← Book details Farashin Izzah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 51 OF 59

Chapter 49

Farashin Izzah Part 1 Complete Hausa Novel · about 12 min read

Kwana biyu bayan haka…Da yamma gidan ya yi tsit as usual

Mami na cikin kitchen tare da Mama Ladi, Abbah bai dawo daga office ba

Ya Umar kuwa yana wajen aiki

Zahra ta sauko daga sama
Sanye take cikin doguwar atamfa mai launin peach da farin scarf

Wayarta na hannunta, hankalinta gaba ɗaya yana kan chatting da da take yi a WhatsApp

Har ta shiga main parlour ba ta ma lura da wanda ke ciki ba

Sai dai…

“Batoul! Ba zaki yi magana ba?”

Wata tsawar Mummy ta sanya ta ɗaga kanta da sauri, ta waigo

Mummy na tsaye a tsakiyar parlour. Batoul kuma na zaune a kan sofa, ta turo baki gaba

“Meye na ji wai?”

Mummy ta ci gaba da magana cikin fushi

“Batoul, me ya sa za ki tashi ki zaɓo min talaka?”

“Ki rasa wanda za ki tsaya da shi sai mutumin da ba shi da komai?”

“Ko kin ga kin yi kama da wacce talaka zai aura ne?”

Batoul ta yi ƙasa da kai
“Mummy… Please ki saurare ni”

“Ni ba…”

Mummy ta ɗaga mata hannu.

“Rufemin Baki shegiya, kin san me zafin talauci yake?”

“Har yanzu yarinya ce ke, ba zan bari ki shiga rayuwar da za ki riƙa wahala ba”

“Na taso cikin wahala, kuma ba zan yarda ’yata ta koma cikinta ba.”

Zahra dai ta tsaya daga bakin parlour, Idanunta na kai-komo tsakanin Mummy da Batoul, Mamaki ya cika fuskarta

A zuciyarta ta ce,
‘Batoul? Talaka? Ban taɓa tsammanin za ki tsaya da mutum irin wannan ba’

A hankali ta sauke idanunta, sai hotunan Saudat.. da unguwarsu da irin rayuwar da ƙawayenta suke ciki… suka ratsa zuciyarta.

Ta ɗan girgiza kai a hankali da sauri

‘No impossible, wannan ba zai yiwu ba. Allah Ya yalwata wa kowa Allah Ya fitar da masu wahala daga ƙuncin rayuwa, amma tunanin fadawa wannan rayuwarma zubi ne’ Ta yi wannan addu’ar ne a ranta

Sannan ta ci gaba da kallonsu.

Mummy kuwa har yanzu ba ta gama masifar nata ba ganin kamar har sannan Batoul bata fahimtarta

“Na yi ta wahala kafin Allah Ya ɗaga ni, ba zan bari ki rushe rayuwarki da hannunki ba”

Batoul ta ɗan ɗaga kai Idanunta sun cika da ƙwalla

“Mummy shi fah mutum ne nagari, yana da ilimi, kuma yana da burin rayuwa”

Mummy ta yi wata irin dariyar ganin wautan Batoul
“Burin rayuwa?, Buri zai ciyar da ke ne?, Buri zai gina miki gida?, Buri zai siya miki mota?, Buri zai sa ki ci Mai kyau kisha mai kyau?”

Batoul ta cije laɓɓanta, ta yi shiru

Mummy ta sake cewa
“Ki ji ni da kyau, daga yau.. kar na sake jin sunansa, kar kuma na sake ganin kina magana da shi balle ki barsa ya zo gidan nan, Idan kina son zaman lafiya a gidan nan.”

Batoul ta sunkuyar da kai, ba ta ce komai ba

Sai ɗan gunguni da take yi a hankali, alamar ba ta gamsu da maganar ba

Zahra kuwa…
Ta tsaya tana kallonsu cikin mamaki, ta rasa me za ta ce, ko me za ta yi

Saboda wannan ne karon farko da ta ga Mummy cikin irin wannan matsanancin fushi saboda maganar saurayi kuma ta san tabbas Mummy nada gaskiya


Parlour ɗin ya yi shiru na ɗan lokaci, Mummy ta gyara mayafinta ta ja dogon tsaki

“Na faɗa miki abin da zan faɗa. Ki yi yadda kika ga dama”

Ba ta ƙara kallon Batoul ba, ta juya ta nufi staircase cikin takunta na isa, har ta ɓace sama…

Ba tare da ta waiwayo ba.

Batoul kuwa… ta zauna na wasu daƙiƙu tana kallon ƙasa, hannunta riƙe da gefen hijabinta

Fuskarta ta nuna taɓuwa sosai
A hankali ta ɗauki wayarta daga kan center table

Ta buɗe ta, contacts ta shiga, ta tsaya na ɗan lokaci tana kallon wani suna

Sai ta latsa kira, wayar na ringing… ta miƙe tsaye ta fara tafiya a hankali zuwa staircase

Zahra dai har lokacin tana tsaye tana mamakin Batoul, har Batoul ta fara hawa matakalar

Batoul ta ci gaba da riƙe wayar a kunnenta, da ta zo wucewa…

Zahra ta matsa gefe cikin ladabi ta ba ta hanya, ba a ce komai ba

Batoul ma ba ta kalle ta ba, sai kawai ta ci gaba da tafiya

Can… a ɗayan ɓangaren wayar aka daga

Batoul ta sauke wani ajiyar zuciya, da ƙyar ta ce

“Hello…” Muryarta can ƙasa

Ba tare da ta tsaya ba… ta ci gaba da tafiya zuwa ɗakinta tana magana cikin siririyar murya har ta ɓace daga ganin Zahra

Zahra ta tsaya a matakalar, ta bi Batoul da kallo har ƙofar ɗakinta ta rufe

Sai ta ɗan haɗe gira, ta sauke numfashi

Ba ta san ko wa Batoul ta kira ba, ba kuma ta damu da bincikensa ba. A hankali ta girgiza kai ta ci gaba da hawa zuwa ɗakinta…

A zuciyarta tana addu’ar Allah Ya sauƙaƙa duk abin da yake damun kowa a cikin gidan.

Yau ta kasance Asabar…Tun bayan breakfast…

Mami na zaune a main parlour tana rubuta wasu abubuwa a cikin ƙaramin notebook

Zahra ta sauko daga sama cikin lazzi
“Good morning Mami.”

“Morning Baby.

Ta zauna kusa da ita
“Me kike rubutawa?”

Mami ta nuna mata notebook ɗin
“Abubuwan da za a saya miki.”

Zahra ta haɗe gira
“Na me kuma?”

Mami ta kalle ta
“Kin manta ne? Ba tomorrow za ki koma off-campus ba. Ko kina tunanin da kayanki na gida kawai za ki tafi?”

Kafin Zahra ta ba da amsa…
Sai aka ji muryar Abbah daga corridor

“Ready?”

Su biyun suka waigo.

Abbah ya fito cikin shigar weekend wears dinsa, murmushi kwance a fuskarsa

Zahra ta miƙe
“Abbah Ina za mu je?”

Abbah ya yi kamar bai ji tambayar ba

“Driver ya wanke motar?”

“Eh sir” Ya Umar ne ya amsa yana saukowa daga sama

Abbah ya ce
“Mu tafi toh”

Mami ta miƙe tana yafa laffayanta dake ajiye a goge a gefe Mami ta ɗauka ta yafa

Duk compound suka wuce, suka shiga mota, mota biyu ce ta face daga gidan

A gaba… Motar Abbah ne, a baya kuma driver na biye da ita

Da suka isa babban shopping mall…

Zahra ta tsaya tana kallon girman wajen, ta kalli Abbah.

“Abbah… Me za mu saya ne haka?”

Abbah ya yi murmushi
“Duk abin da za ki buƙata.”

Mami ta ce
“Ki daina tambaya, koma menene idanunki zasu gani”

Suka shiga ciki, Nan ne aka fara zagaya side zuwa side

Da farko…
Mami ta fara zaɓar mata bed sheets masu kyau, Duvet, Pillows, Pillow cases, Blankets masu laushi, Towels kala-kala, Bathroom mats, Laundry basket, Mirror, Table lamp, Study lamp, Storage boxes, Laundry bag.

Zahra ta riƙe goshinta.

“Mami!!! Ya yi fa”

Mami ba ta ma saurare ta ba.

“Wannan ma ƙara”
“Ga wannan ma… shi ma ɗauka.”

Ya Umar na biye da trolley, yana zuba su

Can ya kalli Zahra, ya girgiza kai

“Baby Gidan nan ko shop zaki buɗe ne a ciki?”

Ta yi dariya.

“Wallahi ba ni ba ce, kana gani ai, Mami ce”

Mami ta harare su
“Ku ci gaba da surutunku. Idan kun kai mata kayan gobe za ku gane dalilin da ya sa nake saya”

Daga nan…
Suka wuce wani babban boutique

Nan Abbah ya ce
“Baby Ki zaɓi abin da kike so”

Zahra ta fara ƙin yarda
“Abbah… Ina da kaya”

Ya girgiza kai
“Na sani, amma waɗannan na can off-campus ne”

Daga ƙarshe…
Ta fara zaɓar wasu dogayen gowns, Abayas, hijabai kala daban-daban, Slippers na cikin gida, Flat shoes, Sneakers, Handbags, Perfumes, Skin care products, Jewelleries masu kyau

Mami tana biye da ita tana gyara zaɓinta lokaci zuwa lokaci

“Wannan ya fi, wannan kuma ya fi dacewa da ke”

Ya Umar kuwa… Sai ɗaukar shopping bags yake yi, har ya fara gajiya

Ya kalli Abbah
“Abbah! Ni kaɗai ne porter a gidan nan?”

Abbah ya yi dariya
“Kai ne babban yaya, don haka ka ɗauka”

Zahra ta riƙe cikinta tana dariya
“Sorry Yaya.”

Ya nuna mata yatsa
“Ke ce silar wahalata yau ba? Zan rama oo”

Ta yi dariya sosai.

Bayan sun gama…
Suka shiga wani restaurant da ke cikin mall, suka yi lunch tare, suna hira suna dariya

Abbah lokaci zuwa lokaci yana kallon Zahra, yana jin daɗin yadda farin cikinta ya bayyana ƙarara a fuskarta.

Bayan sun gama… suka fito
Aka saka duk kayan cikin boot na motoci, sa suka kama hanyar gida…

Zahra ta jingina da kujerar motar, ta kalli Mami

Ta ce cikin tausayin murya
“Mami! Ni ban san me zan ce muku ba, soyayyar da kuke nuna min har ya fara yawa”

Mami ta shafa hannunta
“Ke ɗaya ce Allah Ya ba ni, kuma ke ce Autar gidan”

Abbah ya juyo kaɗan daga gaban motar, ya ce da murmushi,

“Ina matukar son yara masu kokari both School da Islamiya and you’re always making me proud, secondly Ina son gani yarana suna nuna mun kauna kuma kullum suna manne da Ni, halinki ne tun kina jaririrr”

“So, this is nothing hakkina ne na sauke miki”

Zahra ta yi murmushi mai cike da godiya.

Ta ɗaga kanta k
“Nagode… Allah Ya saka muku da aljannatul Firdaus”

“Ameen.” Suka amsa tare…

Da suka isa gida, bayan
Motocin suka shige cikin compound

Suna parking, masu aiki suka fito da sauri, kowa ya fara ɗaukar shopping bags

Duk suka kai parlon Mami na sama, suka ajiye kamar Mami kamar yadda ta umarta

Zahra tun da ta sauko daga mota…

Sai ta fara murza kafa ta ce

“Wayyo… Na gaji”

Ya Umar ya wani kalleta

“Ke kika gaji? Ni da na ɗauki bags ɗin nan fa? kinji nayi complain?”

Ta yi dariya
“Sorry Yaya, Duk kauna ce”

Ya girgiza kai kawai yana murmushi

Duk suka wuce ciki
Abbah ya wuce ɗakinsa domin ya huta, Ya Umar ma ya nufi nasa

Mami da Zahra kuma suna zaune a main parlour, a gabansu akwai fresh juice da Anty Binta ta kawo musu

Can…
Mama Ladi ta shigo

“Hajiya.”

Mami ta ɗago kai
“Na’am.”

“Akwai wani mutum a waje, yace ya zo wajenki”

Mami ta gyada kai
“Ki ce ya shigo.”

“To Hajiya.”

Ba a ɗau lokaci ba…
Wani mutum mai matsakaicin shekaru ya shigo

A hannunsa akwai wata babbar Ghana Must Go mai cike da kaya

Da ya shiga… Ya durƙusa cikin ladabi

“Barka da warhaka Hajiya”

“Yauwa, sannu da zuwa” Mami ta amsa

“Ka gama?”

Ya yi murmushi
“Alhamdulillah Hajiya, na gama duk yadda kika ce”

“Kuma na tabbatar komai ya yi kyau, In shaa Allah”

A dai-dai lokacin…
Zahra ta sauko daga sama, Wanda bata daɗe da hawa ba

Da alama ta canja kaya ne, ta ƙaraso parlour, ta zauna kusa da Mami

Mami ta waigo gare ta
“Baby! Miƙo min wayata”

Zahra ta ɗauko wayar Mami daga kan side stool, ta ba ta

Mami ta buɗe banking app ɗinta, sai ta ɗaga kai

“Faɗa min account number ɗinka.”

Mutumin ya fara karantawa a hankali

Mami ta shigar, ta sake tabbatarwa, sannan ta danna transfer

Wayarta ta yi ƙaramar ƙara

“Sent” Ta miƙa masa wayar

Nan take fuskarsa ta washe

“Haba Hajjiya, ke ce ai, nasan ma ya shigo, inma bai shigo ba toh network ne”

“Allah Ya saka da alheri Hajiya!Allah Ya ƙara arziki”

“Ameen” Mami ta amsa

Yana godiya ya miƙe sannan ya juya ya fita

Zahra ta kasa danne son sanin abin, ta matsa kusa da Mami

“Mami… Who is he?”

Mami ta nuna Ghana Must Go ɗin

“Dauka Ki kai sama”

Zahra ta turo baki
“Na waye? Ina zan kai?”

Mami ta yi murmushi kaɗan
“Buɗe ki gani mana”

Zahra ta zaro ido
“Really?”

Ta matsa kusa da jakar ta durƙusa, ta buɗe zip ɗin a hankali

Tana buɗe wa… ta tsaya cak
“Eh?”

Ta saka hannu ciki, ta ciro wata sabuwar atamfa, ta buɗe ta

Kyakkyawar dinkin ya fito sosai a jikin atamfar

Ta ɗaga ta gwada a jikinta, sai ta haɗe gira

“Mami… Size ɗina ne.”

Ta sake saka hannu, ta ciro wata

Ita ma size nata ne, ta sake ciro ta uku

Duk… Size ɗinta ne, ta ɗaga kai a hankali

Idanuwanta cike da mamaki ta kalli Mami

“Mami…”

“Duk…”

“Nawa ne?”

Mami ta jingina da kujera, ta yi murmushi
“Eh naki ne”

Na ɗan daƙiƙa… Zahra ta kasa cewa komai

Ta sake kallon atamfofin, ta sake kallon Mami

“Wait.. dama tailor ne?

Mami ta gyada kai
“Na kai masa su tun kwanaki. Na ce ya gama kafin ki koma off-campus”

“Saboda na san daga yau za ki fara tattara kayanki.”

Zahra ta buɗe baki cikin mamaki
“Ashe wannan ne… Shi ya sa kika riƙa cewa kar na shiga ɗakinki kwanakin baya”

Mami ta yi dariya
“Kin gane yanzu?”

Zahra ta yi murmushi ta rungume atamfar da ke hannunta

Sai ta matsa kusa da Mami ta rungume ta da ƙarfi.

“Mami… I’m speechless

Mami ta shafa kanta cikin taushi

Zahra ta sauke kanta a kafaɗar Mami, tana murmushi kamar ƙaramar yarinya…

“Wai duk nawa ne?”

Mami ta yi mata kallon nan na manya
“Ina ga Size dina kika gani”

Sai Zahra ta fashe da dariya, man take ta miƙe tsaye

Ta riƙe atamfa ɗaya a hannunta

“Mami… One minute!”

Ba ta jira amsarta ba, ta juya da gudu

“Kee! Ki yi a hankali!” Mami ta yi mata tsawa ganin gudu take yi

Kai tsaye ta nufi ɗakin Abbah, ta yi knocking sau ɗaya

“Come in” ta tura ƙofar

Abbah na zaune kan kujerarsa yana shan coffee, ya ɗago…

Sai ya ga Zahra na tsaye da wata atamfa a hannunta

Ya ɗan yi murmushi
“My Baby! Lafiya?”

Ta ƙarasa da sauri, ta durƙusa gabansa

“Thank you so much Abbah.”

Ya haɗe gira
“Na me kuma?”

Ta ɗaga atamfar
“Yanzu tailor ya kawo”

“Allah Ya saka maka da alheri”

Abbah ya yi murmushi kawai, ya shafa kanta
“Sun miki kyau?”

Ta gyada kai da sauri.l
“Very much! Sun yi kyau sosai”

“Nagode.”

Abbah ya ce cikin nutsuwa
“ki ci gaba da gode wa Allah.”

Ta sumbaci hannunsa.
“In shaa Allah! Allah Ya ƙara maka lafiya da arziki da tsawon rai”

“Ameen, Baby” Ya amsa yana murmushi

Ta yi masa sallama, ta fito daga ɗakin cikin farin ciki.

Da ta dawo parlour…
Mami na zaune a inda ta barta

Da ta ga Zahra na ta murmushi…

Sai ita ma ta yi murmushi, ta juya ta kira,

“Anty Binta.”

“Na’am Hajiya.” Ba’a ɗsu lokaci ba sai gashi ta karasa cikin parlon

“Dauki Ghana Must Go ɗin nan. Ki kai wa Baby ɗakinta, ki jera mata su cikin wardrobe.”

“Toh Hajiya.”

Ta ɗaga babban Ghana Must Go ɗin, ta nufi sama

Zahra kuwa…
Sai bin ta take da ido.

Ta juya ta kalli Mami.

“Mami! Allah Ya bar min ke.”

Mami ta yi murmushi
“Ameen. A tsufar Lafiya”

Zahra ta gyada kai, sai ta juya ta bi bayan Anty Binta zuwa sama
Chapter 51 · 0% Book details