Sashe 8
Jariri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Goggo ta ce. "Au dan ƙaddara yanzu Halifa sai munje asibitin nan bazaka haƙura ba?" Inno ta kalleshi a watse ta ce. "Yoooo ina zai haƙura yana fama da idanun rashin ɗa'a a tsaye-tsaye bishiyar kuka, Ni bansan sanda yahudu ya lalata mutane ba ace wai Jariri ma sai anyi masa BBC wannan ɗiban albarka har ina? da ruwan zafi zaiji ko da allurai sai kace sanda na haifi ubansa allurar akayi masa, kuma uban me ya same shi Allah ba tuba kowane kibibabbe ya yi ɗiban albarkarsa ya gama." Nusaiba ce ta shigo ɗakin da tawul a jikinta ta fito daga wanka ta tsaya jin abinda su Inno suke faɗa.
Inno kallan Nusaiba tayi tana jan dogon salati tana tafa hannu ta ce. "Nusaiba yau sabon ɗiban albarkar da zaki mana kenan wai ke me miji kin fito gandandan kinyi tsaye kina rangaji a gefensa cikin kissa, bakisan kin haramta agaresa ba, anya Nusaiba zamu iya zaman kwana arba'in a gidan nan kuwa, ummm Allah na tuba nima banda abu na me zan zauna yi a gidan yara tsofai-tsofai da ni, bari ma nayi wanka na kira Salisu yazo ya ɗauke ni ya maidani gida bakina alaikum."
Halifa ya tsuke fuska yace. "Inno wai ya kuke neman haramta mun mata ta ne ina ji ina gani, gaskiya nifa sa idon ku yayi yawa wallahi kawai dan ta fito daga wanka ta tsaya kusa dani shikenan ba matata bace?" Halifa ya ƙarasa Faɗa yana rungumo Nusaiba har tawul ɗin jikinta na niyyar faɗuwa, da sauri Inno da Goggo suka saki wani uvan salato lokaci ɗaya Inno har tana runtse ido Goggo ta ce.
"Oh yau naga abinda zai ƙonemun idani ni Hafshe yau na shiga uku Allah na tuba Alla ka yafe mun" Inna daɓar ta zauna kamar wacce ƙwai ya fashewa a ciki tana zubda hawaye ta ce. "Allah mun tuba nida ƴar uwata kana ganin bamu da laifi a ciki, kai jama'a Allah ka yafemu ni ƴasu yau naga takaina Halifa ashe ɗiban albarkar taka takai haka, wallahi nan dai ba gidan zama bane na rantse da Allah kuyi gaggawar tuba kar fushin Ubangiji ya tabbata akanku sakarkaru marasa ɗa'a" Inno na gama faɗa ta bankaɗa zaninta cikin kajarta ta zura hannu ta ɗauko waya ta miƙawa Halifa ta ce.
"Maza maza kiramun Ubanka tun fushin Allah bai sauka a kanmu ba" Halifa ya tsuke fuska yace. "Bazan kira ba ke ki kirashi mana, ke Nusaiba idan bazasu yi masa wankan ba ki karɓa ki masa ki shiryashi mu tafi asibiti, na lura waɗannan tsofaffun nan gaba kafurtamu zasu fara yi" yana gama faɗa ya fice.
Inno ta rushe da matsanancin kuka ta ce. "Wallahi duk waɗannan maganganun rashin ɗa'ar ka gayawa ubanka Salisu Hansai ki wanke musu ɗa mu wuce dan baza'a dinga aikin kafurci a gabana ba"
Goggo taba ɗau lokaci ba ta wanke Jaririn ta tsane shi a towel ta kwantar da shi akan gado Inno sai aukin danna wayya take, ita dai taga lamba amma batasan ko ta wa ta kira tana ji an ɗaga ta ce. "Salisu duniya da lahira waya halicce mu?" daga cen ɓangaren akace "Allah" Inno tace "To wallahi Idan baka maza kazo ka ɗauke mu daga gidan nan ba sai na ɗebe maka albarka, saboda gidan Halifa sam ba gidan zaman musulmi na gari bane, nikam wallahi har azumi sai nayi na tuba ga Ubangiji wannan saɓon Allah har ina, ace dan jaraba yarinya tana cikin biƙi jage-jage amma yaro na naniƙe da ita to Allah ya yafe musu wannan kam ya riga da faru amma tun kafin fushin Ubangiji ya sauka kazo ka ɗaukeni atoh, yoo Allah na tuba dama fa Jikoki ne banda ma ƙaddara me zai kawo ni gidansu" daga cen ɓangare taji an kashe wayar batare da an amsa mata ba. Inno rushewa tayi da kuka tace. "Amma wallahi Salisu ya iya ɗiban albarka ki duba kiga Hansai wai ni Salisu zai wulaƙanta." tana kuka ta miƙe ta nufi hanyar banɗaki dake cikin dakin ta ce. "Wallahi nan ko gidan Ubana me salati ne na barshi kenan bari nayi wanka na fito" Inno ta faɗa banɗaki tana kici-kicin cire kaya taga Hansai tsaye a gabanta. Zaro ido waje Inno tayi tana dafe ƙirji ta ce. "Yau wata sabuwar ɗibar albarkar kike ji da kika biyo ni har banɗaki ki ga tsiraicina?"
FATAN ALHERI FANS🤣🥰👍🏻
_UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉
[17/10, 16:18] Ameera Adam🌚: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/groups/856755331683130/?ref=share
👹 JARIRI 👹
Labari da Rubutawa: AMEERA ADAM
SADAUKARWA GA ƳAN GROUP ƊINA NA AMEERA ADAM FANS GROUP
GARGAƊI
BAN YARDA A SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA.
11&12
Goggo shiru tayi tana raba idanu sai kuma ta juya ta kallo ɗan Jarirn dake kwance saboda tsoro take a barsu su biyu daga ita sai shi a ɗaki, Inno haushi taji ganin irin diriricewar da Goggo takeyi cikin ƙufula ta ce. "Hansai magana nake kina ta wani waige-waige saboda rashin ɗa'a yanzu inba ɗiban albarka ba me zaki mun a banɗaki tsofai- tsofai da rai, Allah na tuba me zaki gani sabo da baki sani ba? Anya hanyar da kika ɗauko me ɓillewa ce Hansai haka kawai ki kai kanki ga halaka yoo halaka mana duk wanda zai ga tsiraicin wani ai hau ta hau shi" Inno ta ƙara tamke fuska ba alamar wasa ta ce. "Hansai tun ban kai kukuna gurin Ubangiji ba ki fice ki bani guri, wallahi banda ma ina duba zumuncin Allah mu biyu muka rage da tuni na kwashe miki albarka kowa ma ya huta" Goggo gabaɗaya ta tsure ƙasa tayi da murya ta ce. "Wallahi Inno tsoro nake ji ina gudun salawaitun da zai ƙara samuna ni kaɗai a ɗaki" Inno ta keɓe baki ta ce. "Hansai me ye gamunmu dake? Uban me zan miki da kika biyo ni ke tsohuwa ni tsohuwa me zan iya yi miki? Yoo Allah na tuba duk ɗiban Albarkar da za'ayi mana me zan iya? Ki fice mun ki bani guri kar fushin Allah ya sauka a kanki ki jaza mini salalan tsiya" Goggo tayi ƙasa da murya saitin kunnen Inno ta ce. "Wallahi Rakiya Jaririn cen nake ji" Inno wata shewa tayi harda tafa hannu ta ce. "Allah na dawo inji kishiyar me yaji. Wallahi Hansai idan baki fitar mini daga bayi ba sai na kwashe miki albarka kowa ya huta, ke da kika ce Jaririn ya fini sau dubu a gurinki to ahir ɗinki karki kara kusantoni, yoo to Allah na tuba ma wacece ke wacce alaƙa garemu Hansai? Allah ya jiƙan me salati dai nasan Mahaifinmu ne sai Mahaifiyarmu Kande banda wannan ki gaya mini dangantakarmu? Wallahi tun muna mu biyu ki fice mini tun kafih nayo yekuwar neman agaji" Goggo tuni idanunta suka ciko da ƙwallah a hankali ta fara takawa ta fice daga banɗakin tana leƙe-leƙe.
Inno ta ci gaba da mita tana cewa. "Ke kiji mace haka kawai kina gidan jikana ki butulcemun saboda yana da abun duniya, sai da kika kwasowa kanki ɗiban albarka zaki tuno da ni, Astagafirullah ina zaman zamana zata jamin masifa da fushin Ubangiji ta sani magana a banɗaki ban shirya ba, banda ma Allah yana kareni da kariyarsa da tuni Sheɗanu basu nuna mini rashin ɗa'a da ɗiban albarka ba, cen kije ki ƙara ta keda ɗan ƙundalon ya yi duk abinda zaiyi kiki ma, Allah na tuba ka yafe mun wannan zunubin da na ɗauka" Inno ta gyara tsayu ta ci gaba da cewa. "Allahumma inni'azubika minal kubisi walkaba'isi, yoo wayasani ma ko dama cen Hansai ta saba ɗiban albarkan a banɗakin Allah na tuba ko ta iya addu'ar shiga banɗakinma oho" Inno ta ci gaba ƴan ƙananan maganganun sannan ta fara wanka.
Goggo kamar wacce ta haɗa gurmin gulma haka ta dinga sunne kai ƙasa tana juye-juye har ta nemi guri ta zauna, a hankali ta fara satar kallon Jariri da ƙyar tayi ta maza ta ɗauko shi ta fara shafa masa mai, tana cikin saka masa kaya Inno ta fito daga wanka tana watsawa Goggo wani kallo. Wayar Inno ce ta fara ringing da sauri ta ɗaga tana faɗin. "Salisu me kakeyi har yanzu baka ƙaraso ba?" Daga cen ɓangaren aka ce. "Wai ke babu me kiranki a waya sai Salisu ne, ɗazu kin kirani ina hanya kike ta kawo ƙorafi gani na shigo gidan Halifan." Inno ta taɓe baki ta ce. "Wai Ado ne?" aka ce. "Idan kin fito kya gani da idonki" Inno ta katse wayar ta ce. "Yara sai tatalar ɗiban albarka saboda bani na haife su ba sun baidani kamar yawun bakinsu sai abinda suka ga dama zasu gaya mini, kai Allah wadaran naka ya lalace bantaɓa sanin zan samu marasa ɗa'a a zuri'a ta ba. Hansai kiyi ki kintsa mu tafi asibitin nan naji ance ba'a san yiwa yara bbc ɗin nan idan rana tayi" Goggo dai bata kula Inno ba ta gama shirya Jariri ta wuce banɗaki a fakaice take watsawa Inno harara, babu jimawa Goggo ta fito lokacin tuni Inno ta gama shiryawa cikin fallelliyar atamfarta, mayafinta ta ɗauko ta fito falo tana zuwa ta sameshi a zaune shi da Halifa suna hira. Riƙe baki Inno tayi ta ce."Ado ashe da gaske kaine wallahi na ɗauka waya ce ta mun ƙarya da naji kamar muryarka ce" Ado yace. "Inno sauri nake fa na biyo dan nasan idan ban zo ba zaki ɗagawa su Daddy hankali ne ana zaune ƙalau" Inno kan kujera ta hau tana watsawa Ado harara ta ce. "Wannan dai ba halin Muntarina ka ɗauko ba wallahi dama nasan sai iyayenku sunyi muku huɗubar tsiya akaina, Allah ya mun tsari da mugun halinka wato iyaka zaka yi mini da ƴaƴana ko? Tashi ka fice Ado ka ɓalɓace bazan kuma magana da kai ba bansan da wane mugun abun kazo ba" Ado ya miƙe tsaye yace. "Brother gaskiya kana cikin hazo waɗannan kayan ciwon kan haka kake fama dasu" Halifa ta gyaɗa kai fuska ɗauke da damuwa yace. "Bro Adam ya na iya? Haka zanyi haƙuri har lokacin tafiyarsu yayi" Inno baƙin ciki ya cikata jin maganganun dasu Halifa suke yi ta fara matsar ƙwalla ta ce.