← Book details Juyin KwaÉ—o Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 25

Sashe 24

Juyin KwaÉ—o Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Asra na sanye da wata Thawb kalar ruwan zuma, ta ɗora Muƙawar a kanta, wanda bai ɓoye dogon gashin kanta ba, tana tafiyarta irin ta jarumai, dan sam ba ta tafiya irin ta sauran mata. Da hannu ta yi wa hadiman Iqrah alama da su basu wuri, hakan ya sa duk suka fice daga wurin, Iqrah ta miƙe tsaye tana kallon 'yar uwarta.

“Barka da zuwa Ukti!”

Cewar Iqrah tana murmushi. Ita kuma Asra sai ta murtuke fuska tana binta da kallon tuhuma, dan haka kawai take jin ba ta yarda da ita ba. Da farko tace mata ba ta son wannan haɗin auren, ya za'ayi yanzu kuma ta zo tana murmushi?... Dole dai da akwai abin da take ƙullawa.

“Sarƙoƙi ne Darvesh ya aikoni da su, yace a kawo miki ki zaɓi wanda kike so”

Cewar Asra, tana yi wa bayin alama da su nunawa gimbiya kayan da suka zo da su. Iqrah ta nufi wurin bayin, ta ci gaba da duba sarƙoƙin, sai fara'a take abinta.

“Wannan sun fi kyau”

Ta nuna wadda ta fi burgeta. Hakan ya sa Asra ta duba wadda ta zaɓa, ba tare da ta furta komai ba ta sallami bayin, sai da suka fita sannan ta dubi 'yar uwarta da kyau.

“Ina mai fatan Allah yasa ba wani abin kike shiryawa ba”

Cewar Asra, Iqrah ta kuma yin murmushi.

“Kada ki damu 'yar uwa, ba zan aikata abin da yake ba dai-dai ba!”

“Ni ma haka nake fata”

Cewar Asra tana jinjina kai, da haka ta fita ta bar Iqrah a wurin.

Salma Ahmad Isah ✍️

_Pages ɗaya ya rage book 1 ya ƙare, idan regular group kike so za ki tura ₦400 through account details ɗin da zan rubuta a ƙasa. Idan kuma VIP ne sai a tura ₦800._

5487270431
Salma Isah
Monie point

Shaidar biya kuma ta 08130172704.

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

🪄 ...JUYIN KWAƊO...🪄

©️Salma Ahmad Isah

SalmaAhmadIsah @ArewaBooks
SalmaAhmadIsah @Wattpad

Page-14

MAMLAKATUL AFSAH.

Zaune a gaban Malik Safraz Natila ce, sanye cikin baƙaƙen kaya, amma yau fuskarta ba a rufe take ba. Ta nutsu tana sauraron buƙatar Malik da yake so ta biya masa.

“Idan dan ta wannan ne kada ka damu Shugabana. Zan tattaro sauran yarana, za mu bisu har zuwa cikin dajin da suke, kuma zan tabbatar da na ƙwato maka takobinka!...”

Malik Safraz ya yi murmushi, dan ya san aikin Natila, idan tace za ta yi to za ta aikata. Ya sha sakata ayyuka makamantan wannan, kuma cikin sa'a tana nasara. Miƙewa tsaye ya yi, yana goya hannayensa a baya, sannan ya ƙarewa katafaren falon da suke ciki kallo, kana ya juya bayansa yana faɗin.

“Idan kuwa har kika kawo min wannan takobin, zan miki gagarumar kyautar da ban taɓa miki irinta ba!”

Natila ta miƙe tsaye, sannan ta amsa da.

“Zan kasance me cika alƙawari kan abin da na alƙauranta maka shugaba, ba zan taɓa baka kunya ba!”

Malik Safraz ya sake murmusawa, sannan ya juyo ya dubeta.

“Ki je domin ƙwato min takobina!”

Ta risina alamun ta amsa. Kana ta ɗaga kai, kafin kace me har ta ɓace. A lokacin kuma Anser mahaifin Safraz ya iso falon shaƙatawar sarkin tare da masu take masa baya. Sai da ya isa falon sannan ya yi musu izini da su jira shi a waje, sai da suka fita sannan ya dubi ɗansa.

“Wata magana nake ji haka Safraz?...”

“Wata magana kuma?”

Safraz ya mayar masa da tambayar.

“Magana nake a kan ƙwatar takobi daga hannun Uwais!”

“Shin laifi ne dan na karɓi abin da yake nawa?”

Safraz ya tambaya cikin halin ko in kula.

“Abin da nake so ka fahimta a nan shi ne, yanzu kai ne sarkin Afsah, wannan takobin ba zai kareka da komai ba, tun da ko a da rashinsa bai sa ka kasa zama sarki ba”

Safraz ya girgiza kai.

“Ba wai mallakar takobin ne kaɗai abin da ya tsaye min a rai ba. Kasancewar Uwais da Feroza a raye shi ne babban abin da yake damuna... Idan har Uwais ya ci gaba da kasancewa a raye ba zan taɓa samun kwanciyar hankali ba, domin mulkina zai kasance cikin haɗari, wanda ni kuma ba zan lamunci hakan ba!”

Anser ya sake matsawa kusa da ɗansa, sannan ya dafa kafaɗunsa.

“Rabuwarka da Uwais shi ne abu mafi alkairi, idan har ka ce za ka ci gaba da bibiyar rayuwarsa to fa ni da kai duka ba za mu ji daɗi ba. Dan haka a shawarce ka ƙyale shi zai fi!”

Safraz ya ture hannayen mahafinsa dake kan kafaɗunsa, sannan ya tashi sama ya fara yawo a iska yana faɗin.

“Ba zan ƙyale shi ba, dole cikin biyu a yi ɗaya, ko dai shi ya mutu, ko Feroza ta mutu!...”

Yana gama faɗin hakan ya ratsa rufin falon ya fice ta wurin.

MALIK CANGAZ.

Kallon kallo aka shiga yi tsakaninsa da Boka Jalis dake sanar masa da wurin da matasan da yake naima suke. Can kuma sai ya kwashe da dariya yana cilla kansa baya.

“Tabbas zan taƙaita musu kwanakin tafiyar dake gabansu!”

Ya faɗa bayan ya gama ƙyaƙyata dariyar tasa. Cikin rashin fahimta boka Jalis yace.

“Ban fahimceka ba shugabana!”

“Tun a daren yau zan shirya dakaru, sannan na turasu suje su tarbesu kafin su samu isowa nan!”

Malik Cangaz ya bawa Boka Jalis amsa. Shi dai boka bai cce ƙala ba, dan shi ya hango abin da ya hango. Har suka gama tattaunawa da bokan bai sanar da shi wani abu bayan nasara ba. Da wannan farin cikin ya koma fada, duk da akwai manyan baƙi dake zuwa domin halartar bikin gimbiya bai sa ya fasa sawa a shirya dakaru domin turasu ƙwatar mukullin dake hannun baƙin matasa uku ba.

Sai da ya gama da wannan fannin, sannan ya dawo cikin fada ya fuskanci lamarin baƙinsa, a gefe guda kuma shirye-shiryen bikin gimbiya na ci gaba da wanzuwa a fadar, domin duk mutanen gari sun san cewa za'ayi biki a gidan sarki.

EID.

Hannu ya miƙa ya karɓi sabbin tufafin da ya siya a wurin wani mutum dake cikin kasuwar ƙauyen Aban, domin ƙauye aban shi ne ƙauyen da ya zaɓa domin gudanar da ɗaurin aurensa da gimbiya Iqrah. Auren da zai yi amfani da shi wurin tarwatsa zuciyar Iqrah, auren da zai yi amfani da shi wurin rama kwatankwacin abin da Malik Cangaz ya aikata masa.

Sai dai kuma ta wata hanyar wannan auren ya taɓa rayuwarsa, tun farko shi ba son gaskiya yake yi wa Iqrah ba, hasali ma komai yake faruwa tsakaninta da shi duka shiri ne. Domin hatta da farkon haɗuwarsu shiri ce, shirin da ya taso shi tun daga nahiyarsu zuwa Mamlakatul Jiyad.

Domin asalinsa ba ɗan garin ba ne, babu wani abu da ya haɗa alaƙarsa da ta daular Jiyad, cin burin ɗaukan fansa ya sa ya yi takekeniya ya bar nahiyarsu ya kutsa zuwa wannan gari. Lokacin da ya zo garin duka tsarukansa sun tafi dai-dai, ciki har da sawa Iqrah soyayyarsa a ranta. Kuma hakan ma ya tafi yanda yake so, sai dai kuma wa gari ya waya? Domin a ƙarshe shi aka bari da jinyar zuciya.

Duk taka tsantsan ɗin da yake na gujewa soyayyar Iqrah an yi rashin sa'a shirinsa ta wannan fannin bai yi ba. Domin a halin yanzu shi kansa ya san cewa yana sonta, amma kuma ya yi rantsuwa kan ba zai bari soyayyarta ta hana shi ɗaukan fansarsa ba, ko da kuwa hakan zai sake raunata zuciyarsa ne a karo na biyu...

“Eid!”

Kamar kullum, kamar yanda ya saba tunaninta haka yau ma muryarta ta kutso cikin tunaninsa. A hankali ya zauna kan wata bishiya, yana kallon wasu yara dake wasa kusa da bishiryar. Hannu ya kai ya sauƙe Aafa dake kafaɗarsa, sannan ya ajeta a gefensa yana ci gaba da kallon yaran.

Haka kawai murmushi ya suɓuce masa, domin ya tuna da nasa ahalin, da ace har yanzu matarsa Maryam na raye, da ita ma ta haife masa ɗan cikinta... Ɗansa, jin zuciyarsa na ɗacin tunowa da mutuwar Maryam xa ta mahaifinsa ya sa ya kawar da kai daga barin kallon yaran, gudun kada ya haɗiyi zuciya ya faɗi ya mutu ba tare da ya ɗauki fansa ba.

“Daga gobe ba za ka sake kwanan farin ciki ba Cangaz! Zan tabbatar da na ƙuntata maka dai-dai da yanda ka ƙuntata zuciyata!”

Ya furta yana haɗe haƙwaransa na sama da na ƙasa, zuciyarsa na tabbatar masa da cewar zai iya!.

ADVENTURERS.

Bayan shafe tafiyar awa uku a ƙafa, suka yanke shawarar zama su huta a wani daji. Yayin da suke hutawa Uwais yace zai je ya naimo musu abinci, amma sai Arman yace kada ya je, shi ma ya zauna ya huta, tun da shi ma zai gaji ne.

“Ba lalle ba! Shi da mu akwai banbanci!”

Cewar Sana da yanzu ita ma ta zama abokiyar tafiyarsu. Lokacin da suka gane cewa ita ce sun sha matuƙar mamakin ganin matar sarki 'yar saki a wuri irin wanda suka haɗu, bayan ta sanar da su cewa tafiya ce ta kamata har ta kai ga mutanen nan sun kamata, sai suka cire ko wani kokwanto, su ka ci gaba da tafiya da ita har zuwa yanzu.

“Me ya sa na zama ba ɗaya da ku ba?”

Uwais ya tambaya yana murmushi.

“Saboda kai ka kasance ruwa biyu, aljani kuma mutum!”

Sana ta amsa shi, har zuwa yau fuskarta na a rufe da mayafin da take rufe kanta da shi, domin ba ta cika buɗe fuskarta ba.

“Uwais!”

Adam dake yi wa Ivana tausa a ƙafa ya kira sunan. Hakan ya sa Uwais ya dube shi.

“Ya ka ji lokacin da aka ƙwace mulkin mahaifinka, sannan ya kake ji idan ka tuna cewa abin da yake mallakinka na tare da wani da ba kai ba!?”

Adam ya tambaya da biyu, dan lokacin da ya cilla masa tambayar sai da ya saci kallon Arman, kuma ya lura da tambayar ta sa shi cikin nazari. Ivana da ta fahimci inda ya dosa ta daki kafaɗarsa cikin gargaɗi, duk da yau a gajiye take liƙis, saboda ita ne ma suka yada zango ba dan dare ya yi ba, ga ƙafafunta dake mata mugun ciwo, shi ya sa ma ta saka Adam ya mata tausa.
Chapter 24 · 0% Book details