Chapter 33
Farashin Izzah Part 1 Complete Hausa Novel · about 12 min read
Da yamma kamar yadda ya yi mata alƙawari, Ya Umar ya dawo gida ɗauke da wani babban carton.
Tun da Zahra ta hango shi daga parlon ƙasa, ta miƙe da gudu ta tarbe shi.
"Yaya!" Ta kira tana dariya
Ya ɗaga carton ɗin yana kallonta.
"Me kika ce kina so ma?"
Idanunta ta zaro tana masa murmushi ta ce
"Kana nufin...?"
Ya miƙa mata carton ɗin
"Open it."
Da sauri ta karɓa. Ko zama ba ta yi ba, a tsaye ta fara buɗe carton ɗin.
Da ta hango sabon system ɗin a ciki, sai ta kwalla ihu.
"Oh my God!" Ta faɗa tana rufe bakinta da hannu.
A gigice ta kalli Ya Umar kamar zata yi kuka ta ce
"Yaya... thank you!"
Ba tare da ta jira komai ba, ta rungume shi da ƙarfi kamar zata yar dasu
Ya yi dariya yana shafa kanta.
"Congratulations."
Da gudu ta juya tana nuna wa Mama ladi mai aikin gidan.
"Mama! Ki zo ki gani!"
Mama ladi ta ƙaraso tana murmushi.
"Masha Allah Hajiya karama, Allah ya ƙara hazaka da ilimi mai amfani ."
Sauran ma'aikatan gidan ma suka taru.
Kowa na taya ta murna.
"Masha Allah Babyn Abbanta”
Daga nan ta nufi Mami dake sauko wa daga stairs, tana karasa sauka ta mika mata
"Mami, duba mana! Yanzu Yaya yazo min da shi”
Mami ta karɓa tana dubawa, ta yi murmushi
"Masha Allah. Allah ya saka masa da alheri."
Batoul dake zaune tun dazu ta haɗe fuska, sai kuma ta mike kai tsaye ta juya ta haura sama.
Tana shiga ɗakin Mummy ta ganta tana waya, Mummy kuma ganinta yasa ta sauke wayen daga kunnenta ta kashe
"Mummy! Ya saya mata." Ta ce tana hade fuska
Mummy da rashin fahimta ta ce
"Wane abu?"
"System mana."
Da sauri ta miƙe tsaye, ba tare da ta ce komai ba ta fita daga ɗankinta ta sauka ƙasa
Har lokacin Zahra na ta murna tana kallon system ɗin, Mami kuma already ta koma sama
Sai kawai ta ji...
Paf!!! Mari ya sauka a kumatunta.
System ɗin ma ya kusan faɗuwa daga hannunta. Ta dafe kumatunta cikin razana
"Mummy..." Ta kira da ƙyar
Mummy ta ƙwace system ɗin daga hannunta.
"Wai ke me kike ɗaukar kanki ne?” Ta faɗa cikin tsawa
"Batoul na university, ba a taɓa saya mata irin wannan ba. Sai ke!"
Zahra ta haɗiye hawaye.
"Ai... Batoul bata taɓa tambayar Abbah ko Ya Umar su saya mata ba."
"Stupid!" Mummy ta katse ta.
"Ki yi min shiru!" Ta sake wanke ta da wani mari.
Nan take Zahra ta zauna a ƙasa dabas ta fashe da kuka sosai
A dai-dai wannan lokacin Ya Umar ya shigo parlon da sauri idanunsa suka sauka kan Zahra dake kuka sai kuma kalli Mummy.
"Mummy..." Bai ƙarasa magana ba ta katse shi
"Eh, ni ce na mare ta." Ta faɗa tana kallonsa ido cikin ido.
"Ka zo ka rama mata mana” Parlon ya yi tsit, Mama ladi ta juya tsum tsum ta koma kitchen
Ya Umar ya kalli Zahra da idanunta suka kumbura saboda kuka sai kuma ya sauke idanunsa kasa
A hankali ya ce,
"Mummy... kiyi hakuri"
Ya ƙarasa ya ɗaga system ɗin daga inda ta jefar da shi.
Ya miƙa wa Zahra. "Ki je ɗaki."
Da ƙyar ta karɓa.
Ba tare da ta kalli kowa ba, ta juya ta haura sama tana kuka.
Kai tsaye ta shiga ɗakin Mami. Tana shiga Mami ta ganta cikin wannan hali, ta miƙe da sauri.
"Lafiya?" Zahra ta faɗa jikinta tana kuka.
Nan da nan ta ba ta labarin abin da ya faru. Mami ta yi shiru tana saurarenta har ta gama.
Sai ta ɗago fuskarta.
"Maganinki ba ke ce kike yarda da duk abin da take faɗa miki ba?"
Zahra ta yi shiru.
"Ba har kin manta irin abubuwan da take miki a baya ba?"
Ɓata fuska tayi tana kallon wani wajen
Mami ta ci gaba.
"Shi har wani lokacin kike daukar kafarki ki tafi part din can ba, sau nawa nake miki iya ka? Alhali ba ta taɓa son ganin ci gabanki ba”
Ta dafa kafaɗar Zahra "Ki saurare ni da kyau."
"Daga yau... Idan na sake ganin kin je side ɗinsu ko kina sauraren shawaran da take Baki…wallahi zan ɓata miki rai."
Zahra ta share hawayenta.
A hankali ta gyada kai
"Toh Mami."
Mami ta rungume ta tana shafa bayanta.
"Ke dai ki ci gaba da zama yadda kike. Allah yana tare da masu zuciya mai kyau."
Abbah na shigiwa sai ya nufi ɓangaren Mami
Yana tura ƙofar ya shiga, ya tarar da Mami zaune gefen gado, yayin da Zahra ke manne da ita, idanunta duk sun kumbura saboda kuka.
Da fara'a ya shigo kamar yadda ya saba. Sai dai da zarar idanunsa suka sauka kan fuskar Zahra...
Murmushin da ke kan fuskarsa yayi fading lokaci guda.
Ya tsaya cak yana kallon alamun yatsun hannu da suka bayyana a kumatunta. Idanunta kuwa sun yi jajur saboda yawan kuka.
A hankali ya ƙaraso gabanta. Ya ɗaga haɓarta da hannunsa.
"Baby..." Ya kira cikin sanyin murya.
"Wa ya buge ki?"
Zahra ta sauke kanta ƙasa.
"Mummy ce..." Ta faɗa da ƙyar.
Ya haɗe gira, sabar yadda yaji zuciyarsa na tafasa
"What!? Saboda me?"
Ta haɗiye wani sabon kukan da ya taho mata.
"Saboda Ya Umar ya saya min system."
Shiru ya ratsa ɗakin.
Abbah ya sake kallon fuskar Zahra. Daga nan ya juya ya kalli Mami.
Mami ta san daga yanayin fuskarsa cewa ya fusata matuƙa.
Bai ce komai ba
Ya juya kawai ya fita
Kai tsaye ya nufi ɓangaren Mummy, bai ko yi knocking ba, ya tura ƙofar ya shiga
Mummy na zaune tare da Batoul.
Da ganinsa ta ɗan gyara zamanta.
"Alhaji..."
Bai bari ta ƙarasa ba.
"Hafsat!"Ya kira sunanta cikin tsawa
Ta ɗan razana.
"Meye haka?"
Ya nuna mata yatsa
"Wa ya ba ki ikon ɗaga hannu ki mari 'yata?"
Ta haɗe gira.
"Toh masu ‘ya Wanda ba’a taba musu ita, toh bata da kunya ne shine nake son gyarata?
“Ina tambayan ki wa ya ba ki wannan ikon? No matter what Baki da right akanta”
Ta ɗan yi dariyar raini.
"'Yarka?… Ai Batoul kuma ba 'yarka ba ko? Toh ya kamata ka sani Batoul ce ta cancanci a saya wa abu, ba Zahra ba, tunda Tana gaba da ita”
Abbah ya katse ta da ƙarfi
"Ya isa!" Muryarsa ta amsa cikin ɗakin.
"Ko nawa Umar ya kashe a kan Zahra, ba ruwanki… Kuɗinsa ne…. ‘Yar uwarsa ce. Idan yana so ya saya mata mota ma, ba ki da hurumin hana shi."
Ta taso tsaye.
"Toh ni kuma Uwarsa Nace bai isa ba…. ace bai taba wa Batoul haka ba sai wata can, ni kuma ba zan lamunta ba tunda Kai da kake Uba ma ko sanin bukatunta Baka yi balle ka sauke”
Abbah ya kalleta da wani irin kallo.
"Saboda Batoul ba ta taɓa kallona ba a matsayin Uba ba, balle ta tambaye ni abu, kuma ko ta nema... ba ke ce kike hana ta ba”
Ta ɗan matsa kusa da shi.
"Saboda Zahra ne kake min ihu kamar zaka tashe gidan nan da magana?”
Ya sauke numfashi
"Hafsat..."
Ya faɗa cikin murya mai cike da gargaɗi
"Ki ji da kyau. Daga yau..."
"Kar ki sake ɗaga hannu ki mari min Zahra. Ba ki da wannan right ɗin, Idan ta yi laifi, ni ne mahaifinta, nine zan mata magana. Ko Khadija da ta haife ta, ba ta taɓa marin yarinyar ba. Ballantana ke.
Mummy ta buɗe baki tana kallonsa cike da mugun mamaki
Kafin ta samu damar cewa komai, ya ci gaba.
"Kuma idan akwai abin da bai yi miki ba, ki zo ki same ni. Ba zan taɓa yarda kina sauke fushinki a kan yarinya ba."
Ya juya zai fita
Sai ta yi saurin cewa,
"Alhaji!"
Bai waiwaya ba.
"Kada ki kuskura ki sake taba min ‘ya"
Shi kaɗai ya faɗa.
Daga nan ya buɗe ƙofar ya fita
Mummy ta tsaya a wurin bakin a buɗe
Har Batoul da ke gefenta, kasa cewa komai ta yi
Mummy ta tsaya tana kallon ƙofar da ya fita, fuskarta dai har sannan cike take da mamaki
Batoul ta taɓe baki tana girgiza kai.
"Tabdijam!" Ta faɗa cikin takaici
"Wato saboda an taɓo 'yar goal din nan ne, sai ya shigo yana ta bambami babu kakkautawa." Ta ƙarasa zama bakin gado.
"Wallahi Mummy, ni ban taɓa ganin irin son da yake wa Zahra ba. Kamar ba mu ba ne 'ya'yansa, Anya haka aka barsa kuwa?”
Mummy ta yi shiru na ɗan lokaci.
Sai kuma wani mugun murmushi ya bayyana a gefen bakinta. Ta yi wata 'yar dariya a hankali
"Hmm..." Ta furta.
"Sannu a hankali."
Batoul ta kalleta.
"Mummy what...?"
Ta ɗaga kanta tana kallon Batoul
"Na ce ki kwantar da hankalinki kawai”
Ta faɗa cikin kwantar mata da murya.
"Zan yi maganin shegu."
Batoul ta yi murmushi.
"Da gaske?"
Mummy ta gyara zamanta.
"Eh."
"Wai kina ganin zan zuba ido ina kallon yadda kullum ake ɗora Zahra a kan gaba ne, bar ke da kike babba?"
Batoul ta girgiza kai.
"A'a."
Mummy ta ci gaba.
"Ki bar komai a hannuna.Lokaci bai yi ba ne kawai."
"Amma zan tabbatar na sauke ta daga wannan matsayin da take ganin ta kai."
Batoul ta fara murmushi cike da jin daɗi.
"Na san Mummy ba za ki taɓa bari ta fi ni ba."
Mummy ta shafa kanta.
"Ke ce kawai nake gani naji dadi. Ba zan taɓa bari wani ya zo ya karɓe miki matsayinki ba”
Batoul ta jingina da ita tana murmushi.
A zuciyarta kuwa... ta ji kamar ta samu nutsuwa, domin ta san mahaifiyarta ba za ta taɓa bari Zahra ta rayu cikin kwanciyar hankali ba.
Washegari tun da sassafe Zahra ta shirya cikin tsaftatacciyar uniform ɗinta. White shirt ɗinta ta shiga jikinta fes, black skirt ɗinta kuwa ya ƙara fito da tsayinta, yayin da ta ɗaure gashinta cikin ponytail mai kyau
Da schoolbag ɗinta a hannu ta sauko ƙasa.
A dining ta tarar da Abbah, Mami da Ya Umar, Mummy da Batoul suna jiran ta
"Good morning my loves” Ta faɗa tana murmushi.
"Morning, Baby” Abbah ya amsa yana nuna mata kujera.
Ta zauna suka fara breakfast cikin nishaɗi, sai dai Mummy da Batoul ko kallonta ba su yi ba
Bayan sun gama, ta fita tare da Abbah
Driver ya buɗe musu motar.
Ya Umar ya kalli Abbah.
"Abbah, bari ni na sauke ta."
Abbah ya girgiza kai.
"No."
Ya buɗe ƙofar motar.
"Today she's going with me."
Ya Umar ya yi murmushi kawai.
"Alright, Abbah."
Cikin ƴan mintuna suka isa makarantar.
Da motar ta tsaya a harabar makarantar, Zahra ta juya tana kallon Abbah.
"Thank you, Abbah."
Ya yi murmushi.
"Study well."
"In sha Allah."
Ta sauko daga motar.
Data shiga harabar makarantar, ɗalibai da dama sai kallonta suke yi, wasu kuwa sai mirmushi suke maga
Ita ma cikin mutuntawa take mayar musu ɗaya bayan ɗaya.
Da ta isa ajinsu, ta tarar da Asiya, Firdausi da Saudat sun riga sun zo.
Bayan sun gaisa, morning class suka fara.
Da misalin ƙarfe goma sha ɗaya, wani teacher ne ya shigo ajin bayan sun dawo daga break
Bayan ya amsa gaisuwar su, ya ce,
"I have an important announcement."
Nan take ajin ya yi shiru.
"An buɗe registration na WAEC."
Ya ci gaba.
"Duk wanda yake son yayi jumping or yake son making trial toh yazo ya magana cos za’a fara registration ne daga yau."
Sannan ya yi musu cikakken bayani kan ranar rufewa, kuɗin registration da kuma abubuwan da ake buƙata. Bayan ya gama, ya fita.
Lokacin second break ya yi
Su Zahra suka nufi wani wajen zama a harabar makarantar.
Firdausi ta fara magana.
"Ni kam zanyi a SS2, idan na gama secondary kuma ‘Kasu’ zan tafi”
Suhaima, wacce mahaifinta mai hali ne, ta yi murmushi.
"Ni ma NILE zan yi."
Saudat kuwa ta sauke kanta.
"Ni kam... Allah ne kawai ya Sani, amma bana jin zan cigaba” Ta faɗa cikin sanyin murya.
"Ko wannan karatun da nake yi yanzu ma iyayena dakyar suke iya sponsoring PTA Dina” Tayi shiru
Zahra ta kalleta da tausayi, Firdausi ta ce “ke fah zahra”
Ta ɗan yi murmushi
"Sai na tambayi Abbah."
Asiya ta yi dariya.
"Yar Abbah."
Duk suka yi dariya.
Firdausi ta ce,
"Ai Zahra, ke ba ki da matsala. Duk inda kika ce kina so, nan za a kai ki."
Zahra ta yi murmushi.
"Ina ji ni ma... maybe KASU zan taho tare da ku, bana son bond din nan ya rabu”
Firdausi tace
"Wallahi fah, ko Duk mu tafi ABU zaria please”
Da haka break ya ƙare.
Suka koma aji domin ci gaba da karatu
Bayan wasu awanni aka tashi.
Yau Ya Umar ne ya zo ɗaukar Zahra.
Tana shiga mota ta gaishe sa
Ya amsa yana tayar da motar.
Suna cikin tafiya ne, idanun Zahra suka sauka kan wani babban eatery.
Da sauri ta juya tana kallon Ya Umar.
"Yaya..."
"Na'am?"
"Please ka tsaya."
Ba tare da ya tambayi dalili ba, ya rage gudun motar.
Sannan ya yi parking a gefen eatery ɗin.
Ya Umar ya juya yana kallonta.
Daidai lokacin Zahra ta marairaice fuska kamar wata ƙarama, tana turo baki gaba.
Sai ta ɗaga hannunta tana nuna wani babban eatery da ke gefen titi din
"Please, Yaya..."
Ta kira cikin shagwaɓa.
Ya ɗaga gira.
"Na'am?"
Ta yi murmushi.
"Ka siya min ice cream da shawarma."
Ya ɗan kalleta na wasu daƙiƙu sannan ya yi murmushi.
"Da kuma me?"
Ta girgiza kai da sauri.
"That's all."
Ya gyada kai yana dariya.
"Consider it done."
Ya kashe motar, ya buɗe ƙofa sannan ya sauka.
Kai tsaye ya shiga eatery ɗin.
Bayan ɗan lokaci ya fito ɗauke da leda mai ɗauke da shawarma da ice cream.
Ya buɗe ƙofar motar ya miƙa mata.
"Thank you, Yaya."
Ta faɗa tana wani irin murmushi mai nuna farin ciki.
Ya girgiza kai kawai, ya koma mazauninsa, ya tada motar suka ci gaba da tafiya.
Bayan sun isa gida, mai gadi ya buɗe musu gate suka shiga.
Ta fito daga motar, Zahra na rungume da ledar hannunta tamkar wani zai kwace mata.
Ta shiga parlon tana murmushi.
Mami na zaune tana duba wasu takardu, Abbah kuma yana zaune kusa da ita.
Da ta ganta, Mami ta ce,
"Zahra, je ki cire uniform ɗinki, ki yi wanka sannan ki zo ki ci abinci, sabon mu’allim dinki na hanya”
Zahra ta yi dariya tana girgiza kai.
"Mami, count me out."
Ta ɗaga ledar hannunta.
"Yaya ya saya min shawarma da ice cream."
Mami ta ɗago ta kalli Ya Umar da shigowarsa kenan.
Ta girgiza kai tana murmushi.
"Ya Umar, ka ci gaba da biyewa Zahra haka. Zata ƙarasar maka da kuɗi."
Ya Umar ya zauna yana dariya.
"Ai kuɗina nata ne."
"Na ta kuma nata ne."
Sai ya ɗan dakata yana kallon Mami da wasa.
"Shi ya sa ma ko na yi aure..zan ɗauke ta mu tafi tare."
Zahra ta kwashe da dariya.
Ta juya ta yi wa Mami gwalo.
"Kinga ko!"
Mami ta nuna ta da yatsa.
"Ke! Zo nan."
Amma kafin ta ƙarasa maganar, Zahra ta juya da gudu tana dariya, ta nufi matakala.
Ya Umar ya bi bayanta da kallo, ya fashe da dariya.
Abbah ya girgiza kai yana murmushi.
"Ku biyu kam... Allah kaɗai ya san ranar da za ku daina wannan shirmen. Ko ganina ma bata yi ba”
Murmushi kawai Ya Umar yayi
Abbah ya ce
“Allah muku albarka ya raya min ku”