Chapter 55
Farashin Izzah Part 1 Complete Hausa Novel · about 11 min read
Tun daga fitowarsu daga cafeteria har zuwa School Villa…
Motar ta yi shiru fiye da yadda suka saba, ba waƙa, ba hira, ba dariya.
Zahra tana tuƙi, idanunta na kan hanya hankali kwance, Firdausi na kallonta lokaci zuwa lokaci
Saudat kuwa tunanin abin da ya faru ya hana ta cewa komai.
Da suka isa gida, kowacce ta shiga ta sauya kaya, bayan ɗan lokaci suka haɗu a falo.
Shirun ya sake mamaye wurin.
A ƙarshe Firdausi ta sauke numfashi
“Baby… can I say something?”
Zahra na scrolling wayarta
“Go ahead.”
Firdausi ta haɗa yatsunta
“I don’t think what happened today was fair”
Zahra ta ɗago kai
“What do you mean?”
“Wallahi… guy ɗin bai cancanci marin nan ba.”
Shiru ne ya sake ratsa parlourn
Aasiya ta gyada kai
“I agree.”
“Na ga komai da idona. Jakar ki ce za ta faɗi, shi kuma ya tare ta.”
Suhaima ta ce
“Ko da ba kya sonsa… at least ya kamata ki saurare shi ko da na minti ɗaya ne.”
Zahra ta ɗan yi dariyar raini
“So… yanzu ni ce na zama mara gaskiya?”
Saudat ta yi saurin girgiza kai
“A’a, ba haka muke nufi ba.”
“Muna nufin… maybe kin ɗan yi saurin yanke hukunci cikin fushi ne.”
Zahra ta jingina bayanta da kujera
“Interesting”
Firdausi ta ci gaba
“Baby, tun ranar farko kina treating him harshly. Amma wallahi har yanzu ban ga ya taɓa yi miki rashin mutunci ba, Ina laifin Wanda yake sonka?”
“Rashin mutunci?” Zahra ta maimaita.
“Riƙe min jaka ba tare da permission ba ba rashin mutunci ba ne?”
Aasiya ta ce cikin nutsuwa
“Da niyyar taimako ya yi, Zahra.”
“Exactly,” Suhaima ta ƙara da cewa
“Babu wani mugun intention a fuskarsa, ba dan zaki tafi bane ya rike ki”
Zahra ta miƙe tsaye
“Toh idan kun gama kare shi… ku je ku nemo shi mana.”
“Maybe one of you should date him”
“Since you all like him so much.”
Firdausi ta miƙe itama
“Baby! This is not funny, muna faɗa miƙe ne saboda muna son ki.”
“Muna son ki dinga giving people a chance kafin ki yanke musu hukunci”
Zahra ta yi murmushi, amma murmushin mai cike da ma’ana
“Oh… really?”
“Toh daga yau ku daina shiga tsakanina da duk wanda ya shafe ni”
“Because it’s my life.”
Saudat ta ce cikin sanyin murya
“Zahra… don’t say that, ai an zama ɗaya”
Ta waiwaya ta kalli Saudat
“Then don’t judge me.”
Falon ya sake yin tsit, ba wanda ya ƙara magana.
Zahra ta ɗauki wayarta daga kan center table, ta juya ta nufi ɗakinsu
Firdausi ta kira sunanta
“Baby…”
Ko waiwayowa ba ta yi ba ta shiga ɗaki, ta rufe ƙofar da ƙarfi
Kaf!
Shiru ya sake mamaye falon.
Firdausi ta zauna tana dafe goshinta
“Mun ɓata mata rai.”
Aasiya ta sauke numfashi.
“Amma dole ne wani ya gaya mata gaskiya.”
Suhaima ta kalli ƙofar ɗakin
“Ban taɓa ganin ta haka ba.”
Saudat kuwa ta yi shiru..
A zuciyarta tana addu’a kawai, ta san Zahra tana da zuciya mai kyau…
Amma kuma ta san idan ta fara yin fushi, tana ɗaukar lokaci kafin ta sauko daga kai….
Tun bayan misunderstanding ɗin da ya faru a falo…
Zahra ba ta sake fitowa ba, ta zauna a ɗaki tana scrolling a wayarta, amma ko ita kanta ta san ba ta maida hankali kan abin da take yi ba.
Can wajen Maghrib, Firdausi ta buga ƙofar
“Baby…”
Shiru…. Ta sake bugawa
“Abinci ya kusa haɗuwa.”
Daga ciki Zahra tayi magana cikin zuciya
“I’m not hungry.”
Firdausi ta tsaya na ɗan lokaci kafin ta ce
“Okay… idan kin canza ra’ayi, ki fito ki ci, dan ko a cafeteria baki ci abinci ba”
Daga haka ta bar bakin kofar
Can bayan magrib
Kitchen ya cika da ƙamshin abincin da Firdausi ta girka.
Kowacce ta zauna a parlon a spot ɗinsa, sai spot din Zahra ce kaɗai babu kowa
Saudat ta kalli wajen
“Ba za ta fito ba?”
Firdausi ta girgiza kai
“Na mata magana… ta ce ba ta jin yunwa.”
Aasiya ta sauke numfashi
“Ta yi fushi sosai.”
Suhaima ta ce
“Mu ba ta lokaci kawai.”
Suka ci abincinsu cikin nutsuwa, ba irin dariyar da aka saba ba
Bayan sun gama…
Zahra ta buɗe ƙofar ɗakin a hankali ta fito bayan ta tabbatar sun gama cin abinci
Ta wuce kitchen ba tare da ta ce wa kowa komai ba, ta buɗe cupboard
Ta ɗauko corn flakes, ta zuba a wani white ceramic bowl
Ta ɗauko chilled milk daga fridge ta zuba a kai.
Ta dawo parlorn ta zauna, ta riƙe spoon ɗin tana ci a hankali
Ba ta kalli kowa ba, suma cikinsu babu wanda ya yi attempting mata magana
Da ta gama… ta wuce kitchen din, ta wanke bowl ɗin da kanta, ta mayar da komai inda ya dace
Sannan ta koma ɗaki
A falo kuwa…
Firdausi, Aasiya, Suhaima da Saudat suna zaune suna hira.
Wani lokaci har su yi dariya
Amma duk lokacin da suka kalli hanyar ɗakin Zahr ko kuma suka tuna da ita
Sai hirar ta yi sanyi.
Firdausi ta ce a hankali
“Wallahi ban saba ganin ta haka ba, Duk abun ya dame ni”
Saudat ta ce
“Ni ma.”
A ɗaki…
Zahra ta kwanta jingine da pillow, ta shiga Instagram.
Notifications nata ba su da ƙidaya. Verified pages, Fans, Friends, Messages.
Ta riƙa replying kaɗan-kaɗan, Can ta buɗe class group nasu na WhatsApp
Nan ta ga wani message pinned
📌 Assignment Due: Tuesday, 8:00 AM.
Ta zaro ido
“Oh shoot…” Ta tuna Ashe an basu assignment
Da sauri ta miƙe ta nufi bakin kofar
Sbd kullum idan akwai assignment, Firdausi ce ke tattara su ta kammala musu kafin kowacce ta yi editing nata
Ta kai hannunta bakin handle din, sai ta tsaya
Ta tuna abin da ya faru da yamma, ta ja hannunta a hankali
“No… it’s okay.”
Ta koma kan gado ta zauna, ta buɗe contact list, ta nemo sunan Class Rep, ta danna call.
Bai daɗe ba ya ɗaga
“Hello, Zahra.”
“Hi.”
“Hope you’re good?”
“Yeah… Alhamdulillah.”
“Actually, I need today’s assignment.” Zahra ta faɗa
“Oh, that’s easy. Ina da soft copy.”
“Send it to me, please.”
Shiru na daƙiƙa biyu ya biyu baya
Sai ya ce cikin wata murya mai nuna alamun ɗan jin daɗi,
“Or…”
“Since you’re Zahra…”
“Just send me your registration number.”
Ta haɗe gira
“My registration number?”
“Yeah.”
“I’ll do the assignment for you.”
“You don’t have to stress yourself.”
Zahra ta ɗan yi shiru sai ta ɗan yi murmushi
“Seriously?”
“Of course.”
“You’re my course mate.”
“And… I’d be happy to help.”
Ta ɗan yi tunani
“Okay… thank you.”
Tana kashe wayan ta tura masa registration number ɗinta ta WhatsApp.
Nan take blue tick ya bayyana, sai ya aiko mata da reply.
“Done. Give me a few minutes.”
Zahra ta jingina da headboard ɗin gadonta, ta ajiye wayar a gefe.
A karo na farko tun bayan faɗar da suka yi… ta ji ɗan sauƙi a ranta….
Daren ya ƙara yin tsit… Bayan kowa ya gama abin da yake yi, ɗaya bayan ɗaya suka fara komawa ɗakin
Aasiya ta ɗauki blanket ɗinta tana miƙewa
“I’m sleepy.”
Suhaima ta yi hamma
“Same here.”
Saudat ta ɗauki hijabinta ta naɗe ta a hankali kafin ta ɗora kan sofa.
Firdausi ta kalli Zahra, wacce har yanzu take jingine da headboard tana danna wayarta.
Ta yi niyyar cewa wani abu sai kuma ta fasa.
“Good night, girls.”
“Good night,” Aasiya, Suhaima da Saudat suka amsa a tare.
Zahra ba ta ɗago kai ba sai dai ta ce cikin sanyin murya,
“Good night.”
Kowacce ta kwanta a wajenta.
Na wasu sakanni… ba wanda ya sake magana
Firdausi ta miƙa hannu ta kashe babban hasken ɗakin.
Sai hasken bedside lamp kaɗai ya rage,
Zahra ta ɗan jima tana kallon ceiling.. sai ta miƙa hannu.
Click.
Bed lamp ɗin ma ya mutu, duhu ya mamaye ɗakin.
Aka fara jin ƙarar AC kawai da numfashin waɗanda bacci ya fara ɗaukarsu.
Duk bacci ya ɗauke su a haka…
The following day…
Ƙarar alarm ta fara tashi da ƙarfe hudu na safe
Firdausi ce ta fara buɗe ido, ta miƙe ta kashe alarm ɗin kafin ya tada sauran mutane
Sai dai kafin ta juya… ta hangi Zahra tuni ta tashi
Tana zaune bakin gadonta, ta riga ta yi alwala, hijabinta a hannunta, tana shirin fita sallar Asuba a masallacin cikin villan
Firdausi ta ɗan yi mamaki
“Baby… kin riga mu tashi?”
Zahra ta ɗan kalleta
“Yeah, Ina shirin tashin ku knn”
Muryarta a sanyaye take, ba kamar kullum ba, ta saka hijabinta
“Na tafi masallaci, a can zanyi sallah Yau”
Ba tare da ta jira amsa ba, ta buɗe ƙofar ɗakin ta fita.
Firdausi ta bita da kallo, ta sauke numfashi
“Maybe… yau za ta sauko daga fushin.”
Sai kuma ta juya Tana kallon masu bacci ta yi saurin tashi
“Girls… wake up.”
Aasiya ta buɗe ido a hankali
“Already? It’s Fajr?”
Suhaima da Saudat ma suka miƙe, kowacce ta ɗauki hijabinta.
Bayan sun yi alwala, suka nufi ƙaramin masallacin da ke cikin School Villa tare suma
Garin ta yi tsit, Iskar safiya na kaɗa bishiyoyin da ke cikin estate.
Ɗalibai kaɗan ne ke tafiya zuwa masallaci
Bayan sun idar da sallah, suka dawo gida.
Zahra ta shiga kitchen ta fara haɗa coffee
Firdausi ta tsaya bakin ƙofa tana kallonta
“Need help?”
Zahra ta ɗan juyo
“No, I’m fine” Ba ta ƙara cewa komai ba bayan haka
Firdausi ta fahimci har yanzu fushin bai gama sauka ba, ta juya ta bar kitchen
Cikin mintuna talatin…
Kowacce ta yi wanka ta shirya
Aasiya da Suhaima suna gaban mirror suna gyara fuskokinsu
Saudat na saka wristwatch ɗin da Zahra ta taɓa ba ta kyauta.
Firdausi ta fito cikin navy blue abaya
“Girls… let’s move.”
Zahra ta ɗauki key ɗin motarta daga kan dining table
“Come on.”
Babu surutu kamar yadda aka saba, suka nufi inda motar take
Zahra ta buɗe motar, kowacce ta shiga
Motar ya yi ƙara bayan ta kunna, ta fita daga School Villa
A hanya…
Morning rush ya fara sbd weekdays ne, Motoci, Napep, Students na tafiya zuwa lectures.
Firdausi ta kunna rediyon motar ganin yadda motar yayi wani shiru
An ɗan yi shiru kafin announcer ya fara gabatar da labaran safe.
Sai kwatsam…
Wayar Zahra da ke haɗe da Bluetooth ta fara ringing.
Screen ɗin motar ya haska
Unknown Number.
Firdausi ta ɗan kalleta
“Again?”
Zahra ta haɗe fuska, ta danna Decline.
Bai wuce daƙiƙu goma ba… Wayar ta sake ringing
Unknown Number.
Aasiya ta ce
“Maybe it’s important.”
“No” Ta sake katse kiran.
Karo na uku… Sai ya sake shigowa
Wannan karon Saudat ta ce cikin nutsuwa
“Baby… try ki ɗaga mana. Wataƙila ba shi ba ne”
Zahra ta sauke numfashi, ta danna Accept tare da saka speaker
“Hello?”
Shiru ne da farkon sai can wata nutsattsiyar murya ta fito
“Good morning, Miss Zahra.”
Ta haɗe gira
“Who’s this?”
“Someone who has been trying to apologize.”
Nan take ta gane muryarsa, shi ne dai, wannan saurayin nan
Ba tare da ta ba shi damar ƙara magana ba… ta katse kiran
Ta kashe Bluetooth gaba ɗaya.. Motar ta sake yin shiru
Firdausi ta ce a hankali,
“Wallahi… wannan guy ɗin bai da sauƙin haƙura”
Zahra ta ci gaba da tuƙi
Fuskarta ba ta nuna komai ba, dan ma is hardly kace akwai abun dake damunta
Amma a cikin zuciyarta… tambaya ɗaya ce kawai ke yawo
‘Ta yaya ya samu number ɗina?’ Ta San numbernta isn’t visible to everyone, a department dinsu ma ba wanda yake da shi
Da suka isa university, parking lot ya riga ya cika da motoci
Zahra ta faka motarta kamar yadda ta saba
Ta ɗauki jakarta, ta fito cikin nutsuwa.
Elegant black abaya ce a jikinta, premium silk veil da matching handbag. Tafiyarta kaɗai na ɗaukar hankali
Idanunta na gaba, bata waiwaya straight to her front take kallo
Suna tafiya zuwa faculty… can nesa kaɗan…
Sai ga wani saurayi, shi ne, sanye cikin light blue shirt da black trousers
Ya tsaya gefen pathway kamar wanda yake jiran wani.
Da ya hango Zahra… Sai ya ɗan gyara tsayuwarsa
Idanunsu suka kusa haɗuwa.. amma… Zahra ko kallonsa ba ta yi ba
Ta wuce a gabansa kamar iska, ba ta nuna ma ta san yana wurin ba.
Shi kuwa… kamar ya biyo ta, amma sai ya kasa biyo bayanta din
Sai kawai ya bita da kallo, wani ƙaramin murmushi mai cike da haƙuri ya bayyana a fuskars, ya juya ya nufi wani building daban
Da suka shiga lecture hall, lecturer bai iso ba tukuna.
Students na ta hira, wasu na duba notes, wasu kuma na ta dariya
Su biyar suka zauna a baya
Firdausi ta fara buɗe notebook ɗinta, Aasiya na duba assignment.
Sai Suhaima ta juya ta kalli Zahra
“I’m sorry to say this…”
Zahra ta ɗago kai
“What?”
“Please… ki saurare shi ko sau ɗaya.”
Zahra ta haɗe gira
“Excuse me?”
Suhaima ta ɗan yi murmushi
“Besides… guy ɗin kyakkyawa ne.”
Firdausi ta yi shiru tana jiran amsar Zahra. Aasiya ta ɗan sosa kai
Saudat kuma ta sunkuyar da kai.
Zahra ta yi wata ƙaramar dariya ta raini
“Ina ruwa na da kyawunsa?”
Ta jingina da kujerarta
“Kyau ɗin nasa za mu ci idan ya aure ni?”
Suhaima ta yi saurin cewa
“Ba haka nake nufi ba…”
“A’a, bari na gama.”
Zahra ta ɗan gyara zamanta.
“Ban san me yasa kike magana haka ba, Suhaima.”
“Lemme tell you something.”
“I’m not his mate… by all means.”
“Tsaurin ido ne ma da shi har ya zo ya tare ni yana cewa yana sona.”
Ta ɗan yi shiru kafin ta ci gaba.
“Baya ganin ko manyan influencers da celebrities da suke flooding my DMs ban ba su kulawa ba?”
“Me ya sa yake tunanin shi zai zo kawai ya tsaya gabana, then I’ll suddenly fall for him?”
Firdausi ta kalli Zahra
“Baby… love isn’t about status.”
Zahra ta ɗaga hannu
“Please… not again.”
“Ni bana son wannan discussion.”
A dai-dai lokacin… Lecturer ya shigo, duk hirar ta tsaya
Amma Suhaima ta ci gaba da kallon Zahra cikin tausayi, a zuciyarta tana jin cewa…
Ba girman kai ba ne ke hana Zahra sauraron saurayin.
Akwai wani abu da Zahra ke ɓoyewa, wanda har yanzu babu wanda ya fahimta.