← Book details Jariri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 20

Sashe 15

Jariri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daga cen wajensu Halifa kokawa sosai suke yi, Halifa ba ƙaramin mamakin ƙarfin wannan Jaririn ya yi ba ganin Jaririn har ƙasa yake damfarar da shi. Wannan karan Jariri ya samu nasarar jefar da Halifa cen ƙasa da sauri ya yi sufa ya faɗa kanshi yana wawure-wawure yana cewa. "Daddy zan sha." Inno na ganin haka ta kuma fashewa da dariya da ƙarfi ta cewa Jariri. "Maza tsotse shi tass idan kaso komawa ciki ma ka danne shi ka koma"

INA MIƘA SAƘON GAISUWA TA GAREKU MASOYA😂😂😂 WANNAN KARAN HALIFA NA GANIN SALAWAITUN RAYUWA IDAN JARIRI YACE ZAI KOMA CIKI AI BA KANTA 😂😂😂

_UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉
[12/11, 11:41] Ameera Adam🌚: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️

*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/groups/856755331683130/?ref=share

👹 JARIRI 👹
Labari da Rubutawa: AMEERA ADAM

SADAUKARWA GA ƳAN GROUP ƊINA NA AMEERA ADAM FANS GROUP

GARGAƊI
BAN YARDA A SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA.

29&30

Goggo ta ce. "Haba Rakiya wannan ai sabon salon rashin imani ne yanzu idan ya nemi komawa ciki a gurin Halifa ai mun ga ta kanmu, ba Halifa kaɗai ba hatta mu sai mun shiga siraɗallazi." Sai kuma Goggo ta tuntsire sa dariya harda hawaye sannan ta ce. "Kai jama'a ni da Adahama waya ga Halifa da sake sabuwar haihuwa." Aikuwa lokaci ɗaya suka ƙara kwashewa da dariya Inno ta ce. "Da kuwa ranar munga ɗiban albarka ido biyu" Uwani da ke cikin banɗaki ta ce. "Rakiya ki dubi Allah da ma'aiki ku buɗe ni daga bayin nan wallahi banda zarni da wari babu abin da nake shaƙewa a ciki" Inno ta ce. "Uwani wallahi idan kinga kin fito sai ƙurar wancen Ƙunduss ɗin ta lafa dab baza ki jama bana rawar banjo ba haka kawai."

Halifa ganin Jariri na niyyar cimmasa yasa ya ci gaba da ihu yana neman taimako amma shiru kake ji, Halifa na ganin haka ya rushe da kuka yana cewa.

"Jama'a dan Allah ku agaza mini wallahi zai kashe ni" ganin ihun ba zai kaishi ba yasa Halifa ya taƙarƙare ya ɗurmawa Jariri dundu a abaya da sauri Jariri yayi tsalle ya ɗaga shi yana muzurai da zare idanu. Da gudu Halifa ya miƙe yana shirin fita wannan karanma Jariri yayi caraf ya ƙafar wandonsa. Halifa cikin kuka yace. "Dan Allah kayi haƙuri ɗana wallahi bazan ƙara dukanka ba." Jariri sakinsa ya yi yace. "Tashi Daddy " ba musu Halifa ya miƙe fuska duk ta jiƙe da hawaye.

Jariri ya kalli ƙofar ɗakinsu Inno yace. "Kaje ka buɗe ƙofar ɗakin cen, ni kuma zan buɗe ta cen" ya ƙarasa faɗa yana kallan ƙofar ɗakinsu Daddy.

Halifa daɗi yaji dan yasan wannan da ma ce ya samu da zai iya guduwa ta ruwan sanyi ba tare da ya wahala ba, kamar Jariri yasan tunanin da Halifa yake yi kenan yace. "Kuma wallahi Daddy idan ka fita daga ɗakin sannan sai sawa gidan nan wuta kowa ya mutu." yana gama faɗa ya tofar da yawu a ƙasa sai ga wuta ta kama a guri, jikin Halifa ne ya ɗauki rawa da sauri yace. "To Ranka shi daɗe sai abin da ka ce." Jariri tafiya ya fara yi yana tafe yana rangaji yana tura ciki gaba.

Su Inno na jin haka suka rafka ihu lokaci ɗaya suna fashewa da kuka, Goggo harda sakin fitsarin tashin hankali.

Halifa bai damu da kukan da suke ba dan shi daɗin hakan ma ya ji da ace shi kaɗai zai sha izayar Jariri gwara ace kowa ma yaji ba daɗi daa mutuwar yawa kaka ce.

Jariri bugu ɗaya ya yiwa ƙofar ta ɓalle yana tsaye yaga Mummy da Daddy suka riƙe da juna sai gumi suke, ƙugu ya riƙe yana kallansu sannan ya nuna su da hannu yace.

"Ku fito nan"

Ta rasulu na jin haka ta hau rawar jiki gumi na keto mata ta ko'ina, daga Daddy har Mummy rasa wanda zai fara yin gaba akayi, Daddy ne ya kalli Mummy yace. "Kije ana magana mana"

Mummy maƙalewa tayi tana tirjewa ta ce. "Kai ka wuce mana" Jariri yace. "Wallahi duk wanda ya bari nazo gurin da yake sai ya goya kansa..." Tun bai rufe baki ba da sauri suka matso suka fito cikin falon.

Jariri bai bi ta kansu ba ya juya gurin Halifa da yake ta faman buga ƙofa su Inno na kuka, yana zuwa bugu ɗaya ya yi mata itama ta ɓalle sannan ya leƙa ya nuna su Inno yace. "Maza kuma ku fito" bai waiwaye su ba kai ƙatsaye ya fice daga falon ya nufi ɗakin da su Nusaiba suke itama bugu ɗaya suka yi mata ta buɗe sasannan ya taso su suka nufo babban falo gurin da ya bar Halifa da su Daddy.

Jariri kallan Daddy ya yi yace. "A duk faɗin gurin nan wa kafi so" Inno da ke wajen su Goggo har bangaje su take ta matso ta ce. "Ɗannan gani nan nice uwarsa" Jariri ya cewa Daddy. "Wai haka ne?" Daddy ya gyaɗa kai sannan yace. "Hakane ranka shi daɗe."

Jariri ya wuce ya fisgo cajar Laptop ya miƙawa Daddy yace. "Ungo kayi mata ciki ashirin" Daddy shiru ya yi yaƙi karɓa Inno nan take ta hau zare idanu. Jariri yasa hannu ya janye Daddy da Inno gefe yace.

"Ku kun fita daga cikin lissafi. Ku fa kowa ya nuna mini wacce yafi so ko wanda ya fi so" duka shiru sukayi ganin gaka yasa Jariri ya guga musu tsawa yace.

"Ba za ku yi magana ba?" cikin haɗin baki suka ce. "Babu wanda muka fi so" Jariri ya gyaɗa kai yace. "To shikenan"

Yana juyawa ya tawagar Mudul nan take sai ga wasu ƙananan Jarirai sun fara shigowa daga waje kowanne hannunsa ɗauke da bulali, dakatar da su Jariri ya yi sannan ya ƙarasa gurin Daddy ya ɗaga bulalar hannunsa ya yi tsalle ya zuba masa a ƙeya, nan take Daddy ya hau susa yana roƙon Jariri. Jariri bai saureshi ba ya juya gurin Inno tun kan ya ɗaga bulalar ta fara kuka tana roƙonsa.

Iya ƙarfinsa ya ɗaga hannu ya ɗaurewa Inno ƙeya da bulalar nan take ta kwanta a gurin banda birgima babu abin da take yi, Kallan ƴan uwansa Jarirai ya yi yace. "Na baku dama kuyi ta zane su da bulalun hannunku."

Tun bai rufe baki ba suka fara zuba musu mulalin hannunsu, Ta rasuwa duka biyu akayi mata ta sume a gurin Inno, Goggo da Inna Lami tun suna cikin hayyacinsu har suka fara fita. Ganin wannan ba zata kai su ba yasa Daddy yayi kukan kusa ya girgije ya miƙe haka ya dinga wartar Jariran ɗaya bayan ɗaya yana bugawa da ƙasa.

BARKA DA JUMA'A🤹🏻‍♀️

_UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉

*FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️

*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/groups/856755331683130/?ref=share

👹 JARIRI 👹
Labari da Rubutawa: AMEERA ADAM

SADAUKARWA GA ƳAN GROUP ƊINA NA AMEERA ADAM FANS GROUP

GARGAƊI
BAN YARDA A SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA.

31&32

WANNAN SHAFIN SADAUKARWA NE GAREKI FATIMA BINTU INA GODIYA ƘWARAI ALLAH YA BAR ƘAUNA🥰🥰🥰🥰🥰

Daddy iya ƙarfinsa ya zage ya dinga ɗaukan Jariran duk wanda ya warta sai kaji tim ya buga shi da ƙasa, amma wani abun mamaki yana buga su da ƙasa sai ka ga sun girgije sun mulmula sun miƙe tsaye, Halifa ma ganin haka yasa ya fara yin yadda ya ga Daddy yana yi kusan lokaci ɗaya suka dinga ɗaukan Jariran suna wurgarwa ƙasa.

Jariran cikin haɗin baki suka dinga ƙyaƙyata dariya da an buga su da ƙasa sai kaji sun tuntsire da dariya, lamarin da ya sa Daddy da Halifa suka fara shan jinin jikinsu kenan. Daddy ne ya ɗan dakata yana raba idanu kamar almara haka yaji Jariri ya sure shi ta baya, daga Halifa har sauran mutanen zaro idanu sukayi suna kallan wannan lamarin, Halifa da sauri ya ƙarasa gurin da Jaririnsa ya sunkuci Daddy ya fara ƙoƙarin jan Daddy nan fa suka fara ja'inja, Jariri yana ja Halifa yana ja.

Bai yi aune ba shima Halifa yaji ƙanƙanin hannu ya sureshi aikuwa ya ƙwalla ƙara yana neman agaji, Jariran nan haka suka mayar sa Daddy da Halifa kamar ƙwallo suka fara wurga su sama suna caɓewa.

Inno da ke kwance cikin fitar hayyaci ita Goggo da ƙawayen ta fara cewa. "La'illaha'illahu, Innamal'a'amalu binniyati..." kafin ta ƙarasa faɗa Goggo ta ce. "Li'ilafikuraishin aniyar jiririn nan ta bishi..." Jin sun fara karaton ƴan ayoyi yasa Jariri ya damfara Daddy da ƙasa ya juyo gurinsu Inno haka ya dinga binsu da bulali yana cewa.

"Ku rufe mini baki na ƙarajin kunyi karatu sai mayar da bakin ku ya koma ƙeyar ku" Inno da ƙawayenta haka suka yi shiru ban da ihu babu abun da suke yi.

Daddy da ke gefe a yashe hannu biyu yasa ya dafe bayansa cikin azaba yace. "Wash! Jama'a nikam rayuwata ta zo ƙarshe na yafewa kowa nima ku yafe mini" Jaririn da ya sunkuci Halifa ne yaje bakin ƙofa ya juyo yace.

"Shugaba ni dai na tafi da wannan kuma ku samo rabonku" Halifa yana jin ance an za'a tafi da shi ya rungumo ƙofa yana cewa. "Me gida dan Allah kayi haƙuri ka kyaleni karka tafi da ni" Jaririn yace. "Iyalaina suna cen suna jiran na kai musu kai babu abin da zai hana na tafi da kai" Jariri dake gurin su Inno ya juya gurinsu Halifa yace. "Kai Kuɗubale zo nan ba shi kaɗai za'a tafi da shi ba, kuma wannan babban kan ba naka bane nawa baka ganin Daddyna ne"

Jaririn da ke ɗauke da Halifa ya ƙaraso ya sauke shi, Halifa da gudu yayi sufa ya shige cikin su Mummy da Nusaiba, Jariri ya kalli sauran ƴan uwansa Jarirai yace. "Kowa ya ɗauki rabonsa nida Daddy da Mummyna zan ɗauka" tun bai rufe baki ba Jariran suka buga uban tsalle suna cewa. "Yeehh Yau akwai shan lagwada" kowa ya tafi dan kama wanda yake san ɗauka, ɗakin banda ihu da kukan tsofaffi ba abin da yake tashi a ciki.
Chapter 15 · 0% Book details