← Book details Farashin Izzah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 50 OF 59

Chapter 48

Farashin Izzah Part 1 Complete Hausa Novel · about 12 min read

Zahra ta yi wata irin ƙara.
"Mamiiii ki tausaya min, Ni ba chef ba ce."

Mami ta yi dariya
"Bance ke chef bace, kawai Ina son mace mai iya kula da gidanta ne”

Ta miƙa mata wuƙa
"Ga albasa, ki fara."

Zahra ta karɓa kamar wacce aka tilasta, ta fara yanka tana ta ƙorafi.

"Wallahi Ni dai zan kai ƙara wajen Abbah ya ceci ni."

Mami ta yi kamar ba ta ji ba
"Ki yanka daidai. Kar ki sare yatsanki."

Can bayan mintuna kaɗan...
Idanun Zahra suka fara zubar da hawaye saboda albasa kamar yadda jiya ya mata

Ta ɗaga kai
"Mamiiii Ga shi na fara kuka, haka fa kullum yake min”

Mami ta kalle ta
Ta kasa riƙe dariyarta.

"Albasa ce, ba kuka ba ne, shame on you”

Zahra ta share idanunta
"Ni dai ban yarda ba. Albasa azzaluma ce."

Duk masu aikin kitchen suka yi dariya
Mama Ladi har sai da ta riƙe cikinta

A ranta taji dadin maganar komawarta hostel ko ba komai zata huta da wannan matsin lamban da Mami ta tsiro sa

Mami kuma na ci gaba da koya mata girki a hankali
Yayin da Zahra ke ta ƙorafi, duk da a zuciyarta ta san Mami na yi ne domin amfaninta.

Daren ranar...
Bayan an idar da sallar Isha'i, an gama dinner, kowa ya watse zuwa ɗakinsa

Abbah kuwa yana zaune a parlonsa na sama. Mami na gefensa tana karanta masa wani littafin story

Sai Abbah ya ɗaga kai
"My dear”

"Na'am."

"Ki kira min Baby."

Mami ta gyada kai, ta ɗauki wayarta ta kira Zahra

A ɗakinta... Zahra na kwance tana scrolling Instagram

Wayarta ta fara ringing, da ta ga Mami ce... ta ɗaga da sauri.

"Na'am Mami?"

"Zo parlour ɗin Abbahn”

“Yanzu, Mami?”

"Eh."

"Toh Mami."

Ta kashe wayar, ta sauko daga kan gado, scarf ta dauka ta ɗaura a kai" Ta fito

Da ta isa... Ta yi knocking

"Come in."

Ta shiga, ta a ƙarasa….
Ta zauna a ƙasa kusa da ƙafafun Abbah kamar yadda ta saba.

Ta ɗago tana kallon su biyun
"Meye laifi?"

Abbah ya yi murmushi
"Ba laifi bane Baby, magana ce."

Zahra ta gyara zamanta
"Ina ji, Allah sa kuɗi zaka bani”

“Keep quiet, Baby”

Abbah ya kalli Mami sai ya dawo da kallonsa kanta.

"Maganar hostel."

Da jin haka...
Zahra ta ɗan gyara zamanta sosai, ta haɗe yatsunta cikin fargaba

Abbah ya ci gaba
"Ni da Mami... Mun yi magana sosai, mun kuma yi tunani."

Mami ta gyada kai
"Eh."

Abbah ya yi murmushi
"Daga ƙarshe dai mun amince"

Na ɗan daƙiƙa...
Zahra ta kasa magana, ta zaro ido

"Abbah Kuna nufin..."

Abbah ya katse ta
"Za ki koma hostel."

Fuskar Zahra ta cika da wani irin farin ciki, da sauri ta rungume Abbah.

"Really? Abbah?"

Abbah ya yi dariya
"Eh, da gaske."

Ta juya da sauri ta rungume Mami
"Mamiiii! Thank you."

Mami ta shafa bayanta
"Amma..."

Nan take Zahra ta sake nutsuwa, ta san akwai sharuɗɗa.

Mami ta ce
"Ba hostel ɗin cikin school ba. Za mu kama miki gida ne a off-campus"

"Mai kyau, mai tsaro, kuma inda za ki samu kwanciyar hankali"

Abbah ya ɗora da cewa,
"Ba za mu yarda ki zauna ko'ina ba, za a nemo wajen da ya dace"

Zahra ta gyada kai da sauri
"Komai ma ya kasance, na yarda"

Abbah ya yi murmushi
"Yanzu dai ki saurare ni."

Ta zauna da kyau.

"Na farko…. Karatunki shi ne abin da ya kai ki can, ba yawon banza ba"

"Na biyu... ki kiyaye sallolinki, kada ki bari rayuwar hostel ta canja miki addininki."

Mami ta karɓa
"Na uku... ki yi hulɗa da mutanen kirki, ba kowa ne aboki ba, ba kowa ne za ki shigar da shi cikin rayuwarki ba."

Abbah ya ce
"Na huɗu... kada ki yarda wani ya rinjaye ki da abin da bai dace ba, Idan akwai wata matsala... Ni da Mami muna nan” ya sauke ajiyar zuciya

“Ki kira, Kada ki ɓoye mana"

Mami ta ƙara da cewa
"Kuma... Kada ki raina kowa saboda Allah Ya hore miki abin duniya, ki ci gaba da taimakon mutane, ki ci gaba da kasancewa Zahra ɗin da muka sani"

Idanun Zahra suka ɗan cika da ƙwalla, ta gyada kai

"In shaa Allah, ba zan ba ku kunya ba."

Abbah ya shafa kanta
"Na san haka. Shi ya sa ma muka yarda."

Sai ya ɗan yi murmushi.
"Sunday mai zuwa... za ki koma"

Zahra ta sake yin murmushi
Sai ta juya ta kalli Mami, ta sake kallon Abbah

"Sunday?"

"Eh."

"Kafin lokacin za a gama shirye-shiryen."
Sannan Abbah ya ƙara da cewa,

"Umar gobe zai fita, daga can zai wuce school dinku, sai ya nemo miki gida mai kyau da tsaro, mai ruwa, mai wutar lantarki. Kuma kusa da school, ba na son ki riƙa wahala"

Zahra ta dafe bakinta da hannunta, ta kasa ɓoye farin cikinta.

"Ya Allah..."

"Nagode Abbah."

"Nagode Mami."

Mami ta yi murmushi

Abbah ya yi dariya
"Yanzu je ki kwanta, gobe akwai lectures."

Zahra ta miƙe, ta fara sumbatar hannun Mami, sannan na Abbah

"Allah Ya saka muku da aljannatul Firdaus."

"Ameen ya Rabb” Suka amsa tare

Da murmushin da ya ƙi barin fuskarta.. ta fita daga parlon

Har ta isa ɗakinta, ba ta daina murmushi ba.

Ta faɗa kan gadonta tana rungume pillow, a hankali ta lumshe idanunta

A zuciyarta kuwa...
Ta fara tunanin yadda rayuwarta za ta kasance

Washe gari...
Tun da sassafe Zahra ta shirya cikin wata atamfa mai launin navy blue da silver, veil ɗinta a daidaice a kanta, agogon hannunta da ƙaramin bracelet suna ƙara haskata

Ta yi sallama da Mami da Abbah, ta wuce compound, ta shiga motarta.

Cikin nutsuwa ta kama hanyar makaranta.

Da ta isa parking lot...
Ta ɗauki handbag ɗinta, ta kulle motar ta nufi faculty

Tun daga nesa...
Ta hango Firdausi da Asiya suna tsaye ƙarƙashin wata bishiya suna jiranta.

Da suka hango ta...

Firdausi ta ɗaga hannu
"Madam Celebrity!"

Zahra ta yi murmushi
"Ku daina fa."

Ta isa wajensu, suka rungume juna.

Asiya ta tambaya
"Yaya maganar hostel?"

Zahra ta yi murmushi kawai, ba ta ce komai ba.

Firdausi ta taɓe baki
"Wai kada ki ce har yanzu ba su yarda ba"

Sai Zahra ta ce a hankali
"They agreed."

Na ɗan daƙiƙa... Firdausi ta zaro ido

"Wait... da gaske?"

Zahra ta gyada kai
"Eh, amma off-campus. A can za su kama mana gida"

Firdausi ta yi ihu
"I knew it!" Ta rungume Zahra da ƙarfi

Asiya ma ta yi murmushi sosai
"Alhamdulillah, wlh na yi farin ciki"

A daidai lokacin...

Suhaima ta ƙaraso wajen
"Tun daga can nake jin ana ihunku, me ya faru?"

Firdausi ta juya da sauri
"Suhaima! Guess what? Zahra is joining us!"

Suhaima ta kalli Zahra
"Da gaske?"

Zahra ta gyada kai tana murmushi
"In shaa Allah."

Suhaima ta yi murmushi sosai
"Yeee, ahh Ma shaa Allah, Ashe Duk zamu haɗu”

Firdausi ta ce
"Ba ma huɗu kawai ba, gida ɗaya, Department ɗaya, Department Course ɗaya, aji ɗaya"

Asiya ta yi dariya
"Kuma wahala ɗaya"

Duk suka kwashe da dariya.

Suhaima ta kama hannun Zahra
"Allah Ya saka wa Abbah da Mami da alheri."

"Ameen” Zahra ta amsa cikin murmushi.

Nan suka ci gaba da hira

Zahra na ba su labarin yadda ta zauna da Abbah da Mami har suka yi mata nasihohi kafin daga ƙarshe suka amince.

Suhaima ta girgiza kai
"Wallahi kin yi sa'a da iyaye Zahra, Ni fah is hardly kiga an zaunar da Ni ayi min nasiha duk da rayuwar Jin ɗaɗi da nake yi”

Zahra ta sauke kai cikin godiya
"Alhamdulillah."

Da lecturer ya shigo... Suka wuce lecture hall, kowa ya samu waje ya zauna

Lecture ya fara. Kusan rabin sa'a da fara lecture...

Wayar Zahra da ke silent ta fara rawar vibration a cikin handbag.

Ta ɗan leƙa, Yaya Umar Calling...

Ta ɗaga gira cikin mamaki, ta nemi izini wajen lecturer

"Excuse me sir."

Ya gyada kai. Ta fito daga lecture hall

Da ta ɗaga wayar...
"Assalamu alaikum Yaya."

"Wa alaikumus salam, Kina Ina?" Ya ce cikin nutsuwa

“Department dinmu”

Ya ce "Ina cikin school ɗinku, gaban Administrative Block. Ki zo na ɗan ganki."

"Okay." Ta katse wayar, ta nufi inda ya faɗa

Tun daga nesa ta hango motarsa, ya jingina da ita
Sanye cikin farar shirt da baƙar trousers, fuskarsa kuma sanye da black sunglasses. Hannayensa cikin aljihunsa.

Da ya hango Zahra... ya cire gilashin, ta ƙaraso tana murmushi

“My Yaaya”

"Baby girl, ya school din?”

"Lafiya lau" ta amsa

"Ya aiki?" Ta tambaya

"Alhamdulillah."

Sai ya ɗaga wani file da ke hannunsa
"Na gama duba gidaje, akwai guda biyu amma ɗaya ya fi” yayi shiru na ɗan lokaci ya tsaya yana kallonta sai kuma ya ɗaura

"Na yi magana da mai gidan da yamma zan kai Abbah ya gani, Idan ya amince... sai mu biya."

Fuskar Zahra ta fara murmushi
"Da gaske Yaaya?"

Ya gyada kai
"In shaa Allah zai yi miki, yana kusa da school. Tsaro yana da kyau, kuma akwai ruwa da wuta"

Zahra ta yi murmushi
"Alhamdulillah"

Sai ta ɗan kalle shi
"Yaya sannu da gajiya Allah Ya saka da alheri"

Ya ɗan yi murmushi
"Bakomai Baby, ki koma lecture”

Ta yi dariya
"Okay” Sai ta yi masa bye da hannu

Yayi murmushi shiga motarsa, Ita kuma ta juya ta nufi lecture hall cikin sauri

Da ta shiga...
Firdausi ta matsa kusa da ita tana raɗa
"Me ya faru?"

Zahra ta yi murmushi kawai, sai ta raɗa mata
"Yaya ne, ya zo duba mana gida."

Firdausi ta yi murmushin farin ciki, ta ɗaga babban yatsanta sama
"Perfect."

Daga nan...
Su biyun suka mayar da hankalinsu kan lecturer... har yamma suna makarantar

Bayan sun gama lectures na ranar Zahra ta yi sallama da Firdausi, Asiya da Suhaima

Ta shiga motarta. A hankali ta ja motar ta kama hanyar gida

Cikin tafiyar, zuciyarta cike take da tunanin gidan da Ya Umar ya ce ya gani, sai kuma Saudat da bata gani ba

Lokaci zuwa lokaci sai ta yi murmushi ita kaɗai
“Allah Ya sa Abbah ya so shi…”

Tana isa ta shigar da makarantar

Sai ta hangi Abbah zaune a ƙarƙashin gazebo yana shan tea na yamma, wasu takardu kuma a gabansa.

Fuskarta ta cike da murmushi ta karasa wajensa
“Abbah!”

Ya ɗago kai
“My Baby.”

Ta ƙarasa da sauri, ta zauna kusa da shi, basu ma gama gaisawa ba ta ce

“Abba gidan fa?”

Ya yi dariya
“Kin ma fi ni son sanin labarin”

Ta yi dariyar kunya
“Please tell me.”

Ya ɗan jingina da kujerarsa
“Na je”

Ta zuba masa ido.

“Na gani, na duba komai. Security, Environment, Distance daga school, Ruwa.Wuta, Parking lots, komai” Sai ya yi ɗan shiru.

Zahra ta kasa haƙuri.
“Abbah… Please…”

Ya yi murmushi
“It’s okay, I liked it”

Nan take fuskar Zahra ta cika da annuri
“Really?”

Ya gyada kai.
“Har ma… an riga an biya”

Na ɗan daƙiƙa… Zahra ta zaro ido

“An biya?”

“Eh, Sunday sai a kai kayanki.”

Ba tare da ta shirya ba… ta rungume Abbah
“Thank you! Nagode sosai Abbah. Allah Ya saka maka da aljannah.”

Abbah ya yi dariya, ya shafa kanta

“Ameen! Sai dai…”

Ta ɗaga kai.

“Kada ki manta da alkawarin da kika yi mana”

Ta gyada kai cikin sauri
“Ba zan manta ba, I promise”

Ya yi murmushi cikin gamsuwa
“Good girl”

Ta yi masa sallama, ta shiga cikin main parlour

Tana taka ƙafarta ciki…
Sai idanunta suka sauka kan Mami

Tana zaune a sofa, a gabanta akwai wasu magazines da cup ɗin shayi, tana magana wasu Mama Ladi Akan su haɗa mata kayan girki akan Island

Zahra ta tsaya cak, ta tuna jiya da shekaran jiya ma haka Mami ta mata

Sai ta haɗe bakinta, maganar da zata yi ta komar da shi ciki

A zuciyarta ta ce
“Innalillahi… shikenan Yau ma haka zan kare a kitchen?”

Ta kalli Mami, Mami kuma ba ta lura da ita ba, hankalinta na kan abin da take karantawa

Nan take…
Zahra ta fara taku a hankali, making sure bata making any sounds , kamar wacce take tafiya a kan ƙwai

Data ɗaga kafa, sai ta fara tabbatar da crocs ɗinta ba su yi ƙara ba

Ta riƙe handbag ɗinta da ƙarfi don kada zip ɗin ya yi Kara shima

Da ta kusa ƙarasa staircase…
Sai Mami ta ɗaga kai

Zahra ta tsaya nan take, ta lumshe ido
“Wayyo…”

Amma sai Mami ta sake mayar da hankalinta kan magazine ɗinta

Zahra ta saki numfashi a hankali, ta ci gaba da tafiya irin ta ɓarawo

A haka har ta haura sama, da ta isa ƙofar ɗakinta… ta yi saurin shiga, ta rufe ƙofar a hankali

Ta jingina bayanta da ita, ta lumshe idanunta sannan ta sauke wani dogon ajiyar zuciya.

“Alhamdulillah…”

Ta yi dariya ita kaɗai
“Wallahi Mami za ta mayar da ni chef, ko maid”

Ta faɗa tana jefa handbag ɗinta kan gado

A can kasa kuwa…
Mami ta ɗaga kai ta kalli saman bene, ta yi murmushi ita kaɗai

Ta girgiza kai cikin nishaɗi
“Wannan yarinyar… ta ɗauka ban gane abin da take yi ba”

Ta ci gaba da shan shayinta tana murmushi, yayin da Zahra a ɗakinta ke murna kamar wacce ta tsallake wata babbar jarabawa

Sai ga Ya Umar ya shigo parlour ɗin

Sanye yake cikin casual wear, makullin motarsa na jujjuyawa a yatsunsa

Da ya hango Mami na murmushi ita kaɗai…

Sai ya tsaya
“Mami?”

Ya ƙarasa ya zauna kusa da ita.
Ya ɗan karkatar da kai yana kallonta.

“Lafiya kuwa? Tun daga ƙofa na shigo na tarar kina murmushi, a fada min bin farin cikin?”

Mami ta yi dariya
“Hmm Yarinyar nan ce”

“Wace?”

“Baby mana, Banda ita waye?”

Ya Umar ya yi murmushi
“Me kuma ta yi?”

Nan Mami ta ba shi labarin yadda Zahra ta shigo gida, da yadda ta hango ta zaune a parlour, da yadda ta fara taku a hankali…

Kamar wacce ta zo sata
Da yadda ta riƙa tabbatar da crocs ɗinta ba su yi ƙara ba

Har ta shige sama tana tunanin ba ta lura da ita ba.

Da Mami ta gama…

Ya Umar ya kwashe da dariya.
“Wallahi Baby akwai ta da abin dariya”

Mami ta girgiza kai tana dariya
“Zan ɗauke mata yanzu, amma tana dawowa gida Hutu ta shiga uku wlh, dan ko space ba zan bata ba”

Ya Umar ya ɗan daidaita zamansa, ya ce cikin dariya,

“Mami please ki bi ta a hankali, kada ki tsorata ta da kitchen ɗin nan”

Mami ta harare shi.
“Au? Ni zan bi ta a hankali?”

Ya Umar ya yi dariya
“Eh mana, Kaɗan-kaɗan”

Mami ta ɗaga gira
“Toh Idan aka kaita gidan mijinta fa? Inaga zata na kiran ka ne Yaya ka min order breakfast, lunch da kuma dinner, Kaga ai haka ne mijin ma ba zai gaji ba”

Ya Umar ya riƙe ciki yana dariya
Mami ta ci gaba da cewa,
“Dole ne fah ta saka a ranta zata koya, Allah ko na sallame masu aiki ta fara yi, don gobe kada wani ya ce ba a raineta da training ba.”

Ya Umar ya girgiza kai yana murmushi
“Okay Mami. Na gane”

Ya miƙe tsaye
Har yanzu dariya yake yi

“Allah ya taimake ta ta iya ɗin”

Mami ta ce da sauri
“Ba ita kaɗai ba Allah ya taimaki wanda zai aure ta ma, don sai yayi hakuri”

Ya Umar ya sake fashewa da dariya.

“Kai Mami kin gama da ita.”

Yana dariya ya juya, ya nufi staircase.

Mami kuwa ta girgiza kai tana murmushi, ta ɗauki cup ɗin shayinta

Ta ce a hankali,
“Wannan yara nawa Kullum sai sun sani dariya, Allah ka albarkace rayuwar su”

Ba free book bane, aji tsoron Allah a biya ni hakkina
500 ne ta wannan 7084571222, Hauwa Jibrin Opay
Shaidar biya ta nan 08110615256 Hauwajay writes
Chapter 50 · 0% Book details