← Book details Jariri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 20

Sashe 3

Jariri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

SADAUKARWA GA ƳAN GROUP ƊINA NA AMEERA ADAM FANS GROUP

GARGAƊI
BAN YARDA A SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA.

3&4

Inno kan katifar da Goggo take kai ta faɗa jikinta na ɓari tana ƙoƙarin fisgar bargon saboda ceton ranta, Goggo wani uban salati ta rusa wanda yasa Nusaiba miƙewa zumbur ta tashi zaune, Inno banda ihu babu abinda takeyi tana kabarbari.

Cikin magagin bacci Goggo ta ce, " Oh nikam na shige su yau me nake ji kwarto da tsohon daren nan, yo ni Allah na tuba banda lalacewar kwaratan zamani me zai yi da tsohuwa? Gabaɗaya komai ya saki kamar robar wando..." bata ƙarasa faɗa ba Inno ta ruƙunƙumota sakamakon buɗe bargon da tayi sukayi ido huɗu da jaririn da yake ta washe mata wawulan bakinsa yana ƙara dafe ƙeya, haɗe da wata irin tafiya me tafe da rangwaɗa.

Goggo ta kuma mirtsike idanu ta ce, "A'uzubillahi minasshaɗanirrajim Rakiya tashi kiji yau za'a nuna mun salawaitun iskanci ido biyu, oh ni ɗiyar Mahammadu ka rasa wacce zaka afkawa sai ni tsofai-tsofai da rai wannan ai sai dai ka kasheni da raina." Nusaiba ce ta janyo wayarta da ke ƙasan fulo ta haska gurin su Inno. Ganin Goggo da Inno kaɗai a gurin Nusaiba taja tsaki ta ce, "Dan Allah Goggo da tsohon daren nan zaku dinga mana ihu ba sai a zaci da gasken kwarto bane ya shigo" Firgigit Goggo ta mirje ido raɗau ta kai kallanta kan Inno, a hassale ta fisge bargon ta ce. "Rakiya wani sabon salawaitun kika samo zaki hau wani fisge-fisge cikin dare?" Inno tana ƙoƙarin ƙara danna kanta cikin bargo ta ce, "Karki buɗe ni Hansai yana nan bina yake wallahi aljani ne ba mutum ba" Goggo ta ce, "Yo nikam yau na gode Allah Inno wai ko gamo kikayi ne?"

Inno ta gyaɗa kai har lokacin jikinta rawa yake ta ce, "Wallahi Jaririn Nusaiba ba mutum bane aljan ne shi ne ya biyo ni" Da mamaki Nusaiba ta kalli jaririnta dake kwance yana shaƙar bacci ta ce, "Wai Inno ko dai mafarki tayi ne take mana magagin bacci har da sumbatu?" Goggo ta ce, "To gane mun hanya dai ƴar nan?" Nusaiba zata yi magana Halifa ya shigo sanye da jallabiyya da waya a hannu yace. "Nusaiba lafiya nake jiyo ihun Inno?" Goggo ta ce, "Ina fa lafiya gamu a zaune cikin taraddadi da salallami" zaro ido ya yi yace. "Me yake damunta?"

Goggo ta ce, "Wai jaririn cen ta gani ya biyota shine ta zo ta shige bargo ni bansan wane irin salawaitu bane, ace jariri ya taka ƙasa kwana ɗaya da haihuwa." Halifa yace, "Ruɗewa ce kawai irin ta Inno amma wannan ko ɗan goye ai bazai yarda da abinda ta ce ba. Ku rarrasheta kunsan dai halinta da raki" Inno ta ɗago da kai ta ce.

"Halifu wallahi wannan ɗiban albarkar baza'ayi dani ba, maza ka kira mun ubanka Salisu a daren nan yazo ya ɗauke ni mu tafi gida, wannan rashin ɗa'ar har ina?" Halifa yace, "Haba Inno kinsan me kike faɗa kuwa karfe biyun dare fa. Gaskiya ni bazan kira Daddy yanzu ba haka kawai a tayar musu da hankali, ki dinga abu da lissafi mana" Inno hawaye ta fara yi ta ce, "Halifa ni kake gayawa haka saboda nazo gidanka ko? Yoo wace uwa ce ma a gidan naka gida kamar akurkin kaji, kasan gidan Salisu ya zarce naka ɗari bisa ɗari har kake wulaƙanta ni saboda ɗiban albarka. Har abada bazaka ƙara ganina a gidanka ba, ai laifin Salisu ne da na dage zan zauna wankan jegon nan ba sai ya mun nasiha ba a matsayinsa na ɗana, Allah na tuba tsofai-tsofai dani banda rashin imani wane irin zaman wanka zanyi yanzu, ai Halifa kaine ma babban mara imani na tabbata da uwarka Halima ce ta kai shekaruna bazaka bari tayi wannan aikin wahalar ba, wallahi idan baka kira mun Ɗana ba sai na kwashe maka albarka a daren nan kowa ma ya huta." Halifa ya tsuke fuska yace, "Inno dan Allah dare ne fa yanzu karki tashi moƙota ki bari zuwa safiya inyaso duk yadda za'ayi sai ayi, amma sai magana kike da ƙarfi haba dan Allah dama akwai wanda ya miki dole ki zauna ne?"

"Hansai dan Allah ki ɗauko madoki ki bashi duka na kawai ya rage kayi Halifa, wallahi duk masifarka babu mai hanani tafiya a daren nan shima uban naka zan kirashi idan yace bazai zo ba nayi tafiya ta cikin duniya. Dama wa nake da shi Allah na tuba daga Allah sai ma'aiki" Nusaiba cikin ƙosawa ta ce. "Inno dan Allah kiyi haƙuri zuwa safiya idan fa aka kira Daddy yanzu sai ya ɗauka wani abun ne kinsan yana da hawan jini, kar a tayar masa da hankali a samu matsala"

Inno sakin baki tayi lokaci ɗaya ta ɗauki wani salati gabaɗaya suka tsaya suna kallonta, sai da ta dire ta ce,"Nusaiba amma Allah wadaranki ke kam anyi gantalalliya bansan wacce irin yarinya bace me mugun alkaba'i, aniya bi aniya. Aniyarki ta biki Salisun kike ja wa wannan mugun ciwon saboda ɗiban albarka, to bakinki ya faɗa kanki muguwa kawai anya ke jinina ce kuwa kike nufina da sharri amma dai anyi maras ɗa'a" Halifa ya shigo ɗakin cikin takaici amma sai ya tausasa murya saboda yasan indai ta haka ne sai su kwana Inno bata daina musu sababi ba yace.

"Inno waya hallicemu wa muke bautawa?"

Inno ta kalleshi baki a sake ta ce, "Halifa kafurta ni zaka yi to wallahi ko Ubanka da addinin ya ganni bare kai gantalalle" Halifa bai kulata ba ya cigaba da cewa.

"Ki dubi girman Allah Inno kiyi haƙuri zuwa safiya kinsan dai Allah yafi kowa, na haɗa ki da shi ki bari zuwa safiya mayi maganar"

Inno ta ce, "Au Halifa haɗani zakayi da Ubangiji na? Wallahi ba dan Allah ba da adaren nan zan tafi kowa ma ya huta, tunda banida kowa babu mai ƙaunata." Goggo ta fara matsar kwallah ta ce." Rakiya karki mun haka saboda Allah idan kika shiga gari ina na kama ina zani wa nake da shi? Mu biyu kaɗai fa muka rage kema in kika tafi ya zanyi?" Inno ta taɓe baki tayi ta ce.

"Hansai dama wace alaƙa garemu? To nasan dai uwarmu ɗaya ubanmu ɗaya bayan haka fa? Da kinsan da haka kina ji Halifa na kwashe mun albarka kikayi shiru saboda rashin ɗa'a. Wallahi kunci daraja ɗaya amma zuwa safiya zanga uban da zai hanani tafi" Ta ƙara matsar kwallah ta ce.

"Dama nasan Nusaiba ba ƙaunar zamana take ba waya sani ma ko ita ta turo ɗan ta ya tsorata dan na bar gidan jikana" Nusaiba zatayi magana Halifa ya ɗaga mata hannu yace.

"Inno yanzu koma dai meye kiyi haƙuri badai Daddy kike so a kira ba? To Allah ya kaimu safiyar duk abin da kike so za'ayi." Inno ta ce "Shikenan Allah ya kaimu kuma wallahi tas a kunnensa duk ɗiban albarkar da kuka yi mun" tana gama faɗa ta koma ta kwanta.

Goggo ma ta koma ta kwanta Halifa ya ƙarasa bakin gadon Nusaiba yana shafa jaririnsu cikin so da ƙauna, Goggo ta ɗago ta tafa hannu ta ce.

"Halifa wata sabuwar salawaitun fitsarar zaka yi wa ƴar mutane a gabanmu, wallahi a hir ɗinka fita ka bamu guri ba nace maka yarinyar nan haramiyarka bace har sai tayi arba'in." Halifa tsaki ya yi zai yi magana Inno ta ɗago ta ce.

"Halifa wannan jarabar har ina kai amma gaskiya albasa batayi halin ruwa ba, lokacin da uwarka Halima ta haifeka sai da ta yi wata biyu cir a gidansu, zaka fice daga ɗakin nan ko sai na ɗebe maka albarka kowa ya huta?" Halifa kamar ya yi kuka saboda takaici Nusaiba zatayi magana ya mata alama da ido, cikin takaici ta gyara kwanciyarta ta kwanta Halifa ya fice yana ƙunƙuni.

Washegari da sassafe Inno ta fito falo ta fara ƙwalawa Halifa kira, cikin bacci Halifa ya fara jiyo muryar Inno na kiransa. Guntun tsaki ya yi ya ƙara jan bargo ya rufa bai yi aune ba yaji ta fara buga ƙofarsa da ƙarfi tana cewa.

"Halifa ka kira mun Ubanka kace ina nemansa maza-maza yazo" Halifa ba yadda ya iya ya fito fuska a tsuke ya karɓi wayar Inno ya nemo mata lambar mahaifinsa ya kira.

Inno na jin an ɗauka babu ko sallama ta ce, "Salisu dan Allah maza kazo gidan nan ga ɗan ka sai tijara yake mun tun tsakar dare, kazo ka bi mun haƙƙina dan maganganun da ya gaya mun ƙiris ya rage ciwon zuciya ya kama ni, wallahi ko maƙiyina bana fatan a gaya masa kwatankwacin abin da Halifa ya gaya mini" daga cen ɓangaren Daddy ya ce.

"Gaskiya bai kyauta ba amma kiyi haƙuri Inno me ya faɗa miki inyi masa faɗa" Inno ta saki baki ta kalli Halifa cikin ƙufula ta ce.

"Allah ya tsinewa faɗan da zaka yi masa Salisu" nan take ta rushe da kuka ta ci gaba da cewa. "Yanzu duk ɗiban albarkar Ɗanka ya mun a iya faɗa kawai zaka yi masa saboda rashin ɗa'a. Kayi zamanka na yafe dama na lura ba ƙaunata kake ba kafisan Ɗan akaina, wallahi daga yau Salisu ko a mafarki kar inƙara ganinka a gaba na. Ƴar uwata Hansai ta isheni rayuwar duniya dama tare kuka ganni da ita, Allah na tuba dama wacce tsiyar kuke bani. Ƴar uwata dama ita ce rufin asirina"

Daddy yace. "Ayi haƙuri gani nan zuwa yanzu..." Inno bata jira ƙarashen zancen ta ba ta kashe wayar. Halifa na tsaye ya cika fam banda harara babu abin da yake aika mata.

Inno kallan sa tayi sheƙeƙe sai kuma ta wuce kitchen ta ɗauko muciya, dai-dai ƙafafuwan Halifa ta zauna ta ajiye muciyar tace. "Idan baka mun duka ba ka raina ubanka Salisu kuma wallahi bari ya zo gidan nan a gaba na sai na sa ya kwashe maka albarka kowa ya huta" Halifa ya ja dogon tsaki yace.
Chapter 3 · 0% Book details