Sashe 42
Fuska Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yayi ajiyar zcy kinsan zan
baki tunda nina ce zan baki amma yanzu kisan
zuyi ta jin haushin yan uwanmu zasu tsaneki na
soma hawaye wannan karon na shirya na yarda
in fuskanci ko wace irin matsala ce kai dai ka
sallame ni yamike yana jijjiga yarinya sbd kukan
da take yi yasa mata lebanshi abaki ya dan
jijjigata sai tasoma bacci ya mannata akirjinshi
sannan ya zauna bai san me zai ce mata ba yaje
ya kwantar da ita sannan ya fita gurin dr yaje ya
bashi bayani kan babies suna jin yunwa mamansu
tana fushi ta hanasu nono dry likita yayi sannan
ya rubuta kalar madaran da ta dace dasu ya ce
koda tana basu nono ba dole ne ya ishe su ba
dama sai an hada da madara yaje ya sayo ya
kawo nan da nan aka dama masu suka soma sha
shi kuma ya koma abj sbd bai sanar ba gashi
suna cikin wasu bincike ne washe gari yayi lagos
Nikam har sannan naki bada nono na, kwananmu
uku aka sallame ni mukayi gidansu momy dama
su abba basu sani ba haka nan momy ta hana a
fada ma mama.
Ran kwana hudu ya iso da kaya
niki niki mota guda tamkar masu kayan tashi, duk
na yara ne.
Su rahama suka fita da su hadiza
kowa baya jin dadi yanda yake ganina rai cunkus,
bana cin abinci.
Hadiza tace Allah yau sai na
gaya wa mama, su anty aina'u. ma da gangan
suka yi shiru har alhaji ma sai yaji.
Rahma tace
a'a ya umar ne yace likitocin sun ce kada a
matsa mata fa!
Hadiza tace ba dai ya son ya
matsa mata amma na taba ganin mai jego ba cin
abinci kuma ba zata ba yara nono ba sai shegen
bakin rai?
Ni kam dama na kosa su fita tunda
naji zuwan ya umar yau kama sai ya sallame ni,
ya zauna bayan ya dauko yarinyar.
Bansan me
yasa yafi daukar yarinyar ba, maman 'yan biyu na
same ki lafiya?
Banza nayi mishi yace yarinyar
nan tana kama dake sosai, shi ya sa nafi sonta.
Na harare shi, wannan ba damuwa ta bace ni
yanzu damuwata ka sake ni, ban ma kaina adalci
ba in har naci gaba da zama da kai.
Duk sanda
na dube ka ina tuna wuyar da ka bani tare da
bakaken maganganun da kasha gayamin amma in
ka sake ni zan yafe maka kuma raina ya huce.
Ya
tsugunnan gabana yanzun to wa zai shayar min
da yarana?
Wai zai kula min dasu?
Nayi
murmushi sannan nace ka manta da faridarka?
Wacce ta iya yiwa yara tarbiya kuma 'yar masu
tarbiya?
Ya zauna kasa, ban da magana a yau amma kiyi
hakuri.
Nace na daina yarda kana min wayo da
yawa, gashi ka samu yaran da kake muradi,
san...sallamar mama ce ta katse ni, ina take
mara hankalin yarinyar, dan ubanki ba a bada
nono ni na baki nawa?
Ta shigo bata 'yar ta bata
nono ko in tsine mata yanzun nan.
Ko kuma ki
biyani nawa.
Don kin sha wuya su suka dora
miki?
Ba Allah ne ya doro miki ba?
Gani nan tun
daga haihuwarki na samu hawan jini amma ban
hana ki nono ba sai ke?
Kuka na saka su momy
suna ta ba mama hakuri tace ba fa zata tafi ba
sai na basu nono.
Ta dubi ya umar tace kai kuma
faruk baka gaggaura mata mari?
Yarinya mara jin
magana.
Ya umar yasa ta cinyata, momy ta ciro
nonon ina kuka aka sa mata.
Nan ko ta kama sai
sha tace, shima yana bacci ya umar don mugunta
sai da ya taso shi shima suka saka mishi nono
ya hau sha, ranar nayi kuka har da ciwon kai.
Da dare ya umar ya shigo na dan dube shi
wallahi duk ya rame.
Ya ce me da me kike so
game da suna gobe zan koma jibi zamu zo da my
farida saboda tana dubai yau zata dawo, na dube
shi ina ruwana da suna?
Ni fa babban sunana ka
sallame ni.
Yace zan sallame ki amma ki bari ayi
suna mana!
Nace ran suna?
Yace da dare ba.
Nace shi kenan yace to ki saki ranki ki dinga cin
abinci kina basu nono, na ce nifa ba zan iya ba
da nonon nan ba.
Ya ce ke da su daya ne a raina
kinji asmy?
Yanda yayi maganar cikin muryar
tausayi don haka sai ya bani tausayi.
Ya umar ya kashe kudi da sunan nan tamkar a
kasa yake hako su.
Ni kallonshi ma nake yi.
Akwati saiti daya yayi min guda biyar, zannuwa
talatin da shida ga key din mota ta academy 'yar
mai kyau sabon sanfur ga hajji da umara sannan
ga takardun gidan shi na nan kaduna, yace na
wane halak malak ko bayan ranshi ko ba ma tare
nawa ne.
Alhaji da mama fada suka kama yi wai
duk iskancin da nake yi har ya birge shi ya min
kyauta haka?
Abba da momy cewa suka yi babu
ruwanku wannan tsakanin miji da mata ne.
Haka
yasa ni jin tausayin ya umar nasan yana yi ne
don in zauna dashi in daina maganar saki to ni
bana son shi haka nan bana son 'ya'yanshi.
Farida ma tayi hidina sosai, dangi sunyi hidima
da mu.
Akayi suna yara suka ci momu da abba,
kowa ya wadatu da kayan suna.
Rago biyu shanu
bibbiyu haka ya umar ya yanka.
Daren ranar na
jira shi dan ganin takarda bai zo ba har sai da
nayi bacci.
Ya shigo yaran yaje ya tsuguna
gabansu yayi musu adduo'I sannan ya sunbace
su, yazo kusa dani ya sunbaci kumatuna sanna
ya aje min wata 'yar farar takarda kusa dani,
sammako yayi don haka bamu hadu ba, ni kam
ban ma ga takardar ba sai da ina karyawa naga
takarda na dauka da sauri ina dubawa.
Cewa
yayi:
ki min afuwa ba zan iya sakin ki ba saboda
son da nake miki, ki zabi wani horo mai tsanani
wanda kike ganin yafi kowanne horo wahala ki
min shi, na yarda in dai zaki janye batun saki.
Sannan ki taimaka ki kula mini da yarana domin
ki tuna ko ba aure na san zaki iya kula min da
yarana don zumunci.
Kina da hakuri, ki kara
hakurin na gode
Tsaki naja sannan na yaga takardar, nace ba zan
iya zama da kai ba in ko ka ki wallahi zaka ga
wulakanci ganin idonka.
Haka mukayi ta yin
wankan jegon nan yara kam ko kallonsu bana yi,
nono kuma sai momy ta tsaya a kaina sannan
zan basu, in ko ba ta nan in dage ince sun sha.
Satinmu uku ya umar yazo dubamu sanda shigo
suna ta kuka ni ko ina kallon filn dina, kuma ina
jinsu dama ko suna kuka sai dai wani ya dauke
su ya basu ruwa, har mamakin su momy keyi wai
ko da labari basu taba jin labarin shashashar
uwa uwa irina ba, kashe TV yayi sannan yayi
bedroom, ya dauko su yana duba na ranshi bace.
Ban san irin qin da kike min ba asma'u, ko baki
sona ai kya so 'ya'yanki.
Na dube shi in dai ba
zaka sake ni ba toh baka soma ganin takaici ba
ya umar.
Yayi shiru can yace toh bata nono shi
kuma sai in bashi madara, nace bani dashi.
Na
mika na fita.
Innalillahi wa inna ilaihir raji'un
kurum yake ambata a zuciyarshi.
Haka ya basu
ruwa da madara, gashi ba aikin shi bane duk ya
bata jikinshi.
Sai ga nafisa ta dawo daga
makaranta, nan ta taimaka mishi ni kam ina
tsakar gida.
Haka muka yi arba'in ko yawon arba'in bamuyi
ba su abba suka ce maza in shirya zasu kira
mijina a waya mu tarkata mu koma tunda
iskancin da nake ma yaran kenan.
Inje in ma zan
kashe su ne in kashe su.
Da na sa ma momy
kuka sai tace kada in mata kuka itama tafi son
yaran a kaina don haka bazata iya kallon cin
fuskar da nake yi ma yaran kuma jikokin da tafi
so duk cikin jikokinta, haka na hakura saboda
dama gurinta kadai nake ganin fuska yanzu kan
yaran nan har rahma tsiya mukeyi da ita.
Waya
abba yayi ma ya umar kan cewa yazo ya kwashe
mu yace toh amma ba cikin wannan satin ba,
saboda farida bata da lafiya yanzu ma asibiti
zaije kaita.
Abba yace assha, me ya same ta?
Yace wallahi ciwon ciki haka ta kwana abba yace
Allah ya sawake mata.
Farida tana ta murkususu
tamkar zata mutu, likitoci suna ta bincike kanta,
ya umar tare da wasu abokanshi suna ta kai
kawo a kofar da aka rubuta emergency.
Kusan
awa daya likitocin suka yi ta fita daya bayan
daya, duk wanda ya umar ya tunkara sai yace
yana zuwa.
Daga karshe babban likitan ya fito ya
dubi sy ya umar yace wanene mijinta?
Cikin
fargaba ko ta mutu ne ya umar yace nine.
Likitan
yace biyo ni office.
Bayan likitan mai suna dacta bashir M ya bashi
hannu sun gaisa yace matsalar matarka nake son
shaida maka.
Ya umar ya gyara zama.
Dacto ya
bar rubutun da yake yi yasa gindin biron akan
habarshi.
Kasan matarka tana shan giya?
Ya
umar ya mike da sauri, dr kace me ne?
Kasan me
kake fada kuwa?
Dr yace calm down my friend.
Da yawa matanmu suna irin wadannan dabiun.
Ya umar ya katse shi to ni matata bata shan
komai sai da coke ina zaton baka san aikinka ba.
Ya fita yana masifa ya isko su aminu in da ya
bar su.
Yace kunji wannan wawan likitan wai
farida tana shan giya, kuzo ku taimaka min in
canza mata wani asibiti.
Likitan yayi kokarin
fahimtar da ya umar amma abin ya faskara dan
yayi fushi sosai.
Aminu da sali kam basu ji wani
mamaki ba, domin sun jima suna zargin farida
dan dai basu da shaida ne, amma sun taba
ganinta da wani alhaji a wani guest house amma
sai ta nuna musu wai matar mutumin ce kawarat
kuma tare suke da ita ta shiga ciki ne.
Su kuma
sun san wannan mutumin mane min mata ne.