← Book details Hasashe Ko Buri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 21

Sashe 21

Hasashe Ko Buri Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

“Allah sarki Abbas, baka da rabon wahala, Allah ya soka, Allah kuma ya ce ce ka, kai mai sa'a ne kuwa, abokanka kuwa ka musu kallo na karshe kenan, dan har abada abadan ba za ka kuma ƙara ganin su ba.” Ya faɗa hakan yana mai murmushi, sai ya ciro wayarsa yana mai kai kunne.

“Hello, motan ta tashi sun tawo, to shike nan ina godiya, a miƙa min godiya wajen *Giji Zulƙu* ina matukar godiya kafin zuwa dare na zo, kuma ina farin cikin da Mamba a cikin ƙungiyar halaka.” daga haka ya kashe wayan yana fada yana wai wani murmushi, ya tabbatar ba mutane kusa da shi shiyasa ya saki jiki yake magana a haka, shiga mota ya yi yana mai barin wajen cike da annashuwa.

*ABUJA*

Gabaɗaya Sumayya ba ta cikin nutsuwar ta, tana cikin wani hali, ta ji haushi abin da ya faru, a ce kamar ita mai aji ƴar kwalisa, cikakkiyar mace budurwa mai ji da dukiya tana neman wani amma yake wulakanta, da ba ya ɗaukar number ta, sai dai ta yi mai saƙo ta whatsApp, sai dai ya yi ta gani amma baya reply, daga ƙarshe blocking ɗin ta yi a shekaran juya, tin daga haka take cikin wani yanayi dan ta rasa makama, ba ta san me za ta yi ba, ji take kamar ta je har kaduna ta samu Abbas ta ci mai mutunci ta ji dalilin da yasa yake wulakanta ba kamar ita mai aji tana kula shi dan talaka amma baya ga ta gabansa, ta fara bin abin a hankali amma ta ga abun ƙi yiwuwa, yanzu gashi an ɗauka kusan wata biyu da fara kulawa da ta yi, ba ta manta kalma na karshe da ya ta ɓa shiga tsakanin su ba, ce mata ya yi.

“Sumayya ina da wacce nake so kuma na mata alkawarin zan aure ta, dan haka dan Allah ki fita daga sabgata, in tasan da wannan maganar za ta yi fushi dani sosai, kuma fushinta tamkar ana zuba min garwashin wuta ne a jikina, dan Allah ki rabu da ni." abin da ya faɗa mata kenan ta kasa mai reply domin voice ya mata take kuma ya yi blocking ɗin ta, ta yi kiran duniyar nan bai ɗauka, saboda shi ka canza lambobi da dama amma duka a banza, sai dai me ta kai karshe so take ta faɗa wa mahaifiyar ta, koda kuwa ba za ta so ta ji tana son ɗan talaka amma ta taimaka ta yi mata hanya, rayuwarta na gaba da rugujewa in dai ba ta auri Abbas ba, ji take tamkar ta samu attack na zuciya.

Da sauri Safna ta faɗo ɗakin tana cewa.

“Sumayya! Sumayya!! Sumayya!!!, albishirinki.” gaba ɗaya zazzabi ya rufe ta, dan ko tana ji a yau ɗin nan dole sai ta je asibiti an duba lafiyar ta, a hankali ta budye bakinta ta ce.

“Ke da Allah banda lafiya, ki ƙyaleni ke Please.”

“Na kawo miki maganin zazzaɓin.” idanu ta buɗe a hankali, tana kallon Safna dake tsaye akanta.

“Ina wannan tsinanen yaron da kika haukace ma wa, yanzu na gan shi a cikin haraban gidan nan, yana tsaye da jakan bayinsa ya zo yana neman Abban Haidar.......” ai ba ta ƙarasa maganar ba ta zabura da sauri tana cewa.

“Ab......Ab....Abbas wai.”

“Eh Abbas, yana cikin gidan nan a yanzu haka.” ba ta damu da shigar dake jikinta ba, ta yi waje saboda girgiza kai tana cewa.

“Wai Sumayya ta haukace da yawa.” sa'annan ta ɗauki mata hijab ta bi bayanta.

Tana tafiya tana haɗawa sauri har da haɗawa da gudu-gudu ta fita haraban gidan, tsaye ta hangi Abbas yana mai latsa wayarsa gefen gate, shi ga nufa da sauri-sauri har ta isa gaban sa, ta isa tana haki, kallonsu take yi tana mai yi mai kallon tuhuma, shi kuwa sai a lokacin ya ju ya kalleta, kallo ɗaya ya yi mata sannan ya ɗauke kansa, domin kuwa rigar bacci ne a jikinta mai ragaraga wanda aka ganin kalan kayan da ke cikin jikin ta, tsaki ya ja a cikin zuciyarsa, yana faɗin.

“Wannan yarinyar sam ba fa da hankali, jibi yadda ta fito daga cikin gidan nan.” kafin ya yi wani maganar har Safna ta karasu sannan ta miƙa mata hijabi, ta amsa tana mai sanyawa sai a lokacin ta lura da kayan da ke hukunta, a hankali ta buɗe bakinta ta fara cewa.

“Ab......Ab..........Abbas." take ta yanke jiki a wajen, da sauri Safna ta yi kanta ta na mai cewa.

“Sumayya! Sumayya!! sumayya!!!.” amma ina ta yi nisan kiwo domin kuwa suma ta yi take.

*ABUJA*

Babban Masallacin jumma'a ne wanda ya cika sosai, a yanzu a ka gama ɗaura auren Ukasha da ƴam mata huɗu, abin da ya ma wa mutane da yawa mamaki kenan. Tsaye yake cikin babban riga sai faman murmushi yake yi, ba ƙyarya ya yi ƙyau fiye da misali, farin shadda ce ƙal a jikinsa an mai aiki da golding colour. Gefansa kuwa Umar ne shima ya sha wani shadda, matsawa ya yi kusa da shi ya ce.

“Ango, Ango Allah ya yi dai.” hannusa ya riƙe yana faɗin.

“Wallahi wani farin ciki nake yi sosai, alhamdulillah buri na ya cika.....”

“Saura Hasashen burin....” sai ya kuma sakin wani murmushi.
END.

BOOK ONE is done.

*To jama'a a nan na kawo karshe, kowani cakwakiya za'a warware shi a book 2, dan labarin zai fi ɗaukan zafin duk wannan wasan yara ne, zallan yana tafe.*

Akan darasin ₦500 ne kacal 😎
Ga dukka mai so ya fara booking, sannsn ya min mgn 07038436703

*HASASHE KO BURI* by PRETTYN JAJIRTATTU

[10/3, 22:59] Mrs I ♥️💔: *TEAM OF UKASHA*

_Burin sa dai ya cika ya malla mata huɗu daga differents culture 😁, Shin HASASHE sa sai cika kuwa? Sai a book 2 za mu ji ya zaman gidan zai kaya._

> Fillo Bafullatana : ba ruwanta, mace mai natsuwa da sanin ya kamata ❤️.

> Ashake Yoruba: akwai da ta masifa, sannan ita ma ba ruwanta, amma akwai kishi , kuma ta tsana Hausawa 😁.

> Zuby Kanuri : Mai burin mallakan Ukasha da koran gaba ɗaya sauran, tana da mugun ƙudiri akansa, domin Mai sittin goma ya dafa mata 🔥, shin za ta yi nasara?.

> Maryam Bahaushiya : mai ɓakin buri, da san kai, mai uwa mai dasa ta akan keken ɓera, ita ma burinta mallakan Ukasha dan ba za ta sharing miji da kowa ba..

> Tsakin Zuby Kanuri da Maryam Bahaushiya wacce za ta Malla UKASA.

A BOOK TWO ne zamu ji yadda zaman gidan zai kaya......✍️
[10/3, 22:59] Mrs I ♥️💔: *AMEERATULKHAIRI*
_Da wa kuke fatan ganinta da shi?._
> Haidar : soyayya ta shiga tsakanin su mai zufi. Sannan yana da matsala a gidan su, haka kuma mace wacce za ta yi zaman kishiyoyin da kishiyar Ummisa ya ke so 😁. Boom 🔥

> Abubakar : Adda ta bashi Ameeratul Khairy, haka hankalinsa ya dawo jikinsa, hmmmm waye shi ma oho Ina *Darling* wai .....🔥.

> Suwa ke neman ran AMEERATULKHAIR?

> Wacece ita?
[10/3, 22:59] Mrs I ♥️💔: *Capacity 💃*

*Ƴan US sun ɗau hanya, Shamo ya aura Muheey, Abdul ya aura Ma'eh da cewan da sun kwana biyu za su bi su, sai bangane wannne Alhaji ba?*

> Ya ce ya turosu, kuma yan mai godiya ga ƙungiyar su ta halaka hmmmmm 🔥🔥

> Ba musan ina Alhji zai kai ku ba..... Book 2.

> Mymoon : Taj yana hanya, ko ya zasu ƙarge oho, ga dai I.B gefe guda.......

> Abbas ka shiga wani jalIy ainun, ka tafi Abuja, dan aiki ga Sumayya ta suma saboda kai, hmmmm ko ya kuma zaku sanye oho..... book 2, can fa ga Gimbiya Merry.

BOOK TWO for ₦500 only. Darajar littafin ya fi kuɗin.
[10/3, 23:11] Mrs I ♥️💔: ``` *📢 Albishir Jama'a!*
*Assalamu Alaikum*

Ina farin cikin sanar da ku cewa mun kammala *HASASHE KO BURI — Book One* 🎉

*Book Two* zai kasance a kan *₦500 kacal*.
Ku shirya domin jin ƙarshen wannan zazzafan labari mai cike da rikici, soyayya, kishi da burin zuciya.

> Buri duk ya cika saura Hasashen burin, shin na kowa ne zai cika. Kar ku manta na yi jawabi akan kalaman *Buri* aba ce wanda kowa yake da shi, na wasu alkhairi ne, wasu kuma na su sharri ne, wasu yana cika amma sai ansha siya sosai, wasu kuma har abada baya tabbata.

> *Daga ni — PRETTYN JAJIRTATTU 💪*
Wallafa ce daga zuciya, don ku masoyan karatu 😁🔥✍️✍️✍️✍️✍️✍️
Chapter 21 · 0% Book details