← Book details Juyin KwaÉ—o Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 25

Sashe 15

Juyin KwaÉ—o Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani abu ne ya bada sautin tau a ƙirjin Adam, dan zai iya cewa ya riga kowa sauraron shekaru dubu ɗayan da aka furta. Ita kuma Ivana sai ta ji kamar ba ta fahimci abin da yake faɗa ba, saboda kalar larabcin da yake ya sha banban da nasu, nasa kyakkyawan larabci ne irin wanda ke cikin Alkur'ani me girma. Su kuma ba da shi suke magana ba, dan haka kalaman nasa suka mata wuryar ganewa, duk da taso ta gane, amma da ta ɗora maganar a mizanin hankali sai ta ƙi yarda da gaskiyar. Shi ko Arman idonsa ya lumshe kawai, domin tun da ya kalli mutumin ƙwaƙwalwarsa ta fara raya masa hakan, amma ta ya ya ke nan? Ta ya mutumin da yake rayuwa a 21st century zai dawo 11th century?... Taya hakan za ta kansace?...

“Na san cewa ba lalle wannan maganar ta zauna a kanku ba, domin kuna ganin kamar hakan ba me iyuwa ba ne... To yau ya iyu a kanku, kuma wata ƙila ku zamto ababen misali, domin gagarumin abin da za ku tunkara a gaba!”

Dattijo ya sake faɗi. Arman ya buɗe idonsa, sannan ya kalli tsohon.

“Ya za'ayi mu koma gida!?”

Ita ce kawai tambayar da ta zo ransa, dan bayan ita kuma ba ya jin yana da abin faɗe. Tun da ya furta tambayar Ivana ta gaskata abin da datijjon ya faɗa ɗazu, amma ta yaya su da suke rayuwa a zamanin da dogayen gine-gine suka yawaita a ko ina, da wayoyin hannu, da kafafen sada zumunta, da ababen hawan zamani, da ci gaban technology za su dawo rayuwa a zamanin da babu skyscrapers, babu wayoyin hannu, babu ababen hawan zamani, babu... Babu... Babu, babu komai sai yaƙi da rigima a kan mulki!. Shi ko Adam ko motsi bai kuma ba, ya ƙame ne ƙam yana kallon mutumin, saboda shi yana iya jin kyakkyawan larabcin da dattijon ke yi.

“Dogon labari ne, amma zan yi ƙoƙarin gajarce shi, kafin ku koma gida yana da kyau ku san manya manyan masarautu ukun dake mulkin wannan duniya a wannan zamanin!...”

Ta farko MAMLAKATUL MAJDAL, Babbar masarauta ce, wadda a zamanin nan sam babu kamarta, masarautar na da girma da yawan al'umma na ban mamaki. Mutanen masarautar na rayuwa cike da farin ciki da kuma samun ci gaba a ko wani lokaci, domin sun yi sa'a da samun adalin sarki da ya dace da mulkarsu. Masarautar na da tattalin arziƙin noma, kiwo da kuma ma'adanan ƙarƙashin ƙasa, kana gari ne da ya zamto cibiyar kasuwanci.

MAMLAKATUL MAJDAL tana a ta yammacin saharar Majma, ginin masarautar ya sha banban da sauran masarautu, domin a zamanin za'a iya kiran masarautar da ta zamani. Masarautar na kewaye da ganuwa, wadda aka ginata da duwatsu da kuma taɓo.

A batun yaƙi kuwa sun zarce tsara, domin a ƙalla masarautar na da kimanin mayaƙa dubu goma, waɗan da suke a shirya ga mutuwa, ga kuma kayan yaƙi masu firgita abokin gaba. Rayuwa a MAMLAKATUL MAJDAL tana da sauƙi...

Masarauta ta biyu ita ce MAMLAKATUL AFSAH, Babbar masarautar Aljannu dake a cikin gajimare, Masarautar tana da kyau da tsarin gine-gine masu ban sha'awa irin nasu na waɗan da suke ba bil adama ba. A fagen yaƙi su ma ba'a barsu a baya ba, domin suna da dakaru da kuma kayan yaƙin tunkarar duk wani abokin gaba idan yaƙi ya taso.

Masarauta ta uku kuma ta ƙarshe ita ce MAMLAKATUL JIYAD. Babbar masarautar da a masarautun bil adama ta kasance ta biyu. Masarautar da na kyau da kuma albarkatun ƙasa, sai dai kuma sun yi rashin sa'ar shugaba, domin Allah ya hallata musu mugu kuma azzalumin sarki.

Babban sarki me daraja ta farko, wanda bayan shi a iko ƙasaita izza da mulki babu wani a cikin sarakunan wannan zamani, shi ne Malik WASIMUDDEN BIN ABDUL ADAL. Kyakkyawan matashi kuma jarumin yaƙi, sadaukin sarkin da babu me taka shi ya wuce... Shi ne yake mulkin MAMLAKATUL MAJDAL.

A ƙalla shekarunsa talatin da biyar a duniya, ya gaji mulki ne a hannun mahaifinsa, Malik Abdul Adal Abu Wasim, wanda shi ma ya gada daga wurin nasa mahaifin. Ya fara gudanar da mulkinsa tun yana da shekaru asibirin da biyar, hakan ya faru sakamakon mutuwar mahaifinsa a wannan lokacin.

Malik Wasimudeen ba shi ne kaɗai ɗan Malik Abdul Adal ba, domin bayan mahaifiyar Wasimudeen Malik Abdul Adal yana da wata matar, wadda ita ma take da ɗanta na miji guda ɗaya Amir Ehan Ibn Abul Adal.

Malik Wasimudeen adalin sarki ne, wanda yake gudanar da mulkinsa cikin adalci da tausayinsa ga talakawansa, sannan kuma shi dodo ne ga maƙiyansa, ba shi da imani wurin hukunta mai laifi, kusancin dake tsakaninsa da kai ba zai sa ya ɗaga maka ƙafa ba idan har aka kamaka da laifi. A halin yanzu yana da aure, sunan matarsa DANEEN SANAH (Princess Sanah)...

Tarihin yanda wannan aure ya kasance kaɗai abin mamaki ne, domin Daneen Sanah ta kasance 'ya ga abokin gabar MAMLAKATUL MAJDAL, tun zamanin mahaifin Malik Wasimudeen ƙiyayya da mahaifin Sanah ta samo asali. Kuma har zuwa zamanin yanzu da Wasimudeen ke shugabantar masarautar ƙiyayyar ba ta ƙare ba, duk da ya auri 'yarsa kuwa.

Ta wani ɓangaren ma wannan auren shi ya ƙara rura wutar ƙiyayyar, domin Malik Wasimudeen ya auri Sanah ba da son ran mahaifinta ba, amma kuma ita da Wasimudeen suna son juna.

Sarki me daraja ta biyu kuma shi ne MALIK SAFRAZ BIN ANSER, wanda yake mulkin MAMLAKATUL AFSAH. A tashin farko ba za'a kirashi da adalin sarki ba, kuma shi ba mugu ba ne, amma za'a aje shi a sahun masu yin mulkin taka haye. Wanda bai gaji mulki ba, sannan bai iya gudanar da shi ba.

Asalin sarautar ba tasa ba ce, ba kuma ta mahaifinsa ba ce, sarautar ta kasance ta MALIK DHAAKIR BIN AQEED. Babban sarkin aljannu da ba'a taɓa kamarsa ba. Kaf duniyar nan Malik Dhaakir ɗansa ɗaya, wanda matarsa ta haifa masa shi. UWAIS BIN DHAAKIR, Feroza mahaifiyar Uwais ta kasance bil adama, yayin da Dhaakir ya kasance daga jinsin jinnu, hakan ya sa Uwais ya mallaki ƙudurat guda biyu. Ya kan iya yin duk abin da bil adama za su yi, sannan ya kan iya yin wasu abubuwan na aljannu, amma kuma jinsinsa ya fi ƙarfi a bil'adama, domin hatta suffarsa ta bil'adama ce.

A ƙa'ida Uwais shi ke da gadon wannan kujera ta mulki. Amma sai Safraz da mahaifinsa Anser suka shirya maƙarƙashiya, domin ƙwace mulki a hannun Malik Dhaakir. Sun shirya kashe shi yayin da suke tsaka da wani yaƙi. Kuma shirin nasu ya tafi yanda suke so.

Domin sarki Dhaakir ya mutu a wannan yaƙi, bayan mutuwarsa kuma suka shiga aiki kan shirinsu na biyu, wato yanda za'a yi mulki ya dawo hannunsu. Lokacin da 'yan majalissar sarki suka zauna suna tsara wanda ya kamata ace ya zama sarki bayan rasuwar Malik Dhaakir Safraz da mahaifinsa Anser suka bijiro da wata magana.

Ta cewa a shekarun Uwais a wannan lokacin bai kamata ace ya zama sarki ba, domin a lokacin bai fi Shekarau 9 ba, kuma suka ƙara da cewar sam bai kamata bil'adama ya mulki aljannu ba, ai hakan ma zai zama kamar cin fuska ne ga jinsinsu, sannan hakan zubar da ƙima ne.

Haka suka hurewa aminttatun sarki kunne, waɗan da suka ƙi kuma suka basu cin hancin dukiya, har sai da aka amince da sarki na gaba shi ne Safraz. Lokacin da wannan labari ya iske Feroza sai ta ɗauki ɗanta ta gudu ta bar Masarautar.

A lokacin babu wanda ya damu da tafiyarta, sai a ranar da za'a tabbatar da Safraz a matsayin sarki aka zo naiman takobin sarki na mulki aka rasa. Domin Feroza ta ɗauke shi ta gudu, Kasancewar tun kafin Malik Dhaakir ya rasu ya mallakawa ɗanta Uwais shi.

Hakan ya sa aka naɗa Safraz mulkin, amma kuma har yanzu bai zama cikakken sarki ba, domin sai ya mallakai wannan takobin ne zai zama cikakken sarkin MAMLAKATUL AFSAH. Hakan ya sa har zuwa yau hankalinsa ya kasa kwanciya, domin bai huta ba ya ci gaba da naiman Feroza a duniya ruwa a jallo, domin ya ƙwace wannan takobin da ta gudu da shi.

Sarki me daraja ta uku shi ne MALIK CANGAZ, wato mahaifin Daneen Sanah, matar sarki Wasimudeen, kuma shi ne yake mulkin MAMLAKATUL JIYAD. Babban burin Malik Cangaz a duniya bai wuce kada ya tsufa ba, ko kaɗan sarkin ba ya son ya tsufa, duk da a shekaru a ƙalla ya kai sittin da ɗori.

Hakan ya sa idonsa ya rufe ya shiga naiman bokaye da nalaman tsubbu, domin naima masa maganin tsufa a duniya. Duk da magungunan da ake ba shi na sakawa ya dawo yaro ba hakan ke hana jikinsa nuna tsufa ba a wasu lokutan. Domin idan yau ka ganshi yaro, gobe sai ka ga ya rikiɗa ya dawo tsoho.

Kuma sam shi hakan bai masa ba, shi yasa ya ci gaba da naiman maganin tsufa a duk inda yake, da haka har ya samo wata ƙofa, wadda aka sanar masa da cewa daga zarar ya buɗe ƙofar nan ya shiga, da zarar ya fito babu shi babu komawa tsoho har zuwa lokacin mutuwarsa.

Sai dai wannan ƙofar a kulle take, kuma babu wanda ya san inda makullin ƙofar yake. Babu wanda ya taɓa buɗeta, ballantana har a san abin da ke cikinta. Sai dai duk da haka Malik Cangaz bai sare ba, ya sa an kawo masa ƙofar, ya ajeta a cikin masarautarsa, yana naima tare da binciken inda mukullin ƙofar yake, amma har zuwa yau bai samu ba.

Malik Cangaz azzalumi ne na gaban kwatance, domin ko kaɗan ba shi da imani. Bai san tausayin takala da na ƙasa da shi ba, ba shi da wata suffa ta shugaba na gari. Tsabar zalunci irin na sarkin haka kawai sai ya bushi iska yasa dakarunsa su je su tashi wasu ƙauyinka da ba'a yankinsa suke ba, domin kawai a samo masa bayi, ko a samo masa albarkatun ƙasa.

Yana da dakaru na ban mamaki, waɗan da ya shayar da su ruwan zalunci, domin kamar yanda yake haka ya horesu. Uwa uba kuma kuma ga ƙarfin tsafi da yake amfani da shi wurin yaƙar duk wani wanda ya gagare shi.
Chapter 15 · 0% Book details