← Book details Hasashe Ko Buri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 21

Sashe 20

Hasashe Ko Buri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A kwana bakwai nan yanda kasan sun tafi yawon shakatawa ne dan kuwa kullum suna tare, suna yin chat, da yake sun ta fi da power bank kusan guda huɗu manya-manya wadanda har ila yau basu kare ba.

Ta cikin niƙaf ta sakar mai wani murmushi, tana jin san Haidar a cikin zuciyar. Ta tina chart ɗinsu na ƙarshe.

“Wace irin mace kake so?.”

“Sak ke." Murmushi ta yi sannan ta ce.

“Eh, amma a ra'ayinka ya kake son mace.” a lokacin ya jima kafin ya ce.

“Ina son mace mai juriya, mau baki dan ta dinga ƙwatar kanta a wajen kishiyoyin ta.”

“Wai kana da aure ne." Sai kawai ya fizge wayanta dan yana kusa da ita sannan ya ce.

“A'a ba mata na bane, matan Abba na ne, ba su da sauƙi, mace dai-dai su suke buƙata." Ta so ta ce wani abu amma sai ta fasa.

Numfashi ta ja, tabbas ta yi kuskuren faɗa wa soyayya da wanda ba ta sani ba, hakan ba shine illa ba, shin wanda suke nemanta ba za su bar Haidar da rai kuwa muddin suka sani, ta yi kuskure sosai da ta faɗa wa tarkon Haidar na soyayya. dogon ajiyan numfashi ta kuma sake wa sa'annan ta rinsa idanun da nake cikin nikaf ta buɗe su, sun ja sosai.
Mamakin yadda ta sake da shi take, dole ta nisanci kalmar soyayya domin duk wanda ya yi gangancin kusantar rayuwarta, to kuwa ya na kira ma kansa matsala ne, domin ɗayan-biyu ne ko mutum ya rasa ransa ko mutum ya zaucewa.

Ba ƙaramin abu bane a wajen su hake mutum, sai dai ta dogara da Allah kuma shi ne majibancin al'amura, shi zai mata tsari ga ku duk masu ganin bayanta, mutum uku sun hata natsuwa, sun jakula mata lissafi..............
END.

> Cab Maryam Bahaushiya 🙄🙄🙄🙄🙄. Hmmm akwai abu fa. Ku kuma masoya sannunku *Haidar da Ameeratulkhair* ka ga Abubakar a gefe, sannan har yanzu ba musan wacce ita ba.......muje zuwa dai✍️

🔥 *Let’s goooo!* 🔥
Hit that LIKE 👍 if you're truly *ready for the ride*!
Because *HASASHE KO BURI* isn’t just a story —
*it’s an experience.* 💭✨📚

✍️ _By PRETTYN JAJIRTATTU_ 💕📖

[9/14, 08:00] PRETTY SK NOVERLIST: https://chat.whatsapp.com/LQFBwo1tifs84ZuT6X2xS9?mode=ac_t

❤️ _I love you deeply, Habibah. Always and forever._

Much love and respect to each and every one of you. ❤️🔥
*Keep shining, JAW family!*
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_

🌟🔥 *HASASHE KO BURI* 🔥🌟

*📖 A powerful story filled with dreams, struggles, and destiny!*

💡 *Ka shirya?* Wannan ba labari bane na wasa — *it’s a journey into the heart of dreams and reality!* 😍

PAGE3️⃣9️⃣⏩4️⃣0️⃣

_Bayan wata biyu, abubuwa sun faru da dama wasu na daɗi wasu marasa daɗi, bari mu garzaya kowane bangare dan ji me ya faru a cikin wata biyu._

*UKASHA*

Wani aiki ne babba ya taso mai, dole ta sa yabar ƙasa, dan haka aka sa bikinsa saura wata biyu ta kuma kowane bangare suna ta shirye-shirye gadan-gadan, duk da yace shi ba ya buƙatar komai daga mace sai mace kawai yake so a kai cikin gidansa a yanzu haka ya washegari ne ɗaurin auren Ukasha, dan haka gaba ɗaya ba shi da wani natsuwa, duk da komai kuɗi kwai yake turawa, ba ƙarya ya saki kuɗaɗe domin kowace sai da aka mata akwati guda sha biyu, kuma ya yi ma kowace kaya irin na al'adar su, ya yi ƙoƙari fiye da misali, dan ko ina sai maganar wannan auren ake yi. Sannan duk ya samu fahimta mai kyau ga dukka matan, kuma yana fatan babu mai bashi matsala a ciki, sai dai tun kafin auren, Fillo ta gama mamaye mai zuciya, abun har mamaki yake yi sai dai ba'a mamaki da ikon Allah, sannan baisan dalili ba yana son ganin Ashake, ita kuma masifarta da rashin hakurinta na burge sa, yana son zuwa wajenta hira dan kuwa yana sha sosai, sau ran biyun kuwa suna girmamasa sosai kuma yana jin daɗin haka.

*SAMARI*

Su Shamo kuwa sun gama shirye-shiryen tafiya US domin kuwa sun kammala jarrabawan su, basu ji sakamako ba, sun c daya fito sai a tura musu. Yau ne tafiyar kuma sun gama shiri tsaf, washegari ne tafiya US, hankalin su a ƙwance dan sun gaba biyan kuɗin komai, ba karamin kuɗi suka kashe ba amma da yake a yanzu kuɗi ba komai bane a wajen su, suna wasa da kuɗi, dan dai can ɗin aikin za'a fi samu da ba in da za su, so domin ƴan matan su sun tsaya musu especially ma I.B dan a yanzu ba ƙaramin kuɗi yake da shi ba, sai dai duk ya sun siya filayen kuma ta hannun Alhaji, sannan ya a dana takaddun sosai.

Shamo da Abdul sai da suka san yadda suka yi aka ɗaura musu aure da ƴan matan su kafin su tafi, da cewa aiki yakan kama ƙasa sai a turo su kawai, Muheey ce da kyar mahaifinta ya yarda da hakan dan shi bai kamata mace ta yi aure kuma ta ci gaba da zama a gidansa amma ba yadda ya iya, dan Muheey ta nace, dan a tinanita kar ya je can, ina ya ga fararen fata ya ce ya fasa da ita.
Bayan hargitsin aka ko ɗaya musu aure, ita dai Ma'esh ba'a samu matsala ba ta bangarenta domin kuwa yana magana aka ɗaura auren da cewa bayan wata biyu za ta bi shi ita ma, karya ba'a yi taro sosai ba amma fa an kashe kuɗi. I.B ma yaso haka amma shi babu dama sai dai shi daya dawo ko ta tsiya sai sun aure juna.

*Mymoon*

Tun bayan kammala jarrabawarta Dad ya hanata fita ko'ina, sannan ya mata tambayar akan ina take kai kuɗaɗe dan wasan kuɗin na ta ya yi mugun yawa, haka motocin ta guda biyu duk babu yanzu, da ya tambaye ta sai ta ce.

“Ai tana da hankali, tasan me take yi da shi, ita ba yarinyar ba ce." Dad ya gaji, shi yasa ya kulle gaba ɗaya account ɗin ta, sai dai ba tasan Dad ya gane I.B ke hure mata kunne ba, kawai ya share zancen ne, abin da yafi damun shi bai wuce number Taj da baya shiga kullum.

Zauna yake a kan kujera idonsa na kan tv amma sam baya gane me ake yi a cikin tv domin gabaɗaya kwana biyu ne yana cikin damuwa, saboda sauyawan Mymoon, bayan kuɗaɗe da take wasa da su yanzu haka kamfaninsa guda ɗaya ya ruguje duk saboda hannun jari ya karye a ciki kuma ita ke rike da wannan kamfanin, a yanzu abin ya ishesa ne shiyasa ya zuba mata ido tare da ɗaukan tsattsauran mataki akan ta. wayarsa ya ƙara ɗauka sanana ya kuma kiran numbar nan sai dai kamar kodayaushe in ya kira ba ta shiga, sai dai mai yana kira na biyu wayar ta fara ringing, da sauri ya gyara zaman sa yana mai fatan Taj ya ɗauki wannan, kiran sai dai katse har sau uku, sai ya ajiye wayan yana mai tunanin gobe dole ya tafi dubai domin dubo shin lafiya yake, shurin ya yi yawa, baya kwana biyu ba tare daya kira su ba, amma tun sati biyu baya bai kira shi ba, take wayarsa ta hau ringing da sauri ya ɗauka ganin number Taj ne, picking ya yi yana kai kunnensa take wani dakakkiyar muryar mai cike da amu ta doki kunnensa, gaishesa ya fara yi cikin ladabi, sa'annan ya amsa yana mai ce wa.

“Taj ina ka shiga ne, me ya samu number ka baya aiki, ai da zuwa gobe nan zan shigo dubai ɗin, shirun ya yi yawa meke faruwa ne." Ya kai maganar cikin ɗan damuwa, sai wannan murya ya yi murmushi wanda yake jiyo sautin ta ta cikin wayar sa'annan yace.

“Haba Dad ina cikin koshin lafiya, abubuwa ne suka min yawa sosai, so nake ma in kiraka in ce maka gobe zan dawo Nigeria."" Baisan lokacin da murmushi ya kwace masa ba, sai ya ce.

"Kamar kasan neman ka, nake yi ruwa a jallo, goben dai zaka dawo."

” Eh insha Allah Dad, zuwa goben nan za ka ganni na dawo, fatan duk kuna lafiya lafiya?."

“Alhamdulillah, sai dai akwai yar matsala amma sai in ka iso ɗin.”

“Toh shike nan Dad, ina godiya Allah ya saka da alkhairi.”

“Ameen yarona.”

“A huta lafiya." daga haka ya kashe kira yana mai jin wani nishaɗi da jin daɗin gobe Taj zai shigo, ji yake kamar ya zubar ruwa a ƙasa ya sha dan murna.

Fitowar ta kenan daga kitchen, ta ji wannan hirar Dad yake yi, take ta kuma haɗe fuskan, dan dama ba ta cikin walwala kwana biyun nan, tsaki ta ja tana mai ayyana cewa.

"Ya zo din wallahi wallahi bazan aure Taj ba, gaskiyar I.B gashi ina gani wani zai aureni saboda kuɗi.

“Toh Alhaji mu dai zamu tafi.” Faɗin Abdul yana saba jakkan.

“Shike nan Allah ya tsare hanyar da ku isa ku tabbatar kun samu kun kira ni domin V.I.P ne ba za'a haɗa ku da sauran mutanen da kuka gani ba." Alhaji ya faɗa yana ƙara gyara babban rigarsa.

“Allah ya tsare min ku, fatan sa'a." Faɗin Abbas jiki a mace, wannan shine karo na farko da zasu yi tafiya ba dukkansu ba, daga haka Shamo da Abdul da kuma I.B suka shiga wannan babbar motar dake ɗauke da samarin maza kusan guda goma a ciki, Abbas in da yake ya ɗaga musu hannu jikin sa babu laka domin bai son suyi tafiyan nan ji yake kaman ya bisu amma ina yanzu haka ya kammala shiri ne na tafi aybuja, sai da motar nan tashi ta bar wajen sa'annan ya kaɗa kansa tare da jakan bayan sa, tasha zai nufa daga can zai nufa Abuja, Alhaji na kallon Abbas ya wuce sai ya girgiza kai tare da faɗin.
Chapter 20 · 0% Book details