← Book details Juyin KwaÉ—o Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 25

Sashe 2

Juyin KwaÉ—o Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Da ƙyar muka saka shi ya fito daga gida, yanzu kuma idan ka ci gaba da masa dariya ko zai koma gida ba zan yi ƙoƙarin hana shi ba”

“Asif (Ku yi haƙuri)”

Faɗin Arman yana toshe bakinsa. Ivana ta sake dafa kafaɗar Adam da har yanzu yake a dame.

“Laik Adam! Shabah mu haƙiƙi! Killu mazah! Wa ma bi kaffu!”

(Ka ga Adam, fatalwa ba gaskiya ba ce, duka shiri ne, kuma ba su da ban tsoro).

“Me ya sa za ki faɗi haka? Bayan ni na ganta da idona, wata doguwa, me dogayen farata, idonta ja... Wayyo Maama”

Ya ƙarashe yana rufe fuskarsa, saboda fuskar fatalwar da ya hango. Ivana ta sake dafa shi.

“Ihda! Halla rah jiblak shai. Biddak shai mu?” (Ka nutsu, yanzu zan kawo maka shayi, kana son shayi ko?)

Ya jinjina mata kai yana kallon Arman dake ta ƙoƙarin danne dariyar da ke ciyo shi. Ivana ta gyaɗa kai, sannan ta miƙe ta zagaya ta nufi wurin da zata yi order. Cup uku na shayin ta karɓa, sai dai a yayin da take shirin juyawa ta yi karo da wani mutum da shi ma yake ƙoƙarin zuwa wurin.

Farko kofunan shayin dake jere a kan tray ta fara kalla, da ta ga ba su zube ba sai ta kalli mutumin da ta yi karo da shi. Wani kyakkyawan matashin balarabe ne, wanda ke sanye da baƙar suit, kalar farar fatar jikinsa me ɗaukar hankali ce, haka ma kammaninsa, dogo ne, kuma me matsakaicin jiki, yana da faffaɗan ƙirji, sannan sumar kansa na cikin asken high pade. Yana da buɗaɗɗen ido, wanda yake ɗauke da shuɗiyar ƙwaya, sannan hancinsa dogo ne sosai, ga bakinsa dai-dai wa dai-dai, yana da saje da kuma gemu, wanda suka ƙara masa kyau.

“Ana ba'atazir! Ma intabahat!” (Ki yi haƙuri ban lura da ke ba ne).

Ta ji muryasa me daɗi ta furta, sai kawai ta jinjina kanta, alamun ba komai, sannan ta raɓa shi ta wuce, har ta koma table ɗin da su Armaan suke bai daina kallonta ba.

“Rifaƙ (Guys) ko kun san cewa yau Chris Brown zai yi live performance a Coca-cola Arena?”

Faɗin Arman yana nuna musu takardar sanarwa a cikin wayarsa. Adam da Ivana suka dubi juna.

“Wai yau?”

Adam ya tambaya yana aje cup ɗin dake hannunsa.

“Eh yau, duba ka gani”

Ya miƙa masa wayar , Adam da Ivana suka haɗa kai suna karantawa.

“Za mu je ne?”

Cewar Ivana.

“Akid! (Of course)”

Arman ya bata amsa. Domin duk inda za su je ko za su fita shi ne ke biyan duk kuɗin da za'a kashe, ko cinema za su je shi zai sai musu ticket. Saboda kaf cikin su ukun babu wanda ya kai mahaifinsa kuɗi. Dan mahaifinsa babban ɗan kasuwa ne, wanda yake da kamfanunuwa masa masu zaman kansu.

Shi Adam photographer ne, yana aiki tare da wani kanfanin magazine, ita kuma Ivana musician ce, tana koyar da kiɗan guitar a Repton school Dubai. Sannan tana aikin kiɗa a waƙoƙi idan har an buƙata, duk cikinsu shi Arman ɗin ne ba shi da aikin yi, ba wai dan ba'a naima masa a gidansu ba. Sai dan shi a rayuwarsa ya tsani duk wata harka da ta shafi kasuwanci.

Duk da ya taso a gidan da ake kasuwanci, kuma hakan ya samu asali ne daga nakasar gani da yake fama da ita tun lokacin yarinta. Tun a tasowarsa kawunsa, yayan mahaifinsa ya saka masa ƙin harkar kasuwanci, dan a ko da yaushe abin da yake faɗa masashi ne.

“Harkar jagorancin babban kamfani kamar Alhadi Group of Companies ba na makafi ba ne”

Ya sha faɗa masa hakan tun ba shi da wayo har ya taso ya yi wayo, tun ba ya gane abin da kalaman ke nufi har ya zo ya gane abin da kalaman ke nufi. Sannan tsangwamar da ake yi wa mahaifiyarsa a halinsu ya ƙara cusa masa ƙiyayyar kasancewa ɗaya daga cikin ahalin Alhadi a ransa.

Kuma suna nunawa mahaifiyarsu wariyar launin fata saboda ita 'yar Pakistan ce, su kuma ahalin mahaifinsa larabawan Qatar ne. Shi da ƙanwarsa Gulzar kaɗai iyayensu suka haifa, kuma bayan shi babu wani wanda zai iya gadon kasuwancin mahaifinsa sai Faisal!. Ɗan yayan mahaifinsa da shi ma ya bada tasa gudummawar wurin cusa ƙiyayyar son karɓar jagorancin Majmu'at Shirkat Alhadi (Alhadi Group of Companies).

Zama shugaban Alhadi Group of Companies shi ne babban burin Iƙbal, wato mahaifin Arman. Kuma saboda yana yawan takura masa a kan batun kasuwancin yasa suka fara raba gari. Dan a yanzu Arman ba ya jin yana da maƙiyi sama da kujerar jagorancin gammayar kamfanunuwan Alhadi.

Alaƙarsu da su Adam ta samo asali ne tun daga makaranta, abin da ya sa tafiyarsa da su ta yi nisa shi ne su ba su tsangwamarsa dan yana da ƙarancin lafiyar ido. Kuma sam ba sa ɗaukan cewa bai kai ba, dan yana saka glasses ɗin da za su taimaka masa wajen gani, saɓanin yanda ya taso ana nuna masa cewar tun da ba ya gani shi makaho ne.

“Na ga kamar sauran awa ɗaya a fara wansa fa!”

Adam da ya ci gaba da karanta takardar sanarwar ya faɗa, sai duk su ukun suka dabi juna, kamar wanda suka haɗa baki, haka kowa ya finciki jakarsa suka ruga da gudu zuwa waje, Ivana na faɗin.

“Gara mu yi sauri kafin tikitin ya ƙare!”

Ai a ɗari suka shige motar Armaan ƙirar Ferrari venon, Adam ya figi motar zuwa Coca-cola Arena, kamar yanda suka yi zato ticket ɗin ya kusa ƙarewa. Dan duk da haka sai da suka bi layin siyan tikitin. Yayin da suke bin layin siyan tikitin, Adam ya shiga bawa Adam labarin film ɗib da ya kala jiya. Shi kuma Arman sai kwasar dariya yake, kamar daga sama ya ji an kira shi da sunan da ya fi masa na mutuwa ɗaci a kunne.

“Marhaba makaho! (Hello makaho)”

Idonsa ya rintse, dan ko ba'a faɗa ba ya san wa ya mallaki muryar, dan haka ya buɗe idonsa yana gyara glasses ɗinsa, wanna ita ce ɗabi'ar da ya fi yawan yi, ba ya haura minti goma ba tare da ya gyara zamansa glasses ɗinsa ba, ko da ko bai zame ba. Ya juyo yana kallon Faisal tare da wata budurwa tsaye, dariyar da ya ga Faisal ɗin na yi ita ta fi baƙanta masa rai.

“Ashe kuma makafi ana ganinku a wurare irin wannan?... Na ɗauka makafi ba sa zuwa kallon live performance!”

Ya ƙarashe yana sheƙewa da dariya, budurwa dake tare da shi tana taya shi.

“Ka ga malam! Babu wada ya buƙaci jin ra'ayinka a nan, dan haka bama son tada zaune tsaye.”

Ivana ta dakatar da shi, dan ko kaɗan Arman ba ya iya tanka masa ko ƙanwarsa Sakina idan suna aibanta shi, idan suka taɓa Gulzar ko mahaifiyarsu ne dai ba ya shiru.

“Yi haƙuri malama, ba da ke muke ba, da wannan makahon muke...”

Ya yi fasali yana yin taku uku zuwa gaban Arman, sannan ya yi kamar zai rungume shi, ya kai bakinsa saitin kunnensa yana murmushi, sannan ya furta.

“Jin daɗi da sharholiya irin wannan ba ta kamaceka ba, ka fi dacewa da yin bara a gefen hanya!”

Ya ja baya yana dariya, Ivana ta riƙi kwalar rigarsa a fusace za ta mayar masa da martani, Armaan ya jata baya yana girgiza mata kai. Haka Faisal da budurwasa suka wuce suka barsu a wurin suna dariya.

“Da ka bari na mayar masa da martanin da zai hana shi ba ci daren yau. Amma ka hana”

Arman ya girgiza mata kai.

“Maganganu irin wannan na saba jinsu tun tasowata, ba shi ne mutum na farko da ya fara faɗin hakan ba, dan haka ki share kawai”

Ya ƙarshe yana ɗauke kai, cike da damuwa Ivana ta kalli Adam da bai ce komai ba, dan ba zai ce ɗin ba, tsoro ba zai bari yace komai ba, ko shi ya je ya takalo faɗa Ivana da Arman ne ke tare masa, amma ba ya iya taɓuka komai.

*House No 27, Street 45, Mirdif, Dubai.*

Motar Armaan ta faka a gaban ƙaramin gidan da bai cika girma ba, amma duk da haka ko daga waje ma yana da kyau. Ivana dake gidan baya na motar ta buɗe ta fita, sannan ta goya jakar guitar ɗinta a baya, ta rufe motar tana kalon Adam da Arman dake gidan gaba.

“Me kuka shirya mana zuwa gobe?”

Arman da Adam suka dubi juna, sannan Adam ya sake subanta yana girgiza kai.

“Babu wani abu, sai dai idan mun haɗu zuwa goben”

Ta ɗaga hannunta suka yi fits bump, sannan ta ɗaga musu hannu ta nufi gidansu. Ƙofar shiga gidan ta buɗe, ta shiga, sannan ta rufe ƙofar tana cire takalman dake ƙafarta, ta saka wasu dake aje a bakin ƙofar, sannan ta nufi falon gidan dake a farkon gidan.

“Assalamu alaiki ya Yumma!”

Ta yi wa mahaifiyarta dake zaune a falo tanq cin fruit sallama, fuskarta ɗauke da murmushi, ita ma tsohuwar matar na ganinta ta fara murmushi, Ivana ta risina ta sumbaci kan mahaifiyarta, sannan ta zauna kusa da ita tana cire jakar guitar ɗin dake bayanta, tare da ajeta a gefe, ta gyara gashin kanta tana faɗin.

“Shu yalli ɗabaktil yaum ya Yumma”

(Yumma yau me kika dafa?)

Mahaifiyar Ivana me suna Khadija, wadda Ivana da yayarta Hala ke kiranta da Yumma tace.

“Shish taouk”

“Ba na jin yunwa sosai, dan mun tsaya a Al Fayrooz lounge mun ci abinci tare da su Arman, dan haka ki zuba min kaɗan”

“To”

Cewar Yumma, sannan ta miƙe ta nufi kitchen ɗinsu dake haɗe da falon, dan wata gajerar katanga ce kawai ta raba kitchen ɗin da falon, komai dake cikin falon ba shi da tsada, kuma kayane irin na da, dan a cikin gidan aka haifi Ivana da yayarta Hala, wadda a halin yazu ta yi aure, har da yaronta guda ɗaya.

Mahaifinsu ya rasu tun da ƙarancin shekarunsu, hakan ya sa suka taso ba su san shi ba sai Yumma, suna da rufin asiri dai-dai gwargwado, kuma ba su ɗauki rayuwa da zafi ba.
Chapter 2 · 0% Book details