← Book details Faɗime Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 13

Sashe 12

Faɗime Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun da suka shigo garin Abuja bakin Fad'ime yake a washe tun kafin su fito daga motar ta baza idanu tana ƙare ma ko'ina kallo irin na ƙauyanci. Ta juya bakiwashe domin ta yi ma Hajiya Bintoto magana sai dai kafin ta kai ga furta komai Hajiya Bintoto ta yi wuff tare da fesa ma ta wani abu kamar turare a fuska, galala Fad'ime ta yi tana dubanta da mamaki sai dai kafin ta yi wani yunƙuri tuni idanunta sun fara lumshewa wani nannauyar bacci ya yi awon gaba da ita, sai ta faɗa jikin Hajiya Bintoto.
Shu'umin murmushi Hajiya Bintoto ta saki suna haɗa ido da drivern Motar suka sake sakin murmushi a tare dama iya su kaɗai ne a motar tuni sauran mutanen sun fi ce, tada Motar drivern ya yi da dama shi ne abokin cin mushen Hajiya Bintoto duk wata bak'ar harƙalla da take yi tun daga kan safaran ƴan mata da yara ƙanana da take yi duka da taimakonsa ne.
Hanya ɗoɗar ya ɗauka yana tsala gudu tun suna kan titi har suka fara shiga daji-daji sai da suka yi tafiya mai tsawon gaske tukunna suka iso bakin wani kogo da bazakayi tunanin akwai wani abu ciki ba.
Fitowa suka yi daga Motar Hajiya Bintoto tana riƙe da Fad'ime ita da drivern suka ƙari sa bakin kogon sai dai basu shiga ba suka tsaya sannan Hajiya Bintoto ta ciro waya tare da dannawa Alhaji Bukhar kira bugu ɗaya ya ɗauka yana zuba ma ta kirari da. “sai ke uwar mata kuma uwar duk wasu masu harƙalla kinci dubu sai ceto mai faɗa da cikawa Hajiya Bintoto ikon Allah kin faɗa kuma kin aikata.”
Yanayi mata kirarin ne yayin da kan Hajiya Bintoto yake ƙara girma ɗan kwaran gwan tanajin ita ɗin ta kai, yayin da ta gefan Alhaji Bukhar tsananin farin ciki ne ya sa yake yi ma ta wannan kirari dan ya san in yaji kira daga gare ta to fa tabbas ta samu ne bare kuma yanzu da suka yi za su haɗu ta bashi Yarinyar da a ka samu shi kuma ya bata cikon kuɗin dan kuwa ya bata adibas.
“ni dai yanzu ba wannan ba Alhaji Bukhar gamu fa a bakin kogo nasan kuma a daidai wannan lokaci kana ciki shi ya sa nace da Rabilu Driver mu taho nan kai tsaye.”
Hajiya Bintoto ta kai maganar tana taunar cingum har da bada sautin. Tiss! Tass! Toss!!
Dariya Alhaji Bukhar ya yi ya ce.
“kwarai kuwa ina ciki ko zaki ƙari so ciki ne?”
Ya tambaya da sigar wasa.
Hajiya Bintoto ta zaro tana faɗin.
“wa? Ni wai? Allah sitira ai in ka ganni a lahira kaini a ka yi kai dai ka ƙari so kawai ga Yarinya lafiyayya an samu sweet 16 to 17 years da ita.”
Wata uwar dariya Alhaji Bukhar ya yi tare da amsa ma ta da faɗin. “gani nan tafe”
Ta katse kiran ba'a jima ba sai gashi ya fito daga kogon da in za'a kashe Hajiya Bintoto da Rabilu Driver basa ce ga taƙamaimai ta inda ya fito ba.
Koda ya ƙari so Hajiya Bintoto ta nuna masa Fad'ime da ke sharar bacci, ya yi dariya yana suɗe baki ganin kyakkyawar yarinya haka. Ta ke a wurin ya tura ma ta cikon kuɗin ta asusunta miliyan uku dama miliyan biyu ya bata, cike da farin ciki Hajiya Bintoto ta miƙa masa Fad'ime sannan suka yi sallama ta shiga mota Rabilu yaja suka bar wurin yayin da shima Alhaji Bukhar ko minti guda bai sake bayan ya karanto wasu latsumai daga shi kar Fad'ime suka ɓace daga wurin.

*FAD'IME POV.*

A hankali take motsa manyan idanunta da take jin sun yi ma ta wani irin nauyi, tarr! Ta ware su tana kallon saman ceiling na saitin da take kwance. Lokaci ɗaya abin da ya faru ya fara dawo ma ta ƙwaƙwalwa. Ta zazzaro ido tana ƙoƙarin tashi miƙe a razane sai dai ji da ta yi ta kasa ya sa ta yi saurin kallon jikinta zaro ido ta sake yi ganin ba kayan da ta baro ƙauye da su ne a jikinta ba, wannan wata doguwar riga ce ta yadi kamar irinta ta asibiti sai dai wannan launin baƙi mai ratsi-ratsin ja ne, ga ƙafafunta ɗaure da wata kakkaurar igiya hannunta ma haka, tashin hankalinta ya ƙaru fahimtar abin da ke shirin faru da ita duk a tunaninta ma sace ta a ka yi hakan ya sa ta daddage iya kar ƙarfinta ta kwala ihu wanda ba iya Ɗakin ba gaba ɗaya duka gidan ma sai da ya amsa, ihu take zubawa wai don ko wani zai kawo ma ta a gaji sai dai har ta gaji bata ga kowa ba, maganar da taji ta gefanta ne ya sa ta ɗan juya a razane, ai kuwa idanunta suka yi kyakkyawan gani da santalelan kan Budurwar dake a aske irin rigar jikin Fad'ime shi ne a jikinta ta saka hannu ta toshe kunnenta sakamakon ihun Fad'ime.
Shiru Fad'ime ta yi tana ƙare ma Budurwar kallo duk da ga halin da take ciki amma sai da dariya ta kwace ma ta lokacin da wannan Budurwar ta ɗa go fuskarta ashe ba iya gashin kanta ba hatta da gashin girarta ma ba'a kyale ba, sai da Fad'ime ta yi dariya san ranta sannan ta tsagaita tana duban Budurwar da ta zuba ma ta idanu ba tare da ta ce ma ta ƙala ba duk da tasan da ita take wa dariyar.

“Wai Dan Allah Baiwar Allah na tambayeki ya a ka yi kika koma haka ne kin ganni ki kuwa caɓɗi-jan sai kace Sule almajiri wai ma ina ne nan wurin?”
Fad'ime ta ƙare maganar tana ƙare ma Ɗakin kallo. Tare da ƙoƙarin kwance ɗaurin da a ka yi ma ta.

‘lallai yarinya baki da hankali wato ma baki san ina ne nan ba sai dai nayi miki uzuri dan da gani daga ƙauye kike'
Budurwar ta raya hakan a ranta, kafin a fili ta furta.
“Gidan ƴan yankan kai ne”
Ta faɗa a taƙaice tare da yin tsitt.

Lokaci ɗaya wutar Fad'ime ta ɗauke na ƴan daƙiƙu kafin ta duba Budurwar cikin tsananin tsoro da zaro ido ta furta.

“Gidan ƴan yankan kai dai? Kamar fa haka kika faɗa wai kuma da gaske kike?”

“ni abokiyar wasar ki ce da zan yi miki wasa?”
Budurwar ta faɗa cikin gatse a zuciyarta kuma tana dariyar ganin yadda Fad'ime ta koma lokaci guda daga jin an ambaci gidan yankan kai.

“wayyo Allahna wayyo Inna Fatuh wayyo ni Fad'ime tawa ta sameni”
Fad'ime ta dage ta fashe da kuka tana faɗin hakan kuma bata dena ƙare ma Ɗakin kallo ba da babu uwar komai ciki domin hatta su a saman tayar tiles suke.

Banko ƙofar a ka yi a fusace wani jibgegen mutumi ya shigo yana zazzare ido ya duba Fad'ime da bata dena kuka ba ya ce.
“idan baki rufemin wannan wawwaran bakin ba sai na ƙari so wurin na yankaki na kaima dodo”

Yadda kasan an yi ruwa an ɗauke haka Fad'ime ta yi tsitt da jin kalamansa.
Ya kyaɗa kai ganin barazanarsa ta yi aiki ya juya domin komawa ya ci gaba aikinsa na tsaro, sai dai ji ya yi Fad'ime ta ƙara fashewa da wani kukan da ya fi na baya tana kiran sunan Inna Fatuh. A mugun fusace ya juyo domin ya ƙari sa ko kifa ma ta mari ne ya yi kota dawo hayyacinta sai dai juyowar da zai yi ya ganta tsaye a gabansa kamar wata aljana, gabansa ne ya yi wani irin mummunar bugawa ganin yadda idanunta suka sauya kala jin ƙarar abu na ɗiga ya sa ya yi saurin kallon ƙasar wai ashe fitsari ne ya suɓuce ya fito masa dan tsabar tsoro ɗagowar da zai yi ya sake dubanta Fad'ime ta shammace shi ta hanyar kai masa wani rikitaccen naushi a tsakiyar kansa domin sai da ta wani daka tsalle kamar yar wasan ƙwallon kwando dake shirin jefa kwallo.
Take a wurin ya zube ƙasa sumamme.
Juyawa Fad'ime ta yi tana dariya ta duba Budurwar data miƙe tsaye tana bin ta da kallon tsoro cikin rawar murya Budurwar ta furta.
“wa..wace ce ke? Kuma me kike shirin aika tawa?”
Fad'ime ta yi dariya sannan ta ce.
“Fad'ime suna na kuma ni Mutum ce sai dai a ƙauyenmu anai mini laƙabi da DANGIN JINNU, kefa mene ne sunanki?”

“Jiddarh”

Cewar Budurwar cikin sanyin murya.

Fad'ime tana shirin magana taji muryar wancan Matar ta mafarkinta a gefenta da sauri ta juya ai kuwa taga matar tsaye a gefanta tana faɗin.

“ki gudu muddun kinaso ki tsira da ranki ni zan taimaka miki ki kuɓuta daga sharrin wannan gidan”

Da mamaki Fad'ime ta ce. “wacece ke kuma me ya sa kikeson taimaka min?”

“zan faɗa miki amma ba yanzu ba kedai ki yi sauri tun kafin su cim miki ki bar gidan nan.”

Shiru Fad'ime ta yi tana nazari duk da gefe guda na zuciyarta tsoro ne fall musamman dataji ance gidan nan na ƴan yankan kai ne, amma kuma tana tsoron ta yarda da wannan matar ita kuma ta cutar da ita.

Ido kawai Jiddarh ta zuba ma Fad'ime tana bin ta da kallon tsoro ganin yadda take magana ita ɗaya sai dai batajin abin da take faɗa.

“na amince zan biki domin ki fitar dani daga gidan nan sai dai da sharaɗin zaki sanar dani wacece ke”

Cewar Fad'ime ba musu Matar ta ce ta amince.

Kallon Jiddarh da tsoro ya cika ta Fad'ime ta yi sannan ta ce.

“in kinga zaki biyo ni mu gudu a tare tohm, in kuma kinga zaki tsaya har zuwa lokacin da za'a raba kanki da gangar jikinki ne sai dai nace miki bissalam”

Shiru Jiddarh ta yi tana nazari ba so ɗaya ba kuma ba biyu ba ta sha ƙoƙarin guduwa daga gidan amma ana kamota wani lokacin ma sai ta sha tafiya sosai sai ta fahimci wuri ɗaya kawai take zagayewa wato bakin kogon, gashi gobe ne kwananta zai ƙare a gidan shi ya sa a ka aske ma ta gashin ta domin gobe ne za'a sadaukar wa da dodo jininta.
Chapter 12 · 0% Book details