Sashe 2
Ibtihal Hausa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Saida tayi clearing komai da ya dace kafin ta nufi office ɗin ta ta buɗe ba ƙura sosai taji daɗin yanda ake kula mata da office ɗin ba wani b’ata Lokaci ta fara ayyukanta cikin ƙwarewa da kamewa kasancewar bazata fara cigaba da Ɗaukar ɗalibai ba Sai next week hakan ya sa 12:30 ta bar makarantar Batare da ta kula da
kallon da mutane ke binta da shi ba musamman students ɗin da suka ɗan santa ɗaliban da ta ɗauka lokacin suna level One yanzu kuma suna level four kafin tabar sch ɗin sosai sukayi mamakin dawowarta don Sunyi tunanin ta bar makarantar ne ,
Ta gaisa da wasu daga cikin ɗalibanta cikin ƴar sakin fuska kafin ta nufi mota da niyyar shiga ta ji an yi mata magana daga baya ɗan waigawa tayi ta na kallon mutumin da Kai tsaye yayi kama da jami,in tsaro ya na matsowa kusa da ita tare da mata sallama tare da cewa “Fatan ina tare da Ibtihal Adam”
Ba tare da ta bud’e baki tayi magana ba don na kula magana na yi mata wahala ta gyad’a masa Kai.
Takardar da ke hannunsa ya miƙa mata batare da ta Amsa ba ta ce “na meye”
Ya ce “idan kika ɗaga zakiga komai”
Ta ce “zaifi kyau na ji daga bakinka “
Cikin dakiya domin harga Allah kallo daya yayi mata ya ga ta masa kwajini ya ce”
“Takardar sammaci ce daga Kotu “
Mamaki ƙarara ya bayyana fuskarta ta katse sa da cewa .
“Takardar k’ara kuma wa ya ke ƙara na Akan me “
ya ce “daga SHAREF BELLO KUNYA bisa zargin Kisan cikinsa da kika zubar Zakiga ranar shigar kotun da dukkan sauran bayanan a cikin takardar na barki lafiya”
Ya na gama Faɗar haka ya fice yabarta tsaye ta bisa da kallo kafin ta maida kallonta ga takardar baki sake gabanta na tsanantar faɗuwa…………✍🏽
*Wasa Farin girki muje zuwa ta hanyar comment da sharhi tare da sharing ne kawai zai tabbatarmun da amsuwar labarin a zukatanku idan najiku shiru nima zakujini ɗiffff tamkar anyi ruwa an ɗauke*
https://chat.whatsapp.com/JYPWPtF78zlIr2kJcbp6ms?mode=gi_t
_*Miss Hajo ce*_🤙🏿
🪅*IBTIHAL*🪅
~MALLAKAR~
*HAJARA L SADEQ*
(miss Hajo)
MARUBUCIYAR👇🏼
Auren wata tara
Ni da yaya arman
Matar uncle
Najmat abiy
Komai mukaddari ne
Khadijatul Sabren
Ribar so
Mata ta ce
*And now*
*IBTIHAL*
*DEDICATED TO MY HUSBAND*
🅿️………………………*02*
Gabanta na tsakananta faɗuwa wani kuka ne ta ji ya zo ma ta da sauri ta faɗa mota tare da rufewa ta na haɗa kanta da settearing mota ta na fasa kuka mai tsuma zuciya,
Ta kai 5 minutes ta na kuka kafin ta tsagaita cikin kuka ta ke faɗar “Me na yi wa rayuwarka da tsauri haka kake son ganin baya na meyasa me mukayi muku wata irin ƙiyayya ce haka ,Ya Allah kaika jarabceni akan komai da ke faruwa da rayuwa ta Allah ka sassauta mun ka sakamun zaluncin da bayin Allahn nan suke mana da gaugawa ka shiga lamari na ya Allah ka fitar da ni daga sabon tuggun nan da suke bibiyata da shi Ya Allah ka ciremun Sharef daga rayuwata har abada ka mantar da shi ni wanda ko a hanya muka haɗu bazai shaida ni ba”
“Allahu Allahu rabbi la ushirika bihi shai’an ta dinga maimaitawa tare da ambatar mabanbanta adduoi da sunayen Allah a haka ta ji zuciyarta ta yi sanyi ta samu ƙwarin gwuiwa kafin ta ɗauko tissue ta goge hawayen fuskarta ta tada mota,
Kai tsaye Gidan Aunty Salma da ke Guzape ta nufa Horn ta yi mai gadi ya buɗe mata cike da girmamawa ya na gaishe ta tare da mata sannu da zuwa ta amsa cikin mutuntawa tare da zage handbag d’inta ta ciro 5k ta basa ya amsa ya na ƙara mata godiya da sanya Mata albarka kala-kala,
A Babban falo ta haɗu da Aunty Salma na magana da me aikinta ta na ganinta ta faɗaɗa fara’arta tare da Ware mata hannu da zallar murna ta ce “ga ɗiyata ga ɗiyata “
Ibtihal ta ruga ta faɗa jikinta ta na danne kukan da ke shirin zubo mata ta kasa kawai ta sakar mata kuka,
Hankali tashe Aunty Salma ta ce “me zan Gani haka Ibti na ina murnar ganinki kuma zaki sa kuka haba Dama har yanzu baki girma da koke-koken nan ba ai nazata tuni kin barwa su Afren zauna naji me ke faruwa ta faɗa su na zama tare da kama fuskarta da har lokacin ta ke kuka ta ce”Karki tayarmun da hankali Ibtihal me ya faru”
Takardar hanunnuta ta miƙa mata ta na cigaba da kuka,
Aunty salma ta karanta tsaf kafin ta ce
“What Daman wannan yaron nan bai rabu da rayuwarki ba har yanzu Tantirin ɗan iska har mu zaiyi ƙara ta gidan ubanwa ma ya samu labarin dawowarki cikin uwarsa ya ke magana ka ji Asararre ɗan tambaɗaɗɗa ai ko da mu ya ke zancen maimakon ya ɗauremu insha Allah mu zamu ɗaure sa har igiyarsa tayi saura ki bar kuka ki kwantar da hankalinki ba abunda ya isa ya yi don ubansa”
Cikin kuka ta ce “To Aunty idan fa ya kamamu da hujja, tunda yasan da farko na nuna rashin son cikin har yayimun kashedin muddin na zubar bazai ƙyaleni ba bamu da shaidar Inda cikin ya zuba a baki fa kawai muka sanar masa sannan lokacin baiyi yunƙurin komai ba sai yanzu kar fa ace ya gano wani abu da muke ɓoyewa ni dai I am very scared wlh Aunty”
Ta na lallashin bayanta ta ce “nothing will happen insha Allah ki kwantar da hankalinki je ki huta kiyi salla zansa a kawo miki abinci ki ci ki ƙoshi ba abunda zai faru Alƙawari nayi miki yanzu zanyi magana da Aunty Nafisar ta waya zamu tattauna akan batun”
Ba don hankalin Ibtihal ya kwanta ba ta yi yanda auntyn ta ce amma sam ta gagara samun nutsuwa abincin ma ta kasa ci a haka ta na saƙa da warwara Safa ta zo ta sameta itama ranta ɓace ta hau masifa don mamanta ta faɗa mata komai Kallon yanda Safa ke masifa da Aibanta sharef tayi murya sanyaye ta ce”ni wlh duk a tsorace na ke Safa kar ya je ya gano sirrin da muke ɓoyewa bakisan waye sharef da mahaifiyarsa ba sun wuce duk yanda kike tunani hatsabibaine na gaske”!
Safa ta ce “ba abunda ya isa ya yi kin manta su momy sun fishi D’aurin gindi ta kowace siga ƙauyawan matsiyatan me suka isa su yi ɗan kwalta kawai insha Allah bazai gama da duniya lafiya ba”
Lokaci guda Ibtihal ta haɗe fuska”Safa ta ce “sorry na manta fa bakya son ana aibatasa dayawa ni fa sai na ga kamar ma da son sa a cikin zuciyarki”?
Ta na jan dogon tsaki ta ce “ban shaida baki da hankali ba sai yau safa Ko mai son sharef da ahalinsa ba na ƙauna kawai….”
Safa ta katse ta da cewa shikenan ba sai kin faɗa dalilin ba na tuna to wai yanzu mq me ya tado zancen cikin tun da chan bai bi ba’asi ba sai yanzu in banda neman bala’i.
Daidai lokacin aunty Salma ke shigowa da waya kare a kunnanta ta zauna bakin gado tare da miƙawa IBTIHAL wayar jiki sanyaye ta amsa wanda muryar mahaifiyarta ta daki dodon kunnanta da cewa”Ina kika saka wayarki tun jiya ba ta shiga “
Jiki sanyaye ta ce “momy sim ɗin ce ya lalace amma na sayo wani zan kiraki da shi”
Ta ce “karye-karyen sim ɗin naki na masifa dai zakice kinyi zanga idan Nin ɗinki ya daina miki register layi yanda zakiyi ashe kuma haka wannan ƴan iskan suka ɓullo to abunda nake so da ke ki kwantar da hankalinki bana son ko da wasa ki ɗaga hankalinki abunda yake so kenan daman baya son kwanciyar hankalinki insha Allah ba abunda zai faru sai alkhairi ko Court ɗinma ba za a shiga da ke ba Lawyer kawai zamu ɗauka don yanda kika firgitar nan sai ki ɓata mana shiri ki ci gaba da harkokinki ki manta da su kinji”
Ba don ta gamsu ba ta ce “Toh momy amma wata shaida zamu bayar da zata tabbatar da cikin ya fita”
Ta ce “Salma ta ji da komai zatayi magana da wata ƙawarta Aunty Aisha da ke da asibiti mallakinta ne sannan yanzu zanje gidan aunty Aisha mu tattauna za a bada shaidar da date ɗin da komai sai ma mun kullesa akan ɓacin sunan da yake shirin mana bayan munci nasara”
Ta na sauke nauyayyar ajiyar zuciya ta ce”Momy don Allah ku ƙyalesa kawai Ni dai a tsorace nake ba sai kun kullesa ba kawai a rabu lafiya”ta ce “to naji amma kiyimun alƙawari kin daina kuka akan batun daga yanzu”
Kamar ta na gabanta ta gyaɗa mata kai tare da cewa momy sai yaushe to zakuzo”
Ta ce”insha Allah ba da jimawa ba Afren na gaishe ki dukda bakya nemanta”jiki sanyaye ta ce “ina ansawa momy ki gaishe ta “
Ta ce “ga ta ma ku gaisa shiru ta yi ta na saurare chan momy ta ce”kinga ta maƙe kafaɗa wai ba ta Amsa fushi take da ke bakya nemanta “
Ta ɗan saki murmushi ta ce”anjima zan kira Video call sai na bada hakuri”
Momy ta ce “haka ya kamata ba Salma wayar”
Ta miƙawa Aunty salma wayar ta na jin sanyi a ranta,
Aunty salma ta fita da wayar a kunnanta suna cigaba da tattaunawa.
Safa na kallon Ibtihal da tayi tagumi ta dinga janta da hira har ta samu ta sake suka ci abinci tare sai shida na yamma ta bar gidan ta na jin damuwarta ta ragu ,
ko hajiya batayiwa bayanin abunda ke faruwa saima ta ɗan saki suna hira da hajiya dukda rabin hirar hajiya ce me yi .
8:30 Sukaji bugowar ƙofa Ibtihal ta bi ƙofar da kallo ganin me shigowar ne ya sanyata tashi ta shige bedroom hajiya ta gorgiza kai ta na maida kallonta ga farin matashin da a ƙalla zaikai 33yrs dogo mai ɗan garin jiki kaɗan ta ce.
“Yau Yusufa ne a gidan nawa lallai Ibtihal ta dawo kusan sati biyu fa rabon da ka taka ƙafar ka gidan nan”