← Book details Faɗime Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 13

Sashe 4

Faɗime Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Banza shashasha kawai mai kama da aljanun farko, komai mutum zaiyi bayayi irin na mutane, dubi ke dan Allah kamar wacce aka tonu daga kabari".

"Auta ni ka mara?".

"Na mare ki ko zaki rama ne?"

"Hmmm bazan rama ba amma ka guje abunda zai biyo ba, sanadin wannan marin da kayi min wallahi".

"Idan kin fasa yi min wani abu kin raina Allahn daya halacci ki kinji?, aikin banza kawai".

Ya k'are maganar yana k'arawa gaba ya shige cikin gidan.

"Uhmmm"

Kawai Fad'ime ke yi tana rik'e da kuncinta har yanzu, wani mugun haushin kanta ma take ji mi yasa ma bata d'aga hannu a nan take ta sauke masa marin ba, komai ta fanjama fanjam.

Juyawa tayi ta idasa ficewa daga gidan. Tana fita ta iske su Laure da Sa'ade na jiran fitowarta. K'awayenta ne tun sadda suka dawo gidan Gadonsu, a unguwar suke, tasu ta zo d'aya tsabar suma ba jin magana suke ba.

Tafiya suke buguzun-buguzun, basu aune ba suka ji wani Yaro dake d'an nesa dasu yana cewa.

"Wayyo Jama'a ga dangin Jinnu can ta biyo hanya dangin Aljanu kenan"

Ya idasa fad'ar haka yana nunama wasu Yara dake kusa dashi.

Wani mugun b'acin rai ne ya kama Fad'ime duk duniya idan akwai abunda ta tsana to ace mata dangin Jinnu.

Da gudunta ta k'arasa inda suke, kwai sai dai suka ga tsayuwarta a gabansu kamar wata walk'iya.
Zaro ido sukai a waje suna rarraba ido, wadda ya fad'i maganar ne yayi saurin juyawa zai baza da gudu, kamar walk'iya Fad'ime ta rik'o hannunsa tana kallonsa, jijjga jikinta take tana jefa masa wani mugun kallo.

Laure ce ta rik'e sauran yaran ita da Sa'ade suna cewa.

"Ubanwaye kuke kira da dangin Jinnu iyee?"

"Wallahi Allah bada ku muke ba"

Cewar wani daga cikinsu yana fad'ar maganar jikinsa na d'aukar rawa.

Wadda Fad'ime ta rik'e kuwa yana ji da rashin kunya bai san abunda zai biyo baya ba, yana ji da rashin kunyarsa, saboda wani abu bai tab'a had'asa da Fad'imen ba sai yau.
Ya ce "kaii Isah an fad'a d'in, ance K'anwar Jinnu, ai haka mukaji mutane na fad'a, muma kuma munje mun fad'a, laifi ne mukayi dan mun fad'i sunan da mutane ke fad'i akanki?".

Wata muguwar shak'a da Fad'ime tayi masa, yasa shi fasa wata gigitacciyar k'ara, bai gama dawowa dai-dai ba, tasa d'ayan hannunta ta d'aukesa da wani gigitaccan mari. Wasu taurari ne yaron yaji sun gifta masa, kunnansa ne yaji yayi wani dummmmm, gaba d'aya jinsa ne ya d'auke kwata-kwata baya jin abunda ke wakana.

Fad'ime ta kallesa tana cewa.

"Daga yau idan kunga na taho ku tsaya dan Allah ku jani kunji, idan banci kutumar uban Yaro ba".

Duk abunda take fad'a fa kwata-kwata yaron nan baya ji, jinsa da gaske ya d'auke. Ai ko yana fahimtar haka ya saki wani mugun kuka mai k'ara yana fad'uwa k'asa yana birgima yana magana da k'arfi yana cewa.

"Wayyo Allah na shiga uku na, jama'a ta dod'e min kunne bana ji kwata-kwata, jama'a ku taimaka min na shiga uku".

Abunda yake fad'a kenan yana uban kuka.

Sauran yaran kuwa wani fitsari ne ya kwace masu, sakinsu su Laure sukai suna dariyar mugunta suka kalle suna cewa.

"Abunda yasa zamu barku kuma dan baku fad'i sunan nan bane, kuma zaku iya zuwa ku gaya ma iyayensa, sai a fara nemar masa magani, dan da alama ya kunnansa ya daina aiki".

Suna fad'ar haka Fad'ime tayi gaba suka take mata baya.

Sunzo wani wajan mai tsire kawai Fad'ime ta tsaya tana had'iyar miyau, matsawa tayi kusa sosai da mai tsiren tana cewa.

"D'an juma mai tsire a yanka min na d'ari uku"

Washe baki D'an juma mai tsire yayi yana kallon kyakykyawar fuskar Fad'ime yana lashe baki ya ce.

"Ahh masoyiya Fad'ime ke ce a tahe keda K'awayenki?".

Murtuke fuska Fad'ime tayi tana jin haushin D'an juma mai tsire, wai masoyayirshi, Ubangiji ya kiyaye mata ta so wannan bawan Allahn.
Wani tsaki taja tana k'ank'ance ido ta ce.

"Kaga D'an juma idan zaka bani tsire na d'ari ukun dana ce ka yanke min, ka bani kawai bana son yawan surutu kaji Malam, ko wace ma masoyayir tashi?".

Ta k'are maganar tana harararsa.

Washe baki ya sake yi, shi dai tunda za'a masa ciniki ai ta wuce, domin son kud'i ne da shi baya jin ko yana sonta zai iya bata tsiren nan a kyauta.

Sa'ade ta matso ta kalli Fad'ime a sadda D'an juma ya mik'o mata tsire yana cewa a bashi kud'insa. Hararsa tayi ta ce "kaga na cinye na tafi ban baka kud'inka ba?".

"Ahh to ai kin san bana da mutumci akan kud'i na"

Banza dashi tayi tana jin Sa'ade na cewa.

"Amma Fad'ime karki ci masa tsire kuma al'halin baki da ko sisi fa".

Wata harara itama Fad'ime ta maka mata, ba shiri Sa'ade ta tsuke bakinta tayi shuru.

Guda d'ai-d'aiya ta basu suka amsa suka cinye suna tand'e hannu.

Sai da ta gama ci sana ta kalli D'an juma ta fiddo kud'in nik'an da Inna Fatuh ta bata naira d'ari ce ta mik'a masa.

Amsa yayi tana washe baki, can ya murtuke fuska tamau ganin naira d'ari ce, kallon Fad'ime yake, bala'i cike da cikinsa.

"Kan uba Fad'ime kinga nawa kika bani kuwa?".

"Na sani mana"

"To miye kike nufi dani".

"Yo mifa nake nufi da kai, iya kud'in da nake da su kenan, kama gode Allah ka samu d'ari d'in".

"Ai ko yau akwai bura uba a garin nan, keeeee Fad'ime ni zaki ci ma tsire ki tsaya ido cikin ido ki ce bazaki biya ni sauran kud'i na ba?, to ai ko uwar data haife ce ta dawo duniya na rantse d........ Maganar ce ta katse jin an wasa masa k'asa har kan idonsa.

Murza idonsa yake a haukace, yana murja ido da kyar ya bud'e idon nasa muten sun zagaye shi.

Ihu ya saki ganin yadda tsirensa ya b'aci da uwar k'asa a cikinsa gaba d'ayansa ya lalace, babu wadda zai iya cinsa a haka.

Hango su Fad'ime yayi sun baza da gudu.

Wani ihu ya saki yana cewa.

"Na rantse da tsarkin mulkin Allah yau sai na ci kutumar uban wancan yarinyar Mai kama da aljanu, wallahi Mutane sunyi gaskiya da ake ce mata dangin Jinnu, ai wallahi yau ko za'ayi yak'in duniya na biyu sai an biyani duka kud'in tsire na na rantse kuwa".

Hakuri mutane suka rink'a basa amma ina sai tsine ma su Fad'ime yake daga ita har K'awayen nata, yana Allah wallahi sai an biyasa kud'in tsirensa ko za'ayi mi.

______________
Dai-dai sun iso wajan amsar nik'a, suka ja birki suna sauk'e lumfarfashi.

Dariya kawai Fad'ime keyi su Laure na tayata.

"Kee amma Fad'ime kin shammace sa fa, kawai sai dai yaji saukar k'asa akan kayan sana'arsa".

Cewar Laure tana rik'e cikinta domin ji take ya d'aure sosai, saboda gudun da suka sha da kuma uwar dariyar da suke.

Sauk'e lumfashi Kad'an Fad'ime tayi tana yin gaba taje inda ake saka layi domin amsar nik'a, ita bata sa layi ba ta shige gaba kawai.

Tana cema su Laure.

"Ai kad'an ma ya gani ya ci gaba da tab'a min iyaye sai na yi sanadiyar rugujewar sana'ar tasa walla...

Maganar Fad'ime ce ta mak'ale jin yadda aka wani bangajeta ta fita daga gaban data shiga.

Wata yarinya ce mai jiki sosai k'ibarta har tayi yawa tana kallon Fad'ime data ture tana cewa.

"Keee baki ga layi ake sawa bane?, sai ke isassa kin wani zo kin shige gaba, dama na dad'e ina jin rashin kunyarki to yau da alama zan sauk'e miki ita ne".

Tashi tsaye Fad'ime tayi tana kakkab'e jikinta saboda har sai da ta fad'i lokacin data bangajeta, domin ba k'arama bace wacce ta ture tan, bata jin wannan ko d'an bigeka tayi ba zakai taga-taga zaka zube k'asa ba, yo wannan abu kamar buhu.

Duk irin girman yarinyar hakan bai sa Fad'ime jin wani abu ba, bare azo ga tsoro.

Rik'e k'ugu tayi tana matsowa sosai inda take ido cikin ido ta kalleta ta ce

"Ni kika bangaje?".

"An bangaje ki d'in, ko akwai abunda zaki yi ne?".

Ta fad'a a tsawace tana sake matsowa sosai kusa da Fad'ime kamar zata had'iyeta da ranta.

D'an shafa kanta Fad'ime tayi tana kallon su Laure kyafta masu ido tayi, ai ko suna ganin haka suka shige wajan nik'an da gudu suka warto nik'an dake ajiye, an nik'a shi, suka fito da gudu sukai gaba, mai nik'a na faman kiransu su bashi kud'i, amma Ina sunyi gaba. Fad'ime kuma ganin hankalin mutane ya koma wajan su Laure har wacce ta tureta ma tana binsu da kallo. Batai aune ba kawai taji anyi sama da ita an fyad'a da k'asa ji kake timmmmmmmmm.
Yadda kasan an kada gini.
Kamin ta gama dawowa dai-dai taga Fad'ime ta haye ruwan cikinta ta kama fuskarta sai yakushi take tana kai mata naushi a ciki, sai k'ok'arin k'are kanta take amma ina, taji uwar bari sai kuka take tana kiran azo a ceceta zata kasheta.
Duk irin taruwar da jama'a sukai wajan suna k'ok'arin b'anb'are Fad'ime a jikin yarinyar nan amma Ina abun ya gagara. Shi kansa Mai Nik'an dole tasa ya fito daga Shagon nik'an aka taru dashi ana sun kwace Fad'ime daga jikin baiwar Allahn.

Da kyar da sub'in goshi aka samu Fad'ime ta saki Y'ar mutane, tana uban nishi, tana tashi kuma bata tsaya ba ta k'ara gaba da uban gudu kamar wata zakanya.

Tashi tayi da kyar yarinyar tayi tana kuka. Wata ce ta rik'eta tana cewa.

"Binta mi yasa kika ja Fad'ime, wadda kowa yasan Fad'ime duk garin nan shaid'aniya ce, duk bala'inka waccar yarinyar ta fika".

Kuka Binta ta k'are fashewa dashi tana cewa.

"Na rantse da Allah bazan yarda ba, idan na yarda Allah ya tsine min, wallahi saina gaya ma Innata, wallahi yau sai an d'akko masu Y'an Sadda ko waye ya tsaya mata a garin nan wallahi".

Buguzun-buguzun ta wuce gidansu tana k'ara b'are baki.

__________________
Dandazon jama'a ne a k'ofar gidan su Fad'ime sun taro kowa na tofa albarkacin bakinsa, hayaniya ta kaure sosai a k'ofar gidan mutane na cewa.

"Ai wallahi a fiddo mana ita nan muci uwar shegiya tunda ta addabi kowa a cikin gari".
Chapter 4 · 0% Book details