← Book details Faɗime Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 13

Sashe 6

Faɗime Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abin Duniya da halin FAD'IME ya gama isar Malam Yahaya hakan ya sa ya yanke shawarar aurar da ita domin ta kai minzalin Auren har ma ta wuce domin shekarunta goma sha shida tana gab da shiga na sha bakwai sa'anninta ma zalla duk an aurar da su sai waɗan da ba'a rasa ba irinsu Sa'ade ƙawayenta da suka addabi ƙauye. Da wani mutumi mai suna Ɗan Abba Malam ya yanke shawarar aurar ma FAD'IME kuma hakan ya biyo bayan maganganu ƙarya da gaskiya a kan FAD'IME ne da Lami ta faɗa masa kuma ita ta nema da ya aura wa Ɗan Abba FAD'IME kuma ba musu Malam ya amince domin ta riga ta gama da shi sai abin da take so shi yake yi ba tare da musu ba koda kuwa hakan shi bai kwanta mishi ba sai dai ganin Ɗan Abba mutumin kirki ne a idon kowa na ƙauyen, kuma ma har Mata yake da ita da yara biyu shi ya sa ba tare da wani dogon bincike ba Malam ya yarda zai aura masa FAD'IME dama kuma sara ne a kan gaɓa domin Ɗan Abba ya daɗe da mutuwa a kan son FAD'IME sai dai bata ma san yanayi ba kuma ko yanzu da Mahaifinta ya bashi ita sai wani farin ciki ya cika shi shikenan zai sama muradin ransa FAD'IME ba tare da ɓata lokaci ba a ka tsayar da lokaci da Ranar Aure nan da sati ɗaya kuma a ka fara shirya shirye sai dai a ɓoye ba tare da FAD'IME da Inna Fatuh sun sani ba, gudun abin da zai je ya dawo ya sa Malam ya ɓoye musu batun don ya san muddun FAD'IME ta ce bata so to fa ko sama da ƙasa zata haɗe ne Inna Fatuh ba zata taɓa yarda a ɗaura Auren ba.

Sai dai abin da Malam bai sani ba shi ne tuni Ɗan Abba da Inna Lami sun baza labari a ƙauye cewar FAD'IME zata aura Ɗan Abba kuma tuni gari ya ɗauka daga masu fatan Alkhairi sai masu kushe abin, kuma tuni labari ya koma kunnen Zulay Matar Ɗan Abba ai kuwa tsabar kishi na hauka yi ta yi kamar ta zare ta rasa inda zata saka kanta dan baƙin ciki..

*Nnamdi Azikiwe International Airport, Abuja Nigeria.*

A jere dakakku kuma tsadaddun motocin guda biyar suka faka a harabar airport ɗin securities ne suka fiffito suka tsai tsaya suna jiran ƙari sowar wanda suka zo tarba ba'a ɗauki lokaci ba jirgin ya yi landing fasinjoji suka fara sakkowa ciki kuwa da har da shi dogo ne kuma kyakkyawa ajin farko ɗin nan yanayin fatarsa fari ne mai kyau kana ganinsa kaga wanda hutu ya sama wuri ya zauna tare da shi, sannan jikinsa a murɗe yake kai da gani ka san yana samun kulawa mai kyau ta hanyar yawan motsa jiki, a dake yake tafiya sanye cikin expensive luxury suits Dolce & Gabbana ga wani glasses na gayu da ya maƙala saman fuskarsa, yayin da gefe guda wasu Kyawawan yara ne da ba zasu haure shekaru Biyar ba a duniya mace da namiji cikin shiga ta alfarma suke tare da shi ga kuma tsananin kamanni da suke, cikin taku irin na nutsuwa da salo suka ƙari sa wurin motocin da sauri security ya buɗe masa motar dake tsakiyar ya shiga bayan ya saka yaran ciki, sannan gaba ɗaya suka koma cikin motocin suka tayar a nutse suka bar airport ɗin.

*SAL Estate, Shehu Shagari Way Abuja Nigeria.*

Alhaji Sa'id Ahmad Lamiɗo da a ka fi sani da SAL cikakken ɗan kasuwa ne kuma ɗaya daga cikin manyan mutane da a ka san da zamansu a faɗin Afirka yana da mata biyu da yara shida maza uku mata uku, Matarsa ta fari ita ce Hajiya Salima yaranta huɗu maza uku sai mace ɗaya auta, sai kuma Hajiya Haleema da ke da yara biyu mace da Namiji yaran Alhaji Sa'id Ahmad Lamiɗo sun taso ne cikin tarbiyya da mutunta juna shi ya sa ko bayan da kowannensu ya gama karatu duk sai suka taimakawa mahaifinsu ta hanyar ci gaba da tafiyar da harkokin kasuwa cikin ilimi da hikima ai kuwa lokaci ƙanƙani cikin amincewar Ubangiji arzikin Alhaji Sa'id Ahmad Lamiɗo ya ƙara haɓaka sosai, ko zuwa lokacin da kowanne daga cikin yaran nasa ya yi Aure sai ya gina musu tanƙameman Estate da suke zaune ciki har wa yau da aka saka ma suna SAL ESTATE dake Shagari Way cikin garin Abuja.

Zuwa lokacin da yaran Alhaji Sa'id Ahmad Lamiɗo SAL suka fara tara iyali ne kuma matsaloli ya fara kunno kai hargitsi da rashin fahimta ya fara shiga tsakaninsu duka a kan dukiya sai dai basu taɓa bari mahaifinsu ya fahimci hakan ba, amma ta ciki na ciki kowa shi ya san shirin da yake yi a kan ɗan uwansa hatta yaran Alhaji Sa'id Ahmad Lamiɗo mata a nan Estate ɗin suke zaune da mazajensu kuma hakan ya samo asali ne daga wurin Alhaji Sa'id Ahmad Lamiɗo da ya buƙaci hakan domin burinsa bai wuce ganin iyalansa kansu a haɗe ba kuma suna zaune wuri guda a kaf cikin iyalan Alhaji Sa'id Ahmad Lamiɗo Mutum ɗaya ne baya zaune a wannan Estate ɗin hasali ma baya ƙasar gaba ɗaya shi ne yaron Alhaji Sa'id Ahmad Lamiɗo na uku yana zaune ƙasar Faransa da Matarsa da iyalansa har zuwa wannan lokaci.

Safiuddin Ahmad Sa'id Lamiɗo wanda a ka fi sani da Young SAL sakamakon nickname ɗin sa da ya kasance dai dai dana kakansa wato Mahaifi a wurin mahaifinsa, Safiuddin ya kasance jika na huɗu a familyn SAL sai dai ya kasance daban da sauran Jikokin familyn shi ya sa kakansu Alhaji Sa'id Ahmad Lamiɗo yake kiransa da gagabadau yayin da sauran Jama'a ke kiransa da SAL, Safiuddin Ahmad SAL ya kasance mutum ne na daban da tsarinsa da yanayin Rayuwarsa yasha banbanta da na sauran jikokin SAL family domin ya kasance bai damu da shiga harkar kowa ba kuma Mutum ne mara san hayaniya da kuma surukutu shi ya sa wasu ke kiransa da Miskili sai dai hakan bai dameshi ba rayuwarsa yake yadda yake so sam mata basa gabansa abin da ya saka a gaba shi ne aikinsa na Soja ta gefe guda kuma shi ne mai kula da Babban Companyn SAL dake ƙasar America idan yana can idan kuma ya dawo Nigeria to shi ne mai kula da Companyn SAL na ɗaya dake ƙasar, shi ya sa ya zokale idon da yawa daga cikin Familyn SAL musamman masu jin haushinsa da ganin gatan da Kakansu da ya ɗaura shi a kan muƙamin ya yi masa a ganinsu su ne suka cancanta tun da sun girme shi baya da haka suna da Aure shi kuwa Bama auren a gabansa hakan ma ya sa shi da kansa Tsoho Alhaji SAL ya haɗa Safiuddin Young SAL da ɗaya daga cikin jikokinsa mata da yake ji da ita wato Fidaus ya haɗa su da Safiuddin a kan su fahimci juna sai dai Safiuddin duk da ya kwashe shekaru baya ƙasar hasali ma bai san wacece Fidaus ɗin ba kasancewar a ƙasar Faransa ta taso ta yi karatu a can wurin Yayan Mahaifiyarta dake can, amma Safiuddin ya ce ya yarda da zai aureta koda basu san juna ba tun da har Tsoho Alhaji SAL ya yaba da ita shikenan ai kuwa ba ƙaramin farin ciki Tsoho SAL ya yi ba kuma ba tare da ɓata lokaci ba a ka tsayar da Ranar Auren Safiuddin da Fidaus wata guda ke nan kuma a halin yanzu Safiuddin AkA SAL ya dawo Nigeria ne hutu daga nan idan an yi bikinsa da Fidaus nan da watanni uku ke nan masu gabatowa zai koma da Matarsa can inda yake zaune. Sai dai gefe guda ya dawo da abin mamaki su ne waɗan nan twins mace da namiji da ya dawo da su bayan kuma ya kasance bai taɓa Aure ba, baya da haka akwai wani babban dalilin na dawowar Safiuddin a halin yanzu...
WANNAN KE NAN.

*ƘAUYEN KINKIBA, SOBA LOCAL GOVERNMENT, KADUNA STATE NIGERIA*

*FAD'IME POV*

Tafiya suke ita da su Sa'ade buguzun buguzun gasu biji-biji sai ɓallar raken da suka samo a can fadama gonar ɗan mai gari suke ba abin da ya damesu sai ma fira da suke kwasa cike da garɗin rake har wani waƙa ma suke biyawa wai ita ALJANNATA na mawaƙi Auta Waziri.
Gefe guda Laure da Sa'ade ne ke faman ƙusin-ƙusin sun rasa ta inda za su sanar da FAD'IME maganar da ke bakinsu a kan labarin Aurenta da suka samu duk da sun fahimci duk abin da a ke bata ma sani ba, sai da ƙyar Laure da ta shanye raken hannunta ta duba FAD'IME dake biye sautin waƙar cike da kwarewa yadda ka san ita ta raira ta ce.

“Wai FAD'IME duk abin da yake faruwa a ƙauyen nan baki sani ba?”

Ba tare da FAD'IME ta gama shanye raken da ga gabza ba ta ce.

“ke Laure banason gulma fa ki bar wani nuƙu-nuƙu ki fito ki sanar dani mene ne yake faruwa...”

“au da gasken baki sani ba ke nan to dai gobe aurenki da Ɗan Abba Mijin Zulay kacao-kacao gaba ɗaya ƙauye labari ya ɗauka a kan za'ayi miki Auren dole da Ɗan Abba Mijin Zulay kacao-kacao....”

“Kutm*r ub*a! kayyasan can...”

Zagin da FAD'IME ta mulmulo ya sa Sa'ade da ta katse ta tana bayanin ta yi tsitt tana zaro ido don kuwa a yadda FAD'IME ta yi wannan ashariya zata ɗauka mutanen nata ne suka motso....

“wata FAD'IMEn kike magana a kai! Sa'ade kada ki ce mini ni FAD'IME kike nufi?”

FAD'IME ta yi maganar idanunta a wani wawware tana duban su Laure da Sa'ade gaba ɗaya sai dai wannan karon ba a zafafe ta yi maganar ba, ba kuma cikin nutsuwa ba sannan ta yi maganar ne tana nuna kanta tare da sakin wani shu'umin murmushi.
Chapter 6 · 0% Book details