← Book details Jariri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 20

Sashe 6

Jariri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Inno ɓingirewa tayi a ƙasa ta zuba wani uban salati tana kuka, Goggo ce ta ɗagota zaune itama tana share nata hawayen. Inno kallan Daddy tayi ta ce. "Salisu wallahi idan Halifa ya shiga duniya sai na ɗebe maka albarka, yanzu dama baka ƙaunar Halifa ban sani ba a gabana zaka koreshi ya shiga duniya saboda rashin ɗa'a" Daddy yace. "Inno ke fa kika ce ya fita daga rayuwarki nikuma duk abinda bakya so nima bana sanshi..." da sauri Inno ta ce.

"Ittaƙillah ittaƙillah wallahi karka mun sharri oh na shige su ni jikar mutum huɗu, yanzu haɗani zakayi da yaron nan da uwarsa, jikan nawa na cikina zaka ce bana ƙauna?" Wallahi Salisu idan baka dawo da yaron nan ka fice daga gidan nan ba sai na kwashe maka albaka, ni bansan wacce uwar ma zakuyi mana ba muna zaman lafiya nida ƴan jikokina da farar safiya kuzo ku kawo mana tarzoma"

Goggo ta karɓe zancen da. "Wallahi Rakiya barni dasu Allah yaran nan hukuma ce zata rabamu da su" Abba ya kalli Halifa yace. "Ka wuce cikin gida ka ajiye jakar nan" Halifa murmushi yayi saboda yasan dama Daddy da biyu yayi haka sai yace. "Abba ku bari kawai na tafi gwara na shiga yawon duniya" ya faɗa yana murɗa kofar.

Inno ta kuma matso ƙwallah tana jan majina ta ce. "Allah ya tsinewa yawon duniyar ni ɗin banza da wofi wallahi kanasa ƙafarka ka fita daga gidan nan sai na kai ƙarar Ubanka gurin hukuma, ni zaka tozarta ka ɗebewa albarka ku tashi ku bar gabana kuma ko a mafarki karna ƙara ganinku a gabana, yo dama me kake mun Allah na tuba ba Halifa ne yake mun komai ba, badan shi ba da nashiga wani hali tunda shine uwata shine ubana." Daddy na shirin magana suka ga Inno ta miƙe zata fita da sauri Halifa ya dawo yana sauke jakarsa.

Goggo tsuke fuska tayi ta kalli su Abba ta ce, "Ku fice daga gidan jikana tun kafin na ɓata muku rai da sabon salawaitun rashin mutumci, haka kawai zaku zo ku hargitsa mana gida muna zaune lami lafiya."

Su Daddy miƙewa sukayi suka fita suna murmushi ƙasa-ƙasa Inno ta ɗaga murya ta ce. "Kuma ko a mafarki kar na ƙara ganinku idan ba haka ba na ɗebe muku albarka marasa ɗa'a kawai." Suna fita Goggo ta rufe kofa ta wuce ta ɗauko ruwan wankan Jariri ta wuce ɗaki dan tayi masa wanka. Goggo ta fara yiwa Jariri wanka ta ga ya ƙura mata ido yana kallo hura masa idon tayi da bakinta, nan take yayi tsalle ya ɗafe bakinta tana shirin kurma ihu ya saketa ya dinga tsalle a cikin ruwan kamar ana wulla ƙwallo, daga cikin robar tsalle yayi ya fara ɗafe labulewa daga kan wannan ya faɗa kan wannan, yana faɗowa daga kan labule ya fara fisgar zanin gado yana bankaɗawa yana shigewa yana fitowa, fitowa yayi daga cikin zanin gadon ya hau kan ƙafafuwan Goggo yana tsalle, daga ƙarshe zaninta ya bankaɗa ya shige ciki, wani uban ihu Goggo ta zunduma ta ce. "Ku dubi Allah karka shige mun oh na shigesu yau ga sabuwar salawaitun rashin ɗa'a da iskanci jama'a kuzo zai illata ni."

FANS BA ZAN DINGA POSTING KULLIN BA SABODA LITTAFIN KUƊI DA NAKE YI, ZAN DINGA SAKAR MUKU KO SAU HUƊU A SATI NE.

_Ummou Aslam Bint Adam_😉

*FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️

*ANYA BAIWA CE?*

Na

*AMEERA ADAM*

https://chat.whatsapp.com/DgpHYMMtvIeCjKQQDbsBPN

_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, GAME BUƘATAR VIP POSTING SAU BIYU A RANA ZAI BIYA 400, GABAƊAYA ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 0706 206 2624,DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._

FREE PAGE 3

Ajiyar zuciya Fulani Maryama ta sauke sannan ta ce masa, " Wace ce yarinyar? Kuma daga wane gurin zata xo? Babu damar dakatar da zuwan nata? Ya za'ay na gane ita ce dan na ɗauki matakin daya dace akanta?? "

Boka ya ce, " Daga ni har sauran matsafan duniya babu wanda ya isa ya ja da yarinyar domin ita ɗin FILSIFI ce, abinda muke kira da FILSIFI kuwa aharkar bokan ci, tarraya ko haɗakar shuɗaɗɗun ruhika mabanbanta daga jinsi Mabanbanta, zo ki duba nan " ya ƙarasa faɗa yana buɗe mata wannan jan littafin da ke gefensa.

Zanen wasu matasan mata ta gani guda uku sai dai duk cikinsu babu wacce zanen fuskarta ya fito sosai daga ƙasan kowacce anrubuta wani irin gwamammen rubutu, ta farko ya fara nuna mata yace, " Wannan da kike gani ita ce Muhaibish ita ta rayu ne tsawon dubbannin shekarun da suka gabata, Ƴar Sarkin jinsin Fararen Aljanun ƙarƙashin ƙasa ce, tunda take bata taɓa taka doron ƙasa ba "

Zaro idanu Fulani Maryama tayi tana mamakin abinda ya faɗa, ta biyu ya nuna mata ya cigaba da cewa, " Wannan kuma sunan ta Kalimsiyat Ƴar sarkin fararen Aljanu ce amma ta nan doron ƙasa itama ta rayu atsawon dubbanin shekaru, acikin wani littafin bincike na karanta cewar ta yi rayuwa ne tun bayan zuwan Annabi Yusuf (A.S) ita kuma tunda ta ke bata taɓa nutsawa ƙarƙashin ƙasa ba a matsayinta na jinsin aljanu, kuma ita Kalimsiyat mace ce mara haƙuri mai faɗan gaske, kuma abinciken da nayi dukkan su biyun kashe su akayi bisa doron zalinci, kuma abinda zai baki mamaki kusan duka ruhinsu guda ne, sai dai banbancin nahiya da zamani.
Sai ta Ukun su ita ce aka ce zata xo aƙarshen zamanin nan, sunanta Rayzuta ita ta haɗa dukkan abubuwan da waɗancen suke dashi harma da wanda suka rasa, ƴar baiwa ce me ɗauke da ɓoyayyun al'amura, ita kanta batasan da wannan baiwa tata ba."

Yana rufe baki cikin azarɓaɓi Fulani Maryama ta ce, " To itama ta ukun nasu Aljanar ce? kuma meye alaƙar su da junan su? Kuma meye alaƙarta da gidan masarautarmu? "

" Maryama kenan azarɓaɓin me kike yi? Ai duk gaggauwar asara ta jira samu, kuma duk gaggawar unguwar zoma ta jira a haihu, mai kike ci ne na baka na zuba inkinyi haƙuri sannu-sannu bata hana zuwa sai dai adaɗe ba'a je ba "

Murmushin tayi sannan ta bashi amsa da, " Hmmm Marduska ai Ranar biyan buƙata rai ba'a bakin komai yake ba, na ƙagu na ji matsayin Yarinyar da ka ce da kuma ya alaƙarsu ta ke? "

Marduska ya cigaba da cewa, " Har zuwa wannan zancen da nake miki ruhin su na nan ya wanzu a dora ƙasa, sai dai babu inda zasu ya da zango sai akan cikon ta ukunsu, kuma ba kowa bace cikon ta ukunsu sai Yarinyar da nace miki karki sakankance har ta shigo Masarautar ku, har yanxu mudubin tsafi na ya gagara gano mun mutum ce ko kuma itama tana cikin jinsin Aljan, sai dai bincike ya nuna akwai wani ɓoyayyen al'amar dake bibiyar jinin zuri'ar sarki Aminullahi "

Damuwa ce ƙarara a fuskar Fulani Maryama ta kuma jefo masa tambaya, " Ita yarinyar ba dama ka nuna mun hoton fuskarta yanda zan gane kamaninta? "

Mudubinsa ya janyo ya fara wasu surutai yana watsa masa wani ruwa mai yauƙi, wata irin ƙara suka ji ta tsagewar mudubin har sai da suka tsorata, cikin damuwa Bokan ya ce, " Gaskiya gaba ɗaya aikin da kika zo dashi akwai damuwa da tashin hankali, haka kawai banci nanin ba nanin zata ci ni, na dakata akan binciken Yarinyar nan saboda ceton rayuwa ta "

Abin duniya gaba ɗaya ya dami Fulani Maryama amma duk da haka ba ta gushe ba tana faɗin, " Ka taimaka mun kayimun wani abu, ni da kai kaɗai na dogara "

Wani mugun kallo ya bi ta dashi sannan ya ce, " Baki da hankali ne a gabanki munanan abubuwa suka faru amma zaki ce na taimaka miki kinga idan kinganni a lahira kaini akai, babu uwar da zan iya taimaka miki, bincike na biyu da zan gaya miki shi ne, idan kika sa aka fitar da shi tun yana jariri to ba makawa acikin ƙasa da makwanni goma zai faɗa gurin da zai gamu da ita wannan yarinya kuma dawowarsu shi da ita bazai miki daɗi ba, dabara ta ragewa mai shiga rijiya..."

Zufar dake goshinta ta goge sannan ta ce masa, " Marduska wai dole sai akaina wannan masifun yarinyar zasu sauka? Kaina ya kulle fa, dan Allah ka bani mafita..." katse ta yayi da ƙarfin gaske yana cewa, " Da alama kin manta dokar kogon dutsen, azaba ta gaggawa zata iya wanzuwa agareki " sunkuyar da kai ƙasa tayi ta ce, " Tsafi ya dafa tuba nake bokana Sarkin bokayen duniya, ina gwanin wani ga nawa Aljani Garbunsa ya ƙara ja da zamanin ka "

Motsa bakinsa yayi alamar jindaɗi sannan ya ɗauko wani ruwa dake cikin tukunyar ƙasa ya ɗaga shi sama da hannunsa ya fara surutunsa na tsafi, ya jima ahaka sannan ya sauko da shi ya leƙa wani tiriri ne yake fitowa, sai da ya gama kallon ƙwaryar ya ce, " Akwai wasu ɓoyayun al'amura mai tafe da sarƙaƙiya, da alama shuɗaɗɗun abubuwan baya ne zasu iya dawowa wata ƙila Tarihi ne zai kuma maimaita kansa, amma bani da tabbas harsashe ne nayi, ƙarɓi wannan " Ya miƙa mata wata manyan layu sannan ya cigaba da bayani.
Chapter 6 · 0% Book details