Sashe 12
Jariri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
GARGAƊI
BAN YARDA A SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA.
19&20
Adam da ke riƙe da Inno gyara mata kwanciya ya yi a akan kujera shima ya rufa musu baya dan ganin an shawon kan Goggo, dan tun da tace bazata bisu a mota ba sun san ta zauna kenan. Halifa na ganin Adam na binsa ya wurga masa key yace. "Maza ka taho da motar, sai ka rufe gidan."
Adam ɗaukan mukullin ya yi ya juya ya tayar da motar sannan ya fito ya koma ya janyo gate ɗin ya rufe ya zura sakata sannan ya shiga ta ciki ya buɗe ƙaramar ƙofar ya fito yana fitowa ya datse ta da ƙarfi.
Halifa bai taɓa sanin Goggo na da gudu haka ba sai da wannan tseren ya haɗasu, da ƙyar ya sha gabanta yana haki yace. "Goggo dan Allah ki tsaya kiji, yanzu idan muka koma gida babu ke me zamu cewa su Daddy?" Goggo itama mayar da numfashi take saboda tsabar gudu zaninta ya tattare ya koma kusan gwiwa, takalmanta duk sun shige wajen idanun sawunta kamar yadda yara suke zura ƙafafuwansu cikin igiyoyin takalmin. Sai da ta ja numfashi ta ce. "Halifa kasan Allah yau ko Ubanka Salisu ne yazo bazan shiga motarka ba, haka kawai hatsabibin yaro sai nuna mana salawaitun siddabaru yake yi. Kai bari ma kaji muddin muka koma gida ana yiwa Rakiya sutura zaka sakar mini jika" Goggo na zuwa nan ta fara ƙwallah tana cewa.
"Allah sarki Rakiya ke kuma ta wannan hanyar tazo miki. Mutuwa kenan rigar kowa Halifa wallahi tsakanina da kai Allah ya isa da baka yiwa Nusaiba ciki ta haihu ba ai Ɗanka bazai kashe mini ƴar uwa ba. Kaico rayuwa zan idar da salawaitun tsautsayin da ya sameni ni ɗiyar me Salati." Haushi ne ya fara kama Halifa yace.
"To muje idan munje gidan duk abinda kika ga dama sai ki faɗa, amma wallahi idan sama da ƙasa zata haɗe ba wanda ya isa yasa na saki matata. Kuma karki ƙara yi mini Allah ya isa haka kawai tsofaffi kwata-kwata bakinku baya furta alheri." yana rufe baki Adam ya ƙaraso da motar ya kashe ta sannan ya fito ya zagayo gurinsu.
Goggo tana daga tsaye ta faɗi daɓar irin zaman ƴan bori, hannu ta ɗora aka ta fara kuka kamar wata ƙaramar yarinya, Adam ne ya tambayi dalilin kukanta aikuwa kamar me jira ta kuma rushewa da kuka ta kalli Adam ta ce. "Adamu wai yau ni Halifa ya nunawa salawaitun iyakata. Ya nuna bani na haifi ubansa ba har yake yi mini salawaitun rashin kunya. Maza ka bashi mukullin motarsa ta tun bai rufeka da salawaitun duka ba ya ƙwaci abinsa" Adam yasan rikicin su sarai dafe kai ya yi ya ce.
"Goggo dan Allah ki tashi mu tafi kinga mutane sun fara kallonmu..." A hassale ta katse shi da cewar.
"Adamu wacece ni a gurinka?" Adam a daƙile kamar zai yi kuka yace. "Wace ce kuwa ban Kakata" Goggo sakin baki tayi tana rafka salati sai da ta gama cikin ƙunci tace.
"Haka kake bawa Nadabo amsa dama, gatsal ba ladabi ni kake cewa haka kamar bani da wata salawaitun alaƙa da kai." Goggo ta rushe da kuka tana share majina da gefen zaninta tace.
"Allah na tuba dama wace salawaitun alaƙa garemu? Na san dai nina haifi Ubanka Nadabo bayan wannan sai me kuma? Dama nasan tsaf sai ka kwaso mugun halin uwarka dan wannan ba salawaitun halin Nadabo bane."
Ana cikin haka ya hango Ɗan sahu da sauri ya tsayar da shi dukda Goggo ta ƙona masa rai yace. "To muje ga Adaidaita sahu nan na taro mana" alama ya yiwa Halifa yana miƙa masa mukulli.
Goggo ta yunƙura ta miƙe tana cewa. "Haka kawai da ka nacewa motar kamar gadon ubanka. Me ake da Halifa ni da Ɗansa ya kashe mini ƴar uwa wallahi har abada Halifa ka ƙara yi mini salawaitun magana sai na ɓalɓalce ka."Halifa ƙwafa ya yi bai kulata ba ya shiga mota ya bata wuta ya barsu Goggo anata kiciniyar shiga Adaidaita sahu.
Halifa shi ya riga su Goggo zuwa gida lokacin da suka ƙarasa ana ta kiciniyar kwantar da Inno akan tabarma, Goggo na shiga taje gabanta ta fara matsar ƙwallah.
Ruwa Mommy ta ɗebo aka fara yayyafawa Inno a hankali ta fara buɗe idonta, cikin juyewar kai ta fara kallansu da suke tsaitsaye akanta. Ɗago hannuwa biyu tayi alamun roƙo tace.
"Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Annabi muhammadu bawansa ne kuma manzan sa ne. Saboda wannan ranar aka koyar da mun dan gudun ɗebe mana albarka. Salloli biyar basa wuce ni harda nafila da dai Hansai ce nasan bata cika ƙara farilla akai ba, Wa saumu ramadana har na alhamis da litin baya wuce ni."
KU DAGE DA COMMENTS NA CI GABA DA POSTING KULLIN KAMAR DA.
JAMA'A KUJE KU TAYA INNO AMSA TAMBAYOYI FA😂😂😂😂
_UMMOU ASLAM BINT ADAM😉_
[06/11, 14:58] Ameera Adam🌚: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/groups/856755331683130/?ref=share
👹 JARIRI 👹
Labari da Rubutawa: AMEERA ADAM
SADAUKARWA GA ƳAN GROUP ƊINA NA AMEERA ADAM FANS GROUP

21&22
Gabaɗaya ido suka zurawa Inno dake kwance tana ta sakin zance cikin gigita, Halifa na ganin haka ya ja guntun tsaki ya bar gurin saboda ya lura tsabar ruɗewa ce take damun Inno. Daddy ne ya russuna yace. "Sannu Inno ya jikin?" Inno wani marayan kallo ta bi Daddy da shi kamar bazata tanka masa ba zuwa wasu ƴan sakanni ta ce."Eh to, zakkar ce dai ban samu ikon fitarwa ba ƴan kadarorina basu kai a fitar da zakka ba, gonar bayan gidan Idi me saniya ce sai awaki biyu. A yanzu kam bakin alƙami na ya bushe amma da ana komawa da babu tantama Salisu zai bayar da zakkar a madadina" Goggo na jin haka ta ja da baya ta kife a gurin ta rushe da wani irin matsanancin kuka, gurin shiru ya ɗauka dan da alama kansu ya fara ɗaukan zafi.
Goggo sharce hawayenta tayi ta ɗago ta ce. "Kai jama'a yau ina ganin salawaitin tashin hankali a gidan nan. Amma dai Allah ya tattaro salawaitun albarka ya kwashewa wannan hatsabibin jaririn, ku dubi yadda yasa akayi jinkirin kai Rakiya har matambaya sun dafeta tun daga gida. Wallahi bazan ɗauki wannan salawaitun rashin imanin ba wallahi sai dai hukuma ta rabamu, nikam ba zan yi salawaitun ja'inja da wancen hatsabibin ba amma wallahi yadda aka kashe mini ƴar uwa sai ankashe Halifa da Nusaiba har lahira" Juyowa sukayi suna kallon Goggo saboda yadda ta rikice musu ga Inno take ta zabgo surutai.
Abba ne ya tsugunna gurin Goggo cikin lallashi yace. "Goggo dan Allah kiyi haƙuri kiyi shiru Inno fa ba mutuwa tayi ba rikicewa da tayi"
Goggo wani kallon tsana take bin Abba da shi, saboda takaici rasa abin faɗa ta yi cikin takaici ta rufe Abba tayi da duka hannu bibbiyu ta ce. "Wallahi Na dabo da ba dan bakin Uwa kaifi gareshi ba da babu abin da zai hana in kwashe maka salawaitun albarka ba ka ɓalɓalce kowa ya huta." Abba tashi ya yi yana ƙara bata haƙuri amma Goggo ko ta kansa bata bi ba tana cewa.
"Wallahi Na dabo ko kaine akan Rakiya sai hukuma ta rataye ka bare Nusaiba, yadda Ɗansu ya kashe mini ƴar uwa sai anhukunra su." ta ci gaba da kuka sannan ta ce. "Sai dai idan kuɗi zaka bayar a sake su amma ko cikin dare ne sai na bi na datse igiyoyin numfashinsa."
Babau wanda ya tankawa Goggo ana cikin haka Family Doctor ɗinsu ya shigo hannunsa ɗauke da kayan aiki, da sauri suka tare shi suna yi masa barka da zuwa. Yana zama ya buƙaci da su ɗan basu guri saboda yana buƙatar ya dubata cikin nutsuwa, Goggo ƙaddabe ƙasa tayi akan babu inda zata sannan ta baɗe shi da maganganu.
"Kai yaro dube ni da kyau karka nuna mini salawaitun cin mutumci ido biyu, wanne ha'incin ne basu iya ba iye? Gaya mini meye bakwa yi salan na fita ka cicciri sassan jikin ƴar uwa saboda salawaitun rashin imani. To wallahi kurwar ƴar uwata kur..." Abba ne ya katse ta ya cewa. "Haba Goggo wannan fa likita kuma shi ne fa yake kula da mutanen gidan nan babu wani abun cutarwa da zai..." a hassale Goggo ta ce. "Kai Na dabo ka saurara mini wallahi bar ganin ka tara abin duniya ka yi mini salawaitun duniyanci kar nake kallanku sakarkaru." Dr Muhsin ne ya kalli Abba yace. "Barrister ka ƙyale ta babu damuwa." Goggo ta bishi da harara tana yin ƙwafa.
Abba da Daddy kan kujera suka koma suka zauna Dr Muhsin ya matsa gaban Inno da ke kallonsu da shanyayyun idanuwanta, a hankali ya fara gwaggwada ta yana dubata sannan ya saka mata tare da allurar bacci, ba'a ɗauki lokaci ba bacci ya yi awon gaba da Inno ta fara sauke wahalallen numfashi.
Dr Muhsin ya fara tattara kayansa da niyyar haɗa su kafin ya yiwa su Daddy bayanin abin da yake damun Inno da halin da take ciki, Goggo na ganin haka da sauri ta shaƙo wuyansa katamau tana cewa.
"Alƙur'an babu inda zaka je. Baza ka tafi ko'ina ba sai sai ƴar uwata ta tashi" Dr Muhsn cikin wata irin murya yace. "Baba lafiya me nayi miki ne?" Kafin Goggo ta yi magana Daddy da Abba sun taso kan su Goggo cikin tsananin jin kunyar Dr suka fara magana.
"Haba Goggo dan Allah meye haka kike yi yanzu abin da kikayi kin kyauta kenan?" Daddy ya ƙarasa faɗa yana ƙoƙarin ɓamɓare hannun Goggo daga wuyan Dr Muhsin. Goggo ban da nishi babu abin da take yi saboda yadda ta taƙarƙare ta sa ƙarfi ta maƙure Dr Muhsin, Shi kuma kawaici ya yi ganin Mahaifiyarsu da Daddy ce kuma ga girma dan bazai iya hankaɗe ta. Da ƙyar da siɗin goshi suka cire hannun Goggo daga wuyan Dr Muhsin. Ana cire hannunta Dr Muhsin ya yi caraf ya miƙe ya yi gefe yana maida numfashi.