← Book details Farashin Izzah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 45 OF 59

Chapter 43

Farashin Izzah Part 1 Complete Hausa Novel · about 12 min read

Washegari... Da sassafe bayan Abbah ya dawo daga sallar Asuba...

Ya zauna na ɗan lokaci yana karanta Al-Qur'ani kamar yadda ya saba.

Da ya kammala...
Ya ɗaga kai ya kalli ɗaya daga cikin masu aiki daya shigo zai karɓa key ya wanke masa mota

"Ka gaya wa Umar ina son ganinsa."

"Toh Alhaji."

Bai wuce mintuna biyar ba...
Ya Umar ya shigo.

Ya yi sallama cikin girmamawa.

"Assalamu alaikum, Abbah."

"Wa alaikumus salam."

Ya ƙarasa ya zauna.

Sai dai...

Tun da ya ɗaga kai ya kalli fuskar Abbah... Ya fahimci akwai magana mai nauyi dan haka ya sauke kansa da sauri saboda guilty questions

Abbah ya yi shiru na wasu daƙiƙu, sai ya ce cikin sanyin murya,

"Umar..."

"Na'am, Abbah."

"Kaima yanzu... Uwarka ta raba mu kenan?"

Ya Umar ya ɗago kai da sauri
"Abbah..."

Abbah bai bar shi ya yi magana ba, ya ci gaba.

"Kamar yadda ta raba ni da Batoul?"

Kalmar ta tsaya wa Ya Umar a maƙoshi, ya sauke kansa ƙasa, ya haɗa yatsunsa wuri ɗaya yana wasa da su, ya rasa abin cewa.

Abbah ya jingina da kujerarsa, ya yi wani murmushi mai cike da takaici.

"Just go!!! Ba komai."

Ya Umar ya yi saurin girgiza kai.

"No, Abbah I'm sorry, ba haka bane."

Abbah bai ce komai ba yana kallon wani direction

Sai Ya Umar ya ci gaba da magana cikin damuwa

"Ba wai ta raba Ni da Kai bane, kuma har ace zan ɗauka”

"Wallahi ba haka bane."

"Kawai..." Ya haɗiye yawu.

"Ina tsoron bakin uwa ne Abbah, Mummy ta fusata haikan akai na”

Abbah ya ɗaga idanunsa ya kalli ɗansa, a karon farko...
Ya ga tsoron da ke zaune a cikin idanun Ya Umar ya bayyana, Kawai yaji tausayinsa

Ya Umar ya ci gaba.

"Wallahi Abbah, Ina jira ne ta huce sai na sake komawa wajenta na roketa ta janye bakin data min” ya sauke ajiyar zuciya

"Amma... ba yadda za a yi In janye jikina daga kai, dan kai Ubana ne ai Abbah”

Ran Abbah ya ƙara ɓaci, ba don Ya Umar ya faɗi hakan ba...

Sai don ya fahimci irin tasirin da Hafsat ta yi wa zuciyar ɗansa.

Ya miƙe tsaye a hankali ya juya baya.

"It's okay." Ya faɗa ba tare da ya waiwayo ba.

"Just go Umar” Sai ya ƙara da cewa,

"Thank God... ba ku kaɗai ba ne 'ya'yana."

Kalaman sun soki zuciyar Ya Umar fiye da yadda ake tunani. Ya miƙe da sauri, ya ƙarasa kusa da Abbah a rikice

"Abbah, Don Allah ka yi haƙuri. Wallahi ban taɓa nufin hakan ba ko da wasa, kawai tsoron tasirin bakinta nake ji”

Abbah ko da wasa bai juyo ba, Ya Umar ya tsaya a wurin yana kallon bayan Abbah da mamaki, domin ya san Abbah….

Mutum ne mai yawan haƙuri, ba kasafai yake nuna ɓacin ransa ba, amma yau...

Ya fahimci lamarin ya taɓa zuciyarsa sosai, ya sauke numfashi, sai ya ce cikin sanyin murya,

"I'm sorry, Abbah."

Abbah ya fice daga ɗakinsa, Ya Umar ya bisa a baya

Yana fitowa corridor... sai ya ji wasu hannaye sun zagaye wuyansa daga baya

"Abbaaaaa!" Ya ɗan tsorata kafin ya jiyo muryanta, yayi murmushi

Sai ya ji Zahra na ƙoƙarin hawa bayansa.

"Carry me!" Bai san lokacin da dariya ta ƙwace masa ba

"Ke! Baby ashe haka kike da nawi?”

Zahra ta yi dariya sosai
"Ka ɗauke ni kawai "

Abbah ya kama ƙafafunta, ya ɗaga ta a bayansa.

Ta rungume wuyansa tana ta dariya, shi ma yana dariyar

"Subhanallah! Ashe kina da nauyi haka ban sani ba?”

Zahra ta ɗan buga kafaɗarsa
"Ni? Ka ce ni ce mai nauyi? Kai Abbah..”

Abbah ya yi dariya.

"Ahh, na yi zaton har yanzu ƙarama ce ke har yanzu”

Ta yi ƙara tana dariya

"Kai ma fa... Ashe kana da ƙarfi tunda ka iya ɗaukar Baby mai nawi”

Abbah ya sauke ta daga bayansa, ya dawo da ita gabansa, ya gyara scarf ɗinta da ya ɗan zame

Sannan ya shafa kanta
"Baby."

"Na'am?"

"Ki shirya” Ta ɗago tana kallonsa.

"Driver zai kai ki driving school Ina son ki fara training. Kuma a yi miki driving licence

Murmushi tayi ta ce
"Really?"

Abbah ya gyaɗa kai
"Yes, kin fara girma, ya kamata ki san tuƙi”

Ta yi murmushi har haƙoranta suka bayyana.

"Alright, Abbah na! Thank you."
Ta yi saurin rungume shi.

Shi kuma ya shafa bayanta yana murmushi.

Shi dai Ya Umar na can gefe yana kallonsu da murmushi

Abbah kuwa duk da nauyin da ke cikin zuciyarsa saboda abin da ya faru na Ya Umar...

Murmushin Zahra ya sake dawo masa da wani ɗan natsuwa da ya rasa tun shigowar Ya Umar

Bayan Shekara Ɗaya da rabi...
Lokaci... Shi ne babban mai sauya rayuwa inji Malam Bahause

Tabbas haka ne, dan a cikin shekara guda... Abubuwa da dama sun faru ko nace harda canji

Fatima Zahra ba ita ce yarinyar shekara ɗaya da ta gabata ba.

Yanzu ta zama cikakkiyar budurwa mai cike da nutsuwa da izzah.

Ba ta shiga harkar kowa, bata son hayaniya, bata son gulma. Ba ta son raini, kuma ba ta ɗaukar raini daga kowa, uwa Uba izzah da take da shi…

Idan ta yi magana, toh tabbas sai dai cikin natsuwa.

Idan kuma wani ya ƙetare iyakarsa...
Kalma ɗaya daga bakinta kan isa ta sanya ya san ya yi kuskure.

Mutane da yawa suna kallonta a matsayin mai gadara. Amma waɗanda suka santa sosai sun san ba gadara ba ce

Izza ce
Da kuma sanin darajar kanta.

Karfe 4:30 na asuba
Sautin alarm ɗinta ya karade ɗakin, bata yi wata-wata ba, ta miƙe zaune.

Hannu ta miƙa ta kashe alarm ɗin, ta sauko daga kan gadonta a hankali tana murya kyawawan manyan idanunta wanda yake cike da bacci

Ta gyara night cap ɗinta, kai tsaye ta nufi banɗaki. Ta yi alwala cikin nutsuwa.

Bayan ta fito... ta shimfiɗa sallaya
Ta tsaya gaban Ubangijinta, tayi raka’a biyu kafin ta ɗaura asuba

Bayan ta idar... ta zauna tana karata azkar tana gamawa ta muƙe ta ɗauko Al-Qur'ani ta karanta wash shafuka sannan ta rufe

Ta yi addu'o'inta data Saba yi, sai da gari ya fara haske kaɗan...

Ta miƙe, ta nufi bathroom, kunna shower tayi ruwan ɗumin yana shiga jikinta yadda ya kamata bayan ta shafa shower gel

Bayan ta gama wanka... Ta fito tana goge gashinta da farin towel, ta tsaya gaban dressing mirror

Ta buɗe wardrobe ɗinta, bayan ta ɗan yi tunani.. Ta zaro wata atamfa mai tsadar gaske

Dark emerald green ce mai ɗan haɗe da gold embroidery a hannaye da wuyan rigar, an ɗinka rigar cikin salo mai sauƙi amma cike da classy

Ta saka doguwar skirt ɗinta, haɗi da rigarsa, sannan tayi wani ɗauri

Sannan ta ɗaura matching veil mai tsadar gaske

Ba ta cika son make-up ba, saboda haka... Light powder kaɗai ta shafa ta ɗan saka nude lip gloss

Kafin ta ɗauki turaren oud ɗinta ta fesa kaɗan.

Daga drawer, ta ciro agogon zinariya mai siriri ta saka shi a hannunta. Sai bracelet mai kyau

Ƙananan diamond studs ne a kunnuwanta, sai zoben azurfa mai ɗan white stone a sakiya

Ba ta son cika jikinta da kayan ado, hakan yasa ta bari bata sake saka wani abu ba amma hakan ya ƙara fito da kyan halittarta.

Ta ɗauki Schoolbag ɗinta ta saka laptop, notebook da sauran kayan makarantarta

Ta ɗauki key ɗin motarta, sai ta dauki wayarta

Ta kalla mirror na ƙarshe, ta gyara veil ɗinta, Kafin ta fice daga ɗakin.

Da ta sauko parlour...
Mami na zaune tana shan tea.

“Mami na” ta faɗa da murmushi a fuskanta

"Fatima” Mami faa

Ta ƙarasa, ta zauna ta gaisheta

"Ina kwana Mami."

"Lafiya lau, Baby."

"Kin tashi lafiya?"

"Alhamdulillah."

Mami ta yi murmushi tana kallonta.
"Allah Ya tsare."

"Ameen."

Ta zo fita a second parlor ta haɗu da Mummy na zaune tana duba wayarta

Da Zahra ta zo za ta fita...

Sai Mummy ta ɗago kai
“Ahh, Baby har kin fito kenan?”

Zahra na murmushi ta gyaɗa kai haɗi da gaisheta

Mummy na murmushi tace
"A dawo lafiya, Daughter."

Zahra ta gyada kai
"In shaa Allah, Nagode."

Daga haka ta ci gaba da tafiyarta, tana fito compound...

Mai wanke motocin gidan yana kan nata motar ne, gogewa yake yi yadda yake ƙara sheƙi

Yana ganinta ya yi saurin miƙewa

"Ina kwana, Hajiya."

"Lafiya." Ta amsa a taƙaice.

Ya buɗe mata ƙofar motar, ta shiga

Gatekeeper na ganin fitowarta ya buɗe babban gate.

"Allah Ya kiyaye hanya."

"Ameen." Ta amsa tana kunna motar.

A hankali... ta ja motar ta fita daga gidan

Safiyar Juma'a ce, hanyar cike take nak da cunkoso saboda kai yara makaranta

Zahra na tuƙi cikin natsuwa, duk wani motsinta yana nuna ƙwarewa da nutsuwa.

Bluetooth ɗin motarta na kunne
Muryar karatun Suratul Kahf ce ke ratsawa cikin motar cikin daɗin sauraro

Lokaci zuwa lokaci ta kan maimaita wasu ayoyin a hankali, fuskarta cike da kwanciyar hankali.

Bayan kusan mintuna talatin.. ta iso harabar makarantar, ta rage gudun motar tun daga bakin gate

Ta nufi parking lot ɗin ɗalibai, ta yi parking, ta kashe motar, ta ɗauki handbag ɗinta.

Ta sauka, ta kulle motar
Ta gyara veil ɗinta a hankali, ta rataya schoolbag ɗinta a kafaɗa.

Sannan ta nufi faculty ɗinsu da takunta masu cike da izzah da kwarjini.

A shekara guda da ta shafe a jami'a... Sunanta ya riga ya zama sananne, ba kuma don yadda take a media ba, sai don yadda take rayuwarta a real life

A social media kuwa...
Shahararta ta ƙara ninkuwa.

Solo dates dinta, Classy dressing, Luxury lifestyle.

Da kuma yadda take rayuwa cikin mutunci ba tare da nuna surutai ko neman attention ba...

Duk sun ƙara ɗaga darajarta a idon mutane.

A duk lokacin da ta shiga makaranta... ba sai ta yi magana ba, kasancewarta kawai ya isa mutane su juya su kalle ta.

"Isn't that Fatima Zahra? Wancan Famous din?”

"Wallahi ita ce."

"Kai... she's even prettier in real life."

"Yes, tana part 1 ne ai"

"What?! Na zata ma 300L ko 400L ce."

"Ni ma."

"Ban taɓa tunanin 100L take ba."

Wasu na rada.

Amma Zahra...ko kallonsu ba ta yi Kai tsaye take tafiya

Fuskarta cike da nutsuwa, ba murmushin, ba kuma haɗe fuska ba.

Irin tafiyar nan da ke nuna mutum ya san darajar kansa.

Tana isa gaban faculty..

"Princess!"

Ta waigo.

Firdausi ce ke tahowa da sauri

A bayanta kuma...
Asiya, Saudat da Suhaima.

Firdausi ta rungume ta
"Finally! Ashe yau zaki zo da wuri."

Zahra ta yi murmushi
"Ke ce kika saba zuwa a makare ai, as usual”

Firdausi ta ce
“Celebrity."

Zahra ta ɗan harare ta.

"Fir... Stop it. Ni ba celebrity ba ce."

Firdausi ta haɗa hannu.

"Okay Hajiya. Influencer."

Duk suka fashe da dariya.

A dai-dai lokacin...
Wasu ɗalibai biyu suka wuce ta gefensu.

Ɗaya daga cikinsu ya yi wa ɗan uwansa rada.

"Bro..."

"Wallahi ita ce."

"Fatima Zahra."

"Wacce nake nuna maka a TikTok da Instagram."

Ɗayan ya ce cikin mamaki,

"So anan dama take?"

Firdausi ta ji maganar.

Sai ta kalli Zahra tana murmushi
"Kin ji?"

Zahra ta girgiza kai.
"Ba abin da ya dame ni."

"Mu je class” Ta juya ta fara tafiya.

Su huɗun suka bi bayanta.

Yayin da ɗalibai da dama ke ci gaba da bin ta da kallo... ba don komai ba sai don kyauwunta

Da kuma wata irin izzah da kwarjini da Allah Ya ɗora mata, wadda ke sa duk wanda ya gan ta ya yi tunanin ba sabuwar ɗaliba ba ce, illa ɗalibar da ta daɗe a jami'ar, ko ma wacce take gab da kammala karatu.

Ɗalibai suka fara kwararowa zuwa lecture hall.

Zahra da ƙawayenta suka ƙarasa cikin nutsuwa.

Lecture hall ɗin ya riga ya fara cika, wasu na zaune suna ta hira

Wasu kuma sun riga sun buɗe laptops da notebooks ɗinsu.

Kai tsaye ta nufi layin gaba, ba ta son zama baya.

Firdausi ta kalle ta tana dariya
"Ke dai ba za ki taɓa canzawa ba."

Zahra ta ɗan kalleta
"Meye kuma?"

"Kullum front row."

Ta ɗan yi murmushi.
"Na zo karatu ne Fir, ba yawon kallon mutane ba. As long as zan ji lecture sosai... wurin an ya ishe ni."

Asiya ta girgiza kai
"Zan zama ke toh"

Saudat ta ce,
"Ni ma zan dawo gaba daga yau."

Suhaima ta yi dariya.
"Ni kam daga baya nake ganin komai."

Dariya suka yi, suka zauna.

Zahra ta buɗe handbag ɗinta, ta ciro laptop ɗinta sai notebook da biro.

Ta mayar da wayarta silent mode, ta saka ta cikin jaka.

Firdausi ta kalleta
"Ke baki ma shiga Instagram ba tun da muka zo."

Zahra ba ta ɗago kai ba.
"Aji ba wajen social media ba ne, da mun gama lectures...Zan duba."

Firdausi ta ɗaga hannu cikin wasa.
"I give up. Allah ya ƙara miki son karatu."

"Ameen."

Kafin su ƙara magana..
Lecturer ya shigo.

Nan take...
Hayaniyar hall ta lafa. Kowa ya koma mazauninsa.

Lecturer ya ajiye files ɗinsa a kan teburi.
Ya ɗauki attendance register.

Ya ɗaga kai yana kallon ɗaliban.

"Good morning, everyone."

"Good morning, sir."
Suka amsa gaba ɗaya.

"Hope you're all doing well?"

"Yes, sir."

Ya yi murmushi.
"Good."

"Open your notebooks."

"Today, we're starting a new topic."

Nan take...
Zahra ta buɗe notebook ɗinta. Ta gyara zamanta.

Hankalinta ya tattara gaba ɗaya kan lecturer. Abin da ya kawo ta jami'a shi ne neman ilimi.

Kuma hakan ne ya sa tun farkon shekararta malamai suka fara lura da ita.

Ba don shahararta a social media ba...

Sai don yadda take mayar da hankali, yawan yin tambayoyi masu ma'ana, da kuma rubuta duk wani muhimmin bayani ba tare da wasa ko ɗaukar hankali zuwa wani wuri ba.

Firdausi ta ɗan matsa kusa da Asiya ta yi mata rada.
"Kin ga ta?"

Asiya ta yi murmushi.
"Idan lecture ya fara... ko sunanta ka kira.. ba za ta ji ba."

Su duka suka yi murmushi a ɓoye.
Su ma suka maida hankalinsu ga darasin da ake gabatarwa.

Da lecturer ya kalli agogo... Sai ya rufe marker ɗin da ke hannunsa.

"Alright, that's all for today."

"We'll continue next class."

"Those going for Jumu'ah can leave now."

"See you next week."

"Thank you, sir." Dalibai suka amsa gaba ɗaya.

Nan take lecture hall ɗin ya fara watsewa. Maza suka fara nufar masallacin jami'ar.

Mata kuwa suka fito cikin harabar faculty.

Wasu na zaune suna hira, wasu kuma suna jiran friends ɗinsu.

Zahra ta saka laptop ɗinta cikin schoolbag, ta miƙe tsaye.

Firdausi ta miƙa hannunta tana jan numfashi.

"Wallahi lecture ɗin yau ya gama dani."

Asiya ta yi dariya.
"Ni ma."

Suhaima ta ce,
"Mu je mu zauna a ƙarƙashin bishiyar can. Kafin a kunna ruwan faculty muyi alwala”

A hankali suka fara tafiya tare.

Sai dai... Tun daga lokacin da suka fito daga lecture hall...

Zahra ba ta cikin hirarsu. Idanunta na kan Saudat.

Ba fuskarta take kallo ba... Kayan jikinta take dubawa

Doguwar rigar atamfar da Saudat ke sanye da ita ta tsufa sosai. Launinta ya dusashe.

A gefen hannun rigar akwai inda aka sake ɗinkewa da hannu.

Hijab ɗinta ma ya sha wanki sosai har ya fara rasa sheƙinsa.

Takalmanta kuma...
Sai da Zahra ta lura an liƙe gefensa bayan ya yage.

Ta yi shiru… bata ce komai ba.

Ba ta son ta kunyata Saudat a gaban sauran ƙawayensu.

Har suka isa wani inuwa kusa da faculty. Firdausi da Asiya suna ta hira.

Suhaima ta ce za ta je ta sayi ruwa
Sai Zahra ta zauna kusa da Saudat.

Ta ɗan kalleta.

"Saudat..."

"Na'am?"

"Kina lafiya?"

Saudat ta yi murmushi.

"Alhamdulillah. Me ya sa kika tambaya?"

Zahra ta ɗan yi shiru, ta sake kallon rigar da ke jikinta.

Sai ta mayar da idanunta kan fuskar Saudat.

"Babu komai... Na dai ga kin yi shiru ne yau."

Saudat ta yi murmushin da ya kasa ɓoye gajiyarta.

"Na gaji ne kawai."

Zahra ta gyada kai.….

#Farashin izzah
Hauwajay writes__08110615256
Chapter 45 · 0% Book details