← Book details Ibtihal Hausa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 22

Sashe 12

Ibtihal Hausa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Lokacin Ibtihal na fitowa ta yafa gyale samar doguwar rigar jikinta harara ta ɓallawa Marwan ya waro ido ya na dariya ya ce.

“Tuba nake Shalelen Abba Ni da wasa na ke fa amma fa ba ƙaramun ƙara miki kyau japan ɗinnan tayi ba ƙanwata”

Ta na zama ba tare da ta ƙara kallonsa ba ta duƙursa ta gaishe da Abba cike da soyayya ya amsa ya na tambayarta ya aka gama karatu ta amsa “da Alhamdulillahi Abba ya hanya ai lokacin da nadawo akace baka nan sai naji dama ban dawo ba sai na jira lokacin dawowarka mu dawo tare”

Abba ya yi murmushi ya ce “ai ni kaina ƴata da nasan Ranar zaki dawo da babu inda zanje na ɗaga tafiyar don na taryo shalelena”

Hajiya ta ce “to ai duk sai ku tashi ku koma”

Duk akayi dariya kafin Ibtihal ta ɗan sake suka fara hira da Marwan wanda rabin hirar zolaya ne don marwan akwai zolaya suna ɗasawa sosai da Ibtihal,

sai 10 na dare suka bar part ɗin ga mamaki na washegari sai ga Hajiya Lubna tare da Abba sunzo gaishe da Hajiya yanda hajiya Lubna keyiwa Hajiya zaka rantse ta fi kowa kulawa da ita da ƙaunarta a gidan har da mata tausa wanda wannan shine babban abunda yake sa take ƙara daraja a idon Abba ya ke ƙaunarta saboda yanda ta ke kula masa da mahaifiyarsa da yanda take basa labarin kulawar da takeyiwa hajiya fiye ma da sanda yake nan ita dai Hajiya saidai ta kalleta amma bata taɓa nunawa ɗan nata ba haka ba ne ba ruwanta kowa yayi nagari kansa tunda dai a zage bata zaguwa haka a dake bata dakuwa ballantana baƙar magana chan taje ta yi shiriritarta ita taga za ta iya (Wlh hajiya kin huta🏃🏼‍♀️😂)

Kwanan Abba huɗu da dawowa ya kira Ibtihal ta samesa a palourn sa sosai tayi mamakin ganin yusuf gefensa “matso ƴata”Abba ya faɗa ya na ganin yanda ta yi shock bayan shigowarta.

Matsawa tayi inda ya umarta ta zauna bayan ta gaishe shi ya amsa tare da ɗorawa da cewa”daman wata magana yusuf ya zo mun da ita kan cewar kun sasunta kanku kin amince zakuyi aure shi ne nace bazanyi amfani da maganarsa ba dole sai naji daga bakinki Haka maganar ta ke”?

Abba ya faɗa ya na zuba mata idanu wanda da sauri ta ɗago ta na kallon Abba kafin tayi saurin janye idanunta ta maida ga Yusuf wlh a tunaninta da wasa ya ke kenan da gaske ne Abunda ya faɗa mata zai aikata.

“innalillahi wa inna ilaihiraji’un wannan wani irin tsaka mai wuya ne ta ya zata iya kallon idon Abba ta ce bata son ɗansa mutumin da ya so ta kamar ƴar cikinsa ya tallafe su ita da ɗan uwanta lokacin da nasu mahaifin ya koresu ya sama Mata Aiki ,ya saya mata Mota,Ya Biya mata maƙudan kuɗaɗe ta tafi Ƙarin karatu da dukiyarsa har ta gama da wani ido za ta kallesa ta ce bata son Ɗan sa ta ya zata fara wata zufa ce ta karyo mata ba shiri Abba na lura da ita jin shiru ba ta ce komai ba ya sa shi cewa.
“ƴata ke nake saurara”Saida ta ja numfashi mai ƙarfi kafin ta ce…………✍🏽

_*Miss Hajo ce*_🤙🏿
🪅*IBTIHAL*🪅

~MALLAKAR~
*HAJARA L SADEQ*
(miss Hajo)

MARUBUCIYAR👇🏼
Auren wata tara
Ni da yaya arman
Matar uncle
Najmat abiy
Komai mukaddari ne
Khadijatul Sabren
Ribar so
Mata ta ce
*And now*
*IBTIHAL*

*DEDICATED TO MY HUSBAND*

*Page ɗinnan naki ne Uwar Faredaƴar Amanata Alkhairin Allah ya cigaba da baibaye rayuwarki ya muna mana Auren Quen muzo jos mu raƙashe*😘

🅿️…………………………..*09*

Ta ce”Amma Abba ya na saurayi bai kamata ya aure ni ba matsayi na na wacce ta taɓa Aure har…….”
Rai ɓace Abba ya Ɗaga mata hannu ya ce “kull kar na sake jin wannan maganar daga bakinki Ai yasan da hakan ya ce ya na sonki amsa kawai nake so ki bayar kina son sa”

Da zuciyar Ibtihal za ta fito Allah kaɗai yasan irin halin da take ciki rumtse ido tayi da ƙarfi ta na jin zuciyarta na tsananta bugawa.

“Abba ya ce”ina sauraronki ƴata babu kunya a tsakaninmu ki faɗamun gaskiya kina son Haɗin Aurenki da ɗan uwanki yusuf”

Ba zato yusuf ya ga ta gyaɗa kai ,

Daga yusuf har Abba wata irin nauyayyar ajiyar zuciya suka sauke Wannan na daga cikin babban burin Abba na son haɗa Aure tsakanin Ibtihal da jininsa Kamar yanda tun ta na budurwa ya so hakan Allah dai bai nufa ba,

Wani irin farinciki ne ya mamaye zuciyar Yusuf baisan sanda ya furta kalmar “Thnks you my Love i love you morethan everything”

Abba ya yi murmushi ya ce “to kodai na baku wuri yusuf”

Yusuf ya sosa kai ya na ɗan jin kunya Abba ya maida kallonsa ga Ibtihal ya ce “tashi kije ƴata Allah yayi miki Albarka Gobe insha Allah zanje da kaina har kano muyi magana da mahaifinki”.

Ibtihal ta miƙe ta na jan ƙafafunta da takejin tamkar ba a jikinta ba Ta na ficewa daga part ɗin Abba hawayen da take ɓoyewa suka fara zuro mata ta kasa kwatanta halin da take ciki ji take anya ba mafarki ba ne daƙyal ta kai kanta ɓangaren Hajiya Wanda bata kai ga ƙarasa shiga part ɗin ba ta ɗuƙursa ƙasar bishiyar mangwaron da ke farfajiyar gidan tare da rusa kuka tamkar wacce aka aikowa da saƙon mutuwar Mahaifiyarta kuka take tamkar ranta zai fita ta kai minti Hamsin a wajen ta na kuka babu alamar tsayawa .

“Ƙanwata”

Marwan ya faɗa da mamaki ya na ƙarasowa inda take wanda da sauri ta ɗago kanta tare da fara pretending goge hawayen hakan ya gagara ai ko
Yaro ya kalleta ya san ta ci kuka”

Tsaye ya yi ya na kallonta da mamaki ya ce “Ibtihal kukan me kike me yake faruwa”

Shiru ta yi ta na ɗasa da kanta ta na mayar da mahawayen da yake ƙara ziraro mata.

Ya na zama gefenta tare da miƙa mata handkchiep ya ce “a tunani na ko zaki ɓoyewa kowa damuwarki bai dace a ce har ni kin ɓoye mawa ba Ibtihal me ke damunki”

A hankali cikin shashsheƙa ta ce “bakomai”
Ya na zama gefenta ya ce “ki faɗamun me ke damunki ƙanwata ko da kina ganin babu abunda zanyi miki sai na taimake ki da shawara”

Daidai lokacin yusuf da ya biyo bayanta ya tunkaro wajen fuskarsa ba alamar annuri ya watsawa Marwan wani kallo tare da cewa”Ubanme kake a nan zaune da matata”

Marwan ya ja tsaki tare da miƙewa ya bar wajen,

Itama ibtihal da sauri ta ruga ta wuce ciki ta na kuka Yusuf yayi ƙwafa tare da bin bayan marwan zai fice ya shaƙosa ya ce “don ubanka uban me ka ce mata”

Ya na masa wani kallo ya ce”ka sakeni kasan dai ba ƙarfina kafi ba da Allah malam “yusuf ya ce “to ko zaka gwada dukan nawa marar kunya ai nariga na gano sonta kake kuma wallahi ƙwalelenka na haramta maka ita har abada domin yanzu haka batun aurenmu ake don haka kar na ƙara ganinka kusa da matata ta”

Marwan ya ja dogon tsaki ya na fincike shaƙarsa da yayi tare da cewa”saika tambaye ta idan na taɓa cewa ina sonta kuma baka isa ba ƙanwata ce dole zanyi mu’amula da ita har abada ko wani ta Aura ba kai ba”

Ya na gama faɗar haka ya fice ya barsa salalo wanda cikin zafin nama ya nufi ɓangaren hajiya ko hajiya da ke masa magana bai kula ba ya nufi ɗakin Ibtihal kwance ya sameta rubda ciki sai rubza kuka ta ce rai ɓace ya ce.

“Ba kuka ba kiyi kukan jini mtswww saikace za a aura mata dodo yanda mata ke nacemun ina wulaƙantasu shine don kin sameni a bulus zaki rainawa kanki wayau ki rainamun kashedi na zo nayi miki daga yau karna ƙara ganinki tare da Marwan ko gaisuwa bance ta ƙara haɗaku ba idan ba haka ba zakiga yanda daga shi har ke ranku zai ɓaci”

Ya na gama faɗar haka ya wulla mata Key ɗin tare da cewa”kin fanshi kanki a wajena Bari naje na samo miki maganin ciwon kai idan kingama koke-koken aure ne dai babu fashi ki sa a ranki kamar har an ɗaura an kai mun ke”

Ya na gama faɗar haka ya fice Ibtihal ta Ƙara sanya kuka Kamar ranta zai fita ita wallahi a yanda takeji muddin da zata samu aljanna ta na fatan Allah ya ɗauki rayuwarta saboda bata tunanin zata iya rayuwar Aure da yusuf shi kansa ba shi da hali ballanta mahaifiyarsa meyasa ƙaddara take zo mata a haka?

ita haka zata ƙare rayuwarta ba ƴanci?meyasa rayuwarta bata da sa’a ne wai?idan ance Aurenta da SHAREF Ƙaddara ne to shikuma Yusuf da me za’a kirasa GANGANCI Ɗayar zuciyarta ta bata amsa domin tabbas ta sake ta auri yusuf ta yi ganganci mafi hatsari a rayuwarta domin yanda take ganin ƙiyayyar ta a idon mahaifiyarsa komai zata iyayi “innalilllahi wa inna ilaihiraji’un ya Allah ka kawomun mafitar kaucewa ƙaddarar nan da ke tunkaro ni Allah idan nayi maka wani laifi na tuba ka yafemun”

Washegari da azababben zazzaɓi da ciwon kai ta tashi ga zuciyarta da takejin ta na mata mugun ciwo ta na harbawa da ƙarfi a ƙarshe dai bata ƙara sanin inda kanta yake ba ko da hajiya ta sameta a haka hankali
tashe ta kira Abba ta sanar dashi da kansa tare da taimakon marwan da yusuf aka kaita asibiti wanda karon farko aka bata gado bayan duk wasu gwaje-gwaje da bincike likita ya tabbatarwa da su Abba ta na Stage ɗin farko na Kamuwa da ciwon zuciya daman tun a wancen lokacin ya faɗa musu ta na gab da kamuwa da ciwon zuciya ayi mata duk abunda zai sanyata farinciki to gashi abunda ba’a son ya faru.

Sosai hankalin Abba ya tashi haka Hajiya da ta kasa daurewa ta sanya kuka ta ce”yaron nan Tsakaninmu da shi da uwarsa saidai Allah ya isa jikata yarinya ƙarama sun ɗaura mata ciwon Zuciya “
Chapter 12 · 0% Book details