Sashe 5
Jariri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Miƙe ƙafafunsa yayi da gaba ɗaya gashi ya rufe su sannan ya fara mata bayani, " Zabi na farko zamu iya baki garin maganin da za'a zuba masa a ruwan wanka ina nufin wankansa na farko a duniya kuma ko yaya ne asamu a bashi wannaa maganin ya sha, sai kuma na turare wanda ita Zaliha tana fara Naƙuda zaki turara mata, karki bari yaro ya faɗo ba tare da kin turara shi ba, to idan kika yi haka bazai iya gani da idanunsa ba, har tafiya da magana ke komai da kika sani sai dai ayi masa, saboda zai kasance a kwance sai dai duk abinda za'a furta zai ji shi babu abinda zai iya wanzarwa "
Murmushin jin daɗi Fulani Maryama tayi ganin haka yasa boka ya ce mata, " Sai dai akwai sharaɗin da zaki kiyaye, akwai ruhin wata da na gani tana jingine da shi, zata shigo cikin gidan masarautar ku tana ƙasƙantacciya muddin kika bari ta shigo cikin gidan sarautar, abubuwa marasa daɗi zasu fara faruwa gareki kuma duk ranar da tayi tozali da shi suka haɗa ido, a ranar aljanun dake riƙe da ƙafafunsa zasu tarwatse alƙadarinsu zai karye, idan kika yi sake ta ɗau wani abun ci ko abin sha ta bashi da hannunta to a ranar suma aljanun da ke riƙe da bakinsa zasu gushe zai fara magana, sai dai aranar zai fara wani irin ciwo kamar zai mutu zai yi ta amai ba ƙyaƙyƙyautawa kamar zai amayar da ƴan hanjinsa, hakan zai ɗaga hankalin Mai martaba har yasa anemo wanda ya bashi wani abu tunda shi zaiyi tunanin guba ce aka bashi, amma ba haka bane amayar da gubar da take jikinsa yake ta tsawon shekaru "
_UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉
[11/10, 17:23] Ameera Adam🌚: ☀️ *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/groups/856755331683130/?ref=share
👹 JARIRI 👹
Labari da Rubutawa: AMEERA ADAM
SADAUKARWA GA ƳAN GROUP ƊINA NA AMEERA ADAM FANS GROUP
GARGAƊI
BAN YARDA A SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA.
5&6
Daga cen ɓangaren Mahaifin Nusaiba yace. "Subhanallah Goggo lamarin har yayi tsamari haka? Me zai hana ku daidaita ina Halifan?" Goggo ta ce. "Na rantse da Allah Nadabo sai anbi min haƙƙina ni za'a kawowa sabon salawaitin cin mutumci daga nazo gidan jikata" Abba yace. "To kiyi haƙuri Goggo insha Allah anjima zan zo" a hassale Goggo ta ce. "Idan har sai anjima zaka zo ka bari Nadabo na yafe tunda kai baka damu da martabar mahaifiyarka ba, zan tafi gurin hukumar da kaina ai na Allah basa ƙarewa tunda baka ƙaunata..." da sauri Abba ya katse ta yace, "A'a kiyi haƙuri ina nan tafe yanzu" tana jin haka ta katse wayar gabaɗaya.
Inno shewa tayi ta ce. "Ahayye Allah na dawo inji kishiyar me yaji to wa zai cinye naman idan ba ke ba, kinsan dai tun muna yara ke kura ce to kuma kya nuna mun ɗiban albarka ki kira Nadabo. Wallahi idan bai zo da majalisar ɗinkin duniya ba sai na kwashe masa albarka."
Haushi ne ya kama Halifa cikin ƙunci yace. "Dan Allah kuyi mana shiru haba dan Allah? Tun ɗazu sai abu ɗaya akeyi nikam gaskiya na gaji wallahi, Allah idan su Daddy suka zo tasaku zasuyi a gaba ku tafi ni bazan iya ba kwana ɗaya kacal kunƙi ku barmu muyi bacci cikin nutsuwa." Nusaiba ta ce. "To wai ku dan Allah banda abinku me akayi muku na kiran su Abba? Idan zaman nan ɗin ne bakwa so basai ku koma mazauninku ba?" Inno kallan tsaf ta yiwa Nusaiba sannan ta mata daƙuwa ta ce. "Gidan ku ja'ira mara ɗa'a korar mu kuke yi nida ƴar uwata? Wacce uwar muke ci a gidan naku da har kuke korarmu" Halifa yace. "Inno yanzu mu dawo maganar nama wannan fa ba abin wasa bane wallahi tsoro ya kamani ace kaji biyar babu daga yamma zuwa safiya" Inno ta ce. "Gane mun hanya jikana ni kaina na fara zargin anya babu wata a ƙasa kuwa?" Halifa na shirin magana suka ji ƙarar fashewar abu a ɗakin Nusaiba, da sauri suka nufi ɗakin zanin Inno har yana niyyar faɗuwa, suna zuwa suka samu kwalaben turarenta ne a ƙasa. Baki suka saki suna mamaki Goggo ta ce. "Halifa kuna da ɓeraye ne a gidan nan?" Nusaiba ta ce. "Gaskiya bamu da ɓeraye amma nayi mamaki ya akayi har kwalabe suka farfashe haka?" Inno ta waiga ta kai kallonta ga Jaririn Nusaiba dake kwance kan gado ta ce. "Halifa kasan Allah wannan ɗan ƙundalon na fara zarginsa saboda naga ɗiban albarkarsa ido biyu, anya jinnu basu shafeshi ba kuwa" Halifa ya tsuke fuska ya ce.
"Gaskiya banasan irin wannan Inno ya zaki dinga alaƙanta mun ɗa da aljanu ba naso kawai daga kwalaben turare sun zubo sai ki ce ɗana ne, wai me yaron nan ya tsare miki" Inno ta riƙe baki ta ce. "Ubanka ya tsare mun Halifa ka kiyayeni fa ina nuna maka Annabi kana runtse ido tam, wallahi duk ranar da ya nuna maka ɗiban albarkarsa zakayi bayani da bakinka"
Goggo haushi ya isheta ta ce, "Rakiya wai wannan sabon salawatin ruɗewar meye ya sameki, anya aljanu basu buɗe miki idanu ba? Ke Nusaiba ɗauko mun shi ma inyi masa wanka kar wannan ruɗaɗɗiyar ta ƙara ruɗa mu" Goggo na faɗa ta fice haɗa ruwan wankan Jariri" Halifa ma ficewa yayi aka bar Nusaiba da Inno, Nusaiba cire masa kaya tayi ta wuce ɗakin da Halifa yake dan ta ɗebo kayan Jaririn. Inno na zaune ta ga Jaririn ya buga tsalle ya miƙe tsaye, dafe ƙeyarsa yayi ya fara wani irin zagaye yana yi yana gwalalo mata idanu. Sai yayi gaba kamar zai hau kanta sai kuma yayi baya ya buga tsalle. Ihu Inno ta farayi tana tafe a guje fitsari na bin ƙafafuwanta. Da gudu duk suka fito dan ganin abinda ya faru gabaɗaya suka fara jero mata tambayoyi kala-kala, Inno ji tayi bakinta yayi nauyi kallan ƙofar ɗakin Nusaiba take tana nunawa, da sauri Nusaiba ta shiga dan ɗauko Jaririnta.
Ana cikin haka suka ji bugun gida da sauri Halifa yaje ya buɗe ƙofar Motocin Daddy dana Abba ne kusan tare suka ƙaraso, suna shigowa falon suka gaishe da su Inno sannan suka zauna.
Daddy ya ce. "Halifa Inno ta gaya mun abinda kayi mata meyasa kake yiwa mahaifiya ta haka ne? Yanzu idan ɗanka ya girma zakaji daɗi ya wulaƙanta mahaifiyarka" Inno ta ce, "Gaya masa dai wallahi Halifa bashi da ɗa'a sam, Albasa dai batai halin ruwa ba wallahi da niyyata inkwashe masa albarka kafin kazo" Halifa yace.
"Insha Allah za'a kiyaye Daddy, kuma idan babu damuwa ku wuce da su kawai zuwa gida" Daddy yace. "Dama ai kiran da Inno ta mun kenan to ita Nusaiba wazai zauna da ita?" Inno ta tattakura ta rafka salati.
"La'ilaha'illahu Muhammadur Rasulillahi Sallallahu Alaihiwasallam yanzu Salisu iyaka zaka mun da gidan Ɗanka saboda nazo zaman daɓaro, idan ka tafi dani gidanka wacce uwar zaka bani, Meye bana ci a gidan nan? Wallahi Salisu duk cikin jikoki banyi sa'ar jika kamar Halifa ba, baƙin cikin cin kazar kake mun? Ahir ɗinka wallahi ko a mafarki na kuma jin wannan zancen sai na kwashe maka albarka sakarai maras ɗa'a kawai. Yo idan ban zaunawa jikata ba wa nake da shi da zan zaunawa, kai nifa nazo kenan zuwa sojan badaskare kuma ka ɗebomun kayana tas ka kawo mun gidan nan" Daddy dafe kansa yayi zaiyi magana Halifa ya ce.
"Maganar gaskiya nikam bazaki zauna mun a gida ba, tun da kuka zo gidan nan baccin kirki bama samun isasshe" Abba ya masa daƙuwa yace. "Gidanku Halifa su Inno kake gayawa hakan?" Daddy yayi gyaran murya ya ce.
"Inno ta kiran da kika mun me kike so ayi" Inno ta ɗaga kai sama kamar me nazari ta ce.
"Ɗanka nake san kamun iyaka dashi karya ƙara shiga sabgata, ai inace jikata ce ta haihu ko?" Daddy da Abba suka gyaɗa kai Inno ta cigaba da cewa.
"To kuce ya haɗa ya nasa ya nasa ya bar gidan nan idan mun tafi ya dawo" Halifa ya watsawa Inno harara suna haɗa ido ta rushe da kuka.
Goggo ta kalli Halifa ta ce, "Li'ilafi ƙuraishi aniyarka ta faɗa kanki ƴar uwar tawa kake yiwa wannan mugun kallon to kurwarta kur, oh yau naga sabon salawaitun mugun hali ido biyu anya Nadabo wata rana Halifa bazai rufemu da duka ba a gidan nan kuwa?" Halifa tsaki yayi ya miƙe zai bar gurin da sauri Inno ta riƙo gefen rigarsa ta ce. "Dawo-dawo wallahi sai ka zane mu gwara ka dake mu a gaban iyayenka kar sai sun tafi ka kwashe mana albarka" Sai kuma Inno ta fashe da kuka ita Goggo kamar haɗin baki suke share kwallah. Abba ne ya kalli Halifa yace. "Dawo ka zauna."
Halifa ya cika fam kamar zai fashe ya zauna Abba ya sauko daga kan kujera ya dawo ƙasa yace. "Goggo dan Allah kuyi haƙuri kunsan yaran nan sai ana haƙuri da..." A hassale Inno ta katseshi ta ce. "Allah ya tsinewa haƙurin albarka mun dinga haƙurin kenan har sai ciwon zuciya ya kamamu nida ƴar uwata, wato baƙin cikin rayuwar kuke mana ko Nadabo kuzo ku kashe mu kawai ku huta" Abba dafe kai yayi yai shiru bai ƙara furta komai ba. Daddy kallan Abba da Halifa yayi ya ƙifta musu ido sannan ya fara cewa.
"Halifa yanzu abinda zaka dinga mun kenan kana tayarwa da mahaifiyata hankali, to maza ka fice daga gidan nan ka shiga duniya kowa ya huta gwara nayi rayuwar farinciki da mahaifiyata ya fi mun komai." Halifa miƙewa yayi bai ce komai ba ya wuce ɗakinsa, wata jakar goyonsa ta zuwa gurin aiki wacce yake sa uniform ya ɗauko ya goya ya fito.
Tsugunnawa yayi a gaban Daddy yace. "Shikenan Daddy tunda haka ne ni bari na tafi zan fita daga rayuwarku tunda Inno da Goggo basasan gani na" yana gama faɗa ya mike zai bi hanyar ƙofar.