← Book details Fuska Biyu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 46

Sashe 23

Fuska Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Insha Allah zan kare daga na 2
na gode Taku HALIMA ABDULLAHI K/MASHI.
[7:20PM, 17/10/2016]
@lh@ji
A R: Fuska Biyu 1----18
Ganin yana min kallan qurilla na juya na koma
toilet ya bini da kallo har na shige na kulle qofar.
ahankali ya kulle ido ya sake bude su sannan ya
jingina da bangon dakin a hankali ya furta ya
salam.jikinshi babu qarfi ya fita xuwa falon anty
ya xauna kan kujera wani abu yana mishi yawo
aranshi yayi ajiyar xuciya tare da jingina bayanshi
da kujerar,lkc guda ya kwantar da kanshi,yarinyan
nan ce haka? daman haka qiranta take?wata
xuciyar tace ko dai kaji sha'awanta ne?kafin ya
samo amsa sai yaji maganan anty,ta dubeshi dan
gidana,yayi dan murmushi ya ce ina kuka jene?
tace munje kai abincin biko mana,yace kai mata
kun cika bidia,yanxu tsakanin gidannan dana
baba alhj har akwai wani biko ne ko bai kone ma
kika ce? tayi dry tace hakama mama tace,yaja
murmushi yace ina farida ne? tace aini tunda
muka gaisa tace min xataje gurhn wata qawanta
gashi har magariba bata dawo ba, ya ja tsaki
yace tasan inta fadamin baxan barta ba shine
watan ta tafi?yace anty matsaloli sunyi yawa
dama ina san mu xauna....

Ya dubi agogo ga lkcn sallah yayi bari ayi isha'I
cewar anty daidai nan nazo na wuce su ya dube
ni sannan ya dubi anty yace yarinyar nan ta samu
daurin gindi wurin momy ko gaeshe ni batayi ba .
anty tace harda kai dangidana , da ace tana
gidanka dole ta gaishe ka . yace bari naa dawo.
mukam gidansu rahma muka nufa inda za'aje a
kwashe mu xuwa zuwa gidan kanwar momy da
take u/dosa , dan can xa'aa sa lalle. lkcn da ya
umar ya samu xama da antynshi ya dube ta kin
san anty meke damuna? na farko kamar yanda
kika sani inason yara kin sani anty sannan naa 2
farida tunda ta koma makranta bataso ina mata
xancen haihuwa , ga shegen yawo, look at, lkc
yanxu kusan 9 bata dawo ba haka in taje
makaranta bata dawowa akan lkc ga matsalar
abinci saidai muci na kuku ga yawan zuwa yola
suna yau suna gobe biki na gaji. anty tayi shiru a
ranta tana nazarin me xatace dashi in kuma ta
fad xai yarda? amma duk da haka sai tayi kuru
tace umar yace naaaam tace mexai hana ka
dauki matar ka asma'u ?ya dube ta da sauri tace
kwrai, tana da kyau tana da diri inda bata da
kunya yanxun tana dashi hakanan bata duk
halayen ta daka santa dasu duk ta daina koh
masifa dama sai an tabo ta, snnan zata iya
haihuwa, shiru yayi yana nazarin maganar anty,
ta sake dubanshi sannan kuma xakasha fama da
momy . shiru yayi yana tunanin maganar anty ,
yasan tabbs shi bayason yarinyar saidai zata iya
haihuwa amma ya zai cema momy
Ya dubi anty me zance wa momy? gaskiya don
son yarinyar nan banayi na tsane ta saedae don
son haihuwa , xan nemi komenta ko nace zan tafi
da ita saidai momy ce matsalar. dan na kula
yanxun ban cikin yan harkokinta kuma duk akan
yarinyar ne. anty tace ta baya xaka biyo wato
wurin abba, kafin yayi magana farida ta shigo da
sallama, tare da fadin anty kin ganni sai yanxun
koh? ganin soja yasa tayi tsit tasan tayi laifi tun
xuwan su ta kama gabanta ta zauna ta fadin
danAllh kayi hkr sojana na kir wayar ka taki shiga
ya dubi agogo 9 daidai sannan ya dube ta ina
kikaje? kafin ta bashi amsa wayar ta tafara ruri,
ta duba ta ganin ahj sambo ne yasa gabanta ya
fadi, ta dauka cikin tsorofuskarta daure tace lfy?
yace na kiraki ne naji kin kai gida lfy? tace eh
yace kin manta pant dinki anan , tsaki taja
sannan tace sai anjim, ya kwshe da dariya ta
kashe wayar, yarda duk ta tsargi kanta yasa ya
umar tunanin batada gaskiya, yace ina kikaje
nace? nan ta soma shiryo karya , wlh wta 'yar
set dinmu ce a skul dama nan suke da mijinta ke
aiki can shi ne ya samar mata skul dinmu , jiya
na kirata nace mun zo kd.

Shine tace itama tana kdsai tamin kwatance naje.
yaja tsaki yace wa kika tambaya ya baki izini ?
tace yi hkr , bai kuma magana ba ya dubi anty
xan tafi masaukina , don masaukin gidan nan xai
cika yau.farida ta tashi bari naje ya daga mata
hannu alamar kada ta bishi sannan yace inaso na
samu rest of mind, ba tare da ya jira komai ba ya
tafi , anty tace meyasa xkiyi gngancin nn kinsan
mijinki bayason yawo? tace soja ya cika kishi ne
anty, anty tace ai duk namijin da baya kishn
iyalinshi jaki ne, saidai na wani yafi wani, nan
suka kwanta tna tunanin yanda xata shawo
kanshi dan tasan sojan bai iya fushi ba.kwance
yake rigingine fuskar shi tana kallon
sillntunaninshiyana kan yarnyar ,ganinta yake
cikin slow tana tafiya lkcn da suka wuce da
kawayenta , sannan tazo mashi rai sanda ya
ganta daure da towel santla santalar cinyoyinta
da kogunta ya tuna, nan zuciyarshi ta raya kwarai
xata hafa mishi yara, saidai yasan xai fuskanci
matsala wurin momy , ga yarinyar fa?

Ranar daurin aure gidajan kam da jama'a Mu dai
wannan lkcn muna gidan su Rahma Muna ta
shirya yanda zamu gabatar da walima anjima
bayan dauren aure.Lkcn daurin aure ya karato na
ce kuzo muje gida muyo wanka kunga in gidan ya
dinke da jama'a ba zamu samu gurin shiga
ba,abokana ya Usman suka zo suka kawo mana
drnks wanda zamu yi amfani da su gurin walima.

Na ce su sauke mu gida,suka debe mu wajan har
ya soma cika da mutane,gasu Ya umar da
abokanshi irin su Al-Amin,da sauran su,ban da su
ya Abubakar ga sunan.Muka sakko daga mota
tun kan mu shiga cikin gida Mina ta dame ni da
tambaya don Allah wancan yayanku ne?

Mai
sanye da farin boyl din can?

Na dubi gurin ya
Umar take magana amma sai nayi tamkar ban
gane shi ba na ce wa kenan?

Bilkisu ta ce wanda
jiyan nan muka ganshi cikin kakin Soja, na ce
sunanshi ya Umar shi ne babban yaron Momy,
Fatinma shehu ta ce suna kama gaskiya,yana da
kyau gayen na ce wane kyau anan?

Bilkisu da
Mina har suna hada baki gurin cewa ko ke ya fiki
kyau Queen duk da kina mace, Na ce Allah ya
kyauta,MINA ta ce yana da mata?

Na ce kilama
tana nan cikin gidan nan suka dage kan in tana
ciki don Allah na nuna musu ita....

Tun daga nesa na hango dakin Momy fal da
mutane haka falonta, haka muka ja birki kofar
Anty falon ta da mutane ba su da yawa ban tsaya
dubansu ba na ce ku zo nan dama kayanku na
ciki.Bedroom din Anty muka shige,duk muka zube
mata kan gado,na ce bari na debo mana waina
ko tuwo?

Suka ce wainar dai na dibo na shigo
saina ga ashe harda Faridan ya Umar a cikin na
zauna a falon Anty.

Na shiga ina cewa kai 'yan
iksa ga to matar da kuka ce in nuna maku Bilkisu
ta ce matar Sojan nan?

Na ce eh wata fara, duk
suka tashi da gudu.Suka je suna lekenta.

Suka
dawo suna fadin tana da kyau gaskiya na ta6e ba
ki na ce suyi ta kyansu,Fatima Shehu ta ce
Amma dai ba mamnku daya ba?

Nan na ce
musu,nifa canne gidanmu,maman can gidan ce
Mamana,ba Momy ba, yanda muke dasu yasa na
basu labarin na amma ban sanar dasu yanada
akayi auranmu ba na dai ce ba ma son juna aka
hada mu,sun sha mamaki sannan suna ta min
korafin me yasa bana sonshi dan Allah in yarda
Mina cewa tayi wlh ban da ke da kike tsakani da
sai na ce ina sonshi na ce ki ce mana,aini ba fa
zan zauna da shi ba,ina samun wanda na ke so
wlh dole ya bani sakina, Nan dai muka ci muka
sha muka yi ta shakiyancin mu,sai dai kiji muna
ihu muna cewa waya kwashe da dariya don ko a
school in muna sama mutum iddo ya bani
damu......
Chapter 23 · 0% Book details