← Book details Jariri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 20

Sashe 17

Jariri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jariri ya ɗare kujera yana ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya yace, "Idan baki zo ba kika bari na ƙaraso idan na turmusheki sai na ɗaɗe mazaunanki dan babu abin da zai hanani yagarsu na cinye su tas" Tarasulu wage baki ta fara yi tana bin su ɗaya bayan ɗaya da jemammun idanuwanta, kallo take musu me ɗauke da ma'anar nikam tawa ta ƙare ku gafarceni, tana zuwa kan Inno ta ce, "Rakiya duk duniya ke kaɗai kike bina bashi kuɗi bayan na mutu ki kira su Ɗalha kicr su biya mini kar akaini da kuɗinki na faɗa hannun mala'iku, kinsan dai me Malam me haɗiyar alƙami ya taɓa sanar damu tun yarinta akan haƙƙin wani." Inno ta sharce tata ƙwallar tana fyace majina ta ce, "Yanzu haka zamu yi mutuwar wulaƙanci muna ji muna gani, to Allah shi yafe mana amma nikam tsinke banzan amsa ba dan duniya da lahira na yafe miki, yanzu idan na karɓe na yi wa amintaka ɗa'a kenan?" Jariri ne ya buga musu tsawa yace, "Ke me karɓar wasiyyar basai kin fita da rai ba" aikuwa ko rufe baki bai yi ba gabaɗaya tsofaffun nan suka yage baki suna kuka me nuni cewar ta su ta zo ƙarshe, gurin banda rawar murya da makyarkyatar tsofaffi babu abin da yake tashi.

Daddy ma da yaga basu da wata mafita da sanin makomarsu, janyo gefen rigarsa ya yi ya fara goge ƙwallah. Halifa da su Mummy ban da ido babu abin da suke bin su da su na jikin a sanyaye kamar marasa jini a jika, Jariri tsalle yanyi ya ƙarasa gurinsu Inno ya yi ƙerere yana kallonsu sannan yace, "Maza ku shanye kukanku idan ba haka ba wallahi jikin ku ya gaya miki dan babu abin da zai haɗa na yi lugu-lugu da namanku." Kamar anyi ruwa an ɗauke haka gurin ya yi tsit su Inno suka ja bakinsu suka yi shiru suna sauraron hukuncin da zai yanke akansu.

Jariri wata miƙa ya yi yana dafe cike wanda ya kasance tunɓur dan ko wando babu a jikinsa, yamutsa fuska Jariri ya yi sannan ya kalli Nusaiba da take lungu kamar munafuka , tsalle ya fara yi yana buga ƴar ƙafa kamar ta sauro yace. "Mummy zan sha" cikin Nusaiba ne ya karta nan take gumi ya fara keto mata ta basar kamar bata ji shi ba.

Juyawa ya yi yace, "Ko da yake kafin nazo sha bari na fara rage hanya da waɗance. Tafiya ya fara yi yana wata rangwaɗa yana dafe ƙeya haɗe da wurga ƙafa ɗaya, da sauri ya juyo ya kalli ƙofa yace, "Ku rufo mini ƙofar" tun bai ƙarasa faɗa ba suka ji ƙofofin ɗakin na bankowa da ƙarfi suna rufewa.

Cikin kitchen ya wuce cen saman drowaer ya ɗare ya zaro wata silleliyar wuƙa, sabuwa tana sheƙi ya fito gurin da ya bar su Inno a tsaye, suna ganin Jariri da wuƙa suka ƙanƙame juna suna kurma ihu.

Jariri ɗaga wuƙar sama ya yi ya kalli Tarasulu yace, "Maza ƙaraso na fara da salsale gashin kanki kafin naje kan sauran, idan kuma kika bari na ƙaraso da kaina sara ɗaya zanyi na fille kanki ƙasa. Gara ki bari na fara bi gaɓa-gaɓa" Tarasulu bata da zaɓi haka ta ƙasa jiki a sanyaye ta tsaya gaban Jariri ta ce, "Gani nazo" Jariri ya buga tsalle ya ɗafe kafaɗar Tarasulu ya kalli saitin kumatunta yawun bakinsa na tsinkewa har yana ɗiga ƙasa, ya fara lasar kumatunta.

Ilahirin jikin Tarasulu rawa yake yi hawaye da majina sai ambaliya suke a fuskarta, kallan bakinta ya yi yace, "Buɗe bakinki na gwagwiya naji ko da daɗi." Tarasu cikin kiɗima ta ce, "Ummmmun" yace, "Afke ashe fa kece me aljanu ko?" Da sauki Tarasu ta gyaɗa kai yana jin haka ya zabura ya zame gashin kanta ya fara askeshi, Tarasulu ban da kuka da ihu babu abin da take yi saboda azabar yadda yake kankar kanta kamar yana fafe ƙwarya.

Su Inno tun kafin yazo kansu suka yanke ƙauna suna kuka da barin wasiyya, kafin wani lokaci tuni Kan Tarasulu yayi ƙwal kamar bayan silba, gashin Tarasulu ya fisga ya dinga cusawa a baki yana haɗiyewa, gabaɗaya ido suka zaro suna ta'ajibin wannan lamari na Jariri, kamar ya shiga zuciyarsu haka ya dinga damƙar farin gashin Tarasulu yana wurga musu yana cewa, "Maza kowa ya ci rabonsa, duk wanda bai ci ba sai na yanke kunnuwansa na bashi ya cinye" Kallan kallo aka fara tsakanin su Daddy da su Inno, kowa na tunanin wanda zai fara wannan lamarin a tskaninsu.

Jariri na haɗiye gashin ya fara shaƙuwa da sauri ya ɓingere a ƙasa yana kukan jarirai yana cilla ƙafa, Inno ce tw fakaice shi ta raɗawa Goggo magana a kunne.

"Kai amma wanna ɗan ƙwal uban jariri anyi hatsabibi, dubi ɗiban albarkar da yake gwadawa mutane" kome suka faɗa lokaci ɗaya suka bushe da dariya Inno harda kwanciya a gurin tana ƙyaƙyatawa.

Jariri da ke kwance yana ta kuka haɗe da ciccila ƙafa sama ya ɗan jiyo a fakaice, ya saci kallonsu da wutsiyar ido sai ya kuma kwara ihu haɗe da cewa, "Inno! Wayyo Inno kizo ki ɗauke ni ki kaini gurin Mummy zan sha" Inno da ke jin ƙwarin gwiwa sakamakon tattaunarwa da suka yi da Goggo ta ce, "Sai dai ka mutu a wurin tambaɗaɗɗe maras ɗa'a" Tarasu gefe ta ja ta zauna daɓar tana shafa kanta cikin baƙin ciki. Halifa wani tunani ne ya faɗo masa har sai da farin cikinsa ya bayyana a fili, cikin fakar ido ya fara takawa a hankali har ya faɗa cikin kitchen, yana shiga ya ɗauko taɓarya da sauri ya ɗaga ta sama iya ƙarfinsa ya bugawa Jariri a tsakiyarsa jikinsa da niyyar datse shi gida biyu.

Halifa na saukewa Jariri taɓaryar yaji kamar sauka dukar a jikinsa, nan take ya sulale ya baje a gurin saboda azaba sai gani suka yi fitsari na gangarawa ta ƙafafuwansa. Jariri bushewa ya yi da wata mahaukaciyar dariya yace, "Shege Daddy ya iya saiti" sai ya kuma bushewa da dariya lokaci ɗaya kuma ya murtuke fuska ya kalli ya kalli Goggo yace, "Maza zo ki ɗauki Daddy ki goyashi" Goggo cikin fargaba ta ce, "Da ni kake yallaɓai?" Jariri yace, "A'a da kaina nake" jin haka yasa Goggo ta ƙarasa gaban Halifa da ke baje a ƙasa ta ce, "Da ka taimako min da salawaitun ɗauki amma ni kaɗai bazai iya ba ina ni ina salawaitun Halifa yaro a murɗe kamar ƙarfe." kallon da ya wurga mata ne yasa Goggo ta haɗiye abin da yake bakinta nan ta sunkuya ta fara cicciɓar Halifa sai kake ɓurrrr daaaaarrrrr Goggo na sakin tusa ta ko ina.

FATAN ALHERI🥰

_UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉
FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️

*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/groups/856755331683130/?ref=share

👹 JARIRI 👹
Labari da Rubutawa: AMEERA ADAM

SADAUKARWA GA ƳAN GROUP ƊINA NA AMEERA ADAM FANS GROUP

GARGAƊI
BAN YARDA A SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA.

37&38

Jariri na jin haka ya tattakura ya yi tsalle ya ɗaɗawa Goggo a mazaunanta, gantsarewa tayi tana rafka ihu ta ce, "Kai jama'a wai babu me taimakona daga salawaitun azabtar wannan ne" Jariri bai bi ta kanta ba hannu ɗaya yasa ya ɗaga Halifa sama da yake sakin numfashi da ƙyar, tsawa ya bugawa Goggo yace, "Maza kinga yadda na yi masa haka? To haka nake san ki yi ɗauka ɗaya idan ba haka ba ni da ke ne" Goggo sharce majina tayi tana wurgawa su Inno mugun kallo saboda taso ace tare ya dinga saka su aikin wahalar aiko ba komai tasan sa sha wahalar tare.

Ƙarasawa tayi waje Halifa dake sharɓe cikin jin haushi ta make shi da ƙafa sannan ta yunƙura da ƙyar ta ɗago hannuwansa, sama wajen hannuwansa aikuwa batayi aune ba sai ji kake jigijib ita da Halifan sun kife ƙasa, Goggo kuka ta saka tana dafe baya tana faɗin, "Wayyo Allah kwankwaso na waini wai jama'a ku agaza mini ƙuguna zai ɓalle" Jariri gefe yaja ya wani tuntsire da dariya harda dafe ƙugu sannan yace, "Wallahi idan baki tashi ba zan raba kwankwason naki gida uku" Goggo ɓingerewa tayi ta ce, "Wallahi na gaji da salawaitun rashin imanin nan, idan gida ɗari zaka rabani sai dai kayi ja'iri hatsabibi, sai fiƙi-fiƙi kake da idanu yana karuwar akuya."

Jariri ba ƙaramin bango ya kai Goggo ba, da alama wannan karan ta tuƙe ƙarshe a zuciye ta yunƙura tsaye tana ɗingisa ƙafa, Silbar dake gefe wacce suka sha farau-farau a daren jiya ta ɗauka ya fusace ta ƙarasa gurin Jariri, sai da ta saita tsakiyar kansa ta bashi raaaal saboda baƙin ciko ta ci gaba cewa.

"Shegen abu ƙanƙaninka da kai gajarta kamar inuwar Alli sai azabtar damu kake da salawaitin azaba" wannan karanma tana gama faɗa ta kuma ɗaga silba ta bashi ƙwaaaal a tsakar kansa.

Gabaɗaya shiru suka yi suna kallonta cikin tsoro don sun san kamar bashi ne Goggo take ɗauka a wurin Jariri, zaninta dake cen gefe ta janyo ta ɗaura muryar Goggo har dacewa take saboda faɗa ta ci gaba da faɗin,

"Tsabar tsiya da wasali tun da nake riga ban taɓa cirewa gaban yara ba amma dubi salawaitun iskanci da wannan ƙudul ɗin ya sani, wai ni ce da yarda zani a gaban ƴaƴa da jikoki Allah ya isa tsakanina da kai la'ananne" Goggo na zuwa nan a zancenta cikin baƙin cikin abin da ya yi mata ta kuma ɗaga silbar hannunta sake bashi raaal aka.
Chapter 17 · 0% Book details