← Book details Ibtihal Hausa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 22

Sashe 16

Ibtihal Hausa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Daga majalisa Kai tsaye gidan Marayunsa ya nufa sosai na yi mamakin yanda yaran duk suka rungumeshi suna murna da ɗokin ganinsa,
Yaran ya dinga ɗauka ya na musu dariya tare da musu wasa bantaɓa tunanin ya iya dariya har haka ba sosai ya ke nishaɗi da annashuwa cikin yaran bai bar Wajen ba sai gab da Magrib ya tsaya Masallacin Ƙofar gidansu ya gabatar da Salla kafin ya nufa ciki kamar yanda ya saba sai ya fara zuwa sashen ummy ya yi sallama da su kafin ya wuce na sa sashen,
Ummy ya samu ita da Lenah da Saudat tare da Matar Sadeq Zenat ,suna ta hira tamkar suna hira da mahaifiyarsu ba suruka ba,
Duk suka gaishe sa cikin girmamawa kafin ya zauna su gaisa da ummy ta tambayesa ya al’amuran ya amsa mata da “Alhamdulillah “ya na kallon Lenah bayan ya amsa gaisuwarta ya ce “me ya sameki na ga kinyi shiru”
Ta na narke fuska a shagwaɓe ta ce “Yaya Ka tuna jiya nace maka zanje asibiti Dubiya”
Ya ce “uhm”
Ta ce “to Wacce na je dubawarce ta bani Tausayi gaba ɗaya jikina duk ya yi sanyi wai yaya ciwon zuciya ne da ita Kuma kar kaga gatanta ko me ya haddasa mata ciwon Zuwa na ta farka amma ba ta iya ko magana saidai ta bi mutane da ido karka ganta yaya Kyakyawa kamar ita ta yi kyanta ni tunda nake ma wlh ban taɓa ga kyakyawa kamarta ba ga da ga zani zatayi kyan hali ni wlh gaba ɗaya ta shiga raina lokaci guda “
Shiru ya yi ya na Nazarin maganganun na ta Kamar bazaiyi Magana ba Sai kuma ya ce “Allah ya bata Lfy”
Ta ce “Amen yaya gobe ma zanje na ƙara dubata”
Ya ce “Allah Kaimu take care “
Ta ce “insha Allah “
Yayiwa Ummy sallama ya na barin Palon su Saudat suka saki jiki suna cigaba da hira Lena na kallon Saudat ta ce “Wai Aunty Saudat me ya haɗaki da Yaya Ashraf yanzu kuma Na ga Sai Fushi ya ke fuskarsa ba fara’a “
Ummy ta ce”Ina ruwanki uwar son gulma Umara ce zamu tafi tare shiyasa ta dawo muke shiri”
Lena ta miƙe ta na nufar sama domin ita a chan take ita ummy ta ce ciwon ƙafa gwara ƙasa ta ce “Tab ni za a mayar yarinya wlh faɗa sukayi kuma zan zuga Ashraf idan ba ta koma ɗakinta ba da kaina zan samo masa budurwa”
Saudat ta miƙe a fusace zata Bugeta ta ruga da gudu ta na sama ta na dariya tasan ta taɓo ta don saudat ba dai masifar kishi ba Ta koma ta na huci kamar zata sa kuka ta ce”Allah Ummy autar nan taki Zaneta zanyi ta rainani”
Ummy tayi murmushi ta ce “kunfi Kusa”
Zenat ma na murmushi ta ce “ai gaskiya ta faɗa “
Ta harareta ta na tura baki gaba Ummy ta ce”Ummy ta ce “kinga Maida wuƙar Ai babu Kishiyarku a gidannan insha Allah”
Da sauri saudat ta saki murmushi duk suka sanya Mata Dariya Ummy ta ce “Allahshiryaki”ta rufe fuska ta na dariya a haka Sadeq ya zo ya samesu Bayan ya zauna an taɓa hirar kaɗan dashi don shi mutum ne marar son magana Ba kamar Ashraf ba Kafin matarsa Ta bisa su wuce part ɗinsu bayan sun kira yaran da suke ɗayan palo suna Wasa tare da yaran Ashraf suka wuce ,

*IBTIHAL*
A ranar Ibtihal ta farka saidai ta kasa magana da motsi sai zuwa washegari cikin ikon Allah ta fara maganar saidai ba sosai ba Kamar bata son Magana,
Dukda haka ƴan uwanta sunji matuƙar daɗin ganin haka,
Duk wannan jinyar da take Maman Yusuf ba ta zo ta duba ta ba amma haka tacewa Abba kullum sai ta yi girki ta zo ta duba yanda take jajinta mata batun ciwon da yanda ta damu zata ɗauka har zuciya,
Yinin Ranar Yusuf A ɗakin ya kusan yini wanda baisan a ran Ibtihal ƙara mata Jin haushinsa Yake,
Daƙyal da taimakon Aunty Aisha ta Daure ta kamata har ta iya takawa ta zo alwala ta gabatar da sallolin da ke kanta a zaune domin tunda ta farka aka sanar mata kwananta nawa kwance su ne a ranta,
Lokacin ana Gama La’asr ne ta na sallar lokacin Yusuf ya zuba mata idanu ya na kallonta Aunty Aisha na gefe na haɗa mata fruit salad su kuma sauran ma su jinyar suna waje har momy da hajja da su Aunty Salma Da sauransu,
Safa ce ta shigo tare da Lena Da ke sanye cikin tsadaddiyar Abaya Har ƙasa ta duƙa ta na gaishe da aunty Aisha da ta amsa mata fuska sake tare da tambayarta Ƴan gida ta ce “Duk suna lafiya ya me jiki”
Ta ce “jiki Alhamdulillah gashinan ma Ta na ta salla amma ta kusa gamawa ku zauna”
Suka Zauna,
Lokacin ne Afren ta buɗo ƙofar ta shigo Gadon ta nufa ta ga ba kowa sai ta Koma waige,Safa ta yi mata Dariya ta ce “Auntyn ta Ɓata”
Lokaci guda ta sanya kuka ta na Tirjewa Ƙasa Safa na shirin kamota Lena ta Taso ta ta na Ɗaukarta cike da sigar lallashi ta ce “sorry My Angel Wasa ta ke maki Your aunty She is with you”
Ta na kallonta cikin idanu ta ce “Where is she?
Ta nuna mata inda ta ke zaune ta salamce sallar ta haɗe kai da gwuiwa”
Da sauri ta dire jikinta ta na rugawa ta rungumota ta baya tare da cewa”Aunty mun ɓata da Aunty Safa”
Safa ta sanya Dariya ta ce”Sorry gimbiyata baki san wasa ba”
Ta juyo tare da tura mata baki kafin cikin hausanta ta koyo ta ce”Ba ni ba ke Kawarki ce My friend now”
Suka sanya dariya Aunty Aisha ta ce”Ja’ira yanzu kin iya Hausan Ashe”
Ta ƙyalesu ta na juyawa wajen ibtihal tare da ɗago fuskarta da ta sadda ta na waro idanu ta ce “Aunty What made you cry? What hurts you”?
Ta faɗa a jere “
Safa ta ce “Kuka kuma”
Sai ta taso tare da matsowa gurin har lokacin hawaye ta ke Safa ta ce”Haba Sis meya faru kuma kina Cikin halin ciwon da ba ason kina saka Damuwa a rai don Allah meyasa bazaki cire abunda ya ke ranki ba nasan duk Halin nan da kike ciki bazai wuce akan tsinannen chan Sharef ba So kike ki kashe kanki Ibtihal kiyi mana asararki,Mom ɗinki na sonki,Dad ɗinki ma Ƙaddara ta rabaku kuma insha Allah sai kun dawo kamar da ,Sannan mu ƴan uwanki na sonki,Ƴarki na sonki”duka familynki na ƙaunarki meyasa akan Mutum ɗaya zaki halaka kanki me ya sa sis?Ko dai son Mutumin nan kike………✍🏽

*ZAMU KAMMALA FREE PAGES NA WANNAN LITTAFIN A PAGE 15 KUNA DA DAMAR FARA BIYAN KUƊINSA TUN YANZU 500 TA WANNAN ASUSUN BANKIN 7026166536 OPAY HAJARA ABUBAKAR LAWAL TARE DA SHAIDAR BIYA TA 07026166536*

_*Miss Hajo ce*_🤙🏿

🪅*IBTIHAL*🪅

~MALLAKAR~
*HAJARA L SADEQ*
(miss Hajo)

MARUBUCIYAR👇🏼
Auren wata tara
Ni da yaya arman
Matar uncle
Najmat abiy
Komai mukaddari ne
Khadijatul Sabren
Ribar so
Mata ta ce
*And now*
*IBTIHAL*

*SHAFIN NAN NAKI NE ASIYA SANI FATAN ALKHAIRI GAREKI SIS TARE DA FATAN MIJI NA GARI*🥰🥰🥰

*DEDICATED TO MY HUSBAND*

🅿️…………………………..*12*

Lokaci guda ta ɗago cikin hawaue ta girgiza mata kai sai kuma kawai ta rungumeta ta sanya kuka mai sauti ta kasa magana,
Itama safa hawaye ta ji sun zubo mata,
Itama Afren sai ta hau kuka,
Aunty Aisha Da ta zuba musu ido kawai ta girgiza kai ,
Yusuf ma idanu ya zuba musu cikin faɗa ya ce “Ohh nagano Watau har yanzu Asararren tsinannan chan ne a ranki shiyasa kika kasa amincemum shekara da shekaru amma wlh da kin cika marar zuciya ke da ba ma zan yarda halittar ɗan adam ce ke ba Saidai Dabba Zatayi wannan Rashin Zuciyar Haba Shiyasa Daga Maganar Aurenmu kinbi kin tada Hankalinki to wlh ko mutuwa zakiyi sai an Auramun Gawarki daga baya na binne ki ba ciwon zuciya ba “
A mugun Fusace Aunty Aisha ta ce”Kai wani irin shashasha ne wai yusuf don uwarka to ƙarya kake ba sonta kake ba Da Allah Wuce ka ba mutane guri kuma karna ƙaraga Ƙafarka a asibitin nan daga yau ficemun da Allah”
Ta faɗa a mugun fusace”
Ya fice ya na Huci don yasan ko giyar wake ya sha bai isa tanka mata ba don Abba sai ya kusa tsine masa akan haka ya na matuƙar ƙaunar ƴan uwansa kuma kullum maganarsa suyi musu biyayya tamkar yanda zasuyi mashi ko ma fiye da haka ya fice aunty Aisha ta ja Dogon Tsaki kafin ta ɗauki Afren da ke kuka ta kalli Safa ta ce”saki biyeta ku dinga kukan marar amfani”

Ta fice da Afren da ke kuka”
Lena ta bita da kallon birgewa don Wlh abunda tayi ya matuƙar burgeta saboda ita kanta ji tayi kamar ta shaƙosa ta wanka masa mari don Haushi,
Daƙyal Safa ta lallasheta suka bar kukan Ibtihal na hawaye ta ce “me ya sa Na rayu Safa wlh nafi buƙatar mutuwa da rayuwarnan”
Chapter 16 · 0% Book details