Sashe 11
Jariri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Inno ta kalli Goggo da tayi jage-jage da hawaye da majina ta ce. "Banda abin ki ba sai kiyi masa bayani dalla-dalla ba kya yi masa rashin ɗa'a ai sai ki ja ya ɗebe miki albarka" Jariri ya kalli Inno yace. "Kema ina tafe gurinki ki bani ɗiban albarkar da rashin ɗa'ar" gabaɗaya shiru sukayi kamar wanda ruwan ya shanye.
Tsalle ya ƙara bugawa yace. "Naji kunce iyayena sai kun raba aurensu to naga wanda zai fita daga motar." Yana gama faɗa ya murza sitiyarin motar da ƙarfi nan take mota ta tashi ya fara tuka ta da gudun gaske, Inno da Goggo banda gware da kawuna babu abinda suke yi da ya fisgi motar zaka ji kansu ya bada ƙwal sai kaji sun rafka salati, tun baiyi tafiya me nisa ba Inno ta sume a cikin motar.
Halifa na fitowa harabar gurin ya nemi motarsu ya rasa gabansa ne ya faɗi, suka kalli Juna shi da Nusaiba da take jijjiga jaririnta saboda kukan allurar da yake yi, Halifa da sauri ya ɗauko wayarsa ya fara kiran Inno amma ba'a ɗauka ba, ya kira yafi a irga sannan ya kira ta Goggo sai da ta kusa katsewa ta ɗauka, cikin fargaba Halifa yace. "Goggo lafiya naga babu motar kuna ina" Goggo muryar ta da ƙyar take fita saboda wahala ta ce. "Halifa ku kira ƴaƴa da jikoki ka sanar da su mutuwarmu ataru ayi mana addu'o' domin tamu tazo ƙarshe" Halifa yace. "Waye ya ɗauke ku ne wai?" Goggo murya a shaƙe ta ce. "Jaririnka ne ya ɗauke mu yanzu haka sai fafara salawaitun uban gudu yake, ni da kake gani nayi salawaitun suma yafi a irga babu me tayar dani wahala ce kawai take farfaɗo da ni. Ga Inno dai yanzu kam nasan matambaya har sun dira kanta..." Tun bata gama maganar ba Jaririn ya fisge wayar ya kasheta gabaɗaya.
LITTAFIN ANYA BAIWA CE ANA CI GABA DA KASUWANCINSA GAME NEMAN CI GABANSA ZAI BIYA 200 TA WANNAN ACC ƊIN AISHA ADAM 3090957579 FIRST BANK KO KATIN MTN 0706 206 2624
_UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉
[31/10, 19:52] Ameera Adam🌚: FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️
👹 JARIRI 👹
Labari da Rubutawa: AMEERA ADAM
SADAUKARWA GA ƳAN GROUP ƊINA NA AMEERA ADAM FANS GROUP
GARGAƊI
BAN YARDA A SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA.
17&18
*SHIN KUNA DA MASANIYAR YAWAITA SADAKA YANA MAGANIN MUSIBU?SANNAN TAIMAKO BAYA KADAN, A DUK LOKACIN DA KA BAYAR SAI ALLAH SWA YA KARA YASSARE MAKA AL'AMURRANKA, BAYA GA DIMBIN LADAR DA AKA AJIYE MAKA A RANAR DA BABU SHAMAKI GA ZUWANTA.*
*ASSALAMU ALAIKUM*
*'Yan uwana musulmai maza da mata wanda na sani da wanda ban sani ba. Sunana Fatima* *Aminu wadda aka fi sani daUmmu Saddik ga masu bibiyar littafaina. Taimako nake nema kan wata baiwar Allah da ta kuka min da damuwarta.Wata baiwar Allah ce ƙawata aminiyata kuma maƙwafciyata ta shiga wani hali na buƙatar taimako kun san komai ya zama na kuɗi mijinta aka zo har gida aka ɗauke yau kwana 45 ba amo ba labari mutumin Niger ne ba shi da kowa sai ƙanin mahaifinsu kuma basu kula da ita ba baiwar Allah. 'Yaƴan ta uku tana daya daga cikin wadanda Allah ya jarabta da bandit maganar da nake a yanzu mutanen garinsu kaso saba'in da biyar cikin dari sun yi gudun hijira. Yanzu a halin da take ciki ƴarta ba lafiya ko asibiti ba a je ba saboda babu kudin tafiya. Hakazalika abincin da za su ci ma wuya yake mata. Don Allah duk mai niyar taimakawa ya tuntuɓe ni ta wannan number 08146711395.*
*Idan ma ba ka da halin taimakawa don Allah ko da addu'a ce ku yi mata. Allah ya yi mana maganin abin da ya fi karfinmu. Ya yi mana katangar karfe da sharrin wannan zamani.*
👏👏👏👏👏👏
Halifa ji ya yi jikinsa ya yi sanyi tun daga tsakiyar kansa har zuwa tafin ƙafarsa, ji yake kamar ƙafarsa bazata iya ɗaukansa ba. Kiran wayar ya ƙara yi nan take ya ji ta a kashe, Nusaiba ta tambayeshi me yake faruwa. Sai da ya ɗan jingina da bango sannan yace. "Wai kinji Jaririnmu ya tafi da su a mota" zaro ido waje tayi tana daɗa kallan Jaririnta ta ce. "Banda wanda yake hannuna yanzu? To a ina na taɓa ji Jariri yayi tuƙi idan ba aljani ba" Halifa yace. "Gaskiya lamarin ya fara bani tsoro wallahi, anya kuwa babu shafar aljanu a jikin su Inno amma ta yaya su kaɗai a mota za'a neme su a rasa alhalin babu mukulli a hannunsu." Halifa ƙarasawa ya yi gaban wata kwantaina ya yi wa ma kwantainar sallamar sannan yace. "Dan Allah Malam ka lura da wata mota fara bakin glass a gurin da nayi parking, ko ka ga wanda ya buɗe ta?" Me kwantainar yace. "Gaskiya Abokina ban lura ba tunda ka ga nima a bakin neman kuɗina nake" jiki a sanyaye Halifa ya yi masa godiya ya koma gurin da ya bar Nusaiba a tsaye. Jigun-jigun sukayi aka rasa me magana Nusaiba tayi ƙarfin halin cewa. "Habibi me zai hana ka kira su Daddy ka sanar da su wannan fa ba ƙaramar magana bace." Fuska ɗauke da damuwa yace. "Wallahi ina fargar sanar da su saboda Abba da Daddy kinsan kowanne na da hawan jini bansan ma ta ina zan fara sanar da su ba, kinsan dai kowa zan gayawa abin da Goggo ta faɗa bazai yarda ba to ni me ma zan ce musu? Cewa zan Jariri ya ɗauke su a mota ko me?" Nusaiba ta sauke ajiyar zuciya ta ce. "Habibi tafasar tukunya fa ba ta gefe ɗaya bace wannan ba maganar da zamuyi shiru bace, ya zama dole su Daddy su sani.
Hannu ya zura a aljihu ya ɗauko wayarsa ya kira lambar mahaifinsa, sai da ta kusa katsewa yaji anɗauka. Kamar me ciwon baki haka ya buɗe baki a hankali yace. "Daddy barka da safiya" daga cen ɓangaren Daddy ya amsa sannan Halifa yace. "Daddy dama nace dama... dai.." Daddy yace. "Halifa lafiya kuwa duk naji ka wanj iri" Halifa ƙarfin hali ya yi ya sanarwa da Daddy halin da ake cikin, cikin tashin hankali Daddy ya dinga maimaita, " Innalillahi'wa ilahirraji'un" Daddy ya ci gaba da cewa. "Yanzu kuna asibitin ne?" Haliha yace. "Eh muna cen Daddy" Daddy yace. "Ka nemi securities ka sanar da su abin da ya faru dan suyi gaggawar sanarwa da hukumar asibiti yanzu zan kira Yusuf na sanar da shi halin da ake ciki daga nan zanje Bompai nayi report, inyaso sai ku wuce gida" Daddy bai jira cewar Halifa ba ya katse wayar.
Kamar yadda Daddy ya gayawa Halifa haka ya samu securities ya sanar dasu nan take maganar ta zagaye cikin asibitin, Halifa da Nusaiba adaidaita sahu ya tarar musu suka wuce cen gidan Mahaifinsa, lokacin da suka je suka samu mutanen gidan duk sunyi jigun-jigun saboda tashin hankali.
Lokacin da Jaririn ya fisgi wayar hannun Goggo kusan mutuwar zaune tayi, gashi sai fafara uban gudu yake dasu kamar zai tashi sama. Goggo tun tana iya ihu har tayi laƙwas ga kanta da ƙeyarta duk ta gwabje da jikin motar, daga gefen goshinta har kumbura gurin ya yi.
Kai tsaye bai wuce ko'ina da su ba sai gidan Halifa yana yin parking da sauri ya sauka ya fita, Goggo bata iya komai sai ido da take binsa da shi tana kallan ikon Allah, yana zuwa bakin ƙofa ya kallin kwaɗon da aka rufe gate ɗin yasa baki ya fisgoshi memakon ya wurgar dashi sai kawai ya haɗiye, Cikin Gwaggo ne ya hautsine, nan take ta fara sakin fitsari jikinta na karkarwa.
Daga gurin da yake ya buga tsalle kamar ƙwallo sai gashi a cikin motar yana shiga ya fisgi motar ya wuce cikin gidan da gudu, wannan karan Goggo kan Inno ta faɗa saboda yadda ya fisgesu da ƙarfin gaske, yana shiga ya yi parking ya yi tsalle ya fito daga motar hanyar falon Nusaiba ya nufa yana dafe ƙeya haɗe da tura ciki gaba yana wata irin shakiyyar rawa, kamar wani ɗan ƙwaya haka ya dinga layi sai ya yi gaba sai ya dawo baya har ya shige gida. Goggo duk yadda taso buɗe motar abin yaci tura wayarta ta hango a cen gefe da sauri ta ɗauka ta kunna ta, sashen kira ta nufa tana danna labar tayi dace da lambar Halifa, bugu ɗaya taji an ɗauka.
Goggo ƙasa tayi da murya kamar me raɗa ta ce. "Dan Allah ko waye a layi ya gaggauta zuwa gidan Halifa ya ɗauke mu nida ƴar uwata" Halifa yasan dai Goggo magana take yi amma sam bayajin me take faɗa. Da sauri yace "Goggo ce? Yanxu kuna ina?" Goggo satar kallan ƙofar da Jariri yabi tayi cikin raɗa ta ce. "Halifa ba sanya zakuyi ba kuzo ku fitar dani dan ƴar uwata tuni nasan matambaya sun dafe ta" sai a lokacin Halifa yaji shima sai da yasa a speaker.
Da murnarsa yace. "To kuna ina yanzu zan zo" Goggo ta ce. "Gamu a gidanka idan kuka yi jinkiri nima sai dai ku ɗauki mushe dan Rakiya kam tuni tayi mushe" Halifa na jin haka ya katse wayar da murna ya fara sanarwa da mutanen gidan, Halifa da Adam ne suka taho gidansa.
Halifa na zuwa ya tarar da ƙofa a buɗe da sauri suka shiga gidan, Halifa na zuwa bakin motar ya sa key ya buɗe da sauri Adam ya zagaya ya buɗe murfin motar ya tallafo da ta jima a sume. Goggo na ganin an buɗe murfin motar ta fito da sauri ko bi ta kansu batayi ba ta nufi bakin gate da guje, Halifa ne ya biya yana kira ta waigo ta ce. "Har abada na bar salawaitun gidanka da motarka gwara na shiga duniya na yi mushe a hannun ɗan iskan salawaitun gidanka." Tana rufe baki ta bazama waje a guje Halifa ya rufa mata baya.
🤣🤣🤣🤣 KU TARO GOGGO KAR TA FAƊA SALAWAITUN RAYUWA A ƊEBE MATA ALBARKA
_Ummou Aslam Bint Adam_
[02/11, 19:22] Ameera Adam🌚: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/groups/856755331683130/?ref=share