← Book details Hasashe Ko Buri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 21

Sashe 18

Hasashe Ko Buri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Da ace washegarin ranar ka faɗa min, to da yanzu kun haifa min yaro, amma ka wani ɓoye min, toh wannna number ne abu mai sauƙi ne dab ba sai na yi amfani da system ba, yarinyar akwai basira tasan cewa number ta da cire za ka iya samu domin Code ta cire, kuma na Mtn ne, dan haka number biyu zan baka ka kira a ciki dole a samu ɗaya, bayan 070, sanan 3 ko 6.” ba musu Umar ya fara sanya 6, sai dai number ba ta aiki, sai ya sanya 3 amma ya kira har sau huɗu ba'a ɗauka ba.

“Karka damu, a ciki tabbas akwai, ni yanzu so na ke na leƙa Zuby dan mu gaisa.”

“Okh, hope ka kammala fitar da taswiran asibitin."

“Eh, yanzu zan turo maka ta Email, ka ƙarasa komai sai ka kira mutumin.” daga haka Ukasha ya ɗauki car key yana barin office ɗin. Company biyu garesa ɗaya _ARCHITECT / CIVIL ENGINEERING SERVICES._ Sai kuma _REAL ESTATE DEVOLOPER. Yana Gina gidaje, offices, estate da haya da siyarwa, yana samun kuɗi ba ƙarya.....

Gaisawa suka yi cikin sakin fuskarka, ita dai Zuby akwai ta da fara'a sosai.

“Ba ki ji sosai?.”

“Eh bawani can ba amma na iya.”

“To yi mana inji.” sai ta ɗan jingina da motarsa tana ce wa.

“Sunana Zuby, Ni Kanuri ce, kuma ina alfahari da yaren na, akwai mu da tsafta, ga ƙamshi, uhmmm kuma muna da tsafta sosai. (Inji Zuby, In Kanuri mana, kuma inji togo na, wa so gaji, wa lahi, uhmmm wa so tsatfa sosai.) Sai ya yi dariya.

“Eh kaɗan-kaɗan dai haka, (E, kaɗan kaɗan, dewa wo.).”

“Yaren akwai daɗi, bara na gudu sai zuwa wani lokacin.” Daga haka suka yi sallama yana barin wajen, murmushi ta saki dan sun haɗe idanu kuma ta sanya wannan kwallin.

*KADUNA*

Yau ma wani filin suka ƙara siya, ko bayan da suka koma ciki school, suka riski har an gama lecture, dan haka suka zauna suna hira.

_Shamo da Muheey_

“Yanzu ni da so samu ne, a ɗaura mana aure, da munje in aikin ya kama ƙasa sai ku biyo mu.” ya faɗa da sigan jan hankali, sai ta yi wani murmushin.

“Why not! Ai hakan ya yi sosai.” ta faɗa tana imagine ganinta a jirgi.

_Maryam_

Ita kaɗai ce zaune akan a sit ɗin ta, yau ma Abbas yana je gareji, murmushi ne yalwaccen akan fuskarta, dan baya gajiya da mata ƙyauta ko ya ye, kuma hakan na faranta mata rai sosai, yanzu haka kati ya sama mata na 1k, shine ta ke jin daɗi. Lumshe idanunta ta yi dan jiya ta ji daɗin labarin da ya zo mata na aiki a Abuja, ita ya fiye mata barin ƙasa sau dubu....

_Abbas_

Kamar kullum sanye yake da kayan aikin sa, hannusa duk ya ɓa ci da ɓaƙin mai, dan yanzu ya fito daga ƙasan wata mota, sai ya shiga dan kwada aikin ya yi. Aikam motar ta tashi, sai da zagaye garejin sannan ya dawo.

“Oga komai normal.” sai Ogan ya jinjina kai dan akwai wani spaner da ya riƙe da baki dan shima ƙarƙashin wani motan zai shiga. Sauke ajiyan zuciya ya yi dan wannan motar ta hawalar da shi sosai, amma gashi ta tashi. Bayan Ogan ya gaji ya fito dan motar ta ƙi yin yadda yake so, Abbas ne ya shiga take motar ta tashi, aikam Ogan ya dinga sa mai albarka, yanzu kusan Abbas an yayesa dan abu ɗaya daya gani shike nan, sai ma in ya yi yafi na wanda ya koya mai. Bayan sun yi sallar Azahar suka zauna cin abinci, bread da Pepsi mai sanyi suka siya, suna ci suna korawa, sannan ana hira...........
END.

> Kuna tinanin me nake tinani kuwa..... Anya ba Zahra mai girkin gidan su Haidar ita ce wacce Umar ke na ma ba, mu je zuwa.....

> Ukasha an kusa dai, Ni ma dai bara na kuma faɗin maganar Umar, Allah ya kai mu dai...ameen.

🔥 *Let’s goooo!* 🔥
Hit that LIKE 👍 if you're truly *ready for the ride*!
Because *HASASHE KO BURI* isn’t just a story —
*it’s an experience.* 💭✨📚

✍️ _By PRETTYN JAJIRTATTU_ 💕📖

[9/14, 08:00] PRETTY SK NOVERLIST: https://chat.whatsapp.com/LQFBwo1tifs84ZuT6X2xS9?mode=ac_t

❤️ _I love you deeply, Habibah. Always and forever._

Much love and respect to each and every one of you. ❤️🔥
*Keep shining, JAW family!*
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_

🌟🔥 *HASASHE KO BURI* 🔥🌟

*📖 A powerful story filled with dreams, struggles, and destiny!*

💡 *Ka shirya?* Wannan ba labari bane na wasa — *it’s a journey into the heart of dreams and reality!* 😍

PAGE 3️⃣5️⃣⏩3️⃣6️⃣

_KANO_

A kwance ta riske Abubakar a kan carpect, sai ta fita masu shara ta kira, wasu matasa, Usman mai shara, Nuhu mai cefane da Adam mai girki. Su suka kama shi suka mai da shi kan kadon.

“Adam me aka girka ne?.” Adam da ba zai wuce sa'arta ba ya ce.

“Madam, Doya da ƙwai.”

“Okh, Nuhu zan tura ma kuɗi kaje kasuwa dan yin siyayya, daya dawo Adam ka min dambu.”

“To Madam.” suka amsa tare sannan suka yi waje. Sai ta koma ɗakin, ruwa ta samu ta yayyafa mai amma bai farka ba, sai dai barci mai nauyi ya ɗauke sa.

“Ka yi wani tunanin da ya motsa aljanun da Mai sittin goma ya aiko kenan, dole haka ya same ka, na ce ka dena ta kura wa kanka da sanin kai waye amma ka ƙi ji, shike nan.” daga haka ta nufi part ɗin ta..........

_Washegari_

A ranar suka fara aiki, kuma cikin ikon Allah a waje ɗaya sun samu abubuwa masu yawa. Komai Ameeratulkhair ta gani sai ta rubuta, shi kuma Haidar ya ɗauka, haka dai suka wuni, shi har mamaki yake dan da handglobe take rubutu, a ransa ya ce 'Ameeratulkhairi, ko hannu ba a so mu gani kenan hmmmmm.'

A wani wajen suka kuma kafa tantina, sai dai Ameeratulkhair ta fara gajiya da kayan jikin ta domin kuwa, hijab ne four yeard, sannan ta sanya atamfa doguwar riga a ciki, gaba ɗaya iska ba ya ratsa da kuma niƙaf ɗin ɗaurin cikin hijabi ta yi, ga safa hannu da ƙafa. Shuru ta yi tana mai kallon yadda kowa ke raha daga gefe can, wayarta ta ɗauka sannan ta tura ma Haidar saƙo, dan a iya wunin yau sun wani shaƙu sosai.

“I need your help." Shi ya gani ta tura mai, sai ya miƙe ya isa wajenta.

“Khair, meke faruwa ne?.” sai ta yi mai alamana da ya zauna, zama ya yi, sai ta kuma mai typing.

“Sai zuwa gobe ne zamu isa masauƙin koh?.”

“Eh.” ta kallesa.

“Gaskiya ba zan iya tsallake yau banyi wanka ba.” sai ya yi murmushi.

“Dole sai dai gobe, Ni kaina haƙuri na yi, dan na iya wanka kaman ƙwaɗo.” ta tura mai Emoji na dariya, sai kuma na damuwa.

“Menene, Gimbiya ta.”

“Mamamki nake yi, kai baka sanni ba, ba kasan ya nake ba amma wai kana sona.”

“Zuciyata ta gani kuma ta yaba ne.”

“Zaka iya min alfarma ɗaya dan Allah.” sai ya ɗaga mata kai yana kallonta, so yake ko ƙwayan idanunta ya gani, amma babu dama. Jin saƙo ya shigo ya kalla wayan.

“Minti 30 nake so na yi a cikin nan, dan Allah kar wani ya zo, ina son na sauya tufafi kuma na ɗan sha iska."

“Yadda kika ce, zan miki gadi, a huta lafiya.” ya faɗa yana barinta a wajen. Zip ta zuge na Tintin ɗin sannan ta buɗe na sama yadda iska zai dinga shiga. Hijab ta fara cirewa sannan niƙafa da safa hannu. Lumshe idanunta ta yi tana ɗan kwanciya akan ƙaramin tabarma mai kama da katifa. Fuskar fayau take, haka kuma gashin idanunta sun kwanta sosai baƙaƙe dogaye, yadda kasan dai wata balarabiya, akwai ƙyau fiye da misali, sai ma da ta miƙe, hmmmm mace iya mace mai cikar halitta, akwai jiki dai-dai, sannan Allah ya ba ta dukiyar Fulani masu cika da ɗaukan idanu, doguwar rigar ta cire sannan ta sanya wasu riga da wando marasa nauyi, haka ma hijab ɗin ta sanya mai saukin nauyi, sai ta zauna, ta jima a haka kafin ta kuma rufe fuskarta ta sanya safar ƙafa da hannu, fitowa ta yi ta nufesu dan yanzu tana jin iska sosai.

“Sir Haidar, wannan matar aure ce ko?.” wani ya faɗa yana kallon Ameeratulkhair take nufi su.

“A'a amma soon zan yi wuff da ita.”

“Gaskiya ka yi sa'a akwia kamun kai.”

“Haka ne, iya su sun wadata zuciyata akan ta.” ya faɗa yana kallon taba zama kusa da masu yin girki, hannu kawai ta ɗan ɗaga musu.........

_Abubkar_

Cikin dare ya farka da sunan Allah, kallon kansa yake da mugun tsoro dan yadda jikinsa ya jiƙe da zufa, da ƙyar ya watsa ruwa sannan ya fito sallolin dare da ya manta rabon da ya yi shi ya raye daren dashi, daga nan ya dasa karatun Alqur'ani har asuba ta yi, wani iska ne ya ji na daban na shiga jikinsa.

Misalin 7:30am na safe ya bar gidan lokacin ko Daling ba ta farka ba, abubuwa da ya ne ke masa mugun yawo a cikin kansa. Haka dai ya kusan wuni babu abin da ya iya yi a gidan Tvn. Files ne ya shiga dubawa bayan ya ga wanda yake so ya duba sannan ya yi waje tare da nufin wani address da ya bincika, ya sha wuya sosai kafin ya gane gidan domin bai taɓa zuwa unguwar ba, ya ɗan ƙarasa yana kwankwaso kofar gidan, anjima sosai kafin aka buɗe gani namiji tsaye yasa ta tsaya tana kallonsa da mamaki, sai ya gaisheta yana cewa.

“Na zo gurin mahaifiyar Ameeratulkhair ne, dan Allah tana nan.” sai ta ƙara jigun take ta ɗan saki fuska sanan ta mai iso bayan ta sanarwa mahaifiyar Ameeratulkhair ɗin.

A falo ya zauna, ƙanwar Adda ta ɗibo mishi ruwa, bai sha ba sai ya kuma ƙara gaishe da su cikin girmamawa, suka amsa sai Adda ta ce.
Chapter 18 · 0% Book details