← Book details Faɗime Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 13

Sashe 13

Faɗime Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Ganin Fad'ime tana shirin fita daga Ɗakin ya sa ta yi saurin bin bayanta cikin ƙasa da murya take faɗin.

“ki fa yi a hankali domin Akwai hatsari abin da kike shirin aikatawa.”

“muke shirin aikatawa dai tun da gaki kin biyoni”

Cewar Fad'ime tana dariya shiru Jiddarh ta yi da yake tasan hanya ita take nuna ma Fad'ime inda za su bi kuma sai ya zama na duk inda ta faɗa ya yi daidai da inda wannan matar take nuna wa Fad'ime sun yi tafiya mai nisa sosai cikin gida kuma Allah ya taimaka ba wanda ya gansu, Fad'ime ta yi mamakin irin shegen girman da gidan keda ga wani irin malkwataɗaɗɗen gini da ta rasa gane kansa ita har ta fara gajiya da tafiyar ma suka ƙari sa wani ƙaton fili na gidan da suna iya hango makeken gate ɗin sai kace na wata Masarautar mai shegen girma. Sai dai me zai faru?
Wata iriyar Mahaukaciyar dariya suka ji an kece da ita kuma ba Muryar Mutum guda ba ne da alama na mutane da yawa ne. Cak! Suka dakata zuciyoyinsu na bugun lugude Fad'ime da Jiddarh suka cure wuri guda jin dariyar bata ƙarau ba ce.
Ai kuwa take mutane da maza da mata suka fara bayyana a wurin suna zagaye su Fad'ime da hakan ya da ɗa, ɗaga hankalin su Fad'ime. Mutanen sanye suke cikin wasu jajaye da bakaken dogayen riguna wurin su goma sha ne mafi yawa daga cikinsu jajayen doyayen riguna zumbula zumbula ne a jikinsu ga wata uwar hula dake jikin rigar da suka rufe fuskokinsu da shi.
Cikin Wata kalar murya mai cike da amo su Fad'ime suka ji an fara faɗin.
“wato kune tauraƙaƙu ko muna tsaka da shagalin bikin shekararmu goma sha biyar da kafuwa shi ne kuke ƙoƙarin guduwa ai kuwa kun tafka Babban kuskure domin a yau ba sai gobe ba zaku sama hukunci na daidai da abin da kuka aikata a yau jininku zamu sadaukar da shi ga dodon tsafi.”
Bayan muryar mai amon ta gama wannan bayani duka mutanen suka sake fashewa da dariya kafin su fara karanto wasu latsumai.

Cikin tashin hankali Fad'ime ta duba Matar da ta bayyana gefanta ta furta. “kin cuceni kin ce na gudu gashi kinja za'a kasheni.”
Da mamaki da kuma tsoro Jiddarh ta kalla Fad'ime jin tana magana tana duban wurin da ita bataga kowa ba.
Ɗaya daga cikin mutanen ne mai sanye da bak'ar riga ya fara tunkaro su Fad'ime suna ja da baya cike da tsoro.
“ki daure karki ji tsoro yana matsowa dab dake ki yi ƙoƙarin tuge hular da ya rufe fuskarsa kinji?”
Matar ta faɗa wa Fad'ime. Kasa magana Fad'ime ta yi ganin ya ƙari so wurin nasu tare da ƙoƙarin saka hannu ya riƙo su Fad'ime ta dage iya ƙarfinta ta daka tsalle tare da tuge hular kansa ai kuwa take fuskarsa ta bayyana, cike da tsoro Fad'ime ta zaro ido yayin da Mutumin yaja baya yana kare fuskarsa domin a ka'idar ƙungiya ba'a ganin fuskokin juna.
Cikin tashin hankali da kuma mamaki ɗaya daga cikin matan wurin da ita sanye take da jan kaya ta rufe fuskarta kamar kowa take duban wannan mutumin da Fad'ime ta buɗe wa fuska.

Alamar jinjina Matar nan ta yi ma Fad'ime sannan ta furta. “ki rufe idonki zan taimaka na tserarta dake kamar yadda nayi alƙawari yanzu ma na bari sun ganki ne saboda kiga wannan fuskar saboda ina da Dalili.
Fad'ime bata sama zarafin furta komai ba ta ƙara riƙe hannun Jiddarh da kyau tare da furta, “matuƙar kinaso ki kuɓuta ki rufe idonki zamu tsira tare.”

Ba musu Jiddarh da jikinta babu inda baya rawa ta yi saurin rufe idonta ita ma Fad'ime haka ai kuwa take a wurin suka ɓace, hankalin waɗan nan matsafa ya ƙara tashi ganin abin da ya faru.....✍️

_______
Laifin daɗi....🤷🥱

Wannan shi ne ana wata ga wata. To dai kunji yadda ta kaya, wai shin kuwa kuna ganin su Fad'ime za su tsira, mene ne zai biyo bayan tsirarsu, akwai ƙura fa, shin wanene wancan Mutumin da Fad'ime ta buɗe wa fuska, kuma wacece Matar da ta ganshi sannan me ya sa ta yi mamaki, wacece wannan Matar da take taimakawa Fad'ime, shin yaya rayuwar Fad'ime zata kasance a cikin birni bayan batasan kowa ba???

To dai duka amsoshin nan suna nan cikin wannan labari na mu mai farin jini wato FAD'IME (Dangin Jinnu) 😂 kuma anan Free Page's suka ƙare.

Kada ku manta dama already mun sanar daku Wagga littafi na kuɗi ne a kan farashin Naira Ɗari hudu kacal, (400₦ only)

Ku tura kuɗaɗen ta wannan asusun:

8081129487. Sabi'u Khadija, MoniePoint Mfb.

Sai ku tura shaidar biya ta nan.
Chat via WhatsApp.
0813 047 9973
Or
07067953066.

Sai mun jiku.... Zahrah Royal Star ce 💋 da Nainarh KD.❤️
Chapter 13 · 0% Book details