Chapter 51
Farashin Izzah Part 1 Complete Hausa Novel · about 13 min read
Abbah ya girgiza kai yana kallon Zahra, sannan ya ɗan kalli agogon hannunsa.
“It’s okay… muna wasting time.”
Da jin haka, nan take fuskar Zahra ta sauya. Ta turo baki gaba, idanunta suka cicciko da ƙwalla, tana kallon Mami cikin shagwaɓa kamar ƙaramar yarinya.
“Mami…”
Ya Umar ya saki dariya yana girgiza kai.
“Haba Mami, let’s just go mana. Kin ga Baby ba za ta yarda mu tafi ba”
Abbah ya yi murmushi, sannan ya ce,
“Ai yanzu ya zama dole ki je. Tunda Baby ta yi requesting.”
Mami ta girgiza kai tana murmushi.
“Toh shikenan, ku jira ni.”
Ta juya ta haura sama. Bayan ƴan mintuna kaɗan ta fito sanye cikin kyakkyawar doguwar atamfa mai launin ruwan toka da touches of army green ta yafa masa green mayafi, tana riƙe da ƙaramin hand bag ɗinta.
“Mu je.”
Fuskar Zahra ta haskaka da fara’a
Da suka fito compound, motoci biyu suka riga suka yi warming.
A mota ta farko, Abbah ne tare da Mami.
A ta biyun kuma Ya Umar ne zai tuƙa, Zahra na gefensa.
A baya kuwa, akwai motar masu aiki ɗauke da manyan cartons, foodstuffs, kitchen utensils da sauran kayayyakin gidan.
Mai gadi ya buɗe babban gate, motocin suka fita ɗaya bayan ɗaya.
Bayan tafiya mai ɗan tsawo, suka iso kusa da jami’ar su Zahra
Unguwar ta yi tsit, cike da sabbin gidaje masu kyau da ɗalibai ke zama
Motar Abbah ta tsaya a gaban wani tsararren gida mai kyau, kallon farko zaka masa kasan Estate ne, kowa da side dinsa
Mai gidan ya zo ya buɗe ƙofa cikin girmamawa bayan ya gaisa da Abbah, Students ID ya karba kafin ya barsa suka shiga ciki
Suna shiga a block dinsu Zahra suka yi parking , Zahra ta tsaya tana kallon Estate din cikin farin ciki, School Villa ce
Falon villa din ba babba ba ne, amma yana da yalwa. Daga falon akwai kitchen mai dan girma, sai corridor da ke kaiwa ɗakuna biyu, kowannensu na da toilet da bathroom a ciki
Abbah ya kalli Zahra
“How do you like it?”
Zahra ta yi murmushi har haƙoranta suka bayyana.
“I love it, Abbah.”
Masu aiki kuwa suka fara sauke kaya daga mota bayan Abbah ya basu directive
An fara shigar da babban refrigerator zuwa kitchen, sai microwave, electric kettle, gas cooker mai burners huɗu tare da cylinder, Rice cooker, blender, electric jug.
Kitchen cabinet ɗin dake kitchen din, aka jera plates iri-iri masu kyau, dinner plates, Side plates, bowls, cups, glasses, serving trays da sauran su
Pots masu girma dabam-dabam aka jera cikin cupboard
A gefe guda kuma aka cika shelves da foodstuffs
Buhun shinkafa, semovita, spaghetti, macaroni, Noodles, flour, da duk wani foodstuffs da suka zo mata da shi, har da Kayan miya daban-daban.
Kitchen ɗin ya cika tamkar gidan da za’a kawo amarya ne ciki
A cikin toilet kuwa, masu aiki suka jera sabbin buckets, basin, mop, broom, toilet brush, body wash, hand wash, shampoo, conditioner, toothpaste, toothbrushes, air freshener da Duk wani abu dai da ake using a toilet, komai aka shirya cikin tsari da tsafta
Bedroom ɗin farko kuwa aka shigar mata da akwatinta, aka ajiye shi kusa da wardrobe
Aka shimfiɗa bedsheets masu kyau, pillows aka gyara, duvet aka shimfiɗa cikin tsari
Mami tana bi tana dubawa, tana gyara inda ta ga ya dace, yayin da Zahra ke binsu tana kallon yadda cikin mintuna kaɗan gidan ya koma tamkar gidan da aka daɗe ana rayuwa a ciki
Ta sauke numfashi tana murmushi.
“Ayyah Nagode…”
Ta juyo ta kalli Abbah da Mami.
“Na gode sosai… Allah Ya saka muku da alkhairi.”
Bayan an tabbatar an gama komai, masu aiki suka sake zagayawa gidan domin tabbatar da babu abin da ya rage.
Kitchen ta cika tsaf da kayayyaki, Falon ya kasance cikin tsari
Bedroom ɗinta an gyara shi fes
Toilet ma an shirya su yadda ya kamata
Mami ta sake dubawa sau ɗaya, sannan ta gyada kai cikin gamsuwa
“Alhamdulillah… yanzu gidan ya yi.”
Abbah ya kalli agogon hannunsa
“Toh, mu tafi. Ko za mu bar ku ku huta ne?”
Masu aiki suka fara komawa motocin, su ma suka fito zuwa compound.
Da suka iso bakin motar, Zahra ta matso kusa da Mami ta kama hannunta da hannu biyu.
“Mami…”
Mami ta kalleta da murmushi
“Lafiya Fatima?”
Zahra ba ta amsa ba, ta ƙara matsowa kusa da ita
Ya Umar da ke tsaye jikin motar ya yi dariya.
“Haba Baby, kamar ba gobe za mu sake ganin juna ba”
Abbah ma ya yi murmushi
“Kin san ma gobe idan lectures sun ƙare za ki iya zuwa gida, ba lalle sai weekends ba”
Zahra dai shiru, ta ƙara damƙe hannun Mami
Sai kawai fuskarta ta canza
Nan take hawaye suka fara zubo mata
Ya Umar ya ci gaba da dariya.
“Wai da gaske kuka kike yi ne?”
Amma bai gama maganar ba, sai ya lura hawayen nata na ƙaruwa
Murmushinsa ya ɗan kau
“Mami… Baby fa da gaske take kuka.”
Abbah ya juya da sauri
“Baby…”
Kafin wani ya sake cewa komai, Zahra ta rungume Mami gam, ta fashe da kuka kamar ƙaramar yarinya
“Mami… bana son ku tafi” Muryarta ta karye saboda kuka
“Please… ku zauna ko yau ne”
Mami ta lumshe ido tana shafa bayanta cikin tausayi
“Shhh… Baby na.”
Ta ɗago fuskarta a hankali
“Me ya sa kike kuka haka?”
Zahra ta girgiza kai
“Ban sani ba… amma ina jin kamar zan yi missing ɗinku sosai ne”
Ya Umar ya sauke ajiyar zuciya ya girgiza kai
“Wallahi Baby, kin sa ni ma zan fara kukan zuci”
Abbah ya matso kusa da su, ya shafa kan Zahra cikin kulawa.
“Baby… wannan ma wani sabon mataki ne na rayuwa. Ba wai kin bar gida ba ne. Gida yana nan, mu ma muna nan. Duk lokacin da kika ji kina son ganinmu, ƙofa a buɗe take gare ki.”
Mami ta share mata hawayen da ke zuba
“Kuma kin manta? Kin ce kina son independence saboda result dinki yayi kyau?”
Zahra ta yi ƙaramin murmushi
“Na ce… amma ban san zai yi min wuya haka ba”
Dukansu suka yi murmushi cikin tausayi, Mami ta sake rungumota na ɗan lokaci kafin ta saki ta a hankali, ta ci gaba da lallashinta
Da ƙyar Mami ta samu ta lallashi Zahra ta ɗan saki jikinta.
Ta riƙe fuskarta da hannaye biyu, tana share mata hawayen da suka jika kumatunta.
“Baby… kinga fa.”
Ta yi nuni da ƙofar compound.
“Can compound mates ɗinki za su fara miki dariya. Za su ce ga babbar yarinya nan tana kuka kamar ƙaramar yarinya.”
Zahra ta ɗan yi murmushi cikin kuka, ta goge hancinta.
Mami ta sake cewa,
“Kuma ai su Saudat suna hanya ko?”
Zahra ta gyada kai a hankali.
“Eh… sun ce suna zuwa.”
“Shi kenan. Kafin su iso ma ki gama gyara fuskarki, ko?”
Ta sake gyada kai, duk da hawaye na ci gaba da zuba mata.
Abbah ya matso kusa da ita yana murmushi.
“Baby.”
Ta ɗago kai ta kalle shi.
“Anjima yayanki zai miki transfer. Idan kina buƙatar wani abu, ki saya. Kar ki tsaya kina wahala.”
“Toh Abbah.” Ta amsa cikin sanyin murya.
Ya Umar ya ɗan taɓa kanta.
“Kuma idan wani abu ya taso, ko ƙarfe nawa ne, ki kira ni. Ko da dare ne, zan zo.”
Zahra ta yi murmushi kaɗan
“In Sha Allah.”
Mami ta sake rungumota na ɗan lokaci, sannan ta sumbaci goshinta.
“Allah Ya tsare ki, Ya kiyaye ki daga duk wani sharri. Allah Ya sa albarka a karatunki .”
“Ameen.”
Abbah ma ya yi mata addu’a, Ya Umar ya yi mata bye , sannan suka juya suka nufi motocinsu
Zahra ta tsaya bakin ƙofar compound tana kallonsu.
Sai da motocin suka fita daga unguwar, suka ɓace daga ganinta sannan ta juya da gudu ta koma cikin gidan
Kai tsaye ta shiga ɗakinta, ta rufe ƙofar a hankali
Ba tare da ta cire hijabinta ba, ta faɗa kan katifarta ta rungume pillow da ƙarfi.
Nan take ta sake fashewa da kuka.
Shiru ya mamaye ɗakin.
Sai sautin kukanta kaɗai ke tashi lokaci zuwa lokaci, yayin da take jin gidan da ya cika da hayaniyar su Abbah ɗazu ya koma shiru tamkar ba su taɓa shiga cikinsa ba. Ta lumshe idanunta tana riƙe da pillow ɗin kamar zai rage mata kewar da ta riga ta fara yi wa Abbah, Mami da Ya Umar.
Sai sauke ajiyar zuciya da take yi lokaci zuwa lokaci
Tring… Tring…
Wayarta ta fara ringing
Ta ɗan ɗago kai a hankali, ta share hawayen da bayan tafin hannunta kafin ta miƙa hannu ta ɗauki wayar
Da ta ga sunan Firdausi a screen, ta yi ƙaramin murmushi sannan ta amsa.
“Hello…”
“Madam!” Muryar Firdausi ta zo cike da annashuwa. “Kin isa ne?”
“Eh, na isa! Ina ma gidan yanzu haka, ke kina ina yanzu?”
Firdausi ta yi dariya
“Ina hanya na kusa da school Villa. Gani an area ɗinma. Bari na ƙaraso bakin block ɗin, sai ki fito ki ɗauke ni.”
“Okay, no problem.”
Ta katse wayar.
Zahra ta sauke numfashi, sannan ta nufi mirror.
Ta ɗan gyara kanta, ta sake wanke fuskarta da ruwan sanyi domin rage alamun kukan da ta yi. Ta shafa powder kaɗan, ta ɗauki mukullin gidan sannan ta fito.
Bata jima ba sai ta hango Firdausi na tahowa daga bakin layin
A gefenta kuma akwai wata kyakkyawar budurwa mai kama da ita sosai, suna tafe tare da manyan travelling bags guda biyu da ƙananan handbags sai wasu almajirai da suke biye da su a baya da Kaya a hannunsu
Da zarar Firdausi ta hango Zahra, ta daga hannu tana murmushi, a haka har suka karaso
Suka rungumi juna cikin farin ciki
Firdausi ta yi mata kallon tsokana.
“Anya kuwa baki yi kuka ba? Idanunki sun yi ja fa.”
Zahra ta yi saurin kau da maganar tana dariya.
“Ke dai bari.”
Firdausi ta nuna budurwar da ke tsaye kusa da ita.
“Meet my cousin, Khadija. Ita ma a nan za ta zauna, amma block na gaba.”
Khadija ta yi murmushi
“Nice meeting you.”
“Same here.”
Firdausi ta nuna kayanta.
“Toh Madam, ga kayan nan. Ko za ki tsaya kina kallonmu ne?”
“Ku zo mana.”
Zahra ta yi gaba tana jagorantarsu zuwa block ɗinta.
Suna tafiya suna hira, har suka isa ƙofar apartment dinsu
Ta buɗe ƙofar da mukulli, ta matsa gefe.
“Bismillah… ku shigo.”
Firdausi ta shiga tana jan babban akwatinta, Khadija kuma ta biyo bayanta ɗauke da sauran kayan, almajiran suka ajiye na hannunsu a baranda, Zahra ta basu kudi suka tafi
Da suka shiga falon, Firdausi ta tsaya cak, idanunta na yawo cikin gidan.
“Subhanallah… Zahra!”
Ta juyo tana kallonta.
“Wai wannan gidan Duk saboda karatu ne ko aurar da ke za’a yi a ciki?”
Zahra ta yi murmushi kawai, yayin da Khadija ma ta kasa ɓoye mamakinta tana kallon yadda aka shirya gidan cikin tsari da kyau
Bayan sun gama shigar da kayan Firdausi cikin falo, dukkansu suka zauna kan carpet ɗin saboda gajiya.
Firdausi ta sauke ajiyar zuciya
“Wallahi tafiyar nan ta gajiyar da ni.”
Zahra ta yi dariya
“Ai dole? Ni da na gama Shan kuka na tun ɗazu ma ban gama dawowa hayyacina ba.”
Firdausi ta zaro ido
“Da gaske kika yi kuka?”
Zahra ta ɗan yi murmushi cikin kunya
“Ban sani ba”
Khadija ta yi dariya.
“Ni dai tun da muka zo na lura idanunki sun yi ɗan ja.”
“Shikenan fa, kar ku fara tsokana.”
Dukkansu suka yi dariya.
Suna cikin hira, wayar Zahra ta yi ƙara.
Ta duba screen ɗin
“Aasiya ce.”
Ta amsa.
“Hello.”
“Zahra, mun iso School Villa.”
“Kun iso?”
“Eh, amma ban san block ɗinku ba.”
“Ki tsaya a entrance, gani nan zuwa.”
Ta kashe wayar, ta ɗauki mukulli.
“Mu je mu tarbo su.”
Su uku suka fito tare.
Da suka isa entrance ɗin School Villa, suka hangi Aasiya tsaye tare da wata mata mai kamannin dattaku da kamala. A ƙasa kuwa akwai akwatinta da wasu ledoji.
Aasiya tana hango Zahra ta yi murmushi, suna isa suka rungume juna
Sai Aasiya ta nuna matar da ke gefenta
“Wannan Mamana ce”
Nan take dukkansu suka gaishe ta cikin girmamawa.
Ta amsa cikin fara’a
“Allah Ya muku albarka,”
Zahra ta kama ɗaya daga cikin jakunkunan, Firdausi ta ɗauki wani, Khadija ma ta ɗauki ƙarami.
A haka suka nufi block ɗinsu suna hira.
Da suka shiga gidan, Mamanta Aasiya ta tsaya tana kallon yadda aka shirya komai.
Ta yi murmushi
“Masha Allah… gidan ya yi kyau sosai.”
Bayan sun shigar da kayan, ta juya ta kalli yaran.
“Toh ‘ya’yana, ni zan koma yanzu.”
Aasiya ta rungume mahaifiyarta
“Mama…”
Ta shafa kanta cikin tausayi
“Ki kula da kanki. Ki kula da ibadarki. Kada karatu ya shagaltar da ke daga sallah.”
Ta kalli Zahra, Firdausi da Khadija.
“Ku ma Allah Ya tsare ku. Na ga kun zama kamar ‘yan’uwa, ku riƙa zama lafiya. Idan ɗayarku ba ta da lafiya ko tana da wata matsala, ku tsaya mata. Kada ku bari sharrin mutane ko son zuciya ya shiga tsakaninku.”
Dukkansu suka amsa da
“In Sha Allah.”
Ta ci gaba da cewa,
“Kuma ku tuna, an kawo ku nan ne neman ilimi. Kada ku bari wani abu ya karkatar da hankalinku. Ku riƙa mutunta junanku, ku kiyaye sunayen iyayenku.”
“In shaa Allah Mama” suka amsa
Ta yi musu addu’a sosai
“Allah Ya ba ku sa’a, Ya tsare ku daga duk wani sharri, Ya sa ku gama karatunku lafiya.”
“Ameen.” Suka amsa suna Jin dadi
Da murmushi ta yi musu bankwana, sannan ta juya ta fita
Da dare ya yi, School Villa ya fara yin shiru. Yawancin ɗalibai sun kammala shiga gidajensu
A side dinsu Zahra kuwa, ita, Firdausi da Aasiya ne kawai suka tare yau
Su uku suka ɗan gyara falon, suka jera wasu kayan da suka rage a kan teburi, sannan suka kai wasu kitchen. Bayan sun tabbatar komai ya koma cikin tsari, suka zauna a kan carpet ɗin falo suna huta wa.
Zahra ta miƙa hannu ta ɗauki wayarta ta shiga group ɗin department ɗinsu.
Can sai idanunta suka sauka kan wani sabon announcement.
Ta buɗe shi
Nan take ta zaro ido.
“What?”
Firdausi da Aasiya suka juyo gaba ɗaya suka kalleta.
“Me ya faru?”
Ta sauke wayar tana jan dogon tsaki.
“I didn’t expect this.”
“Expect me?”
Ta miƙa musu wayar
“Ai sun saka lectures gobe 8:00 a.m.”
“Me?”
Firdausi ta karɓi wayar ta karanta.
“Wallahi ba su kyauta mana ba. Yau fa muka shigo.”
Aasiya ma ta girgiza kai.
“Yaushe wai muka saba lectures din safe ne wai?”
Zahra ta kwanta da bayanta jikin kujera tana turo baki.
“Ni har na yi planning zan huta gobe da safe.”
Su uku suka yi dariya, duk da haushin da suke ji.
Firdausi ta ce,
“Shi kenan, madam. Ki tashi da wuri.”
Zahra ta ɗaga hannu
“Allah ya kawo mana ƙarfin tashi.”
Daga nan ta nemo lambar Saudat ta kira.
Bayan ringing kaɗan, ta ɗaga
“Assalamu alaikum Zahratyyy”
Bayan sun gaisa cikin mutunci da faraa
Firdausi ta matsa kusa da wayar.
“Madam Saudat, yaushe za ki shigo?”
Saudat ta yi dariya
“In Sha Allah gobe da safe zan iso.”
“Da gaske?”
“Eh mana.”
Zahra ta ce
“Toh ki yi sauri, kin bar mu kaɗai a nan.”
Suka ɗan yi hira na wasu mintuna kafin suka yi mata sallama.
Bayan sun kashe wayar, Firdausi ta ce,
“Ki kira Suhaima ma pls”
Nan take suka kira ta.
Ita ma tana ɗagawa ta fara dariya.
“Kun dai isa lafiya ko?”
“Eh. Ke fa?”
“In Sha Allah ni ma gobe zan shigo.”
“Da safe?”
“Eh, kafin lectures.”
“Alhamdulillah.”
Suka ci gaba da hira suna dariyar yadda har yanzu ba su yarda ba cewa sun fara wata sabuwar rayuwa ba
Firdausi ta ce cikin murmushi,
“Wallahi har yanzu idan na tuna yau muka dawo off campus, sai na ji kamar mafarki ne.”
Aasiya ta gyada kai
“Ni ma haka.”
Zahra ta yi murmushi.
“Ni kuma har yanzu ban gama missing gida ba.”
Suka sake yin dariya.
Da dare ya ƙara nisa, kowacce ta miƙe zuwa ɗakin domin su huta kafin gobe.
Zahra tana shiga ɗakin, ta zauna a bakin gadonta.
Ta fara kiran Abbah.
Sun yi ɗan hira, ya sake mata nasiha tare da yi mata addu’a.
Daga nan ta kira Ya Umar.
Ya tambaye ta ko komai lafiya, sannan ya tuna mata da ta sa alarm saboda lecture na ƙarfe takwas.
Ta yi dariya.
“In Sha Allah.”
Kafin ta kashe wayar, ya ce
“Good night, Baby.”
“Good night, Ya Umar.”
Sai ta kira Mami.
Muryar Mami kaɗai ta sa fuskarta ta yi laushi.
Sun yi hira na ɗan lokaci, Mami ta tambaye ta ko ta ci abinci, ko gidan ya yi mata, sannan ta yi mata addu’a kamar kullum.
Da ta kashe wayar, Zahra ta yi murmushi.
Ta ajiye wayarta a gefen gadonta, ta kashe fitilar ɗakin, tunda su sun Riga da sun fara bacci
Ta lulluɓe jikinta da duvet, tana jin zuciyarta ta yi sanyi bayan jin muryoyin mutanen da ta fi so.
A hankali bacci ya fara ɗaukarta….