Chapter 56
Farashin Izzah Part 1 Complete Hausa Novel · about 11 min read
Lecture ɗin ya ɗauki kusan awa biyu.. Ko da lecturer yake bayani, Zahra na rubutu cikin nutsuwa kamar yadda ta saba. Duk da haka, Firdausi ta lura cewa yau ba ta yin tsokaci ko tambayoyi kamar yadda take yi a wasu lokutan.
Da aka tashi…
Students suka fara fita ɗaya bayan ɗaya
“Next class ɗinmu fa?” Aasiya ta tambaya
Firdausi ta duba timetable a wayarta
“Forty-five minutes break.”
“Perfect!” Suhaima ta ce. “Mu je garden mu zauna.”
Dukkansu suka amince.
Faculty garden ya cika da ɗalibai, kamar kullum dama baya rasa mutane, wasu na karatu, wasu na ɗaukar pictures, wasu kuma na hira
Su biyar suka zauna ƙarƙashin wata babbar bishiya
Firdausi ta fito da snacks daga jakarta
“Who wants chips?”
“Me!” Aasiya ta ɗaga hannu.
Dariya suka yi.
Saudat na shan ruwa cikin nutsuwa
Zahra kuwa ta cire sunglasses ɗinta ta ɗora kan gashinta, tana scrolling Instagram.
Can…
Firdausi ta taɓa hannunta
“Baby…”
“Hm?”
“Don’t look now.”
Zahra ta ɗaga gira
“What again?”
Firdausi ta yi murmushi
“Guess who’s coming.”
Zahra ta sauke wayarta a hankali, ta ɗaga kai.
Can daga nesa… Saurayin nan ne, amma wannan karon ba shi kaɗai ba
Yana tare da wasu abokansa biyu, suna ta hira suna dariya
Da suka iso kusa da garden ɗin…
Ɗaya daga cikin abokansa ya taɓa kafaɗarsa yana nuna inda Zahra take
Ya waiwayo.Idanunsa suka sauka kanta.
Na ɗan lokaci… ya tsaya.
Sai dai abin mamaki wannan karon, bai ƙaraso ba, bai yi ƙoƙarin katse hirarsu ba
Sai kawai ya ɗan gyada kai cikin girmamawa, kamar sallama daga nesa
Sannan ya ci gaba da tafiya tare da abokansa.
Suhaima ta bishi da kallo
“See? Yau kuma ko karasowa bai yi ba”
Firdausi ta gyada kai
“Maybe ya fara respecting your boundaries.”
Zahra ta mayar da idanunta kan wayarta
“Good! He learned frm his mistakes” Shi kaɗai ta faɗa
Amma kafin ya ɓace daga ganinsu… suka kalli ɗaya daga cikin abokansa ya yi masa dariya yana bugun kafaɗarsa
Saurayin ya girgiza kai kawai yana murmushi, alamar har yanzu ba su daina zolayarsa ba
Saudat ta kalli Zahra
“Kin ga? Ko da ya gan ki, bai zo ya dame ki ba.”
Zahra ta kashe screen ɗin wayarta ta miƙe tsaye, dan bata bukatar wannan convo ɗin at all
“Break is almost over! Let’s go” Ta ɗauki jakarta ta fara tafiya
Sauran suka bi bayanta.
Shi kuwa a can nesa, ashe tsayawa yayi, ya waiwayo sau ɗaya
Ya hango Zahra tana tafiya cikin kwarjini kamar kullum.
Sai ya yi murmushi a hankali ya faɗa wa kansa,
“One day… ko da ba za ki so ni ba, za ki san ni da gaske nake” Ya juya ya ci gaba da tafiya
Kwanaki suka ci gaba da ja.. a hankali…
Yanayin da ke tsakanin Zahra da ƙawayenta ya fara komawa kamar da
Ba wai ta dawo tsohuwar Zahra mai shagwaɓa ba…
Amma ta daina ɗaukar komai a zuciya, suna dariya tare, suna cin abinci tare, suna zuwa lectures tare sai dai abu ɗaya ya canza…
Zahra ta daina saka kanta a yawancin hirarrakin banza da suke yi
Idan suna ta surutu… Ita sai ta yi murmushi kawai, ta dawo wata nonchalant lady ce
Wani lokaci ma ta ɗaga kai daga wayarta ta ce,
“You people are unbelievable.” Sai su yi dariya gaba ɗaya.
Wata ranar Asabar…
Kowacce na gudanar da abin da ya dace da ita.
Firdausi na kitchen tana dafa lunch. Saudat na gyara parlour.
Aasiya da Suhaima kuma na wanke kayan da aka ɓata
Can daga kitchen… Sai aka ji muryar Firdausi.
“Saudat!”
Saudat ta fito
“Yes?”
“Ke kika gama vegetable seasoning ɗin nan baki faɗa ba?”
Saudat ta haɗe gira
“Ni kuma? Ai ke kika yi amfani da shi jiya”
“No, ban yi ba.”
“Wallahi kin yi.”
“Saudat, don’t argue with me.”
“Ni ma don’t accuse me of what I didn’t do.”
Cikin ƴan daƙiƙu… Murya ta fara tashi sosai, don kamar zasu yi dambe ne
“Always kina manta abubuwa!” Cewar Firdausi
A mugun zuciye Saudat ta ce
“Ni na manta ko ke?”
“You always think you’re right!”
“And you think everyone is wrong!”
A falo… Zahra ta ɗago kai daga laptop ɗinta
Ta kallesu kofar kitchen ɗin na wasu daƙiƙu
Sannan ta miƙe ta karasa bakin kitchen ɗin ta ce cikin nutsuwar da ba a saba gani a wajenta ba,
“Firdausi… enough” Ta juya ta kalli Saudat
“You too.”
“Ba seasoning ba ne zai sa ku ɗaga wa juna murya.”
Firdausi ta yi shiru, Saudat ma ta sauke numfashi
Aasiya ta zo ta tsaya tsakaninsu tana murmushi.
“See?”
“Wannan shi ne abin da nake ta faɗa muku.”
“Ba zai yiwu mutane biyar su zauna gida ɗaya ba ba tare da misunderstanding ba.”
“Kowa yana da ra’ayinsa.”
“Kowa yana da halinsa.”
“Amma abin da ya fi muhimmanci shi ne…”
“Idan wani ya ɓata miki rai, ki faɗa masa abin da ya yi cikin lumana”
“Kar ki tara shi a zuciya.”
“Kar kuma ƙaramin abu ya zama babban faɗa.”
Ta kalli Firdausi
“Ko da ya kare tunda Duk mu muka amfana da shi bai kamata ki ce haka ba”
Firdausi ta gyada kai
Ta juya ta kalli Saudat.
“I’m sorry… maybe na yi saurin fushi.”
Saudat ta yi murmushi
“Ni ma I’m sorry.”
Firdausi ta miƙa mata hannu, Saudat ta kama.
Duk suka yi dariya.
Zahra ta girgiza kai tana murmushi
“You people can fight for Africa.”
Firdausi ta nuna ta da yatsa
“Ke dai ki yi shiru amma waya kai ki fushi? Ba ke ce kika taɓa marin mutum a cafeteria ba?”
Dariya ta kaure a falon.
Har Zahra sai da ta rufe fuskarta tana dariya “Firdausi!”
Da yamma.
Aasiya na shirin fara girki.
Ta buɗe cupboard ta an leƙa.
Sannan ta ɗaga murya
“Girls!”
“Kamar vegetable oil ya ƙare.”
Zahra na zaune a sofa tana karanta wani article a iPad ɗinta.
Ba tare da ta ɗaga kai ba, ta zaro ATM card daga wallet ɗinta.
Ta miƙa wa Aasiya
“Take this.”
“If you’re going out, just buy it.”
Aasiya ta karɓa
“Baby, how much should I spend?”
Zahra ta ɗan yi murmushi
“Whatever we need.”
Ta ɗan ɗaga kai ta kalli dukkansu
“And please… tun da duk kun san PIN ɗin card ɗin…”
“Duk wani household need ba sai kun tambaye ni ba.”
“Idan abu ya ƙare, ku saya.”
“It’s our home.”
“Not mine alone.”
Firdausi ta yi murmushi.
“Allah ya ƙara arziki.”
Saudat ta ce
“Ameen.”
Suhaima ta riƙe card ɗin tana kallon Zahra
“Wallahi… ba ki taɓa sa mu jin kamar baƙi a gidan nan ba.”
Zahra ta yi murmushi cikin sauƙi
“You’re not guests.”
“You’re my family.”
Asabar ce.
Bayan sun gama lectures na ranar, Zahra ta fito daga lecture hall tana miƙa hannayenta sama kamar wacce aka sauke wa wani babban nauyi.
“Oh my God… I’m officially exhausted.”
Firdausi ta yi dariya.
“Ke ma kin ji gajiyar?”
“Today was too much.”
Aasiya ta rufe littafinta
“So… what’s the plan?”
Suhaima ta ɗaga gira tana kallon Zahra.
“Baby, don’t tell me we’re going straight home.”
Zahra ta tsaya tana kallonsu na ɗan lokaci kafin murmushi ya bayyana a fuskarta.
“You know what?”
“What?” Duk suka tambaya a tare.
“I think we deserve a break.”
Firdausi ta yi tsalle
“Yeeeees!”
“Let’s go somewhere.”
Saudat ta ce da sauri
“Wallahi ni gida zan koma. Na gaji sosai.”
Zahra ta tunkuɗe kafaɗarta tana murmushi.
“No excuses.”
“Today is on me.”
“Shopping?” Aasiya ta tambaya.
Ta amsa mata “Shopping.”
“Food.”
“Ice cream?”
“Anything.”
Firdausi ta yi ihu
“I love this rich friend of ours!”
Dariya ta kaure a tsakaninsu, daga haka Duk suka wuce inda zahra tayi parking mota
Zahra ta buɗe motarta da remote.
Beep!
Headlights ɗin motar suka yi flashing.
“Everybody in.”
Suka shiga.
Firdausi ta zauna a front seat
Aasiya, Saudat da Suhaima kuma a baya.
Da suka ɗaura seat belts…
Zahra ta kunna motar. Suna Jin 30% of gajiyarsu ya tafi saboda shopping din da zasu
Soft English R&B ya fara fita daga speakers. AC mai sanyi ya mamaye motar.
Suka kama hanya
A cikin motar babu wanda ya rasa abin faɗi.
Firdausi na ba su labarin wani lecturer da ya kasa kunna projector tsawon minti goma.
Aasiya da Suhaima suka riƙa dariya har hawaye.
Saudat kuwa sai girgiza kai take
“You people are impossible.”
Zahra ta yi murmushi tana tuƙi.
A irin waɗannan lokutan ne take jin nutsuwa, babu hayaniya, babu family drama, babu Mummy, sai ƙawayenta kaɗai.
Kusan mintuna ashirin bayan haka…
Suka isa babban shopping mall
Parking lot ɗin ya cika da motoci.
Luxury SUVs, Sedans, Families, Students, Businessmen
Da zarar Zahra ta fito daga motar… Kai tsaye idanun mutane suka dawo kanta
Wasu suka fara raɗa-raɗi
“Isn’t that Zahra?”
“Wacce influencer ɗin nan?”
“I swear she’s prettier in real life”
Dama kullum zancen ɗaya kenan
Firdausi ta yi dariya a hankali
“Celebrity.”
Zahra ta yi rolling eyes
“Can we just go?”
Suka shiga mall, da farko boutique
Firdausi ta gwada handbags kusan guda shida.
Suhaima ta dage sai Zahra ta gwada wani designer sunglasses.
Aasiya tana ta duba skincare products.
Saudat kuwa tana ta kallon prices tana girgiza kai.
“Haba… wannan turaren price ɗinsa zai biya semester registration.”
Duk suka yi dariya.
Zahra ta ɗauki perfume ɗin
“Pack it.”
Saudat ta zaro ido
“Baby!”
“What?”
“Kada ki saya saboda ni.”
Zahra ta miƙa black card ɗinta.
“Use this.”
Cashier ta yi murmushi
“Thank you, ma’am.”
Daga nan suka wuce bookstore
Zahra ta sayi novels guda huɗu.
Firdausi ta ɗauki planner
Suhaima kuwa ta sayi colorful sticky notes.
Sai suka ƙarasa food court.
Burgers, Pizza, Chicken, Milkshakes, Ice cream.
Table ɗinsu ya cika da abinci
Suhaima ta ɗaga spoon
“Moment of silence for this beautiful meal.”
Firdausi ta jefe ta da tissue
“Drama queen.”
Dariya ta sake cika wajen.
Har Zahra da ba ta cika dariya sosai ba.. sai data yi
Bayan sun gama cin abinci…
Suka yi ɗan yawo, suka ɗauki pictures, selfies, videos.
Har Firdausi ta tilasta Zahra ta yi TikTok trend da su
“No way.” Inji Zahra
“Please!”
“Never.”
A ƙarshe dai suka lallashe ta. Video ɗin ya fito da kyau sosai haka ta dinga posting ɗinsu
Karfe shida saura kaɗan Aasiya ta kalli agogo
“We should head home oo, traffic will start”
“True.”
Suka nufi parking lot.
Ba tare da sun sani ba… a can ɗaya gefen parking ɗin…
Wata black Hilux mai tinted glass tana tsaye tun kafin su fito, mutane biyu ne a ciki, fuskokinsu ba su bayyana ba,
Driver ya gyara mirror ɗinsa, Idanunsa suka sauka kan Zahra.
Ta buɗe motarta, ƙawayenta suka shiga, ta tada motar, ta fice daga parking lot cikin nutsuwa
Mutumin da ke gefen driver ya zaro waya
Ya danna wani number.
Da aka ɗaga… ya ce cikin sanyin murya
“They’re moving.”
Daga ɗaya ɓangaren aka amsa
“Good! Don’t lose them.”
“Follow them…”
“But don’t let the girls notice.”
Call ɗin ya katse, Driver ya kunna motar, Hilux ɗin ta fara tafiya a hankali… tana bin motar Zahra
Motar Zahra ta fita daga parking lot cikin nutsuwa, ba tare data kula da motar dake bayanta ba
A cikin motar kuwa…
Firdausi ce ta haɗa Bluetooth da wayarta
Nan take wata waƙar Khaligraph Jones ft. Nyashinski ta fara tashi.
Suhaima ta yi ihu
“Oh my God! This is my jam!” Ta fara rawa a zaunen da take
Aasiya ta buga dashboard da tafin hannunta tana bin beat ɗin.
Har Saudat da ba ta cika shiga irin waɗannan abubuwan ba, sai da ta yi murmushi.
Zahra ta girgiza kai tana dariya
“You people are crazy.”
Firdausi ta juya ta kalleta
“Baby, at least smile.”
“I’m smiling.” Zahra ta ce
Firdausi ta taɓe baki “No, that’s not a smile.”
“Kawai kina showing teeth.”
Duk suka sake barkewa da dariya.
A can baya… Black Hilux ɗin na binsu, ba ta matsowa kusa ba, ba ta kuma yin nisa ba, kawai tana maintaining distance ɗinsu dan kar su fahimta
Sai dai duk inda Zahra ta juya… Nan motar ma take yi
Mutumin da ke seat na gaba ya ce
“Keep your distance.”
Driver ya gyada kai
“She must not suspect anything.”
Mintuna goma suka yi suna tafiya, traffic ya fara yawa, Motoci na shigowa da fita ga uban Napep banda Babur da suka yi yawa
Sai wata trailer ta shigo tsakaninsu. Na ɗan lokaci… Hilux ɗin ya ɓace daga ganin Zahra
A cikin motarsu
Firdausi ta ce
“Baby, let’s stop somewhere mu sayi yoghurt, kinga akwai white rice sai mu haɗa”
Zahra ta girgiza kai
“Tomorrow.”
“Please.” Firdausi ta ce
“No.”
Suhaima ta haɗa baki
“Wai ke ba kya taɓa changing your mind ne?”
“No.” Zahra ta kuma fada
Aasiya ta yi dariya
“Stubborn rich kid.”
Zahra ta nuna ta.
“I heard that.”
Da suka wuce wani traffic light…
Trailer ɗin ta kauce, Hilux ɗin ya sake bayyana.
A wannan karon… Ya fi kusa
Saudat ce ta fara lura, ta ɗan kalli side mirror. Sai ta sake kallon gaba.
Bayan wasu daƙiƙu… ta sake kallon mirror
Hilux ɗin na nan… ta yi shiru.
Ta ce wa kanta
“Coincidence ne.”
Suka sake wucewa wani roundabout
Zahra ta juya hagu
Hilux ɗin ma ya juya hagu.
Saudat ta sake kallon mirror. Gabanta ya fara faɗuwa.
Ba ta ce komai ba, ta ci gaba da lura
Wani speed breaker ya sa Zahra rage gudu. Hilux ɗin ma ya rage gudu.
Da Zahra ta ƙara speed… Shi ma ya ƙara.
Saudat ta haɗe gira, a hankali ta taɓa hannun Aasiya.
“Aasiya…”
“Hmm?”
“Please… Ki duba side mirror.”
Aasiya ta ɗan waiga
“Me zan gani?”
“Waccan black Hilux.”
Aasiya ta kalla
“Na gani.”
“Me ya faru?”
“Ki ci gaba da kallonta.”
Aasiya ba ta fahimta ba.
Sai dai bayan kusan minti biyu ta lura.
Hilux ɗin ba ya wucewa, ba ya kaucewa, yana binsu ne kawai.
Ta haɗe gira, ta sake kallon Zahra.
Sai kuma ta yi shiru
Ba ta son ta tayar musu da hankali ba tare da tabbaci ba.
A gaba…
Zahra har yanzu tana tuƙi cikin nutsuwa.
Firdausi na ta hira Suhaima na dariya.
Ba su san abin da ke faruwa ba.
Sai Saudat ta sake kallon mirror. Hilux ɗin har yanzu na nan.
Wannan karon…
Ta ji wani irin sanyi ya ratsa zuciyarta, ta haɗiye yawu
Cikin ƙaramar murya da ba kowa ya ji ba…
Ta ce
“…Baby…”
Zahra ba ta juyo ba ta ce
“Hmm?”
Saudat ta ɗan yi shiru, ta sake kallon mirror.
Sannan ta ce a hankali…
“I think…”
“…akwai wata mota da ke bin mu.”