Chapter 30
Farashin Izzah Part 1 Complete Hausa Novel · about 11 min read
Bayan sun idar da sallar Magrib... Zahra da Ya Umar suna zaune a parlorn sama. A karo na farko cikin kwanaki masu yawa, ana iya ganin ɗan walwala a fuskar Zahra thought ba sosai ba, amma ya fi na baya
Ya Umar kuwa yana zaune a kujera kusa da ita, yana bata labarin abin da ya faru da lawyers ɗin da suka haɗu da Abbah
"Da farko ma suna mamakin yadda case ɗin ya yi ƙarfi, dan sunci sai ya yarda tukun court zasu raba auren" Ya faɗa
"Da suka ga medical reports da sauran evidence ɗin da aka tattara sai suka ce komai zai yi sauƙi."
Zahra ta yi shiru tana saurarensa ta ce
"Ai yanzu kam Ya Umar ko bai yarda ba idan kotu ta sake ni ai shikenan, sai ya cigaba da halinsa"
Kai Ya Umar ya gyada sai kuma ya ci gaba
"Abbah ma ya jikasu da kudi sosai, ya ce baya son wani kuskure ko kaɗan."
A hankali Zahra ta ce,
"Allah ya saka masa da alheri, Kai ma Ya Umar Allah biya ka, thank you"
"Amin, Zahratyy" Ya Umar ya amsa
Har zai sake magana ne wayarsa ta fara ringing, ya duba screen ɗin, sai ya miƙe tsaye
"Bari na ɗauki wannan call ɗin."
"Okay." Zahra ta amsa
Daga haka ya fita zuwa balcony, Ita kuma ta janyo wayarta.
Ta shiga wani game tana bugawa a hankali, gaba daya hankalinka yana kai kawai, kawai taji an bude kofar parlon
Batoul ce ta shigo, da ganin Zahra sai ta tsaya, sannan ta saki wata dariya
"Toh..." Ta faɗa tana girgiza kai.
"Ashe ƙarshen alewa ƙasa ne fah"
Zahra ta ɗan ɗago kai
Sai kuma ta mayar da hankalinta kan wayarta tamkar ma ba ta ji abin da Batoul ta ce ba.
Batoul ta sake dariya.
Amma da ta ga Zahra ko kallonta ba ta yi ba, sai ta zauna tana latsa wayarta ita ma
A daidai lokacin Ya Umar ya dawo ciki, da ya ga Batoul sai ya haɗe gira, amma bai ce komai ba.
Zahra ce ta miƙe
"Yaya bari na koma sama" Ta faɗa
Ya Umar ya kalleta "Kin fasa hirar kenan?"
Zahra ta yi dariya
"Ai mun gama magana Yaya"
Ta kalli Batoul,
"Hira kuma sai anjima ko gobe Yaya"
Ya Umar ya gyada kai.
"Alright, Baby"
Daga haka Zahra ta wuce sama, shima Ya Umar ya sake fita bayan ɗan lokaci.
Ba tare da ya ƙara kallon inda Batoul take ba
Can bayan isha'i
Lokacin dinner ya yi, kowa ya taru a dining area
Abbah, Mami, Mummy, Ya Umar, Batoul, da kuma Zahra
Da suka iso dining ɗin duk kusan lokaci guda suka iso, Abbah ya lura Zahra tana neman kujerar da zata zauna
Kai tsaye ya miƙe, ya janyo mata kujera da kansa
"Zauna nan Baby" Ya faɗa cikin kulawa
Zahra ta yi murmushi
"Thank you Abbah naa" Ta zauna
Abbah kuma ya ɗauki serving spoon, da kansa ya fara zuba mata abinci
"Kici sosai fah" Ya faɗa
"Likita ya ce kina buƙatar ƙarfi."
Mummy ta yi wata yar ƙaramar tsaki, ta kau da kai
Abbah ya ji amma bai nuna ba
Batoul kuwa... Ko kallon inda suke ba ta yi ,tamkar babu wanda ya dame ta a wajen, ta ci gaba da cin abincinta
Mami dai tana kallon Zahra lokaci zuwa lokaci, tana son tabbatar da cewa tana ci.
Ya Umar kuma lokaci-lokaci sai yana saka mata ruwa ko yana tambayarta ko tana buƙatar wani abu, Mummy sai wani kallo take masa Duk lokacin daya hakan,
Zahra na jin wani abu da ta daɗe bata ji ba, jin cewa tana cikin mutanen da suke ƙaunarta...
Yau ya Kama ranar zaman kotu na farko...
Tun da sassafe gidan Abbah suka fara shiri
Zahra gaba daya jikinta ya gama sanyiz, kana ganinta kasan tana cikin tension,
Mami ce ta shiga ɗakinta, ta same ta zaune gaban mirror tana kallon kanta
Ba kwalliya sosai ta yi ba, wani simple black abaya ne a jikinta da veil dinsa tayi rolling kanta
Mami ta ƙaraso ta tsaya bayanta.
"Kina lafiya?" Ta tambaya
Zahra ta gyada kai.
"Alhamdulillah, Mami"
Mami ta gyara mata gefen veil din ta ce
"Ki kwantar da hankalinki Baby, komai zai zo ya wuce, ko yaki ko yaso dole ya baki takardanki Yau"
Zahra ta yi murmushi, amma a zuciyarta wani irin bugun zuciya take ji, ba ta taɓa shiga kotu ba a rayuwarta
A parlorn kuwa
Abbah, Ya Umar da lawyers suna ta ƙare wasu bayanai na ƙarshe.
Ɗaya daga cikin lawyers ɗin ya riƙe file, cike da documents, medical reports, Hospital records, Photographs, da sauran takardun da za a gabatar
Da Zahra ta sauko, kowa ya tsaya yana kallonta, ba karamin kyau tayi ba
Abbah ya miƙe, ya ƙarasa kusa da ita
"Ready?"Ya tambaya
Ta gyada kai "In sha Allah."
Sai ya dafa kafaɗarta.
"Karki ji tsoro, muna tare da ke...."
Karfe tara da rabi suka isa harabar Kaduna High Court
Tun daga parking area ana ganin mutane na kai-komo
Lauyoyi sanye da bakaken suits, wasu sanye da wigs
Ga masu kallo, da iyalan waɗanda suke da ƙara
Zahra ta fito daga motar a hankali, ta kalli ginin kotun
Wani irin yanayi ne ya rufe mata zuciya
Ya Umar ne ta kamo hannunta
"Hey." Ya faɗa.
"Don't panic."
Zahra ta yi murmushi kaɗan, sai suka shiga
A gefe guda kuma.
Ibrahim ya iso tare da Mama.
Tun daga parking area Mama take ta magana.
"Karka yarda da komai, ka tsaya da ƙafafunka, wannan ai matsalar gida ce, ba ta kai ace na kotu bane, zaku sasanta kan ku"
Ibrahim bai ce komai ba, fuskarsa babu walwala
Da suka shiga corridor ɗin kotu, Idanunsu suka haɗu da na Zahra
Zahra ta kau da kai da sauri
Ibrahim kuma ya tsaya yana kallonta da mamaki, ido ya zuba mata na wasu dakiku
Sai Mama ta ja hannunsa.
"Mu wuce ciki"
Da misalin goma na safe.... Aka kira shari'ar
Kowa ya shiga. Zahra na zaune a layin gaba tare da lawyers ɗinta.
A bayanta Abbah, Mami, Ya Umar da da Anty Jiddah.
A ɗaya ɓangaren kuma Ibrahim da Mama.
Alkali ya shigo, kowa ya miƙe, sai da ya zauna sannan aka zauna
Bayan an gabatar da bayanan shari'ar.
Lawyer ɗin Zahra ya miƙe.
"My Lord..." Ya fara.
Sannan ya gabatar da buƙatar warware auren.
Ya bayyana cewa wanda ake ƙara ya aikata abubuwan da suka haddasa mummunan rauni ga matar nasa.
Da farko Ibrahim ya zauna cikin kwanciyar hankali, sai dai lokacin da aka fara gabatar da hujjoji, hankalinsa ya fara tashi sosai
Likitan da ya kula da Zahra ya bayyana sakamakon binciken da aka yi
Shi kuwa ya bayyana irin raunin da aka samu a jikinta, da yadda aka kaita asibiti cikin matsanancin hali
Lawyer ya miƙa takardun ga kotu.
Alkali ya duba, sannan ya yi wasu tambayoyi
Likitan ya amsa.
Bayan haka aka gabatar da wani report, aa biyu.
A wannan karon, dukan daya mata tana da cikin , gaba ɗayan kotun ta yi shiru
Mama ta kalli Ibrahim da sauri. Ibrahim kuma ya ɗago kai, kamar wanda bai gama fahimta ba, Likitan ya ci gaba da bayani
"The patient suffered a..." Zahra ta runtse idanuwanta.
Mami ta kamo hannunta
Lawyer ɗin Zahra ya ci gaba.
Ya bayyana yadda aka kai ta asibiti., yadda aka yi mata treating din internal injuries, da yadda rayuwarta ta shiga haɗari, sai ya juya ya nuna Ibrahim.
"My Lord."
"Muna da hujjoji da shaidu da ke nuna cewa abin da ya jawo wannan kwanciyarta a asibiti shi ne harin da wanda ake ƙara ya kai mata."
Nan kotun ta sake yin shiru.
Mama ta kasa haƙuri, ta miƙe tsaye
"My Lord!" Ta faɗa
"Duk ma'aurata suna samun matsala! Ba wai dan sun yi faɗa ba sai ace za'a raba su...."
Alkali ya dakatar da ita.
"Madam" Ya faɗa cikin tsauri
"Zauna."
Mama taki zama tana kallonsa, sai da ta ga yadda mutane ke kallonta kafin ta zauna tana gunaguni
Bayan kusan sa'o'i biyu ana gabatar da hujjoji da bayanai, Alkali ya yi shiru yana duba takardun da ke gabans
Kowa ya zuba masa ido.
Zahra kuwa bugun zuciyarta take ji yana karuwa tsoronta kar ace za'a bawa Ibrahim dama
Sai ya ɗago kai, ya fara karanta hukuncinsa ya ce
"Kotun ta amince da buƙatar warware auren, an rushe auren tsakanin Zahra da Ibrahim!!! Saboda hujjojin da aka gabatar sun nuna cewa zaman auren mai cutarwa ya haramta a tsakaninsu"
Nan take hawaye suka cika idanun Mami, Abbah ya sauke numfashi
Ya Umar kuma ya lumshe idanuwansa na wasu dakiku
"Sai dai ba nan hukuncin ya tsaya ba." Alkalin ya ci gaba.
"Saboda raunin da aka tabbatar an haddasa. Kotun ta umarci Ibrahim ya biya diyya da tara kamar yadda doka ta tanada"
Mama ta zaro ido.
"A'a!" Ta faɗa
"Wannan bai kamata ba! Ai kamar zalunci ne, mutum na son matarsa itama haka kuma a raba su?"
Amma babu wanda ya kula ta, cos an riga an yanke hukunci
Da aka tashi daga case din, Mutane suka fara fita
Zahra na tsaye kusa da Ya Umar tana Jin kamar an sauke mata wani nawi ne daga zuciyarta
Sai Ibrahim ya ƙaraso wajenta, ya kalleta, aai ya yi wata yar dariya
"Ai baki san me ba." Ya faɗa
"Ba wai sonki nake yi ba Zahra, abin da nake so shi ne in zama famous, sai kuma ki haifa min kyakkyawan baby like you, that's all, amma me zanyi da mace kamar ki?"
Sai ya ɗaga kafaɗa.
"Yanzu try as much as possible ki raina min ciki, ki kuma haifa min tare da shayar da shi, daga nan kuma na zo na karbe kaya na"
A hankali Zahra ta ɗago kai ta kalle shi a Karo na farko na wasu dakiku ba tare da tace komai ba
Sai kawai wani murmushi ya bayyana a gefen bakinta, murmushin da ya sa Ibrahim ya haɗe gira
Domin bai san cewa cikin da yake magana a kai... ya riga ya zube ba, hamdala tayi a ranta, cos da farko har taji haushin doctor Akan rashin rasa babynta da tayi amma yanzu tayi farin ciki sabod kalamansa
Zahra ta juya, ta kama hannun Ya Umar
Suka ci gaba da tafiya, ba tare da ta waiwayo ba
Yayin da Ibrahim ya tsaya a wajen.
Karo na farko yana jin kamar yayi kuskure dan bai so haka daga gareta ba...
Da suka kama hanyar gida daga kotu kowa ya yi shiru a cikin motar.
Da suka isa gida kuwa, Mami ta tafi sashenta domin ta yi sallah ta huta. Ya Umar ya fita ya amsa wasu kiran waya daga lawyers, yayin da Zahra ta nufi ɗakinta.
Tana cire veil ɗinta ne sai gashi ana sallama, Farida ce ta shigo
"Abbah yana kiranki a parlonsa."
A hankali ta gyara mayafinta ta fito, ta nufi parlon Abbah.
Ta same shi zaune a kujerarsa da Qur'ani a gabansa. Da ta shiga ta durƙusa.
"Abbah" ta gaishe shi
Ya amsa cikin tausasawa.
"Sannu Zahra."
Ta ce, "Yauwa Abbah."
Sai ya nuna mata kujerar da ke kusa da shi
"Zauna." Ta zauna.
Na wasu dakiku babu wanda ya yi magana.
Abbah ya kalleta, Idanunsa cike da tausayi.
"Kin ji sauƙi a ranki?" Ya tambaya.
Zahra ta yi shiru na ɗan lokaci.
Sai ta ce, "Alhamdulillah, naji Abbah"
Ya gyada kai "Madalla."
Sai ya ɗan matso gaba
"Ki saurare ni da kyau Zahra."
Nan take ta mai da hankali.
Abbah ya ce,
"Rayuwa tana da jarrabawa iri-iri. Wani lokacin Allah yana ba mutum abin da yake so, wani lokacin kuma yana hana shi abin da yake so saboda alheri"
Ta sunkuyar da kai.
Ya ci gaba.
"Abin da ya faru yau ba ƙarshen rayuwarki ba ne Fatima, ba kuma yana nufin kin gaza ba, kada ki bari mutane ko maganganunsu su sa ki ji kamar wani abu ya ragu a gare ki"
Hawaye suka cika idanunta.
Abbah ya ci gaba.
"Ke ɗiyata ce Zahra, kuma wallahi babu ranar da zan yi nadamar kasancewarki ɗiyata, kina da tarbiyya, kina da ilimi, kina da iyaye da suke sonki, saboda haka kada ki bari abin da ya faru ya karya ki Baby"
Hawayen da take ƙoƙarin dannewa suka fara zubo mata
Abbah ya ɗan yi murmushi.
"Ki yi kuka idan kina son yi, amma kada ki zauna cikin baƙin ciki, duk abin da Allah ya ƙaddara yana ɗauke da hikima"
Sai ya ɗan yi shiru, sannan ya ce,
"Akwai wani abu kuma da nake so ki sani"
Ta ɗago kai ta dan kalle sa
Ya ce,
"Yanzu da kotu ta warware auren, kin shiga iddah"
Ta gyada kai a hankali.
Ya ci gaba
"Ki ɗauki wannan lokaci a matsayin lokacin kusanci da Allah, ki ƙara ibada. Abin da ya rage miki shi ne ki kula da kanki da kuma lafiyarki, Allah baki miji Nagari da kuma dangin miji Nagari"
Zahra ta share hawayenta.
"Toh Abbah, Ameen Nagode"
Ya gyada kai.
"Allah ya miki albarka."
"Amin, Abbah na" Ta amsa.
Nan take Zahra ta sake fashewa da kuka. Ta matsa kusa da Abbah
Shi kuma ya rungume ta kamar lokacin da take ƙarama, yana shafa kanta a hankali har sai da kukan nata ya lafa
Zaune yake Kansa a kasa yana saurarn matsifar da take yi, inda take shiga ba tanan take fita ba, Kai ya dago ya kalleta sannan ya ce
"Nima ban san haka abun zai kasance ba"
Ba tare da ta damu da abun da zai fadi ba tace
"Dalla kamin shiru, ka bata komai, kwata kwata ba haka na so ba, yanzu ai ka huta" sai kuma ya kalleta ya ce
"Akwai wani changes a zuciya ta, na kuma rasa na menene, Allah yasa ba wai na kamu bane"
Tsaki ta ja, Tana masa wani kallo sai kuma ta mike ta ce
"Daga yanzu kamar yadda ka bata komai, bana bukatar na sake Jin ka ka kira ni dan kana bukatar kudi ko wani abu"
daga haka ta wuce zuwa inda drivern ta yayi parking na tare data sake kallonsa ba ita tasan yadda zuciyarta yake kuna
Masu bukatar cigaba da book 2, zaku iya fara payment ta 7084571222, hauwa jibrin, evidence of payment ta—08110615256. 500 ne kacal
*FARASHIN IZZAH*
Book 1