← Book details Ibtihal Hausa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 22

Sashe 6

Ibtihal Hausa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ta taso cikin maraicin uwa tare da gallazawar matan uba da ƴan uba goma sha takwas wanda dukkaninsu iyayensu sun chusa musu tsanarta ba don komai ba sai don soyayyar da mahaifinsu ya ke nuna mata daman akwai kishi mai zafi da jin haushin mahaifiyarta da mijinsu Malam Mutari ya fifita a kansu domin Rabi’atu macece da duk wanda yayi mu’amula da ita sai ya so ta mace ce mai tsananin kyakyawar zuciya ga haƙuri da kawaici ga kirki da ibada gami da tsananin tsoron Allah wannan shine babban makamin da ta kama Allah ya ɗorata akan kishiyoyinta da ba abunda suka iya sai bin bokaye ƴan tsubbu da malaman boge masu ci da addini bokaye mushirikai,
ba irin asirin da basa mata amma ko kaɗan Allah bai basu ikon cin galaba akanta ba da mijinsu wanda har ta koma ga Allah bai bar ƙaunarta ba.
mutuwarta ta gigiza masoyanta da dama saɓanin maƙiyanta da hakan yayi musu matuƙar daɗi (Allahsarki murnar mutuwa murnar banza).

wanda tundaga mutuwarta malam mutari ya haɗu da hawan jini to daman a wajenta kawai yake samun sauƙi ita ce mai kwantar masa da hankali domin shima mutum ne mai tsananin haƙuri da kamala muddin kaga faɗan sa to ba ƙaramun kai sa bango akayi ba .

Haule ita ce uwar gidansa yaranta goma sai matarsa ta biyu Marariya mai ƴaƴa takwas sannan Rabi’atu itace matarsa ta ukku kuma ta ƙarshe,
ta haifa masa ƴa Ɗaya Hajara yaransa goma sha tara a duniya maza huɗu sauran duk mata ne wanda dukkaninsu a ƴaƴan nasa basa son hajara sai ƙwara biyu kachal Ibrahim da Shafa’atu,wanda ibrahim yayantane itakuma shafa’atu ƙanwartace domin itace Autar gidan dukkaninsu yaran Marariya ne.

Malam mutari mutum ne da ya tara arziƙi a noma tsohon manomi ne da yayi suna a garin,da kewayen kusa da su.

Hajara ta ta so da farinjinin samari kasancewarta jinin asalin fulani gami da rumawa domin mahaifiyarta haifaffiyar Raɗɗa da ke ƙarƙashin wata local govermemt da ke jihar katsina ne,

mahaifinsu kuma malam mutari fulanin haɗeja ne kinga ko jinin rumawa ya haɗu da fulani dole ya haifar da kyakyawa,

hajara kyakyawace tun a zamanin ga hasken fata kuma mahaifinta ya tsaye mata ilimin boko da arabi wanda a ƴaƴansa duk suka gagara yi domin lokacin gani suke rashin galihu ne ya sanya ta ke karatu su ko ƴaƴansu da suke da gata karatun me zasuyi.

A kaf ƴaƴan malam mutari babu wanda yayi ko da makarantar firamari islamiyar ma ba zuwan kirki suke ba hakan ya sa suka ta so cikin jahilci saɓanin Hajara da ta yi zarra a cikinsu domin Allah ya yi mata baiwar ƙoƙari.

Bayan gama karatun sakandire ɗinta malam mutari aure ya so ya yi mata a masoyanta da ke biɗarta amma sam ta nuna ita karatu ta ke son ƙarawa wanda yarda da ita da son karatu da kuma abunda take so ya sanya mahaifinsu aminta ya turata karatu a A B U zaria ,

nan fa cheche kuce ya ƙaru a kanta aka dinga ƙananun maganganu akan malam mutari ya tura ƴarsa karuwaci maganganu kala-kala wanda daga shi har ƴar sa suka toshe kunnansu domin sunsan ba haka ba ne.

Lokacin da Hajara ta gama karatun degiri ɗinta a zaria ranar mahaifinta ya yi farinciki matuƙa adduo’i da fatan nasara da albarka ko ba irin wanda baiyi mata ba.

A lokacin ne wani Aminininsa wanda hulɗar kasuwanci ta hana su ya na sayan kayan nomansa idan ya girbe sunkai shekaru Ashirin suna tare mai suna Alhaji MARZOUQ ya nemawa ɗansa auren Hajara Ba musu malam mutari ya amsa masa da ya ba ɗansa MALEK Auren Hajara amma sai ya tuntuɓeta idan ta amince domin ba zai mata dole ba.

Lokacin da mahaifinta ya zo mata da batun ta ji ba daɗi a ranta domin akwai saurayinta Nazir da sukayi soyayya da shi ya ke matuƙar ƙaunarta ita ma ta ke tsananin sonsa domin ya shafe kusan shekara biyu ya na magiyar ta so shi wanda daƙyal a ƙarshe itama ta faɗa soyayyarsa ba tare da ta shiryawa hakan ba ,
Wanda kafin su rabu ta kwatanta masa har gidansu saboda lokacin babu waya wanda sunyi alƙawarin idan ta koma da sati ukku su zo neman aurenta sannan za ta sanar da mahaifinta game da shi ,

asalinsa lecturer dinsu ne ɗan asalin Kaduna ne dukda son da take yiwa nazir haka ta haƙura ta kasa furtawa domin tayiwa mahaifinta biyayya ,

Abun yazo da gaggawa domin a satin aka Ɗaura musu aure da Malek wanda basu taɓa ganin juna ba ko da a hoto Wanda baƙinciki kamar ya kashe ƴan ubansu da kishiyoyi domin abu ne da ya zo musu a bazata domin a kaf ƴaƴansu babu wanda ya auri kamar ɗan gidan alhaji Marzouq saboda dukkaninsu kusan auren wahala da ci da kai sukayi duk sun jeme sun lalace hakan ya ƙara wutar ƙiyayyar hajara da malam mutari a ransu akan cewa daman yafi son hajara akan duka sauran ƴaƴan su shiyasa bai haɗa kowa da attajiri ba sai ita wanda yayi kamar ma baisan me suke ba,,

An kai hajara gidan mijinta da ke Taraunin Jahar Kanon dabo bisa rakiyar Dangin uwa da na uba don dangin mahaifiyarta na raɗɗa duk an aika musu kuma sunzo sai shafa’atu ƙanwarta kaɗai domin kaf gidan babu wanda ya rakata ta sha matuƙar kukan rabuwa da babanta ta na kuka haka kowa ya tafi ya barta ta sha kuka ta gaji kafin ta haƙura,

Gida ne aka kaita daidai wadaidar mai rufin asiri ɗaki ciki da falo sai baranda da kitchen da banɗaki dukkanin gidan shafe da sumunti wanda lokacin sai wane da wane.

Mahaifinta yayi matuƙar ƙoƙari domin ba abunda bai zuba mata ba na ƴaƴan gata a lokaci,

Tsoro ne ya kamata ganin dare ya tsala ita kaɗai a gida ba alamar shigowar Ango haka ɓarawon bacci ya saceta ba tare da ta shiryawa hakan ba ,

Washegari wasu daga cikin danginsa suka zo wanda ta kula da kallon ƙiyayya da ƙasƙancin da suke mata dukda tasan ta fi su komai kyau wayewa ilimi yawan dukiya kawai zasu gwada mata dukda daidai rufin asiri Allah yayi musu suma saidai su nuna musu su a birni suke dukda suma garin su ba ƙauye ba ne,

Saida Hajara ta yi sati babu Malek ba labarin sa tun ta na tsoro da fargaba har ta haƙura ita kaɗai ta ke kwana abincin gara da komai na buƙata daman mahaifinta ya haɗo ta da su kuma da sadakinta da ya damƙa mata a hannu hakan ya sa ba ta sha wata wahala ba ,gashi ba laifi maƙwabciyarta da suke katanga ɗaya mai suna Farida ta na leƙota akai akai ta kula ba ta da matsala ko kaɗan ga su kuma sa’anni hakan yasa lokaci kaɗan sukayi sabo.

Saida ta cika sati ukku wani Dare har ta fara bacci ta ji mutum na bugun tashinta da ƙarfi da mugun tsorace ta tashi ta na Dunƙulewa waje guda tare da fara salati ta na sanya kuka don a tunaninta ɓarawo ne,

Da Torchlight ɗin da ke hannunsa ya dalleta kafin ya zaro idanu sosai ya na ƙara haskata cikin magana mai kama da ta ƴan maye ya ce”kaii daman wannan kyakyawar BaBa ya auramun “

Sosai tsoro ya kama Hajara kar dai wannan ne mijinta yana magana ya na tangaɗi banda warin giya ba abunda ya ke .

Tsorata ya sanyata tashi za ta ruga ya chafko ta daren ranar ta ƙarfi ya mayar da hajara cikakkiyar matarsa cike da zalunci da mugunta domin ba ya a hayyacinsa ya aikata hakan wanda daga lokacin wani dogon bacci ya kwashe sa wanda ita kuma suma ne ta yi.

Sai ƙarfe takwas na safe ya farka ya na mamakin me ya kawo sa gidan ya dai tuna ya na gidan Club din su sungama shan giya mahaifinsa ya samesa a wajen ya mammaresa tare da tisasa a mota daga nan bai ƙara tuna komai ba sai yanzu da ya buɗe ido ya gansa a wani gida kwance saman gado .,

Jikinsa duk ya masa nauyi ya miƙe idanu ya zubawa kyakyawar budurwar da ke bacci a gefensa ta yi share-share fuskarta hawaye duk sun bushe zuba mata idanu ya yi kafin ya ja dogon tsaki uban me ma ya kaisa kwana gado Ɗaya da matar nan ai yanda ya ɗauki alƙawarin bazai amsa auren dolen nan da mahaifinsa ya yi masa ba domin ya na da wacce yake so haka bazai taɓa haɗa shimfiɗa da wacce ya auro masar ba kai ganinsa ma bazata ƙarayi ba ,

ɗauke idanunsa ya yi ba tare da ya gane koda kamanninta ba ya fice wanka ya yi tare da mayar da kayan jikinsa ba tare da ya ƙara koda kallon Hajara ba ya fice a gida daga nan club dinsu ya wuce ya na ɗaukar motarsa da jiya ya bari a wajen cike da jin zafin abunda mahifinsa ya yi masa na ƙin aura masa budurwarsa Rafaida da baiyi ba ya fice da motarsa ya bar garin kano gaba ɗaya.,

Hajara ba ta tashi farkawa a sumar da tayi ba sai ƙarfe sha ɗaya na safe da rarrafe da kuka ta fito tsakar gida ta na kuka ta hau ƙwalawa maƙwabciyarta Farida kira sosai hankalin Farida ya tashi halin da ta samu hajara a ciki sosai ta jinjina rashin imani na mijinta ita ta taimaka mata ta gyara jikinta tare da mata gashi me kyau ta taimaka mata suka je asibiti aka duba ta bayan an bata magunguna da shawarwarin yanda zata kula da kanta har ta warke kafin su dawo gida saida hajara ta yi jinyar sati biyu da taimakon makwabciyarta farida mutuniyar kirki,

A lokacin ne mahaifinsa ya zo ganinta ko da ya tambayeta lafiya Amsa masa tayi da lafiya qlau ba tare da ta sanar masa komai game da ɗansa ba ya yi mata alkairi ya bar gidan,

Sosai take kewar mahaifinta ga babu waya a wajenta don har lokacin wayarma babu saidai telephone da ba kowa ke samunta ba,
Chapter 6 · 0% Book details