Sashe 7
Faɗime Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai dai kafin ga ɗayansu ya kai ga bata amsa suka ga an yi sama da FAD'IME sannan a ka saketa ta faɗi ƙasa bata gama dawowa hayyacinta ba a ka shiga kifa mata wasu zafafan maruka hagu da dama sai lokacin suka lura da Zulay kacao-kacao da wasu ɗirka-ɗirkan maza biyu dake tare da ita kuma ɗaya daga cikinsu shi ne ya yi ma FAD'IME wannan aika-aika yayin da ɗayan shida da Zulay suke tsaye sai wani numfashin tafarfasan zuciya Zulay ke fitarwa ta riƙe ƙugu tana bin FAD'IME da kallon banza.
FAD'IME da mamaki da kuma ɓacin rai ke nuƙurƙususarta ta miƙe tsaye tana karkaɗe jikinta sannan ta dube mutumin ta ce.
“Waye kai ɗan uwa kuma waye ya saka ka yi gangancin ɓata lafiyar Dangin Jinnu to ina tabbatar maka da ka taɓo tsuliyar dodo domin ba zamu taɓa lamunta ba dole a yi maka hukunci daidai da abin da kayi.”
A tare Laure da Sa'ade suka kalli juna jin kalaman da ke fitowa daga bakin FAD'IME da ta juya musu baya tana fuskantar mutumin sai dai kafin ɗayarsu ta kai ga furta komai Zulay ta wani saki dariyar bosawa tana kallon FAD'IME ɗaiɗai ta ce.
“sannu Dangin Jinnu! Nace sannu Dangin Jinnu to ina tabbatar miki da ba Dangin Jinnu ba ko Dangin ifritu ce ke yau ban ga mai hana na lallasaki ba...”
Kalaman Zulay suka tsaya cak sakamakon juyowa da FAD'IME ta yi tana fuskantarta idanunta sun sauya kala daga na Brown kamar na mage zuwa baƙi mai ratsin ja.
Murmushi FAD'IME ta saki tana faɗin “mene ne na hanzari Aunty kacao-kacao ai sai ki bari nazo kanki ko”
Ta faɗa tana ƙari sawa wurin da Zulay take tsaye jikinta na rawa amma duk da hakan ta yi ƙarfin halin faɗin. “ai kuwa dole nayi hanzari tun da har kika shiga gonata a tunaninki zan bari inaji ina gani ne ki auremin miji hahaha ai bazan taɓa bari hakan ta faru ba shi ya sa ma na hayo waɗan nan ɗirka-ɗirkan mazan majiya ƙarfi su lallasa min ke ta yadda ba zaki ƙara moruwa ba har abada. John a fara aiki.”
Zulay ta ƙare maganar tana sakin dariyar mugunta tare da kallon Wanda ke kusa da ita, ta yi tana yi masa nuni da FAD'IME dake tsaye ta harɗe hannu ko'a jikinta da jin kalaman Zulay..
*FAƊIME...💋🌸💕*
_(Dangin Jinnu)_
©By Zahrah Royal Star & Nainarh KD
06
Aikuwa mutumin da Zulay ta kira da John gadan-gadan ya nufi FAD'IME yana sakin dariyar ƙeta cike da annashuwa na ganin banza ta faɗi Yarinya kyakkyawa haka a ɓagas.
Sai dai me? Taku ɗaya biyu ya yi a na ukun ƙafarsa ta maƙale ya kasa gaba bare baya duk kuwa da yadda yaso sai dai duk da hakan bai haƙura ba ganin wanda suke tare shi ma ya nufa Faɗimen gadan-gadan yana suɗe baki ya sa ya kai hannu zai fizgota ai kuwa saukar hannunsa saman kafaɗar Faɗime ya yi daidai da wani irin azababen duka da a kai masa a gadon baya Yayin da hannun nasa yaji shi tamkar ya sauka a kan wuta saboda wani raɗaɗin azaba da ya ziyarce shi ai kuwa ba shiri ya durƙushe a wurin tare da fasa ihu jin an ci gaba da zuba masa duka a gadon baya.
Cike da takaici ɗayan yaja wata doguwar tsuka yana kallonsa ya ce. “amma fa gaskiya John ban taɓa sanin haka kake ba ai ka bada maza Bara kaga yadda cikakken Namiji yake ji da Mace irin wannan kucakar ƴar ƙauyen domin ba Dangin Jinnu ba ko ƴar sarkin Jinnun ce da kanta tun da har an biyani ban ga abin da zai sa na kyaleta ba.”
Ya ƙare maganar tare da ƙari sawa wurin Faɗime har da gudunsa yana wani ihu tamkar ɗan kwallon da ya sama nasara.
Baya Faɗime ta yi daidai ya miƙo hannunsa da niyyar fizgota ta yi saurin sa hannunta ta riƙe hannun nasa da kyau tare da murɗewa ji kake Hannun ya bada ƙara alamar an karya shi ai kuwa sai ya zube shima a ƙasa yana zambaɗa ihu tare da magiyar ta saki Hannun.
Sakin hannun nasa Faɗime ta yi tare da nufar Zulay da ta fara ja da baya cike da tsoro baki na rawa ta ce.
“ku...kuyi haƙuri na tuba Wallahi nabi Allah na kuma biku haƙiƙa na yarda Faɗime Dangin ku ne kuma ba wanda ya isa yaja da ita ya zauna lafiya...”
Zulay ta kai maganar wani fitsarin tsoro yana ƙoƙarin kwace ma ta hawaye da macijina sun gama wanke baƙar fuskarta.
Dariya Faɗime take tana dunƙule hannu ta ce. “me ma kika ce yau zaki saka a mayar dani ta yadda ba zan ƙara moruwa ba ko? To kafin ki mayar dani haka ni bara na fara canza miki halitta tukunna.”
Faɗime ta kai maganar tare da saka yatsunta mai cike da ƙumba ta karce gefe da gefe na fuskar Zulay ai kuwa take wurin ya fara fidda jini kaɗan kaɗan Zulay kuwa ta saki ihun azaba tana riƙe fuskarta tare da birgima a wurin faɗi take.
“jama'a ku kawo ɗauki Faɗime ta kasheni zane ta yi min a fuska da zaƙwa-zaƙwan ƙunbarta”
“mun shiga uku Faɗime ki kyalesu haka kizo mu gudu tun kafin kiyi kisan kai.”
Cewar Laure cikin tashin hankali tana janyo Faɗime ai kuwa da gudun bala'i suka bar wurin gudu suke basu dakata ba sai da suka shiga kwanar da zai sadasu da anguwansu Laure sannan ne suka tsaya kowaccensu tana faman sakin numfarfashi na gudun da suka sha.
Laure ta ce.
“faɗime kin faɗar min da gaba wallahi nayi zaton da gaske ba ke ba ce.”
Ita kuwa Sa'ade cewa ta yi.
“wai Allah su Zulay kacao-kacao kuma shikenan an yi ma ta zanen barebari.”
Gaba ɗaya suka kwashe da dariya.
Sa'ade ta ƙara da faɗin. “wai amma Faɗime ba zakiyi wani abu ba haka kina ji kina gani zaki bari gobe a ɗaura miki Aure da wancan Ɗan Abban bayan kin fi kowa sanin halinsa na neman Mata?”
Dariya Faɗime ta ɗan yi sannan ta kallesu gaba ɗaya ta ce.
“a tunaninku zan bari hakan ta faru ne? Ai ba zata taɓa saɓuwa ba Bindiga a ruwa...”
“to yanzu mene ne abin yi?”
Laure ta faɗa cike da damuwa.
“ai tuni na samo mana mafita, ku matso kuji.”
Cewar Faɗime tana sakin dariya ba musu suka ƙari sa ƙasa-ƙasa ta sanar da su shirin da ta ratsa ai kuwa a tare suka saki murmushi cike da farin ciki Faɗime ta ce.
“kun ga dama yazo mana a daidai ke nan ko?”
Gaba ɗaya suka ce E, Laure ta ƙara da faɗin. “lallai Faɗime ƙwaƙwalwarki na ja.”
“hhhh to an faɗa miki ni ɗin jahila ce, ku ƙara matsowa ma kuji wani abu...”
Faɗime ta faɗa cike da fariya sannan ta ci gaba da sanar da su yadda shirin nasu zai wakana basu suka rabu ba sai da suka gama tsara komai da zasuyi sannan suka rabu bayan Faɗime ta gama jaddada musu a kan gobe su shirya da wuri sannan ne kowacce ta wuce gida.
______
Ba sallama ta faɗa gidan abin ta tana ƴar waƙarta cike da nishaɗi tana lura da irin kallon da matan gidan ke yi ma ta suna gulma ƙasa-ƙasa amma ta yi kamar bata gani ba sai ma dariya da take yi ta shige Ɗakin Inna Fatuh sai dai bata tarar da ita ba da alama bata dawo ba daga Anguwan da ta tafi hakan ya sa Faɗime ta yi kwanciyarta ba abin da ya dameta ba'a jima ba kuwa bacci mai daɗi ya yi awon gaba da ita duk da lokacin yammaci ne kuma ko can anjima da Inna Fatuh ta dawo ta tarar da ita bata yi yunƙurin tashin ta ba domin a Ganinta hakan babu amfani sai ma tashin hankali da zai biyo baya dan kuwa fitan da ta yi ta sama labarin da ya girgizata a kan batun Auren Faɗime da Ɗan Abba ta kuma fusata da yadda labarin ya zagaye ƙauyen amma ita bata da labari yanzun ma ta dawo ne tana jiran Malam Yahaya ya dawo daga kasuwa ta turkeshi sai ya sanar da ita dalilinsa na ɓoye ma ta batun auren Faɗime da ya yi.
Ai kuwa an yi sallar isha'i ba jimawa Malam ya shigo gidan kuma har lokacin Faɗime bata tashi ba dan so take ta yi bacci ta darje dan akwai abin da ta shirya zata yi a daren yau shi ya sa ta nutsu tana bacci cikin kwanciyar hankali domin ta rantse yau babu mai rintsawa a gidan tun da har a ka munafurceta yau ba zata kyale kowa ba kowa sai yaji a jikinsa tun da har ita za'a ɓoye ma ta magana a kan aurenta ke nan da sai dai taji labarin an ɗaura aure...
Kai tsaye Ɗakin mahaifiyarsa Inna Fatuh Malam Yahaya ya wuce a nutse ya Gaishe ta tare da fara kama kame a kan ta yadda zai sanar da ita maganar dake tafe da shi dan ya yanke shawarar sanar da ita maganar auren in yaso ya lallaɓata ta yarda ita kuma Faɗime zuwa da asuba zai zaunar da ita ya yi ma ta nasiha mai ratsa jiki sannan ya sanar da ita maganar auren.
Da ƙyar ya samu ya iya zayyanewa Inna Fatuh kalaman dake bakinsa.
Tun da ya fara maganar har ya kai aya Inna Fatuh ta zuba uban ta gumi hannu bibbiyu tana saurarensa ba tare da ta katse shi ba har sai da taji ya kai aya sannan a fusace ta ce.
“ka gama? Nace ka gama surutun banza da wofin e mana banza da wofi mana domin ba zan lamunce ba, amma yahayah ka bani mamaki har lalacewar taka ta kai haka ban sani ba?”
Sai kawai Inna Fatuh ta saka kuka tana ci gaba da faɗin.
“shikenan zama bai sameni ba, Lami ta gama dani Lami ta mallakemun ɗa wayyo ni Fattuh.”
Shi dai Malam Yahaya yana zaune gefe abin duniya ya haɗe masa goma da ashirin domin ji yake muddun bai aurar da Faɗime ba a gobe to fa Akwai matsala, da ƙyar ya iya furta.