← Book details Fuska Biyu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 46

Sashe 22

Fuska Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Na ce su sauke mu gida,suka debe mu wajan har
ya soma cika da mutane,gasu Ya umar da
abokanshi irin su Al-Amin,da sauran su,ban da su
ya Abubakar ga sunan.Muka sakko daga mota
tun kan mu shiga cikin gida Mina ta dame ni da
tambaya don Allah wancan yayanku ne?

Mai
sanye da farin boyl din can?

Na dubi gurin ya
Umar take magana amma sai nayi tamkar ban
gane shi ba na ce wa kenan?

Bilkisu ta ce wanda
jiyan nan muka ganshi cikin kakin Soja, na ce
sunanshi ya Umar shi ne babban yaron Momy,
Fatinma shehu ta ce suna kama gaskiya,yana da
kyau gayen na ce wane kyau anan?

Bilkisu da
Mina har suna hada baki gurin cewa ko ke ya fiki
kyau Queen duk da kina mace, Na ce Allah ya
kyauta,MINA ta ce yana da mata?

Na ce kilama
tana nan cikin gidan nan suka dage kan in tana
ciki don Allah na nuna musu ita....

Tun daga nesa na hango dakin Momy fal da
mutane haka falonta, haka muka ja birki kofar
Anty falon ta da mutane ba su da yawa ban tsaya
dubansu ba na ce ku zo nan dama kayanku na
ciki.Bedroom din Anty muka shige,duk muka zube
mata kan gado,na ce bari na debo mana waina
ko tuwo?

Suka ce wainar dai na dibo na shigo
saina ga ashe harda Faridan ya Umar a cikin na
zauna a falon Anty.

Na shiga ina cewa kai 'yan
iksa ga to matar da kuka ce in nuna maku Bilkisu
ta ce matar Sojan nan?

Na ce eh wata fara, duk
suka tashi da gudu.Suka je suna lekenta.

Suka
dawo suna fadin tana da kyau gaskiya na ta6e ba
ki na ce suyi ta kyansu,Fatima Shehu ta ce
Amma dai ba mamnku daya ba?

Nan na ce
musu,nifa canne gidanmu,maman can gidan ce
Mamana,ba Momy ba, yanda muke dasu yasa na
basu labarin na amma ban sanar dasu yanada
akayi auranmu ba na dai ce ba ma son juna aka
hada mu,sun sha mamaki sannan suna ta min
korafin me yasa bana sonshi dan Allah in yarda
Mina cewa tayi wlh ban da ke da kike tsakani da
sai na ce ina sonshi na ce ki ce mana,aini ba fa
zan zauna da shi ba,ina samun wanda na ke so
wlh dole ya bani sakina, Nan dai muka ci muka
sha muka yi ta shakiyancin mu,sai dai kiji muna
ihu muna cewa waya kwashe da dariya don ko a
school in muna sama mutum iddo ya bani
damu......

Wayar anty dake kan mirror ta soma kuka na
duka naga ansa dan gidana nace a raina ya umar
ne na aje hak yayi ta kira su mina suka ce na
dauka nace a'a sojn nan ne suka ce na dai dauka
don Allah tunda ta tana can cikn mutane , ina
dauka ya soma fadin antyn, cikin masifa nace ba
ita. bace tace to ko wcece tce frida tazo, na kshe
wyar sannan nce ina ruwana da wata farida,
kamar kuna ma tana gurin sai gata ta dago
labule tce waye yake ambatar sunana? na mata
wani duba, sannan nace to wma yasan sunanki?
waya damu dake har da za'a kira sunan ki? ta
zaro ido kada ki min rashin kunya don na kula da
take taken ki dama baki da mutunci nace har na
kai ki zaki wani zaro min ido ai ba ki fini ido ba
na juya mata tawa kwayar idon. ta shigo zan
faffala miki mari nima na mike ina fadin ni kuma
sai na kwanta ki duke ni ko?sauran matan falon
suka shigo , suna tmbayr ba'asi tace tun
shigowar mu sai leqenta muke, muna mta dariya
sannan yanxun har da kiran sunan ta nace ke har
abin kallo ce da za'a leke ki? su minaa suna jana
tace kema kinsn na fiki shiyasa da ka manna ma
mijina yaki ki shiyasa kike jin haushi nace ke kin
sani da inason mijinki kinyi kadan ki shigo dan
dai shi kanshi bai min ba nayi wani takun tafiya
da mukeyi in muna masifa nace ki dube ni da
kyau, nafi
Nafi karfin ajin mijinki don haka daina kishi dani
ballagaza ta shigo sosai wai sai ta dake ni ,ni ko
bakina baimutu ba nace koke da mijin nakikukazo
zane ku ma zanyi nan dai aka fita da ita ana
cewa ni yarinya ce karta kulani, su kam su bilkisu
duk da sun san halina amma yau sun sha
mamakina, can dai ya sukakare? oho muka sha
wankanmumuka firo.anty ta kirani nazo tana
tambayar me yahadamu? nace ina zuwa anty in
mun dawo xan gaya miki kinsan mun tara yan
walima,sai waya rahma ke bugomin, tace to a
gate muka ganta ita da mijinta tana gaya mishi
lkcn yan daurin aure sun watse sai dangi mun
hada ido dashi na dauke kaina yi nayi tamkar ban
ganshi ba, kuma karamin gyale na saka, muka
shiga motar su fatima shehu da yake duk drivers
da suka kawo su sunanan sai. gobe zasu tafi
dasu. muna gadan har dare inda muka shiga
motocin kai amaryazuwa gidan ya usmandake u/
dosa kusa dana ya abubakar , sai shirin zuwa
dinner can ma mun cashe. sosai ban sanma ya
umar yana gurin ba sai sanda muka zaun daga
rawar da muka sha lkcn za'a fara ciye ciye , ko
wani yebur mutum 4 ne, muma mu 4 ne dasu
mina jamila tace bari ta samo kujera ta zauna
nace a'a tace wurin su anty salima,(dama dinner
din tare akayi) muna ta ciye ciye mu tare da
barkwanci da muka saba.jin wani mutum nayi
tsaye kusa da kaina, yace donAllah minti 1 nace
wa? yace ke don Allah nace duk abin da kake son
fada fadi a gabansu aminaina ne yace to don
Allah sunan ki fa? in da hali kuma hour gidanku
zanyi mgana fatima shehu ta rigani malam tana
da miji matar aure ce na duke ta nace karya ne
kaga nayi kama da matar aure?

Kafin yayi magana wayata ta soma ringing cikin
jaka na ciro number na gani ba suna, na duka
nace hello...."muryar ya umar ta katse ni. tabbas
ba kiyi kama. da matar aure ba sbd baki ba aure
daraja ba, to maza ki sallame shi kafin nazo na
bata muku rai dukkanku, nunawa nayi bangane
mai maganar ba, nace wanene ke magana, yace
zaki ganshi yanzun in baki sallami bakon ki ba ya
kashe wayar. na shiga waige waige na dubi bakon
nace kada ka damu bani number dinka xan kira
ka nama bayan, sbd yanxun xamu wuce gida. ya
ya fadamin number dinshi yace sunan shi
kasimmuktar,nace sai ya jini. ya tafi su mina
kallona kawai sukeyi suna mamakin yanda na
tsaya sauraron wani namiji, na dinga waige wige
ban ga gurin da ya umar yake ba na dubi gurin
amare rahma ta min alama da hannu, wai ni ko
zangamu da soja (ta nuna da alamar sarawa)
nace e din, haka dinner ta ci ta cinye sannan aka
kwashe mu nace gida xankoma ba zanje gidan
rahma ba, saida su anty salima suka sa baki
sannan mukaje washe gari budan kai ni dai tunda
safe mu ka dwo sbd su mina zasu dauki
hanya.kayan biki su momy mama da momyn
rahma sun hada musu , ni kam momy ta bani
kudi na hada musu kayan shafa suka tafi kowa
ya dauki hanyar garinsu suka barni da kewa ya
umar ya shigo dan sallamar su momy yana
fitowa yaci karo da alhaji suka gaisa, yace dama
inason shiga gurinka muyi sallama.alhaji yace
madallah har zaka tafi? to ina kuma iyalin?

Yace ta tafi tun jiya, yace to ita kuma wannan
zaman ta kenan ko dai akwai matsala ne ? kafin
yayi magana saiga motr abba, ya fito ya nufo su
abba ya mika ma ahj hannu suka gais,ni kuma na
fito zan shiga gidanmu, ahj yace yauwa ke zo
nan, nazo gabana sai faduwa yakeyi, ahj ya d
abba sannan yace na rasa zaman da yarinyan
nan ke yi? bba yace shidin ne nima nayi magana
da momynta su tace kacesi ka gama gininka na
nan? ya tambayi ya umar, ya umar ya dube ni
sannan yace e to , da haka nace amma yanzu na
fasa bar na tafi da. ita. na dube shi da sauri
sannan na dubi su abba nce ni dai donAllah ba
zanje ba gaskiya yabani takar.... saukar mari naji
tas, ban karasa magana ba ahj yace maza dauko
kayanki ku tafi, ya umar yace a'a tabar kayan
zanzo na dauka, tzo muje jin haka nayi cikin gida
da gudu gurin momy ina kuka, tasaki bokitin
hannunta mai dauke da ruwa, lfy asma'u? cikin
kuka nake fadin su abba ne da ahj suka ce nazo
nabi ya umar yanxun nan,momy tace daina kuka
babu inda zakije,nayi ckin dakinta da gudu na.
fada kan gado na kudondune. ina jiyo muryan
abba yana fadin ina sma'un?

Mu hadu a kashi na 2 don jin yanda xata kaya,
domin akwai lbr.
Chapter 22 · 0% Book details