← Book details Juyin KwaÉ—o Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 25

Sashe 23

Juyin KwaÉ—o Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Uwais ya ƙarashe da tambaya. Arman ya girgiza kansa yana ci gaba da haska matar, sannan ya ƙura mata ido. A hankali ya fara takawa zuwa inda matar take, yana daf da durƙusawa a kusa da ita, mutumin da suke sa ran shi ne shugaban mutanen da suka kamasu ya furta.

“Ku je ku fito da su yanzu mu sadaukar da su ga wutar bautarmu!”

Hakan ya sa Arman ya fasa durƙusawa, ya juyo ya kalli abokansa cikin tashin hankali, Ivana ta dubi Uwais, sannan ta dubi Arman, yayin da Adam ya ƙara fashewa da wani sabon kukan yana faɗin sun mutu.

Har zuwa lokacin da wasu mutum biyu suka buɗe ƙofar kejin da suke ciki ba su iya taɓuka komai ba, sai da aka gama fito da su daga cikin kejin, har da matar da a yanzu suka lura da cewa fuskarta a rufe take, aka jerasu a gaban wutar dake ciki.

“Dan Allah Arman ka yi wani abin!”

Cewar Adam cikin kuka. Arman ya lumshe idonsa, yayin da yake lalubo takobin da datijjo ya ba shi a cikin jakar dake bayansa. A lokacin da ya riƙo takobin ya buɗe idonsa, sannan cikin zafin nama ya miƙe tsaye, ya zare takobin yana nuni da shi ga mutanen da suke riƙe abokansa da wannan matar.

“Kada ku cutar da su! Ku ƙyalesu!”

Ya faɗa yana nuna musu takobin.

“Me kuke jira wai? Ku danna min kawunansu a cikin wuta!”

Shugaban mutanen ya basu umarni cike da isa, wanda yake riƙe da Adam ne ya riƙo gashin kansa, yana shirin danna kan Adam a cikin wutar Arman ya yi tsallen albarka, ya ɗaga takobin hannunsa ya datse hannun mutumin!.

Ƙarar da ya ƙwalla ce ta janyo hankalin sauran mutanen wurin. Sannan kuma ita ta razana sauran da suka ga faruwar lamarin. Sai suka yi saurin ja baya daga jikinsu Ivana, yayin da shi ma Uwais ya yi amfani da wannan dama wurin juya sarewarsa zuwa baka, sannan ya motsa hannunsa ya fito da kibiya, tare da sakata a jikin bakar, shi ma ya nuna mutanen da ita.

Adam da Ivana kuma suka yi saurin ɓuya a bayansu, su kuma suka musu garkuwa, amma wannan matar ta ɗazu har zuwa lokacin tana durƙushe a gaban wutar, ba ta motsa ba ballantana ta yi yunƙurin guduwa, kuma kanta a ƙasa, sannan fuskarta a rufe.

“Lalle kun aikata babban kuskure, tun da har kuka iya illata ɗaya daga cikinmu, kuma a sansaninmu... Ina me muku albishir da ba za ku bar nan da rai ba... Dakaru! Ku tabbatar da kun gama min da su yanzu...!”

Cewar shugaban dakarun, nan da suka yi kan Arman da Uwais, amma kuma sam ba su ba su damar cutar da ɗaya daga cikinsu ba, domin sun zage iya ƙarfinsu suna yaƙin kare kai. Ƙarshe ma shi Uwais fuka-fukansa ya buɗe ya tashi sama, daga saman yake harbin mutanen da kibiya, yayin da Arman ya bada himma wurin sarrafa takobi daga ƙasa.

Amma kamar ƙara musu yawa ake. A nan ne fa Arman ya fara gajiya, saboda sam shi bai saba ba, hakan ya sa ƙarfinsa ya fara gazawa, har ta kai ga an samu wani a cikin dakarun ya buga masa wani madoki. Da ya yi nasarar kai shi ƙasa, hakan ya jawo glasses ɗinsa suka faɗi ƙasa, duhu ya mamaye ganinsa, sannan takobin hannunsa ma ya faɗi gefe guda.

Dakaren da ya samu nasarar kai shi ƙasa ya tsaya a kansa yana dariyar cin nasara. Adam da Ivana kuwa na gefe suna ganin ikon me duka, duk yanda suke jin ana batun yaƙi a tarihi ne kawai, ashe akwai lokacin da za su tsinci kansu ana yaƙi a gabansu. Ita Ivana Uwais ma ya fi bata mamaki, dan su duka ba su taɓa sanin cewa yana da fuka-fuki ba.

Lokacin da Arman ya faɗi suka ankara, dan haka ita da Adam suka yi wurin domin ceton abokinsu dake laluben glasses ɗinsa a ƙasa, domin ba ya ganin komai, yayin da shi kuma mayaƙin dake kansa ya ɗaga mashi yana shirin soka masa...

“Kai!...”

Cewar Ivana hankali tashe, yayin da ta nufi wurin Arman da gudu, Adam na binta a baya. Sai dai kafin su ƙarasa wurin, wani takobi da aka cillo daya can baya ya caki mayaƙin a ciki... Hakan ya sa suka taka birki suna kallon mayaƙin, yayin da yake silalewa zuwa ƙasa.

Baki buɗe kuma dubansu ya zarce zuwa inda aka wullo takobin, ganin wannan matar ta ɗazu tsaye, kuma riƙe da takobi yasa suke san cewa ita ce wadda ta cillo takobin wannan takobin. Take mayaƙan da abin ya faru kan idonsu ita ma suka far mata, tsayuwarta ta gyara, tare da gyara riƙon takobinta, tana jiran isowarsu, kuma har zuwa lokacin fuskarta a rufe take.

Ai suna isa wurin da take aka fara yaƙin gaske, dan yanda suka baibayeta sai kace za su cinye namanta ɗanye, amma ba ka jin komai sai ƙaran takobinta, daga ta kai suka wuri za ka ga gawa na faɗuwa ƙasa timm. Nan fa wurin ya yamutse, gawawwakin mutanen nan ne kawai suke zuba.

A lokacin kuma Adam da Ivana suka samu isa wurin Arman dake yashe a ƙasa, suka samu suka ɗaga shi zaune, sannan Adam ya ɗaukar masa glasses ɗinsa da glass ɗin frame ɗaya ya fashe, amma duk da haka suka saka masa, domin ya samu ya ga wannan bidirin da ake a filin.

“Sannu Arman”

Cewar Adam yana miƙar da shi. Zaman glasses ɗin ya gyara, yayin da ya tsayar da dubansa a kan matar nan ta ɗazu dake ta'asa a filin wurin, hatta Uwais ɗan kallo ya koma... Domin yanda take sarrafa takobi a wurin ya matuƙar basu mamaki.

*

Arman ya sa hannu ya buɗe kit ɗin glasses ɗinsa, domin ɗaukar wanda ya rage masa, tun da wanda yake tare da shi ya fashe. Guntun glasses ɗin ya ɗauka, sannan ya sa hannu ya cire na idonsa, kana ya saka wanda ya ɗauka, ya maye wurin wanda ya ɗauka a cikin kit ɗin da wanda ya cire a idonsa.

Ya kuma gyara zaman glasses ɗin a idonsa, sannan ya saka yatsun hannunsa a cikin sumarsa da ta yamutse, yana ɗaga kansa, tare da kallon Ivana dake zaune kan sleeping bag ɗinta, dan bayan sun rasa tent ɗinsu a kan sleeping bag ɗin suke kwana. Yanayin zamanta kaɗai zai sa ka gane cewa a gajiye take, domin sai da ta jingina da bishiyar dake kusa da ita, tana bincika wani abu a cikin backpack ɗinta, yayin da suke magana da Uwais.

Ya juya kansa zuwa ɓarin damansa, inda Adam ke zaune a kan tasa sleeping bag ɗin, shi kuma lafiyar camera ɗinsa yake bincikawa saboda ɗazu ba a gama yaƙin nan ba sai da ya ɗaukeshi a hoto. Batun yaƙi da ya gifta a cikin kansa ya sa ya yi saurin kallon wannan budurwar ta ɗazu da ita kaɗai ɗinta ta ƙarar da mayaƙan ɗazu.

Tana zaune daga kan wani itace, ta saka wani ƙyalle tana goge jinin da ya ɓata takobinta mai tsananin kaifi, wanda ta yi ta'asa da shi ɗazu. Hankalinta kwance, kamar ba ita ce ta yi kashe-kashen ba. Har zuwa yanzu da suke zaune a wurin ba ta yi magana ba, hakan yasa suka fara zaton ko kurma ce. Shi kuma Uwais yana daga gefen Ivana, yayin da take masa bayani a kan chocolate ɗin da ta ba shi.

“Miye ma kika ce sunan shi?”

Ya tambayeta yana juya ledar chocolate ɗin. Ivana ta yi murmushi a gajiye, ita ba ita ta yi yaƙin ba, amma haka take jinta a gajiye. Ko wannan tafiyar ƙafan da suke ma ai dole ta gaji, tun da abu ne da ba ta saba ba.

“Shukulata, da turanci kuma Chocolate!”

Ya jinjina kansa yana taɓe baki, sannan ya kaita baki zai ci da ba tare da ya cire laidar ba, ta yi saurin dakatar da shi.

“A'a zai ka cire ledan fa”

Ta karɓa daga hannun shi, sannan ta buɗe masa ledan, shi dai kallonta kawai yake, ta sake miƙa masa.

“Mi ye shi ledan?”

Ta yi dariya.

“Ana sakawa ne domin ya bawa chocolate ɗin kariya daga datti ko cutuka kafin a ci, kuma yana ƙara tsayin daɗewar chocolate ɗin...”

Ya sake jinjina kansa.

“Kuma yana da daɗi?”

Ta gyaɗa masa kai tana nannaɗe gashinta cikin top knot bun. Uwais ya saka chocolate ɗin a baki, sannan a hankali ya gutsira, ya fara taunawa yana juya idonsa.

“Da akwai daɗi ba?”

Ivana ta tambaya.

“Akwai daɗi sosai”

Ya bata amsa yana murmushi. A dai-dai lokacin kuma Arman ya tambayi wannan matar.

“Wacece ke? Me ya sa waɗannan mutanen suka kama ki?”

Tambayar da ya mata ta jawo hankulan sauran. Suka dubeta, cak ta tsaya da goge jinin da take, sannan ta kallesu da idonta.

“SANA!”

Kawai suka ji ta furta, sannan ta sa hannu ta yaye ƙyallen da ta rufe fuskarta da shi, cikin su ukun babu wanda ya santa, amma shi Uwais ya san fuskarta, ba ma ita kaɗai ba, har ma da sauran 'yan uwanta uku babu wanda bai san kamarsa ba, duk da bai taɓa ganinsu ido da ido ba.

“DANEEN SANA BINT MALIK CANGAZ!?”

Shi ne kaɗai abin da Uwais ya samu furtawa.

IQRAH.

Zaune take a wani wuri da aka keɓe a fadar domin shaƙatawa. Akwai wani (Fountain) dake tsakiyar wurin, yayin da (grass carpet) ke zube a ko ina na wurin, sannan akwai iska me daɗi dake busawa a ko ina. Hadimanta na zaune a ƙasa, yayin da suke bata labaran nishaɗi, ita kuma sai murmushi take. Domin duka wasu tsare-tsare da suke ita da Eid na guduwarsu a ranar da za'a ɗaura aurenta ya kamalla, hatta da ƙauyen da za'a ɗaura musu aure Eid ya zaɓa musu.

Yanzu ranar ɗaurin auren kaɗai suke jira, domin sun yanke cewa ba za su gudu ba sai a ranar da za'a ɗaura auren. Buɗe ƙofar shiga sashen da aka yi ya sa hankulansu ya koma zuwa wurin, Asra tare da wasu bayi har uku ne suka shigo wurin. Ko wacce baiwa na ɗauke da wani (tray) da aka rufe da ƙyalle.
Chapter 23 · 0% Book details