Chapter 52
Farashin Izzah Part 1 Complete Hausa Novel · about 11 min read
Washe gari tun kafin alfijir ya ketare, ƙarar alarm ta cika ɗakin.
Tring… Tring… Tring…
Zahra ta buɗe ido da ƙyar, ta lumshe su kuma.
“Firdausi… kashe mana wannan alarm ɗin.”
Firdausi ma ta rufe fuskarta da pillow.
“Ni? Ba ni ba ce na saka ai”
Aasiya ta yi dariya daga ɗayan gefen gadon.
“Ku tashi mana. Lectures fa ƙarfe takwas ne.”
Zahra ta ja dogon tsaki.
“Wallahi whoever invented morning lectures ba mutumin kirki ba ne.”
Su uku suka yi dariya kafin suka miƙe.
Suka yi alwala suka yi sallar Asuba, suka zauna suka yi azkar na ɗan lokaci, sannan kowacce ta shiga bathroom ta yi wanka.
Cikin kusan awa guda, su ukun sun gama shiryi tsaf.
Firdausi da Aasiya sun yi kyau cikin simple dress dinsu, amma Zahra… Dama ko a’ina take sai ta haska
Ta fito sanye cikin wata doguwar abaya mai tsada, color ɗinta ya yi matuƙar dacewa da kayan, agogon hannunta da ƙaramin handbag ɗinta sun ƙara mata armashi. Komai nata cikin nutsuwa yake, babu ƙawata mai yawa, amma duk wanda ya kalleta sai ya sake waiwaya.
Suna fitowa daga School Villa, ɗalibai da dama ma suna fitowa zuwa lectures na safe.
Compound ɗin ya cika da hayaniyar ɗalibai. Wasu na dariya, wasu na gudu saboda sun makara, wasu kuma na jiran ababen hawa.
Sai dai kusan duk inda Zahra ta wuce, idanu suna binta ne…
“Ba ita ba ce?”
“Wallahi ita ce.”
Wasu na raɗaɗi, wasu kuma suna waiwaya suna kallonta.
Amma Zahra ko kaɗan ba ta nuna alamar jin abin da ake faɗa ba.
Ta ci gaba da tafiya cikin nutsuwa, kai a tsaye, tafiyarta cike da kwarjini, fuskarta ɗauke da natsuwa da izza
Idan mutum ya gan ta a wannan lokacin, ba zai taɓa tunanin cewa ita ce Zahra mai yawan hira da ƙawayenta ko wacce ke shagwaɓa wa Abbah da Mami kamar ƙarama ba.
A wannan lokacin, cikakkiyar budurwa mai cike da kwarin gwiwa ce
Da suka fito daga gate na School Villa, sai suka hangi yawancin keken Napep sun riga sun kwashe ɗalibai zuwa makaranta.
Babu ko ɗaya a wajen.
Zahra ta tsaya cak
“Oops.”
Ta kalli hanya sannan ta kalli Firdausi
“Matsalata kenan.”
Firdausi ta ɗaga gira
“Wace matsala?”
“Ni kam wallahi ba zan iya trekking ba. Ga shi babu Napep.”
Aasiya ta yi dariya
“Ni ma ban ga ko ɗaya ba.”
Firdausi ta kalli agogon hannunta.
“Kar mu makara. Let’s try mu fara tafiya, ko za mu samu wani a gaba.”
Zahra ta turo baki.
“Please… let’s wait zasu iya zuwa yanzu”
Ba don ta so ba, ta biyo su ganin sun fita yawa
Suka fara tafiya….
Suna tafiya suna kallon ko za su ga Napep
Amma babu….
Sun ka ƙara tafiya, har sannan babu
Da suka yi nisa sosai, Zahra ta fara rage sauri
“Firdausi…”
“Hmm?”
“Wallahi na gaji.”
Firdausi ta yi dariya
“Mun rage tafiya ne fa.”
“Shi ya sa nake cewa ba zan iya ba.”
Ta sake ɗan tafiya “Wayyo ƙafafuna.”
Aasiya ta yi dariya
“Princess, ki yi haƙuri yanzu kam ai mun iso”
“Ban taɓa yin irin wannan tafiyar ba wallahi.” Daga haka suka cigaba da tafiya
Amma sai complain take yi duk hanya.
“Da ace Napep ya zo.”
“Da ace mun fito da wuri.”
“Da ace lectures ɗin ba na safe ba ne.”
Firdausi da Aasiya dariya kawai suke yi
Da ƙyar suka isa harabar makarantar.
Zahra kuwa tuni gajiyar tafiyar ta bayyana a fuskarta.
Da suka shiga lecture hall, ta sauke jakarta a kan kujera sannan ita ma ta zauna da ƙyar.
Ta jingina bayanta tana sauke numfashi
“Wallahi… idan zan zauna a School Villa, dole sai na nemo solution. Wannan trekking ɗin ba nawa ba ne.”
Firdausi da Aasiya suka kalli juna, suka fashe da dariya, Zahra kam shafa ƙafafunta tana jin kamar sun yi mata nauyi fiye da yadda ta taɓa tsammani
Lecturer ne ya shigo hakan yasa class din yayi tsitt
Zahra gata zauna a kujerarta na gaba, jingine da baya, fuskarta babu ko alamar murmushi. Duk lokacin da lecturer yake bayani, ita dai lokaci-lokaci tana shafa ƙafafunta a hankali.
Lecturer ɗin ya ɗaga kai yana kallon class, sai idanunsa suka sauka kan Zahra.
Ya yi murmushi
“Zahra, what happened today? You don’t look like yourself.”
Class ɗin gaba ɗaya suka waigo suna kallonta.
Zahra ta ɗan bata fuska
“Sir… I trekked to school because there was no transportation. That’s why I’m exhausted.”
Kafin ma lecturer ya sake magana…
Sai class ɗin gaba ɗaya aka fashe da dariya
Wani har yin wani k’ara
“Famous ce fahh”
Wata kuma ta ce,
“Seriously?”
Nan take ran Zahra ya ɓaci
Ta juya a hankali ta kalli class ɗin gaba ɗaya da kwarin gwiwa irin nata
“What’s so funny?”
Nan take wasu suka sake fashewa da dariya.
Ta yi ƙaramin tsaki
“Mtss.” Ta juya ta zauna ba tare da ta ƙara kallonsu ba.
Ko lecturer ɗin sai da murmushi ya kusan suɓuce masa, amma ya daure ya ciye.
Ya gyara murya.
“Alright, everyone. That’s enough. Let’s continue with the lecture.”
Nan ya ci gaba da koyarwa.
Da lecture ya ƙare, Zahra ta fito abinta dan gaskiya Yau sun bata mata rai, ta tsaya a ƙarƙashin wata bishiya, ta ciro wayarta
Sai ga kawayenta sun biyo ta
Kai tsaye ta yi conference call da Abbah, Mami da Ya Umar.
Da suka ɗaga, ba ta bari sun yi magana ba.
“Wallahi ni dai a kawo min mota ta. Idan ba so ake ƙafafuna su tsage ba. Kun ga yadda nake ji kuwa?”
Abbah ya saki dariya
“Haba Baby, har haka?”
“Abbah, ba zan iya trekking ba wallahi.”
Ya Umar ya yi gyaran murya.
“Lazy girl”
Kamar zata yi kuka ta ce
“I mean it fah, yanzu haka kafafun ma dakyar suke amfani”
Ya Umar yayi dariya
“Za a kawo miki…”
Zahra ta yi murmushi
“Na sani.”
Sai ya ƙarasa da cewa
“Pay before delivery.”
Ta zaro ido
“Haba My Love!”
Ya Umar ya yi dariya
“Ai kin iya marairaicewa.”
Ta kasa haɗiye dariyarta, ta juya ga Mami
“Mami, ki sa baki mana.”
Mami ta yi dariya.
“Ni kam ba ruwa na. Yanzu idan na shiga tsakaninku, daga baya sai ki haɗa kai da shi ku gwale ni.”
Dukkansu suka yi dariya.
“Kai Mami!”
Abbah ya girgiza kai yana murmushi.
“Alright. Za a kawo miki motar.”
Nan take fuskar Zahra ta washe
“I love you Abbah na!!”
Ta kashe wayar cike da farin ciki.
Firdausi ta ce
“Saudat da Suhaima sun iso.”
Zahra ta yi murmushi
“Really?”
“Eh, amma babu key.”
Ba tare da ta tsaya ba, Zahra ta buɗe jakarta, ta ciro mukullin gidan ta miƙa musu.
“Ku kai musu.”
Firdausi ta kalleta
“Ke fa?”
Zahra ta yi saurin girgiza kai.
“Ni? Babu inda zan je. Wallahi idan na sake yin wannan tafiyar, ƙafafuna za su balle.”
Su biyun suka fashe da dariya.
Aasiya ta karɓi mukullin
“Toh Madam Princess, zauna ki huta.”
Suna dariya suka juya suka tafi.
Zahra kuwa ta nufi wani cool-down spot da ke ƙarƙashin manyan bishiyoyi a harabar makarantar.
Ta zauna a hankali tana sauke numfashi, ta buɗe Snapchat, ta ɗauki hotuna masu yawa, ta saka caption tana posting
Bayan ta gama, ta koma Instagram.
Ta shiga replying messages da chatting, yayin da iska mai sanyi ke kaɗa veil dinta, tana jin daɗin hutun da ta samu bayan gajiyar safiyar da ba za ta manta da ita ba
Bayan kusan mintuna talatin tana zaune a cool-down area tana chatting a wayarta, wani matashi ya ƙaraso gabanta.
Dogon saurayi ne, sanye cikin riga da Wanda masu kyau, ya tsaya yana murmushi.
“Hey…”
Zahra ba ta ko ɗaga kai ba.
Yatsunta na ci gaba da yawo a kan screen ɗin wayarta.
Ya sake matsowa kaɗan
“Hello.”
Shiru…. Ko kallonsa ba ta yi ba
Ya ɗan yi dariya
“Baiwar Allah, magana ake miki fa.”
Amma kamar ba da ita ake yi ba.
Hankalinta gaba ɗaya na kan wayarta.
Saurayin ya ɗan dafe kansa cikin mamaki
“What’s going on?”
A can gefe kuwa, Firdausi, Aasiya, Saudat da Suhaima na tahowa.
Tun daga nesa suka hango Zahra zaune, suka kuma ga saurayin tsaye a gabanta yana ta magana, ita kuma ko motsi ba ta yi.
Firdausi ta yi murmushi
“Guys… akwai drama.”
Saudat ta ce a hankali,
“Bai dan wacece Zahra ba kenan”
Su huɗun suka ci gaba da tahowa.
Da suka ƙaraso kusa da ita, Zahra ta ɗaga kanta a hankali.
Da ganin Saudat da Suhaima, nan take fuskarta ta canza.
Ta miƙe tsaye da fara’a.
Ta fara rungumar Saudat
“Welcome, darling!”
Sannan ta rungumi Suhaima
“So good to see you!”
Suna dariya cike da murnan ganin juna
Saurayin ya zaro ido
“Dama kina magana?“
Ya girgiza kai
“Na d’auka ai kurma ce ke”
Zahra ba ta amsa masa ba, ta ɗauki jakarta a hankali.
Sannan ta juya ta kalle shi daga sama har ƙasa, kallon da bai ƙunshi fushi ko murmushi ba, sai cikakkiyar nutsuwa da izza.
Ba tare da ta ce masa komai ba, ta mayar da kallonta ga ƙawayenta.
“Let’s go.”
Ta yi gaba cikin tafiyarta mai cike da kwarjini.
Su ma suka bi bayanta
A gefen wajen kuwa, wasu ɗalibai da suka ga abin da ya faru suka fashe da dariya.
Wani ya taɓa kafaɗar saurayin.
“Allah ya ƙara, oga.”
Wani kuma ya ce,
“Ka ga kamar ita za ka tare? Wrong address, boss.”
Dariya ta ƙara tashi a wajen.
Saurayin ya sosa kansa cikin kunya ya bar wajen
Ita kuwa Zahra, ko waiwayowa ba ta yi ba. Ta ci gaba da tafiya tare da ƙawayenta, kamar ba wani abu ya taɓa faruwa ba.
Bayan sun gama ɗan hutun da suka yi, su biyar suka koma lecture hall domin lecture na gaba.
Har yanzu lecturer bai shigo ba, ɗalibai kuwa na ta hira cikin ajin.
Su ma suka zauna a layinsu.
Firdausi ta kasa haƙuri, ta juya tana kallon Zahra.
“Madam… Gist us mana. Me ya sa ba ki kula saurayin nan ba ko kaɗan?”
Zahra ta ɗaga gira ta kalleta, sannan ta yi mata wani irin kallo.
“Firdausi…”
“Na’am.”
“Kin ga na yi kama da wacce zai tare ne?”
Firdausi ta fashe da dariya
“A’a ba haka nake nufi ba.”
Aasiya ma ta fara dariya
“Toh amma gaskiya, ko ɗaga kai ba ki yi kika kalle shi ba. Ta yaya kika san abin da yake so?”
Zahra ta ɗan gyara zama, ta ɗora hannunta kan tebur.
“Whatsoever… jikina ya ba ni. Kuma da na kalle shi na farko, na ga it’s written all over his face.”
Suhaima ta yi dariya.
“Wai ke kina ganin mutum sau ɗaya ki gama karanta shi?”
Zahra ta ɗan yi murmushi
“Ba koyaushe ba… amma wasu mutane, fuskokinsu suna faɗin abin da bakinsu bai faɗa ba.”
Saudat ta ce,
“Toh idan ba haka ba fa?”
Zahra ta ɗaga kafaɗa.
“Then that’s not my business.”
Firdausi ta girgiza kai tana dariya.
“Har naji masa kunya, kin masa rashin M”
“Ni?”
“Eh mana. Ko amsa sallama ba ki yi ba.”
Zahra ta haɗe fuska.
“Saboda ban san shi ba. Kuma ban ga dalilin da zai sa na tsaya hira da stranger ba.”
Aasiya ta ɗan yi murmushi
“Shikenan Madam”
Zahra ta ce. “Better”
Dukkansu suka fashe da dariya a lokaci guda.
A dai-dai lokacin ne lecturer ya shigo ajin.
Nan take hayaniyar ta lafa, kowa ya gyara zamansa, aka fara lecture na gaba
Da lecture na ƙarshe ya ƙare, ɗalibai suka fara fita daga hall ɗin a hankali.
Zahra ta miƙe tana ɗaukar jakarta, ta kalli ƙawayenta.
“Girls, mu wuce cafeteria mana, yunwa nake ji”
Firdausi ta girgiza kai
“A’a, tunda mun gama lectures na yau, gara mu koma gida. Mu dafa abinci kawai, zai fi.”
Aasiya ta gyada kai
“Ni ma haka nake gani.”
Suhaima ta ce
“Sure, tunda we’re done for today”
Saudat ta yi murmushi
“Toh mu koma”
Zahra ta turo baki
“Toh… abun hawa fa?”
Kafin ma ta rufe baki..
Sai wata Napep ta zo ta tsaya kusa da su.
Aasiya ta yi dariya
“Lucky you!”
Firdausi ta ce
“Allah ya ji kukanki.”
Zahra ta yi murmushin nasara
“See? Allah yana sona.”
Dukkansu suka yi dariya
Suka shiga Napep ɗin suka nufi School Villa.
Da suka isa gida, kowacce ta shiga abin da ya dace da ita.
Firdausi ta nufi kitchen
Ta ɗaura girki, tana haɗa abincin rana yayin da ƙamshi ya fara cika gidan.
A gefe guda kuma, Saudat da Suhaima suka shiga ɗayan ɗakin suna gyara kayansu, suna jerawa a wardrobe tare da shirya sauran kayayyakin da suka zo da su.
Aasiya na taimaka musu lokaci-lokaci, ita kuma Zahra ta ɗan zauna tana hutawa kafin daga baya ta shiga kitchen tana taimaka wa Firdausi da ƙananan abubuwa
Bayan komai ya kammala, suka haɗu gaba ɗaya a falon.
Aka jera abinci a kan center table.
Kowacce ta zauna ta fara cin abinci cikin nishaɗi
Ana cikin ci, Firdausi ta ce,
“Guys, kun ji abin da Zahra ta yi yau da safe kuwa?”
Nan take Suhaima ta ɗaga kai
“Me ta yi?”
Firdausi ta fara ba su labarin yadda Zahra ta yi ta complain tun daga School Villa har zuwa makaranta saboda trekking.
Ta kwaikwayi yadda Zahra ke cewa
“Wallahi ƙafafuna za su balle.”
Dukkansu suka fashe da dariya.
Saudat har ta dafe cikinta
“Ke Zahra!”
Aasiya ta ƙara da cewa
“Da muka isa lecture hall, kamar za ta yi kuka saboda gajiya.”
Firdausi ta ce,
“Sai kuma ta kira gida tana cewa a kawo mata mota, wai idan ba haka ba ƙafafunta za su tsage.”
Falonsa ya kaure da dariya.
Suhaima ta girgiza kai
“Princess kenan.”
Zahra kuwa, kamar ba da ita ake magana ba.
Ta ci gaba da cin abincinta cikin nutsuwa ba tare da ta ko ɗaga kai ba.
Daga ƙarshe ta ce cikin sanyin murya,
“Ku gama dariyar. Gobe ma idan babu Napep, ni ba zan fita ba.”
Wannan maganar tata ce ta sake sa falon ya kaure da wata sabuwar dariya.