Sashe 17
Juyin KwaÉ—o Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Daga haka suka juya suka fara tafiya a kan hanyar da ya nuna musu, kowa a cikinsu jikinsa a sanyaye yake, ban da Arman, wanda ya sa fata da yaƙinin cewa ko ba yau ba tabbas za su koma gida, kuma zai tabbatar da hakan!.
Sai da suka yi nisa sosai, sannan datijjon nan ya soma ja da baya, ya tsaya a gaban bukkarsa, ya lusmhe idonsa yana taɓa jikin bukkar, nan da nan bukkar ta ɓace, kamar ba'a taɓa hallitar wata bukka a wurin ba. Ya buɗe idonsa yana murmushi, sannan ya daka tsalle, kafin ya dire ya bi iska ya ɓace.
Sun ɗauka cewa tafiyar mai sauƙi ce, dan tun da suka kama hanya ba su tsayawa sai idan sun lura da lokacin sallah ya yi, kuma daga sun tsaya sun gabatar da sallahr za su ci gaba da tafiya, duk da jikin kowanne a cikinsu a sanyaye yake, Arman ne kaɗai ke ƙokarin ƙarfafa musu gwiwa. Ba su tsaya yada zango ba sai da dare ya yi, shi ma a cikin dokar daji suka kafa tantinsu guda uku.
Amma ba su shiga sun kwanta ba, suka zauna a waje suna jin ɗumin wutar da suka hura. Sai a lokacin Adam ya buɗe jakar abincin da tsoho me abin al'ajabi ya basu, ya shiga fitar da kayan ciki.
“Ni dai ba na jin zan iya cin wannan abincin”
Faɗin Adam yana nunawa Arman, Arman da ya nutsa duniyar tunanin 'yan uwansa ya dube shi.
“Za ka ci idan har abincin da muke da su suka ƙare”
Adam ya yi shiru kawai... Ita kuma Ivana na gefe tana duba service ɗin wayarta babu ko ɗaya, chajin wayar ma ya kusa ƙarewa.
“Ba service, ba wutar nepa, babu abincin da muka saba ci, babu komai na more rayuwa!”
Cewarta tana aje wayar, dan ta ga babu amfanin da za ta mata.
“Ba ki da chaji ne?”
Adam ya tambayeta, ta jinjina masa kai.
“Ina da solar, gobe sai ki yi chajin”
Ta sake jinjina kai tana shan tea ɗin da suka dafa.
“Ban taɓa tunanin cewa zan wayi gari na yi rayuwar da babu abubuwan ci gaban zamani ba, wai ashe akwai lokacin da rayuwa za ta juya mana mu kasance a halin da ba mu isa mun yi communicating with wani ba?”
Faɗin Adam yana rufe system ɗinsa.
“Duk abin da zai faru damu a gaba ba mu da masaniyarsa, ba mu da ikon canza komai”
Arman ya ba shi amsa.
“Kuma ka san ina ga kamar wannan babbar dama ce na samu da zan ɗauki hotunan abubuwan da babu photographer ɗin da ya taɓa gabatar da su, masarautun mutanen da, al'adu da shigarsu da ma abincinsu!”
“Ƙwarai, kuma ina ga kamar wata dama ce da za ta sauya tunanin Arman a kan Alhadi!...”
Adam da Arman suka dubi Ivana da ta yi wannan furuci cikin mamaki...
“Ke! A wannan duniyar fa ba su san masana'anta ba ballantana babban kamfani kamar Alhadi, ta ya za'a samu wani kamfani da zai sa Arman ya sauya ra'ayinsa kafin mu koma gida?”
“Masarautun zamanin nan suna kama da kamfanunuwan zamaninmu!”
Ta basu amsa, suka sake duban juna, amma shi dai Arman bai ce komai ba. Har suka gama zaman hirar suka koma cikin tent ɗinsu suka kwanta, cike da fatan wayar gari lafiya.
MAMLAKATUL JIYAD.
Cike da ƙasaita, izza da isa wani basaraken matashi ke tafiya, kamar wanda ba ya son taka ƙasa, hannayensa goye a baya, yayin da masu gadinsa ke take masa baya. Wasu irin kayan sarakunan da ne a jikinsa, wanda kai daga ganinsu ka san sun amsa sunansu kayan alfarma.
Sai da suka kai ƙarshen dogon falon dake ƙarshen sashen sarki, sannan ya dakata, hakan ya sa su ma dakarun dake take masa baya suka dakata, cike da izza ya daga hannayensa, ba sa jira ko buƙatar ya furta musu abin da yake buƙata, cikin hanzari mutum biyu dake cikinsu, suka ƙara matsawa kusa da shi, sannan suka kama rigar sarautar dake saman kayan nasa da za'a iya kira da alkyabba.
Suka sauƙeta daga kan kafaɗunsa, sannan suka ja da baya a tare suna riƙe da rigar tasa, sai da suka ja da baya, sannan mutum biyun dake jikin wata ƙofa da aka ƙera da zallar baƙin ƙarfe suka buɗeta, hakan ya bayyanar da doguwar matakalar da ta yi ƙasa zuwa harabar fadar. Kuma daga ƙarshen matattakalar akwai wani keken doki da matuƙinsa, wanda ke jiran fitowar sarki.
Cikin wannan takun nasa na izza ya soma tafiya, har ya kai ƙarshen matattakalar, matuƙin keken dokin ne ya sauƙa daga wurin da aka tanada dominsa, ya buɗe gidan baya na keken, inda aka tanada domin zaman mai martaba, sai da ya shiga ciki ya zauna, sannan matuƙin ya rufe ƙofar keken dokin.
Kana ya koma wurin zamansa, ya fara sarrafa dokuna biyun dake jan keken, suka bar ginin fadar, suka hau wata hanya ɗoɗar, wadda za ta sadasu da hanyar barin gari, da yake kowa ya san keken dokin sarki masu yasa gadi ba su yi ƙoƙarin dakatar da su ba, suka yi saurin wangale maƙareriyar ƙofar ganuwar masarautar.
Ko da suka bar fadar dajin dake kusa da masarautar suka kutsa, dokunan na gudu a cikin dajin, yayin da Sarki Cangaz dake keken dokin ya matsu da su kai ga ƙarasawa fadar bokansa. Domin a daren jiya ya samu saƙo daga wurin bokan nasa, kan yana son ganinsa a safiyar yau, hakan ya sa ya yi sammakon tashi.
A lokacin da ya ji dokunan tare da keken sun tsaya cak, matsuwa tare da zaƙuwarsa na son ganin bokan ta ninku, ta yanda bai jira matuƙin ya buɗe masa ƙofar ba, da kansa ya buɗe ya fita, duk wata izza da isa da yake nunawa a masarauta a cikin dajin bai yi ta ba. Hasalima sauri ya yi ya faɗa wani gida dake jikin bishiya a cikin ƙungurmin dajin.
Yana buɗe ƙofar ya kutsa kai cikin gidan, babban boka Jalis dake durƙushe a gaban wani maƙareren allo ya ɗaga kai ya kalli Cangaz kammaninsa suke a na matashi, domin akwai wani sabon tsafi da boka Jalis ɗin ya haɗa masa a kwana nan, wanda yake sawa kamanin matashin kan yi tsawon kwanaki a jikinsa har na kimanin mako biyu, durƙushewa ya yi a gaban bokan, yayin da Boka Jalis ke ƙare masa kallo, fuskarsa ɗauke da murmushi.
“Ka yi kira na amsa Jalis, da fatan da wani labari me daɗi ka zo min”
Muryarsa me ɗauke da izza da ƙasaita ta furta suna duban juna shi da Boka Jalis.
“Ƙwarai kuwa shugaban talakawa. Mafarkin da ka daɗe kana yi na tsawon kwanaki ne ya zama gaskiya...”
“Ka yi saurin sanar da ni abin da yake faruwa”
Ya yi saurin katse shi, dan sam ba ya son wani tambihi, boka Jalis ya girgiza kai yana murmushi, sannan a hankali ya juyawa Malik Cangaz fuskar allon dake aje a gabansa, Malik Cangaz ya kalli allon dake ɗauke da hoton wasu matasa uku, waɗan da sam kammaninsu da kuma shigarsu ba ta yi kama da ta mutanen duniyarsu ba, cike da kokwanto ya kalli boka.
“Baƙi aka yi daga wata duniyar?”
Boka Jalis ya girgiza kai.
“Ba za mu iya kiransu da baƙi daga wata duniyar ba kai tsaye, amma za mu iya kiransu da baƙin sa'a, masu tafe da cikar mafarkinka... Kalli ka ga”
Ya ƙarashe yana nunawa Malik sarƙar wuyan Arman.
“Wannan shi ne makullin ƙofar da muke ta naiman mabuɗinta... Wannan makullin shi ne ƙarshen abin da zai sa ka ci gaba da zama a matashi har duniya ta naɗe”
Lokaci guda Malik Cangaz ya saki wani ƙassaitaccen murmushi, suka haɗa ido da Boka Jalis.
“Shin a ina waɗannan matasan suke? Domin ba na so na ƙara ko da sa'a guda ba tare da na buɗe ƙofar nan ba”
“Ai ba'a nan gizo yake saƙar ba Shugabana, waɗannan matasan uku da kake gani, sam ba mutanen wannan zamanin namu ba ne, ƙaddara ce ta yi JUYIN KWAƊO da rayuwarsu zuwa wannan zamanin namu. Kuma a halin da ake ciki su ma suna fafutukar yanda za'a yi su koma zamaninsu. Sannan an sanar da su cewa wannan ƙofar taka ita ce ƙofar da za ta mayar da su zamaninsu, dan haka su ma kansu suna tunkararka ne, ba kai ne kaɗai kake naimansu ba...”
Malik Cangaz ya miƙe tsaye, ya yi taku uku tare da juyawa boka Jalis baya.
“Ai ko ba za su taɓa komawa zamaninsu ba, domin ba zan taɓa bari su kai ga ganin ƙofar nan ba, ballantana har ta kai ga sun samu damar shiga cikinta... Zan sa a naimo min su duk inda suke a duniyar nan, domin a karɓo min makullin da suke tare da shi, saboda na buɗe ƙofar nan na cika burina!...”
Ya ƙarashe yana bushewa da dariya, shi dai Boka Jalis bakinsa ya ja ya yi shiru, dan ba zai sake cewa komai ba, shi ya san abin da ya gani kawai, domin Malik Cangaz farkon yaƙin ya sani kawai, bai san ya ƙarshen yaƙin zai kasance ba, kuma shi ɗin ma da ya sani ba zai faɗa masa ba domin tsira da rayuwarsa...
Malik Cangaz ya juyo tare da duban Boka Jalis.
“Haƙiƙa yau ka sanar da ni labarin da ya fi ko wanne daɗi a duniyar nan, dan haka dole na maka gagarumar kyauta, sannan ina gayyatarka zuwa wurin ganawa da yariman masarautar Azad, wanda zai zo tare da mahaifinsa a kan maganar auren Gimbiya Iqrah, da fatan za ka zo?”
Boka ya jinjina kai yana murmushin ɓoye sirrin zuciyarsa.
“Ƙwarai kuwa shugabana, zan kasance a wurin a lokacin da ake buƙata!”
DANEEN IQRAH.
Yalwataccen hasken rana da ya fara ratsowa cikin masarautar ne ya samu damar shiga ɗakinta ta hanyar ƙatuwar tagar dake saman ɗakin. Hasken ranar ya samu nasarar sauƙa a kan wata kyakkyawar hallita dake kwance a kan katafaren gadon dake tsakiyar ɗakin.