← Book details Hasashe Ko Buri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 21

Sashe 8

Hasashe Ko Buri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Kace su nema Baba am, in ya amince to.” aikinta ta ci gaba da yi, can sai ya dawo yana murna an bashi dubi biyar. Bafullatanar da ke wanke-wanke ta kalla ƙaninta da suke kama da juna sosai, kafin ta ce komai sai ga wata mata ta fito tana magana da fillancin.

“Ban kuɗin.” yaron ya kalleta tare da juyawa ya fice, yana ji tana kiran sunan sa 'Moddi.' amma ya shareta. Budurwa da ba za ta wuce shekara 20 ba ta yi murmush. Take ta wani haska, dan a lokacin na mata kallon tsab. Ƙyaƙƙyawace ajin farko, tana haske mai sosai, sannan ga uban hanci ma sha Allah, duk da ta ɗauka ɗan kwalli amma gashin mai uban tsayi ya sauka har gadon baya.

“Dada am (Mama) ya gudu ai, kinsan Moddi da son kuɗi.”

“Zai dawo ai.” matar ta wuja ta koma ciki. Su huɗu suke rayuwa, Ita Fillo, Dada am wato mama amma ba ita ga haifesu ba, kishiyar Mamarsu ce, mahaifiyarsu ta rasu tin suka yara, Dada am ce ta raine su, ita ma ta haihu amma yaron ya ɓace tin yana ƙarami, ko ita Fillo lokacin tana jaririya ya ɓa ce, an dai ce lokacin shekarunsa 6 ne.

Alhamdulillah domin suna rayuwa cikin ni'imar Allah, ba sa samun matsala da Dada am, domin Fillo yarinya ce natsatstsa shuru-shuru. Da dai shiga wani hali sosai da aka fasa aurenta da wani da take mutuwar so, saboda ƙwajin jini dukka 'AS' ne, daga lokacin ta ɗaura aniyar ba za ta ƙara soyayya ba sai bayan ta yi aure, da faruwan al'amarin wata na uku kenan, sannan kusan kullum sai anyi sallama da ita amma ba ta fita sam. Sai ta ce su nema Baba am.................

*KADUNA*

Su uku ne suke zaune suna raha kwanin sha'awa, sam babu mai damuwa a cikin, dan a yanzu suka ƙara tabbatar da Allah yana matuƙar ƙyaunarsu. A yanzu I.B ya riga ya rikita Mymoon da zazzafar soyayyarsa. Yadda kasan asiri koma ya ce sai ta yi, domin kuwa ya iya sarrafa mace fiye da lissafi, hatta mota ta mallaka mai. Shi dai yana cikin alheri dumu-dumu. Sun zama wasu manyan mutane, dan ko su Shamo suna jan kuɗi ba wasa suna target ɗin su mallakar mota. A dai-dai lokacin Abbas ya dawo daga garaji dan alhamdulillah yanzu yana samu ba laifi, wata rana dubu uku ko biyu. Kuma yana jin daɗi in ya samu, kuma yana fatan nan gaba ya fi haka dan haɗama Merry lefe. Bai manta ba a lokacin da ya faɗan masu Abdul ba, dariya suka sa mai suna ganin wautarsa ƙarara amma ya share su dan shi yasan mai ya taka, kuma ya dogara ga Allah.

“Assalamu Alaikum.” suka haɗa baki suna amsawa. Shamo ne ya kalla kayan jikin Abbas ya yi murmushi yana faɗin.

“Aboki, kana wahalar da kanka wallahi, dan Allah ji yadda ka kamo duk ka yi ɓaki ma........... Ka bar wahala Merry nasan za ta taimaka maka amma kai dan aci da Gumi ka ƙi......”

“Shamo bar ɓata miyanka, kasan Abbas, in ya faɗa abu baya sauyawan mu dai mu tayasa da addu'a. Ga wannan wallahi bansan ganinka cikin kayan nan, kuma wannan aikin.....” da sauri Abbas ya fizge rigar da I.B ke miƙa mai yana faɗin.

“Good da ka san ban sauya ra'ayi. Kuma in addu'a ce ku zan yi ma wa.”

“Abbas wallahi muna sonka, bamu son ganin kana aikin mai wahala, kafimu haske amma jibi yadda ka koma, mukan sai wani fresh muke yi.” sai dai ya kalla Abdul da ƙyau, kaman zai ce abu amma ya fasa tare da shigewa bayi dan yin wanka. Yasani ba sai sun faɗa mai ba, suna sonsa sosai, kuma ba sa son aikin da yake yi, suna yawan faɗa mai, su za su nema amma shi ya wuta sai suba shi amma ya ƙi sam. Kuma ba ƙarya wani fresh suke dan kuwa ba ƙaramin daɗi suke ci ba. Haka zai dawo ya tadda uban leda tsire, balango, drinks, marada kuwa hmmmm, sannan komai suka ci sai sun aje mai, wani lokacin ya ci in sun matsa. Bayan ya fito wanka ya samu suna shirya wa tare da cika ɗakin da ƙamshi.

“Ka shirya mu ajeka a ƙofar gidan su Merry.” I.B ya faɗa yana taje ɗan gemunsa. Dayake yana son zuwa, aikuwa suka shirya dukkansu. Sun yi ƙyau kaman za su wani taro, Abbas ne ya zura wata jallabiyarsa, sun mai tsiya da ya cire amma ya yi banza da su. Mota suka hau, a hanya Abbas ya ce su tsaya bayan Abdul ya faka dan duk sun iya mota hatta Abbas ya iya. Bai jima ba ya dawo riƙe da leda baki.

“Mutumina me aka siyo ne?.”

“Merry na son awara shine na siya mata.” dariya suka kwashe suna kallon Abbas da hankalinsa ƙwance kuma ya yi banza da su. Shamo da ke gefensa ya dafa kafaɗarsa yana faɗin.

“Abbas, da baka siya ba, taya mace kaman Merry ta ci awaran bakin hanya.”

“Hmmmm za ta ci.” ya faɗa da confidence ɗin sa dan yasan duk abin da ya ba ta cike da nishaɗi yake amsa kuma bai ta ɓa ganin sauyin yanayin a fuskarta ba, shiyasa ko ba yawa yake siya mata abu in dai yasan tana so. Yanzu haka awaran dari biyar ya siya mata............✍️
END.

> Tab akwai ƙura fa, hmmmmm mudai na mu ido, 🥱🙄🙄🙄🙄🙄

> Hmmmmm ✍️✍️✍️✍️ ba wasa *HASASHE KO BURI* tafiyar wannan na daban ne domin akwai abubuwan ban mamaki, taɓa zuciya, ruɗani da zalama irin na ɗan adam. Mu daihe zuwa.......... PAID BOOK ne 😏 by PRETTY SK NOVERLIST 🥰

🔥 *Let’s goooo!* 🔥
Hit that LIKE 👍 if you're truly *ready for the ride*!
Because *HASASHE KO BURI* isn’t just a story —
*it’s an experience.* 💭✨📚

✍️ _By PRETTYN JAJIRTATTU_ 💕

https://chat.whatsapp.com/LQFBwo1tifs84ZuT6X2xS9?mode=ac_t

*_HASASHE KO BURI_*

_SADAUKARWA_
*🌟 I proudly dedicate this platform to all the strong and creative minds of our team — JAW (Jajirtattu Writers Association).*
You are more than just writers — *you are voices, strength, and inspiration!* ✍️💪

🕊️ *May Allah keep us united, uplift us, and make our pens a means of positive change.*

Much love and respect to each and every one of you. ❤️🔥
*Keep shining, JAW family!* 🌺

https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.

💔 *_HASASHE KO BURI_* 💔

> 📖 A powerful story filled with dreams, struggles, and destiny!

💡 *Ka shirya?* Wannan ba labari bane na wasa — *it’s a journey into the heart of dreams and reality!* 😍

🛤️ *Rayuwa tana tafiya...* _Kowa na da *burinsa*, amma ba kowa ne ke iya cimmawa ba. Some dreams are *sweet hopes*, others are silent battles_💭⚔️

PAGE1️⃣3️⃣⏩1️⃣4️⃣

*ABUJA*

Misalin ƙarfe 8:30pm, Ukasha ya kira wannan numbern, sai da ya yi kira uku tukun aka ɗauka, wani dakakkiyar murya ce da mai amsakuwa a cikin kunnansa, bayan sun gaisa Ukasha da duk da bai ga mutum ya mai ƙwarji ya ce.

“Baba am, ɗazu ne na ga Fillo, shine na nemi ta fito na gabatar da kaina gareta, sai ta aiko sai na fara magana da kai, shine na ke neman izini.” yana ji mutum ya ja dogon numfashi.

Shigowarsa kenan ya zauna a parlour, Kallon Fillo ya yi take ci abinci tana kallo, shi ya ƙosa ya aurar da ita, saboda ya gaji, a ƙalla a yau wannan shine na shida a kiransa.

“Gobe ka zo na ganka.” take ya mai kwantance tare kashe bayan dan ko godiyan Ukashan bai amsa ba. Shuru ya yi dan a yanzu Fillo ce damuwansa akan wanda zai aura mata, ba wai ba ta masu bin ta bane, sai dai da yawa sha'awarta ke kawo su, kuma yana gane haka, so yake Allah ya haɗa shi da wanda zai ya amsa da ya mai da amanar Allah zuwa garesa. Babban abin farin cikin shine Fillo duk abin da suka za ɓa mata ba musu shi take accepting.

“Bingel am ( Ƴata ko ɗana) waye aka kuma ba wa numberta?.” da ya faɗa da Hausa dan shi ya ƙware da Hausa sosai.

“Baba am, bansan shi ba nikam.” ta mai da mai da fillanci.

“Voɗi ( yayi kyau).” take Dada an ta fito dan ba tasan ya shigo ba.

“Jabɓama ( sannu dazuwa), Awarti?( Ka dawo?).” ya ɗaga mata kai. Sai ta nufa kitchen Dan haɗo mai abinci.

*Barcin ya ɗauke da da wuri, shi kam Umar ya dage, sai haɗa numbers yake amma number ɗaya yake so ya kuma jarrabawa sai dai daga kira an ɗaga ya yi magana an kuma kashewa, yanzu ya yi kira na huɗu kenan, take na biyar na shiga aka ɗauka.

“Assalamu Alaikum”

“Uban wa ke magana." Muryan gardi ya dakeesa. Sai ya ma ze dan ba yau ya saba kiran maza ba a haɗe-haɗen number.

“Ka ya ƙuri, mistake ne, wata nake nema.”

“Ka kira number mata ta kace mistake ne, dama zargi ta na ke yi, to Allah ya tona muku asiriiiii.” ƙit Umar ya kashe kiran tare da sanya wayar a fightmood tare da kwanciya yana faɗin.

“Zargin uban me, ka mannamin hauka.” daga haka ya shafa addu'ar barcin yana rufa da duvet................

*KADUNA*

A bakin get ɗin gidan su Muheey suka faka, wannan shine karo na biyu da ya zo, bayan sun ɗan jima sai ga ta tafito cikin wata arniyar less maroon, ta yi mugun ƙyau haka kuma sai wal-wal take yi, tana isowa ta sakar mai murmushi tana mai bismillah da ya shiga. A cikin motan suke hanke yadda ake kallon love, sannan suka riga mota, a ɗayan layin suka sauke Abbas, dan ko kusa da gidan ba su ƙarasa ba saboda hango masu bindiga. Dariya Abbas ya musu sanan ya sauka, su kuma suka bar area dan a ɗan kwai nisa tsakanin su da Mymoon.

Mymoon duk ta fi nisa dan haka still, Abdul ya fara sauka sannan I.B ya amsa tuƙin motarsa ya nufi gidan su Mymoon.
Chapter 8 · 0% Book details