← Book details Fuska Biyu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 46

Sashe 20

Fuska Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abin ya ta bashi mmk hr ya kai ga tambayarta a
ina ta koyo wadannan salon,sanar da shi ta yi ai
ma'abociyar karance-karancece, dan haka sai ya
yi murna da jin haka ta mantar da shi komai.
dani da ke mkrnt muka gama jarabawa a ka
bamu hutu. kamar nasan ba zai zo dauka ta ba
na ce Balkisu in direban ku yazo daukarki zai sa
min hannu ku sauke ni kaduna.Ta ce in an zo
daukarki fa?

Na ce bros dina na Abujan nan ne
zai zo daukata,kuma gidan shi zai kai ni ni ko ina
son ganin Momy,Mina ta ce kai Queen ki tsaya a
Abuja nan basa sai muna ziyartar juna ba?

Na ce
kin sani ne? ba ma shi da shi ne sosai zai matsa
min gara in je gurin Momy haka ko direba su ya
zo suka sauke ni har gida Murna gurin Momy
kamar me musamman ganin yanda na koma.Sun
gaisa da Balkisu sannan suka dauki hanyar
jigawa ko na ce Kano,Momy ta ce me ya hana
Soja yaje ya dauko ki?

Na ta6e baki sannan na
ce kila ya manta,ta ce wane irin ya manta?

Na ce
ina wayata ne?

Ta ciri min ta ce gata sai kin
saka a caji na ce zan kira Rahma ne ta san na
dawo.

Momy ta ce ina ruwan Rahma in taje gaida Mama
ta kan shigo mu gaisa ai Usman ya yi sa'ar
mata,na ce sosai ma ita ce dai ba ta yi sa'ar miji
ba,Momy tana dry ta ce shima ai ba ruwanshi na
ce ni kam gare ni ba shi da kirki,Anty ta shigo ta
ce 'yan mkrnt hr kin iso?

Na ce eh ina yini Anty?

Muka gaisa ta ce ke da maigidan ne?

Na ce a'a
kawata ce suka rage min hanya,Momy ta ce shi
ne zai zo ya dauko ta yana fama da Amarya?

Ai
zai zo ya same ni, Anty ta ce a"a Momy kin san
ko bayan ta taho yaje?

Ta ce ba wani zuwa da
zai yi wannan kawar tata da suka kawo ta tun da
daga jigawa aka je dauko ta amma na cikin Abuja
bai je ba ki ce yana da niyya.Tunda nazo kaduna
bai ta6a zuwa ba,Momy kuma bata neme shi ba
don koda ya yi mata waya bata ta6a mishi
zancena ba, Ko ta ce yaya ba muyi hutu ba?

Ko
kuma nazo bai zo ba sannan ta lura bai ta6a
kirana ba, don haka ta ce ta san maganinshi.

Abbada ya nemi ba'asin zamana a kaduna,Momy
ta ce nazo ganin gida ne.Hutun mu na sati 4 ne
saboda SS2 zamu shiga rannan na shiga gidanmu
mun gaisa da su Mama,sai ga Rahma.

Na ce yauwa kawata,dama ina ta jiranki ne kizo
ki raka ni saloon,ta ce muje nima ki biya min na
wanke nawa na ce lallai Momy zata ba ni sai dai
kije gurin Ya Usman ko ke ma Mama ta baki?

Mama ta ce zo gashi Rahma,Rahma ta fita tana
dry tare da fadin wasa nake Mama,gidan su
Momy shiga na yi wanka ina kwalliya muna hira
da Rahma muka ji sallama gabana ne yayi wani
mugun faduwa ban san mai sallamar ba,na gama
na saka riga da siket na atamfa 'yar Holan mun
fito falo Momy ta ce ga kudin gyaran kan na ce
dari biyu ma za ki ban.

Ta ce rike dari biyar din
na amsa zamu fito kenan akayi sallama kofar
Momy gabana ya sake faduwa ta daga labule ta
shigo,Nan take na gane ta.

Faridar Ya umar don
bayan hotonta da na gani hr da kalandar su na
gani dakin Mama hr da agogon su sanye take da
wani shegen leshi wanda kyawunshi ya nuna
tsananin tsadar shi.

Ruwan madara ne da ratsin
ja dan gyalenta shi ma ja, Haka takalmi da jaka
na dauke kaina daga dubanta duk da ba son
mijinta nake ba sai na ji kishinta yana yin kallon
da take min tana tunanin nice matar mijinta
tunda duk sauran taga su lkcn bikinta,sannan
taga idon da yake ce mata yarinyae ba kyau
ba,sai ido kamar na mujiya....

Ni dai muka fita kofar waje muka yi kici6is da Ya
Umar ya dube ni cikin mmk ba komai ya ba shi
mamaki ba yanda ya manta dani har ga Allah ya
manta da wata matarshi a mkrnt yanzu mai zai
ce ma Momy ban ko kuma kallon shi ba na sa
kai na fita abina,Rahma ce ta tsaya gaishe shi ta
biyo ni me yasa bako gaida shi ba?

Na ce yanzu
ba da ba ne,ba zan dauki wulakanci ba ko dama
don ni sane na jur wani abina.

Shi kam da ya
shiga gurin Momy sai ya shiga kame-kame yana
cewa shi sam mkrntr ba su mishi waya su anyi
hutu ba,Aliyu ne. ya dauko ta ba shi ba ne amsar
da Momy ta bashi kenan,ta fita daga dakin,Farida
ta dube shi Soja na wadda tafi ta yanzu ita ce
Asma'u din? ya ce eh kawai shi yasan Momy
tana fushi dashi ne don ko gaisawa sama-sama
suka yi ta,Ya kai Farida dakin Antynshi sanda na
dawo daga saloon na gansu zasu shiga
gidanmu.Yanayi tamkar ban gansu da na wuce
abina,na samu Momy tana yanka Alayyahu na
amshi yankan Anty Amarya tana ciki tana tuka
tuwan shinkafa,dama su baka gane mai girki
komai tare suke yi.....

Gefen baki suka kwana da farko neman masauki
ya ce zai yi a hotel,Momy ta ce duk gidan nan ko
can gidan Alhj ba gurin kwana sai ka kaita hotel
saboda ta raina mana arziki?

To kuje sai da safe
a gabn Farida ta fadi haka,nan yake ya gyara
musu gefen baki tunda Aliyu baya nan haka nan
su Jamila.Jamila da Nafisa suna gidan Anty
Salima shi ko ya Aliyu sunyi tafiya da Abba ni dai
ina can kuryar dakin Momy koma falo na zauna
ba zan ta6a gyara musu gurin kwanciya ba,da
safe ma sanda suka shigo na gama karyawa
kawaye da Mina Turaki ina jin sanda suka yi
sallama yi na yi tamkar ban san suna yi ba,Suka
zauna Momy ta fita suka gaisa ya Umar sai
hararata yake,na mike na shige cikin daki,ina
amsa wayata,dakin Anty suka yada zango karfe 2
suka tafi bai ce ma momy komai game dani ba
haka nan nima ban ce kala ba dama bana so ace
in bishi Momy ma ba ta ce komai da hutun mu
yana karewa ta mishi waya bai zo ba ba ya turo
kudi wai Aliyu ya yi min shopping sannan yajw ya
biya kudin makaranta hakan ce ta kasan ce muka
koma makaranta......

Tun daga wannan ganin ban kuma ganin ya Umar
ba,har muka gama SS2 muka shiga 3 duk hutu
Momy zata aiko a dauke ni ta ce ma Abba ita ce
na dinga zuwa kaduna saboda in an gama gini
shi nan zan zauna, ko da Abba ya tuntua6e shi
da wannan batun sai ya ce haka ne don haka ya
saka shiriritar gama aikin nima haka na ke so,
domin yanzun shi kan shi da zai ganni ba yabon
kai ba yasan na fi karfin wulakanci daga shi har
matarshi basa gabana na samu labarin an ce
tana da ciki amma watan cikin hudu ya zube
yanda nake ji gurin su Jamila tamkar zai yi kuka
saboda zubewar cikin na ce su karata.

Duk da
matsatsin fiar da ya Umar ke ma Farida hakan
bai hanata hulda da abokan shashancin ta ba,ta
kan fake da zuwa gidan Yarta dake nan Abuja
cikin ta ma cire shi tayi saboda yana bata
matsala da abokan harkarta.

Alhj Sambo shi ne
ya hada ta da likitan da ya cire mata cikin.
********** cikin Yardar Ubangiji muka kammala
karatunmu bayan kammala komai aka bamu
kyautuka kowa ya kama gabanshi sai dai abn
farin ciki ina daya daga cikin dalibai uku da
makaranta ta za6a don daukar nauyinmu,muyi
karatun Likita saboda hazakarmu in ka ji ana
Asma'u to a kaduna ne Amma Abuja har gobe
Queen suke kirana.....

Sai da muka dawo gida na samu Momy zata biki
jos danginta na bita muka tafi ansa bikin Hadiza
da Shema'u Sai na Ya Usman da Aminiyata
Rahma,Hadiza da na Ya Aliyu ne haka Shema'u
yaron yayan Mamanta ne Sadik.

Tun da biki ya
matso ba mu da sukuni kawayena su Mina duk
na gayyace sy kuma nasan za su zo.

Biki ya yi
biki kenan,na musu ankonmu duka don har da su
cikin kawayen aana gobe daurin aure suka iso
Mina tariga su isowa saboda tafi kusa,sannan
Balkisu sanda Fatima shehu ta iso mun gama
shirin tafiya lunchen ko hutawa bata yi ba ta yo
wanka muka fito,muna ta shakiyancinmy da
muka saba,Kowace direbansu ya kawo ta, don
haka muka shiga motar su Mina muka shiga
tunda shi direban su ya huta haka muka kayata
gurin tamkar taurari gaba kin su Mina baya
gajiya da fadin Queen duk in da na bi nan sauran
mutune suka dauka Queen-Queen,duka amaran
lunchen gurin daya muka hada tunda duk gida ne
har angon shema'u tunda ya saba dama dasu ya
Usman ni da Jamila mun dauki kwalayan
abubuwan da zamu raba ma mutane muna kaiwa
gurin ajiye wakafin mu sona rabawa,Anty Saluna
ta kira ni nazo ta ce ina aurans Na ce wane aure
kuma?Har ga Allah ni ina mantawa wai ni matar
aure ce,Har mijin kanshi na manta da batunshi.

Ta ce iye lallai Asma'u kin hadu shi yasa ko dan
gyale ba ku saka ba,na ce share kin ji har zan
tafi Anty Fatima ta ce kishiyarki ta ko zo?

Na ce
tazo bata zo ba ban sani ba,anty Aina'u ta ce na
ganta gab da zamu zo nan na ce ita ta sani ni
ina ruwana......
Chapter 20 · 0% Book details