← Book details Fuska Biyu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 46

Sashe 21

Fuska Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Guri ya yi guri,na rasa duk inda nayi jama'a
kallona suke,ga mai wakar ya kama Asma'u
Queen ban san da wanda ya sanar dashi sunana
ba,Har da fadin Queen din Umar Soja marmari
daga nesa,naja tsaki na ce bar hada ni da wani
Soka,Jamila ta dauki kafadata ta ce dama tun
dazun nake son in ce miki duk wanda ya kira ki
zamu dau mataki kanshi,na ce jacan ki bani
guri,yanzu nake tashena wannan Sojan ya min
Tsufa,don haka duk wanda ya kira ni zuwa zanyi
muka saka dariya ni da su,gashi dama muna da
wata sara ni da su Mina,in munyi abin dariya
mun dara sai muce wa ya dukanmu Jamila ta ce
Allah ya shirye ku,Haka aka sha lunchen muka
taso muna mota su Mina suka dame ni wai
wanene Umar Soja? na ce don Allah ku bar
zancan shi nima ban san shi ba,Fatima shehu ta
ce ba wani ba ki so nw musan Saurayinki kawai
Queen.Jamila zata yi Magana na toshe mata baki
amma sai da ta ce musu mijinta ne,na ce kunha
nayi kama da matar aure?

Muna tsayawa kofar
gidanmu Anty Salima ta miko min yaronta Muslim
ta ce don Allah Asma'u ki kai danku gurin
Momy,na ce yaron nan kato da shi yana tafiya ga
surutu amma sai kuyi ta daukan shi?

Ni dai ba
zan dau ke ka ba sauka ka taka da kanka.Anty
Aina'u ta ce dama ke ai ba ki san yara na ce ku
ai yaranky sun cika kuya Anty Fatima ta ce kema
in ki haifa kin rike naki na ce ba konai suka shige
gidanmu mu kuma muka nufi gidan Abba da
kawayena ina rike da muslim sam ban kula ba
she su Ya Umar da ya Abubakr ne a gurin tare da
wasu daban ban san su ba.Muslim ne naga ya
kwance hannunshi ya ce ga Dadyna ya nufi gurin
Ya Abubakar.Mina ta ce la ji yaro da wayi yasan
Babanshi ko ba Babanshi ba ne??

Na ce
Babanshi ne mana Bilkisu ta ce yayanki ne, Na ce
shi ne Na farkonmu a dakin mu muka zo gota su
yi nayi tamkar ban gansu su ba saboda ya Umar
dake gurin sai naji su Mina suna gaishe su, har
mun gota naji muryar ya Abubakar yana cewa kE
Asma'u zo nan na juya na zo shi nake duba na ki
kallo gurin Ya umar, na ce gani ya ce ke har
yanzu.....

Kanki bai dana hayaki ba ko?

Na 6ata rai ya ce
gaba kina kallonmu kin wani dauke kai sama
sannan dubi shigarki babu ko dan gyale kin daura
gwargwaro a kai gashi a waje tamkar ba matar
aure ba ko?Na dubi sasheb ya Umar da gefen ido
waya yake amma na kula da kallom da yake min
da gefen ido, na wuce ban ce komai ba, Fatima
Shehu ta ce wai da gaske kina da aure ne?

Na ce
don Allah muje ciki.

Falon Momy na bar su na
shiga dakin Anty Amarya dan na dan watsa ruwa
kasancewar gidan bai cika kamar gidanmu ba,tun
da nan gidan Maza ne wanka nake na tuno ya
Umar da na ganshi yau in har ba zan manta ba
yau shekara biyu da wata shida kenan rabona da
na sa shi a idona.

Ya Allah sam ban ji zuciyata
tayi farin ciki da ganin shi ba,duk da cika da kyau
da kwarjini da na lura ya kara,sannan ga kudi da
ya zauna.

Can waje kam ya Umar ya dubi Muslim
sannan yasa hannu ya dauke shi tare da fadin zo
nan big boy,yayi sha'awar yaron kwarai da
gaske.Yanzu kam ya matsu yaga dan kanshi.

Farida ya lura abin bai dame ta ba,in yayi la'akari
da yanzun makarantar da ta koma tafi dauke
mata hankali,ko dai zai............sai kuma yaja
tsaki yayi shiru,yana son yin shawara da Anty shi
ya dubi Abubakar ya ce bari na ga Antyna,Muslim
ya ce zanje gurin Dadyna,ya Umar ya ce nima
Dadynka ne ai ya ce a'a ga Dadyna nan Ya Umar
ya mika shi suna dariya ya ce jeka gurin Babnka
ya nufi cikin gidan ma ba mutune sosai kamar
yanda ya zara ya shiga gefen Antynshi babu
shamaki,ko ina shiga yake kai tsaye ya shige
bedroom yana fadin ina Antyn tawa take?

Ni
kuma na fito daga ni sai wani dan tawul wanda
iyakarshi cinyata,kallonaya tsya nayi wani abu ne
yaji shi tub daga yatsun kafarshi har kanshi
idunanshi sun kasa daukewa daga kaina.
[2:07PM, 13/10/2016]
@lh@ji
A R: Fuska Biyu 1----18
Ganin yana min kallan qurilla na juya na koma
toilet ya bini da kallo har na shige na kulle qofar.
ahankali ya kulle ido ya sake bude su sannan ya
jingina da bangon dakin a hankali ya furta ya
salam.jikinshi babu qarfi ya fita xuwa falon anty
ya xauna kan kujera wani abu yana mishi yawo
aranshi yayi ajiyar xuciya tare da jingina bayanshi
da kujerar,lkc guda ya kwantar da kanshi,yarinyan
nan ce haka? daman haka qiranta take?wata
xuciyar tace ko dai kaji sha'awanta ne?kafin ya
samo amsa sai yaji maganan anty,ta dubeshi dan
gidana,yayi dan murmushi ya ce ina kuka jene?
tace munje kai abincin biko mana,yace kai mata
kun cika bidia,yanxu tsakanin gidannan dana
baba alhj har akwai wani biko ne ko bai kone ma
kika ce? tayi dry tace hakama mama tace,yaja
murmushi yace ina farida ne? tace aini tunda
muka gaisa tace min xataje gurhn wata qawanta
gashi har magariba bata dawo ba, ya ja tsaki
yace tasan inta fadamin baxan barta ba shine
watan ta tafi?yace anty matsaloli sunyi yawa
dama ina san mu xauna....

Ya dubi agogo ga lkcn sallah yayi bari ayi isha'I
cewar anty daidai nan nazo na wuce su ya dube
ni sannan ya dubi anty yace yarinyar nan ta samu
daurin gindi wurin momy ko gaeshe ni batayi ba .
anty tace harda kai dangidana , da ace tana
gidanka dole ta gaishe ka . yace bari naa dawo.
mukam gidansu rahma muka nufa inda za'aje a
kwashe mu xuwa zuwa gidan kanwar momy da
take u/dosa , dan can xa'aa sa lalle. lkcn da ya
umar ya samu xama da antynshi ya dube ta kin
san anty meke damuna? na farko kamar yanda
kika sani inason yara kin sani anty sannan naa 2
farida tunda ta koma makranta bataso ina mata
xancen haihuwa , ga shegen yawo, look at, lkc
yanxu kusan 9 bata dawo ba haka in taje
makaranta bata dawowa akan lkc ga matsalar
abinci saidai muci na kuku ga yawan zuwa yola
suna yau suna gobe biki na gaji. anty tayi shiru a
ranta tana nazarin me xatace dashi in kuma ta
fad xai yarda? amma duk da haka sai tayi kuru
tace umar yace naaaam tace mexai hana ka
dauki matar ka asma'u ?ya dube ta da sauri tace
kwrai, tana da kyau tana da diri inda bata da
kunya yanxun tana dashi hakanan bata duk
halayen ta daka santa dasu duk ta daina koh
masifa dama sai an tabo ta, snnan zata iya
haihuwa, shiru yayi yana nazarin maganar anty,
ta sake dubanshi sannan kuma xakasha fama da
momy . shiru yayi yana tunanin maganar anty ,
yasan tabbs shi bayason yarinyar saidai zata iya
haihuwa amma ya zai cema momy
Ya dubi anty me zance wa momy? gaskiya don
son yarinyar nan banayi na tsane ta saedae don
son haihuwa , xan nemi komenta ko nace zan tafi
da ita saidai momy ce matsalar. dan na kula
yanxun ban cikin yan harkokinta kuma duk akan
yarinyar ne. anty tace ta baya xaka biyo wato
wurin abba, kafin yayi magana farida ta shigo da
sallama, tare da fadin anty kin ganni sai yanxun
koh? ganin soja yasa tayi tsit tasan tayi laifi tun
xuwan su ta kama gabanta ta zauna ta fadin
danAllh kayi hkr sojana na kir wayar ka taki shiga
ya dubi agogo 9 daidai sannan ya dube ta ina
kikaje? kafin ta bashi amsa wayar ta tafara ruri,
ta duba ta ganin ahj sambo ne yasa gabanta ya
fadi, ta dauka cikin tsorofuskarta daure tace lfy?
yace na kiraki ne naji kin kai gida lfy? tace eh
yace kin manta pant dinki anan , tsaki taja
sannan tace sai anjim, ya kwshe da dariya ta
kashe wayar, yarda duk ta tsargi kanta yasa ya
umar tunanin batada gaskiya, yace ina kikaje
nace? nan ta soma shiryo karya , wlh wta 'yar
set dinmu ce a skul dama nan suke da mijinta ke
aiki can shi ne ya samar mata skul dinmu , jiya
na kirata nace mun zo kd.

Shine tace itama tana kdsai tamin kwatance naje.
yaja tsaki yace wa kika tambaya ya baki izini ?
tace yi hkr , bai kuma magana ba ya dubi anty
xan tafi masaukina , don masaukin gidan nan xai
cika yau.farida ta tashi bari naje ya daga mata
hannu alamar kada ta bishi sannan yace inaso na
samu rest of mind, ba tare da ya jira komai ba ya
tafi , anty tace meyasa xkiyi gngancin nn kinsan
mijinki bayason yawo? tace soja ya cika kishi ne
anty, anty tace ai duk namijin da baya kishn
iyalinshi jaki ne, saidai na wani yafi wani, nan
suka kwanta tna tunanin yanda xata shawo
kanshi dan tasan sojan bai iya fushi ba.kwance
yake rigingine fuskar shi tana kallon
sillntunaninshiyana kan yarnyar ,ganinta yake
cikin slow tana tafiya lkcn da suka wuce da
kawayenta , sannan tazo mashi rai sanda ya
ganta daure da towel santla santalar cinyoyinta
da kogunta ya tuna, nan zuciyarshi ta raya kwarai
xata hafa mishi yara, saidai yasan xai fuskanci
matsala wurin momy , ga yarinyar fa?

Ranar daurin aure gidajan kam da jama'a Mu dai
wannan lkcn muna gidan su Rahma Muna ta
shirya yanda zamu gabatar da walima anjima
bayan dauren aure.Lkcn daurin aure ya karato na
ce kuzo muje gida muyo wanka kunga in gidan ya
dinke da jama'a ba zamu samu gurin shiga
ba,abokana ya Usman suka zo suka kawo mana
drnks wanda zamu yi amfani da su gurin walima.
Chapter 21 · 0% Book details