← Book details Faɗime Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 13

Sashe 11

Faɗime Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Haba Fad'ime wai kuwa kin san irin gidan da za'a kaiki kike fad'in baki zuwa, gida ne irin na y'an gayu mai bene sama da k'asa, gashi har makaranta za'a sakaki, kiyi kallon abubuwan duniya, amma kina zaune a k'auyen nan miye zaki sani a duniyar nan, da abunda ke cikinta, koni nan da dai basa son Manya ai ni ce zanje bake ba wallahi, ki dai yi shawara Fad'ime kar ayi tafiyar nan babu ke".

D'an shuru Fad'ime tayi, tana tunani, hak'ik'a tana son birni ita mayiyar son zuwa cikin birni ce, da son ganin abunda ke cikin birnin, to amma kafin tashinta tayi wani mafarki wata mata tazo mata tana jaddada mata cewa karta sake ta yarda da tafiyar da Inna Lami take ta matsawa tayi, tana gama fad'a mata haka ta b'ace shine ita kuma ta farka kawai ta iske Inna Lami a cikin d'akin, suna magana akan tafiyar da aka gama gargad'inta da kar taje a cikin baccinta.

Inna Lami dake kallon Fad'ime tana d'an murmushi ganin maganar tada fad'a mata kamar tayi tasiri a cikin ranta, domin ganin yadda ta fad'a duniyar tunanin.

"Uhuhmm kuma fa hakane Inna Lami tabbas ina son ganin yaya birni yake, domin idan na dawo naba K'awaye na labari, domin garin nan mutane d'ai-d'ai ne ke zuwa birni".

Fad'in Fad'ime tana duban Inna Lami dake murmushi sosai a yanzu.

"Yawwa ashe kin gane, kuma idan kece kika fara zuwa birnin nan kamin su, ai kin wuce da ajinsu nesa bama kusa ba, zaki dawo y'ar gayu a k'auyen nan namu, ki dawo kinfi kowa iya d'aukar wanka".

Dariya Fad'ime ta saki tana sakkowa ta kalli Inna Fatuh data saki baki da hanci tana duban Inna Lami dake murmushi kamar ta Allah.

"Inna Fatuh ki had'a min kayana zanje birnin aikatau d'in yanzu".

Rik'e baki Inna Fatuh tayi ta dafa kafad'ar Fad'ime tana ji gabanta na d'an fad'uwa da tafiyar Fad'imen, domin Allah ya sani har cikin ranta bata aminta da tafiyar ba, bata kwanta mata a rai ba.

"Fad'ime miye ya canza miki tunanin a d'an k'ank'anin lokaci haka?, ke nan yanzu har Lami zata gaya miki magana ki yarda lokaci d'aya, har tayi sanadiyar canza tunaninki a d'an lokaci haka?".

Turo baki Fad'ime tayi tana ji itafa Allah wallahi saita je birnin nan, domin Inna Lami ta gama saka mata rai da abubuwan k'aryar data shinfid'a mata.

Ganin rigimar da take son farawa yasa Inna Fatuh cewa da sauri.

"Allah ya baki hakuri bari na had'a miki, indai birni ne gaki can kinje ai, ni bana son ganin b'acin ranki ai. Duk dai inda kike ai k'aryar mutum ya iya cutar dake a'ato, idan ma mutum ya manta gara ya tuna".

Ta k'are maganar had'e da gogar zana da take ma Inna Lami.

Inna Lami kuwa tana jinta sai ma jawo kayan Fad'ime tayi ta cewa bari ta had'a mata da kaina ma, ba sai Inna Fatun ta had'a ba.

Abunda Inna Lami take da zumud'in tafiyar nan ta Fad'ime fa, k'ara ba Inna Fatuh mamaki yake had'e da tsoron wani abu take shiryawa wallahi.

Auta ne yayi sallama a k'ofar d'akin Inna Fatuh yana cewa.

"Inna ki fito ga Haj Bintoto can fa ta fara gajiya da jiranki. Ita kuma Fad'imen da ake jira dan ubanta bata fitowa ne ita zatai jira ne?".

Fad'ime data dawo d'akin yanzu bayan ta wanki idonta tayi tsakar tsaka tsami tana saka kaya da sauri sai zumud'in tafiyar take sosai. Turo baki tayi tana murgud'a ma k'ofar d'akin Inna Fatuh baki had'e da harara kamar Auta ne take gani wajan.

Inna Lami da sauri ta jawo hannun Fad'ime da k'ullin kayanta ta ce.

"Kai Auta ina ruwanka da ita, bana son irin haka fa tom".

Auta dake murmushin gefen baki shima yabi Fad'ime da harara yana cewa.

"Kai yau dai zamu huta da kawo k'arar shaid'aniyar yarinyar nan, haba mutum yana mutum amma kamar Aljani tsabar jaraba da rashinji, anya Fad'ime ba rabi aljan rabi mutum aka haifeki ba kuwa?".

Dak'uwa Inna Fatuh tayi masa tana binsa da wata uwar harara tana cewa.

"Kai Auta ka fita ido na, na rufe na rantse da Allah ka kiyaye ni fa".

Gaba Auta yayi bai tankama Inna Fatuh dake masa masifa har lokacin ba.

Inna Lami dake cikin d'akinta bayan ta fito da Fad'ime ta barta waje ita dasu Inna Fatuh da Auta.

Ta kalli Bintoto a hankali tana cewa.

"Bintoto kin tabbatar gidan yankan kai zaki kaita?".

Bintoto dake murmushin cin nasara da samun kud'in da zatai idan ta kai Fad'ime wajan Alhaji Bukhar, ba k'ananun kud'i zata samu ba, harma da ita Inna Lami za'a bata wani abu daga ciki, shi yasa ma ta amince.

Kallabin dake kanta ta k'ara turo shi gaba, domin daka kalli yanayin Bintoto zaka shaida y'ar duniya ce ta gidan gaba, sai wani taunar chingum take idonta kansa an baura masa kyalli, ta ce.

"Haba Lami sai kace baki sanni ba, ai nake gaya miki idan Fad'ime ta tafi ta tafi kenan bazata tab'a dawowa ba, kuma nake sanar dake ba gidan yankan kai zan kaita ba, kamar suna anfani da mata ne suna tsafi dasu, kamar k'ungiyar asiri dai haka, ai kina jin labarinsu ko?".

"Eh tabbas muna jin labarinsu, dama duk masu kud'in nan dake cikin birni ai da yawansu ba kud'in Allah da Annabi bane, na tsafi ne".

"Yawwa, tun da kin gane mubar maganar a nan saina dawo zan taho miki da naki kason, domin Alhaji Bukhar ya dad'e yana neman yarinya budurwa mai shekaru irin na Fad'ime ba'a samu ba, sai ni ya ba cigiyar ya ce idan har na samo masa zai bani kud'i masu yawan gaske, dan haka kema dole ki samu kud'i masu yawa daga ciki".

Wani kalar murmushi Lami ta saki tana kallon Bintoto kamin zatai magana suka ji muryar Inna Fatuh na cewa.

"Wai Ina Lamin ne, da ita Bintoton miye kuke k'ullawa ne cikin d'akin, idan ba rashin gaskiya ba ai sai ku fito waje kuyi maganar da zakuyi mana".

Da sauri Lami ta kamo hannun Bintoto suka fito tana fad'in.

"Haba Inna Fatuh miye zamu shirya kuma?, kawai fa ina sake gaya mata ne ta kula da Fad'ime sosai".

Wani kallo kawai Inna Fatuh tabi su dashi tana tab'e bakinta ta ce.

"Hmmmm Ohho maku dai, idan ma akwai abunda kuke k'ullawa gara tum wuri kuma daina, kuje tun wuri ku warware abunda kuke shirin aikatawa domin dai Fad'ime ba mutum ce kamar kowa ba da......
Da hanzari Inna Lami ta tari hanzarin Inna Fatuh tana cewa.

"Inna Fatuh mi ya kawo duk wannan canzan Kuma?".

"Uhuhmm ai kin san miye nake nufi dashi Hajiya".

Inna Fatuh ta k'are maganar tana b'alla masu harara su duka.

Bintoto data gaji da maganar ta su ta kalli Fad'ime dake tsaye sai murna take ita ta ce.

"Fad'ime muje ko gari na haske bamu bar cikinsa ba kuma, na so iyanzu mun kusa cikin garin Kano wallahi".

Rik'o hannunta Bintoto tayi. Inna Fatuh kamar zata fashe da kuka tayi saurin cewa.

"Baza'a bari Babanta ya dawo suyi ban kwana bane?, kofa K'awayenta basuyi sallama dasu ba".

Inna Lami da sauri ta ce "a'a Inna Fatuh indai Malam ne zan sanar dashi da kaina, dama kuma ai yasan da tafiyar tasu a yau d'in, K'awayenta kuma ai Inna Fatuh nake ganin kin san tun jiya ta sanar dasu, ai sunyi bankwana tun jiyan ko Fad'ime?".

Ta k'are maganar had'e da duban inda Fad'ime take rik'e da hannun Bintoto.

"Eh munyi sallama dasu idan sunzo sun tambaye ni Inna Fatuh ki ce na tafi birni saina dawo, zanyo masu tsaraba idan zan dawo".

Wasu y'an hawaye Inna Fatuh ta share tana fad'in.

"Ai shikenan Fad'ime Allah Ubangiji ya tsare ki da tsarewarsa, za'a gaya masu hakan".

Inna Lami ta tab'e baki a fakaice tana dannama Inna Fatuh harara.

Har k'ofar gidan Inna Lami da Auta suka raka su Bintoto Inna Fatuh kuwa k'in fita tayi.

___________________
Tafiya suke sun mik'e hanya domin zuwa inda zasu hau mashin domin fitar dasu daga K'auyen, babu yawan mutane a hanyar sai y'an tsiraro suma sai a d'auki lokaci basu had'u da wani ba.

Fad'ime kamar ance ta waiga ta hango matar nan da tayi mafarkinta d'azo cikin bacci, yanzu ma tana nesa da ita take ce mata.

"Fad'ime karki sake kibi Matar nan zuwa birni, bana fad'a miki ba karki sake kije?".

D'an sake waro ido waje Fad'ime tayi, kawai saita sami kanta da d'aga k'afad'arta tana cewa.

"Ni sai naje wallahi, haka kawai nayita zama a K'auye nida nake so na zama y'ar gayu na auri mai kyau d'an gidan y'an gayu, wallahi saina naje".

"Karki sake ki bita zakiyi nadama Fad'ime".

Turo baki gaba tayi ta sake d'aga kafad'arta alamar bazata ji maganar abunda take gaya mata ba.

Bintoto dake rik'e da hannun Fad'ime jin tana magana ita d'aya yasa Bintoto juyowa a zabure tana kallon inda Fad'ime ke kallo tana magana, sai dai bata ga komai ba, hasali ma maganar Fad'imen ce kawai take ji.

D'an girgizata Bintoto tayi tana cewa.

"Ke Fad'ime kanki d'aya kuwa kike magana ke d'aya".

Da sauri Fad'ime ta juyo inda Bintoto take tana murmushi ta ce.

"Babu komai wata mata ce fa na gani take ce min wai kar na biki zuwa birni".

A haukan Bintoto bata kawo komai a ranta ba saima cewa tayi.

"Hhhh so take tayi Miki bak'in cikin zuwa birni ne, manta da ita kawai muje waje na k'ure mana".........✍️

*FAƊIME...💋🌸💕*
_(Dangin Jinnu)_

©By Nainarh KD & Zahrah Royal Star

10
Last Free Page.

*ABUJA CITY*
Chapter 11 · 0% Book details