocinsu na daga gefen ƙofar shiga gidan.
Hannunsa ya kai kan inda madannan sirrin buɗe ƙofar gidan suke manne a jikin ƙofar, daga gefe kuma door bell ne, wanda aka yi shi domin baƙi, dan idan har ɗan gidan ne babu buƙatar ya danna door bell, tun da duk sun san kalaman sirrin da suke buɗe ƙofar. Lambobin ya saka, nan take ƙofar ta buɗe, ya shiga yana kallon masu aikin gidan dake kaikawo, sanye cikin uniform iri ɗaya.
“Haidar!”
Ya yafito ɗaya daga cikin masu aikin, Haidar ɗin ya nufo shi yana amsa masa cike da ladabi, Arman ya miƙa masa mukullin motarsa, sannan yace.
“Motata tana waje, ka saka min ita a gareji, idan ka saka key ɗin kuma ka aje shi a nan”
Ya nuna masa wani abu me kama da basket dake aje kan wani cupboard dake farkon gidan, wanda ya ƙunshi tarin makullan motocin da mutanen gidan ke hawaya. Kuma daga jikin cupboard ɗin ma za ka iya hangen manya manyan motocin dake garejin, dan akwai ɗan glass dake wurin da zai baka damar hakan.
Haidar ya karɓi key ɗin, sannan ya nufi ƙofar fita, yayin da shi kuma ya kutsa kai cikin kyakkyawan gidan, bayan wani ɗan gajeren corridorn dake bakin ƙofar shigowa, za ka iske hanyoyi uku, ɗaya ita ce wadda zata sadaka da upstairs, kuma duka ɗakunan kwanan gidan suna sama. Ɗaya kuma ita ce wadda za ta sadaka da living room, wanda yake ƙunshe da sitting areas guda biyu, tare da dinning area, sannan akwai kitchen ta kusa da dinning area.
Kuma ta cikin falon za ka fita harabar garden ɗin gidan, dake ƙunshe da swimming pool. A kusa da swimming pool ɗin kuma akwai kujerun zama, wanda aka saka su a ƙasa, kamar dai zurfin swimming pool ɗin, kuma tsakanin wurin da suke da swimming pool ɗin glass ne kawai ya raba, ta yanda kana iya ganin ruwan cikinsa idan kana zaune a wurin.
Da farko hanyar da za ta sada shi da upstairs ya nufa, amma sai ya juyo ya fasa bi ta nan, dan ta cikin living room ɗin ma akwai wani stairs ɗin da zai kaika sama. Ya bi ɗayar hanyar da za ta kai shi living room, komai dake cikin living room ɗin gray color ne, daga can dinning area ya hangi mahaifinsa Iƙbal Alhadi, tare da mahaifiyarsa Zahra Ali, zaune suna dinner.
Wurin ya nufa yana kallon Imminsu, wadda ita ma ta ankara da shi, yana isa inda take ya sunkuya ya sumbaci kanta, sannan ya kama hannayenta ya sumbata.
“Masa'ul khair ya Immi (Barka da yammaci Immi)”
Zahra ta yi murmushi tana kallon ɗanta, ta shafa kansa tana amsawa.
“Shu wa aina Gulzar?” (Ina Gulzar ne?)
Ya tambaya ganin bai ganta tana dinner tare da su ba, Immi ta amsa masa da.
“Ab us ne khaana khtm krte dekha aur kamre mein waaps chla gaya”
(Yanzu ta gama cin abincinta ta koma ɗaki)
“Ɗayib ana rayih (Okay ni ma na tafi)”
ya bata amsa cikin harshen larabci, saɓanin ita da ta masa magana da harshen Urdu, ba wai dan bai iya mayar da amsa cikin yaren ba, sai dan ya san ita ma Immin tana jin larabcin.
A wasu lokutan ma idan za su yi magana tsakanin su uku sai su dinga haɗa larabci da Urdu, saboda Urdu shi ne harshen Zahra. Ba tare da ya yi wa Abby magana ba ya shiga ƙoƙarin barin wurin, sai dai tun da ya tsaya a wurin shi Abbyn ke binsa da kallo, ya lura da yanzu sam Arman ba ya son masa magana, saboda daga ya masa magana zai tado masa da zancen zama shugaban kamfanin Alhadi.
Kuma ya lura da ɗansa ba ya son maganar kamfanin ko abin da ya shafe shi, idan zai iya tunawa ma rabon Arman da kamfaninsu tun shekaru biyar da suka wuce, lokacin da suka yi murnar cikar kamfanin shekaru 30 da kafuwa. A yanzu babban burinsa bai wuce Arman ya zama shugaban Alhadi Group of Companies ba. Domin ba ya so ya mutu ya bar gadon kujerar shugabancin kafanin a hannun ɗan ɗan uwansa Faisal.
A cikin halayen arziƙi Faisal ba shi da guda uku ƙwarara, kuma sam bai yi kama da wanda zai zama shugaba na gari ga ma'aikatan kamfanin ba, sannan a ƙa'ida, idan har Arman ya ƙi amincewa da karɓar shugabancin kamfanin to Faisal shi ne wanda zai karɓi kujerar. Ƙoƙarin karkato da hankalin Arman shi ne abin da yake ta son yi tun kafin lokaci ya ƙure musu, amma shi Arman ya kasa ganewa.
A ko da yaushe yana ɗaukan kansa a ba jowa ba, ya bar zuciyarsa ta mutu, saboda an ce masa dan yana da matsalar gani ba zai iya zama jagoran kamfanin Alhadi ba. Kuma saboda yanda ake aibata lalurar tasa yasa ya tsani duk wata harka ta kamfanin.
“Armaan ina zaka je ba ka gaishe da Abby ba?”
Immi ta dakatar da shi, hakan ya sa ya juyo, ya kalli Abby da shi ma ke kallonsa.
“Masa'ul khair Abby”
Ya faɗa daga nan inda yake, dan a yanzu ko kusantar Abby ba ya so, daga ya kusance shi zai ji kamar yana kusantar kamfanin Alhadi ne. Abby ya sauƙe numfashi yana kallon ɗansa, sannan a hankali ya jinjina kansa yana amsawa, Arman na jin ya amsa ya juya ya nufi sama.
Dan sam ba ya ma son zamansa da Abby ya yi tsayi, dan daga sun ɗan jima a wuri zai fara masa maganar da ta mutuwarsa ta fita daɗin sauraro a kunnensa. Yana shiga corridorn ɗakunansu ya hangi Gulzar na nufowa downstairs da alama wani abin za ta yi a ƙasa.