Chapter 40
Farashin Izzah Part 1 Complete Hausa Novel · about 12 min read
Gidan Alhaji Muhammad Nasir ya fara cika da baƙi. Manyan motoci na shigowa ɗaya bayan ɗaya.
’Yan uwa ne, Abokan arziki, harda ma manyan ’yan kasuwa abokan Abbah na cikin da wajen ƙasa
Mata cikin kyawawan atamfofi da leshi masu tsada, haka ma Maza cikin shaddoji masu tsada
Kowa na shigowa da murmushi, ana gaisawa, ana tarbar baƙi
Garden ɗin gidan ya canza gaba ɗaya kamar Wanda ake biki
Videographers da photographers kuwa suna ta zirga-zirga, suna ɗaukar hotuna da bidiyo daga kowane lungu
Abbah ya ci gaba da kallon agogon hannunsa. Ya Umar ya matso kusa da shi
“Abbah… Ina jin ya kamata yanzu sun kusa dawowa.”
Abbah ya yi murmushi
“Eh…
Kuma ina son a ɗauki reaction ɗinta tun daga bakin gate.”
Ya juya ya kalli videographer daya ke tunkararsu
“Da zarar motarta ta iso…. Kai ka fita, Ka tabbata ka ɗauki komai
Daga lokacin da za ta sauko har zuwa lokacin da za ta shigo ciki”
Videographer ɗin ya gyada kai
“Okay sir.”
A can layi kuwa…
Motar Zahra ta ƙaraso, Driver ya danna horn
Poo! Poo!
Sai dai… ko alamar za’a buɗe Gate babu
Driver ya sake danna horn
Har yanzu…. Shiru
Ya ɗan zaro kai ta window.
“Mai gadi! Bude mana gate ɗin mana, mu ne fah”
Mai gadin ya leko
“Yi haƙuri, bari na je na sanar da Alhaji.”
Ya juya da gudu ya nufi cikin gida.
Driver ya haɗe gira.
“Wannan kuma wani sabon tsari ne?”
A bayan mota…
Zahra ta gaba cika da fushi
“Wannan kuma wani irin iskanci ne?” Ta sake kallon gate.
Horn ɗin ya sake dannawa
Amma har yanzu… ba a buɗe ba
“Wallahi… zai gane ni ya shanya ai wannan ma iskanci ne, shi da Abba
Dagaa haka ta buɗe ƙofar motar, ta sauka
Da sauri ta nufi bakin gate dan ranta ba kadan ba ya ɓaci
A dai-dai lokacin…
Ta ji wani irin ƙarar ƙananan fan a sama, ta ɗaga kai
“Eh?”
Wani drone camera ne ke shawagi a samanta, yana zagaye da ita yana ɗaukar bidiyo daga sama.
Ta bi shi da kallo cike da mamaki.
“Wannan kuma?”
Har ta ɗaga hannunta tana ƙoƙarin buga gate…
Sai aka buɗe ƙofar
Anty Jiddah ce ta fito tana dariya.
“Wayyo… Princess har ta fara fushi kenan?”
Zahra ta ɗan sake fuska
“Anty Jay… Wai me yake faruwa ne? Mun daɗe muna horn, amma dan iskanci an ƙi buɗewa.”
Anty Jiddah ta yi dariya.
“Haba… shine har ɗan wannan abun zai ɓata miki rai princess?”
Ta kamo hannunta
“Zo mana”
Zahra ta bi ta da ido
Har yanzu dai ba ta fahimci komai ba. Suna shiga cikin compound…
Kafafunta suka tsaya cak, Idanunta suka sauka kan wani babban banner
Idanunta na bin hotonta dake jikin da kuma wishes message na jikin
Numfashinta ya ɗan tsaya na wasu dakiku
“Wai…” Ta ƙara ɗaga idanunta tana kallon
Balloons, Flowers, Kayan ado, Manyan tebura, Baƙi, Photographers, Videographers
Sai ta rasa inda za ta fara zuwa, ta juya a hankali
“Abbah…?” Muryarta ta fito can ƙasa saboda she’s speechless
A dai-dai lokacin… sai aka fara tafawa
Taf! Taf! Taf!
Dukkan baƙin suka miƙe tsaye suna murmushi, suna kallonta. A tsakiyarsu…
Abbah ya fito, sanye cikin wata farar shadda mai matuƙar ido
Fuskarsa cike da murmushi irin na uba mai alfahari da ’yarsa.
Ya buɗe hannayensa
“Happy Birthday… My Princess.”
Zahra ta tsaya tamkar wacce aka dasa, ta kai hannu ta rufe bakinta
Idanunta suka cika da ƙwalla nan take
“Abbah…” Ta faɗa da ƙyar
Ta girgiza kai kamar wacce ba ta yarda da abin da idanunta suke gani ba
“All this…”
“…for me?”
Abbah ya yi murmushi
“Everything…”
“…is for you, Baby.”
Kafin ya ƙara cewa wani abu…
Zahra ta yi gudu taje ta faɗa jikinsa da ƙarfi, ta rungume shi gam
Hawayen farin ciki suka gangaro a fuskarta
“Thank you, Abbah…”
“Thank you so much… and I love you more than life itself”
Abbah ya rungume ta yana shafa bayanta
“Allah Ya ƙara miki albarka…”
“Ya sa ki zama abin alfaharinmu kullum.”
Mami ta share hawayen farin cikinta
Ya Umar kuwa ya yi dariya yana girgiza kai
“Na gaya muku…”
“Baby za ta yi kuka.”
Dukkan wajen ya kaure da dariya da tafi…
Har yanzu Zahra na manne a jikin Abbah tana kuka irin na farin ciki
Ba ta ma san lokacin da hawayenta suka jike gaban shaddarsa ba.
Abbah kuwa bai damu ba
Sai shafa bayanta yake cikin kulawa irin ta uba.
“Ya isa haka, Baby…”
“Yau ai ranar farin ciki ce”
Ta ɗan janye jikinta kaɗan, amma har yanzu hannayenta na riƙe da hannun Abbah tamau.
Ta share hawayenta tana dariya lokaci guda.
“Wallahi ban yi tunanin haka ba. Ko kaɗan.”
Abbah ya yi murmushi.
“Shi ya sa muka ɓoye miki.”
Daga bayan Abbah… Sai aka ji wata murya.
“Ai idan mun gaya miki, ina armashin surprise ɗin?”
Zahra ta ɗago kai da sauri
“Yaya!”
Ya Umar ne sanye cikin wata shadda navy blue mai matuƙar kyau ga ɗaukar ido, yana taku a hankali yana murmushi
Da ya iso gabanta…
Sai ya buɗe hannayensa.
“Birthday girl…”
Ba ta bari ya ƙarasa ba ta yi saurin faɗawa jikinsa ta rungume shi da ƙarfi
“Yaya… Nagode sosai…
Wallahi ban san me zan ce muku ba ba.”
Ya Umar ya yi dariya yana shafa kanta
“Aikin Abbah ne kaɗai”
Ta ɗan janye tana kallonsa
“Amma na san kai ma kana ciki.”
Ya ɗaga kafaɗa cikin wasa
“Maybe…”
Ta ɗan bugi kafaɗarsa
“Ai ba faɗin gaskiya zaka yi ba”
Ya yi dariya
“Okay… Na amsa laifi na
Dukkan mutanen wajen suka yi dariya
A dai-dai lokacin…
Mami ta fito daga cikin baƙin
Sanye take cikin wata doguwar atamfa mai launin champagne gold, veil d’in ya yi matuƙar ƙara mata kwarjini
Tun daga nesa…
Fuskarta cike take da murmushi.
Da Zahra ta hango ta…
Sai ta saki hannun Ya Umar
“Maamiiii…” Ta nufi inda take da gudu
Mami ta buɗe hannuwanta, Zahra ta faɗa jikinta ta rungume ta sosai
Mami ta sumbaci goshinta cikin ƙauna
“Happy Birthday, Princess
Allah Ya ƙara miki shekaru masu albarka. Ya sa ki zama abin alfahari duniya da lahira.”
“Ameen…”
Zahra ta amsa tana goge hawayenta
Mami ta ɗan ja baya ta riƙe fuskarta da tafukan hannunta
Ta kalleta daga sama har ƙasa.
“’Yar kyakkyawa. Allah Ya tsare miki wannan kyawun.”
Ya Umar ya yi saurin cewa cikin dariya,
“Mami… Don Allah kada ki fara kuka yanzu, ba ke ce ake yi wa birthday ba.”
Mami ta harare shi.
“Waya tambayeka? Wai kai ka fi kowa surutu ne?”
Dariya ta sake kaurewa a wajen
Abbah ya girgiza kai yana kallonsu
“Baƙi fa na jiran birthday girl.”
Zahra ta juyo ta kalli Abbah.
Sai ta yi murmushin da ya haskaka fuskarta gaba ɗaya.
Anty Jiddah ta yi dariya tana tafa hannuwanta.
“Eh haka ne kuma fah! Baƙi fa duk suna jiran birthday girl.”
Ta kama hannun Zahra
“Zo da sauri, muje, kafin ki kije ki gishe da Mamas and Babas dinki”
Ba tare da Zahra ta samu damar tambayar inda za su ba, Anty Jiddah ta ja ta zuwa ciki suka haura sama, ɗakinta suka shinge
Wata garment bag ta ciro daga kan gado, ta buɗe ta a hankali
Zahra ta zaro idanu tana kallon kayan
“Wooow…” ta furta
Doguwar gown ce mai launin baby pink, an yi mata aiki da stones masu kyalli na azurfa a wuya da hannaye, yayin da ƙasan rigar ke shimfiɗewa cikin tsari irin na princess
Anty Jiddah ta yi murmushi.
“Wannan ce dress ɗinki na yau. Ki sa ki fito.”
Zahra ta dafe ƙirjinta
“Anty Jay… Kin san ban son abubuwa masu yawa a kaya”
Anty Jiddah ta taɓe baki
“Toh Yau kuma a haka muke son ganinki, dole ki saka. Ki hanzarta.”
Bayan wasu mintuna…
Zahra ta fito daga ɗakinta
Rigar ta zauna a jikinta tamkar an zana mata ita
Pink ɗin ya ƙara fito da hasken fatar jikinta
Ɗan makeup mai sauƙi da Anty Jiddah ta mata ya ƙara mata kyau sosai
Anty Jiddah ta dafe baki
“Ma shaa Allah …
Princess kenan.”
Ko Zahra kanta sai da ta yi murmushi tana kallon kanta a mirror
“Na yi kyau ne?”
Anty Jiddah ta yi dariya
“Kin yi mana
Wallahi idan ba na nace ba kawai a aurar da ke yau.”
Dukansu suka yi dariya, da suka sauko ƙasa…
Sai aka fara tafi
Taf! Taf! Taf!
Baƙi suka miƙe tsaye suna murmushi
Photographers suka yi ta ɗaukar hotuna.
Videographers kuwa suna ta zagayawa suna kama kowane motsinta
Ya Umar ya ƙaraso gabanta
Ya miƙa mata hannunsa cikin girmamawa.
“My Princess.”
Ta yi murmushi ta saka hannunta cikin nasa.
Ya ja ta a hankali
Suka fara zagaya tsakanin baƙin tana gaishe su, wasu ma bata dan su ba, Fatan alkhairi kawai suke mata
“Allah Ya ƙara shekaru masu albarka.
Allah Ya cika miki burinki.”
Ta na amsawa cikin fara’a da ladabi
“Nagode sosai! Ameen.”
Bayan ta gama gaisawa da manyan baƙin…
Ya Umar ya dawo da ita tsakiyar taron
A nan ne aka kawo katafariyar birthday cake mai hawa uku.
Kowa ya fara rera
“Happy Birthday to you…
Happy Birthday dear Zahra…”
Wajen ya kaure da dariya
Zahra ta yi ta dariya tana girgiza kai.
Abbah ya tsaya a bayanta
Ya ɗora hannunsa a kan nata.
“Ready?”
Ta gyada kai tana murmushi
A tare suka riƙe wuƙar, ta yanke cake ɗin
Nan take…
Tafi ta sake kaurewa.
Flash na cameras suka cika wajen
Wasu na ɗaukar pictures. Wasu na recording videos.
Ya Umar ya ɗan shafa cream kaɗan a kumatunta.
Ta zaro ido.
“Yayaa!”
Kafin ta rama…
Ya riga ya matsa baya yana dariya.
“Ba za ki same ni ba.”
Dariya ta sake cika wajen.
Bayan komai ya ɗan lafa…
Abbah ya matso kusa da ita.
“Baby.”
“Yess Abbah?”
“Zo mu je.”
Ta bi shi ba tare da tambaya ba
Ya tsaya a bayanta. Ya ciro wani silk scarf.
“Rufe idanunki.”
Ta yi dariya
“Abbah…
Wani surprise kuma?”
“Ki yi biyayya.”
Ta lumshe idanunta
Ya ɗaure mata scarf ɗin a hankali.
Sannan ya kama hannunta
“Ku ba mu hanya.”
Baƙi suka matsa gefe.
Shi kuwa ya riƙe hannunta cikin kulawa.
Yana tafiya a hankali
Ita kuma tana binsa tana murmushi
“Abbah… Ina za mu?”
“Ki yi haƙuri. Mun kusa.”
Da suka isa… Ya tsaya
Ya juya ta, ta fuskanci wani wuri.
Sai ya kwance scarf ɗin daga idanunta a hankali.
“Open your eyes…”
Zahra ta buɗe idanunta.
Na farko…
Ba ta fahimci abin da take gani ba
Sai da ta ƙara lumshewa ta sake buɗewa.
Wata sabuwar mota ce
Latest model.
An yi mata ado da manyan ribbons masu launin pink da gold, Balloons sun zagaye ta.
A saman bonnet ɗinta an rubuta da furanni
“Happy Birthday, Princess Zahra.”
Numfashinta ya tsaya
Ta kai hannunta kan bakinta
Idanunta suka cika da hawaye.
Ta juya a hankali ta kalli Abbah.
“Ab… Abbah…”
Muryarta ta kasa fitowa sosai.
Ta sake kallon motar, ta sake kallon Abbah.
“Wai…
…tawa ce?”
Abbah ya yi murmushi mai cike da ƙaunar uba.
“Eh! Ke kaɗai, Kyautarki ce.”
Hawaye suka gangaro a kumatun Zahra ba tare da ta iya hana su ba.
Ta girgiza kai tana murmushi.
“Wallahi…”
“Ban taɓa tsammanin haka ba.”
Ta yi saurin rungume Abbah da ƙarfi.
“Nagode…”
“Nagode sosai, Abbah.”
“Allah Ya saka maka da Aljannah.”
Abbah ya shafa kanta cikin tausayawa
“Babu abin da ya fi faranta min rai…”
“…sama da ganin murmushinki, Baby.”
A bayansu kuwa…
Tafi, ihu na murna da walƙiyar cameras suka sake cika sararin gidan, yayin da kowa ke kallon Zahra cikin farin ciki da yi mata fatan alheri.
Zahra kuwa ta kasa cire idanunta daga kan motar
A hankali ta matsa gabanta.
Tamkar mai tsoron kada abin da take gani mafarki ne.
Ta kai yatsunta ta shafi bonnet ɗin motar.
Sanyi ya ratsa tafin hannunta
Sai ta yi murmushi tana girgiza kai.
“Abbah…”
“Da gaske tawa ce?”
Abbah ya saka hannu cikin aljihunsa ya ciro wani ƙaramin velvet box. Ya buɗe shi
Key ɗin motar ne a ciki.
Ya ɗaga shi yana murmushi
“Ki karɓi kyautarki, Princess.”
Wajen ya sake kaurewa da tafi
“Taf! Taf! Taf!”
Zahra ta dafe bakinta
Ta karɓi key ɗin da hannaye biyu
Ta jingina shi a ƙirjinta.
Kafin ta sake rungume Abbah.
“Allah Ya bar min kai. Allah Ya saka maka da mafificin alkhairi.”
“Ameen.”
Abbah ya amsa yana shafa kanta.
Mami ma ta matso kusa da su.
Idanunta sun yi ja saboda farin ciki.
Ta ɗora hannunta kan kafaɗar Zahra.
“Ki gode wa Allah, Baby.”
“Duk wata ni’ima tana tare da godiya.”
Zahra ta gyada kai da sauri.
“In shaa Allah, Mami.”
“Alhamdulillah… Alhamdulillah…”
Ya Umar ya zo ya tsaya a ɗayan gefenta.
Ya miƙa mata hannu
“Congratulations.”
Ta yi dariya ta rungume shi
“Thank you, Yaya.”
Ya ɗan karkata yana raɗa mata a kunne
“Yanzu dai ba za ki dame ni da cewa ‘Yaya ka siya min mota’ ba ko?”
Ta tura shi da ɗan ƙarfin wasa
“Ni ban taɓa cewa ka siya min mota ba. Amma da ka saya ma zan karɓa.”
Ya Umar ya ɗaga hannu.
“Kun ji ta ko? Wannan yarinyar ba ta da kunya wajan cinye min kuɗi”
Dariya ta sake cika wajen.
Anty Jiddah ta yi saurin cewa,
“Okay! Lokacin pictures ya yi.”
Nan take photographer ya shirya.
Abbah da Zahra
Ta tsaya gefensa tana riƙe da key ɗin motar.
Flash!
Sai Mami ta shiga.
Flash!
Ya Umar ya shiga.
Flash!
Sai aka kira sauran ’yan uwa, ana ɗaukar group pictures.
Bayan hotuna… Abbah ya ɗauki microphone.
Hayaniya ta yi ƙasa. Kowa ya juya yanay, Ya gyara tsayuwarsa
“Alhamdulillah… Dukkan yabo ya tabbata ga Allah! Yau rana ce ta musamman a gare ni.”
“Ba don an yi birthday ba kawai…Sai don Allah Ya ba ni ’ya da kullum take ƙara sa ni alfahari.”
Ya juya ya kalli Zahra.
“Baby… Duk abin da nake yi miki…”
“Ba don ina son in nuna wa duniya wani abu ba ne, Ina yi ne saboda kina da tarbiyya, da kuma sanya min murmushi a fuskata da ko Yaushe kike yi”
“Kuma kina ƙoƙarin zama abin da zai amfani addininki da al’ummarki.”
Idanun Zahra suka sake cikowa da ƙwalla, ta sunkuyar da kai cikin kunya.
Abbah ya ci gaba,
“Ina roƙon Allah…”
“Ya ci gaba da tsare miki ke. Ya ba ki ilimi mai amfani.”
“Ya sa ki zama haske ga iyalanki da duk wanda ya san ki.”
“Ameen…”
Kowa ya yi tafi
Mami ta share hawayenta, tabbas Wanda yayi hakuri zai ga ribarsa
Ya Umar ya yi murmushi cike da alfahari
Shi kuwa Abbah ya sauko daga inda yake tsaye.
Ya kamo hannun Zahra.
Ya sumbaci goshinta cikin tausayawa irin na uba.
#FARASHIN IZZAH
#08110615256