← Book details Exiled Prince Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 23

Sashe 3

Exiled Prince Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

" na kira , na kira me za ka yi ? ,ko ba ka son na fadi sunan wanda ya haifi lusarin namiji kamar ka ? tun kafin na sa a cire maka kai , ka fice min da ga fada "

a hankali Malik ya sauke ajiyar zuciya kafin ya ce " Aymane , tun ina yi maka cikin ruwan sanyi , ka sauka da ga kujerar nan "

wani makirin murmushin geffen fuska Aymane ya saki , kafin ya juya ya kalli wani dogari da ke tsaye bakin kofar fadar , da hannu ya mishi allamun ya cirewa Malik kai

ba musu dogarin nan ya tako gadan² ya na zaro takobi wai cire kan Malik
lokaci guda Malik ya kai hannu baya ya fido gun ya juya ya harbe dogarin nan tsakiyar kai , nan take ya fadi kassa matace

ba karamar razana Aymane da mutanan fadar su ka yi ba
a hankali Malik ya juyo , ya saita kan Aymane ya na fadin " idan na ga dama , move guda zan yi na aika inda ka aika mahaifina , amma zan ba ka damar ci gaba da rayuwa , ka sauka da ga kujerar nan "

cikin bacin rai Aymane ya mike tsaye ya na fadin " ba ka da ikon ce min na sauka da ga saman kujerar nan , kai da kanka ka bar ta , kowa ya na shaidar ka hakura da kujerar nan a bisa tsarin masarautar nan , duk Malik din da ya hakura da kujerar shi , ba shi da izinin komowa da sunnan zai koma saman kujerar shi , dan haka ba ka da ikon ce min na sauka "

ya na gama rufe bakin shi ya ga Rafik ya shigo cikin fadar ya na fadin " as a direct descendant of Malik HACHIM bin JAABAR, he has every right to claim the tron ​​of his late father, even if he renounced him "

" Gaskiya Rafik ya fada , dan haka malam ka tattara kayanka ka yi gaba " Fadin Diya ya na karasowa geffen Malik ya tsaya ya na sakin murmushi

" No ! " Aymane ya fada da karfi ya na mikewa tsaye ya ci gaba da cewa " No , ba ka da izinin ce min na sauka , ba ka san irin famar da na sha kafin na hau saman kujerar nan , tun kafin ka shigo duniya na shirya hawa na kujerar nan ta Malik dan har yaron MALIKAT INAS na kashe , na kuma sace mahaifar ta dan kar ta samu wani babyn , amma wannan banzan uban naka ya auri kanwar Daddy , ta haife ka , tun ranar da ka shigo duniya , tawa duniyar ta ruguje , ni na sakawa part din Malik wuta shekara shidda baya kawai dan ka mutu na dawo na kashe Malik , amma wani ikon Allah dan banzan yaron nan ya rayu , okay na hakura , why za ka dawo ? me ya sa ba ka yi zaman ka a cen ba ? amma sai da ka dawo ka shiga tsakanina da burina , amma ban hakura ba ni na juya kwakwolwar Hakim ya harbi Malik saboda ya kassa kashe shi , ni na sa Rouksar zuba mata poison cikin abincinka , ni na saka ta sace ruhin MALIKAT AL'UMU , amma wacen banzar yarinyar ta ruguza shirina baki daya , why ba za ku bar ni na hau kujerar nan cikin konciyar hankali ba ? why ? , wlh ko da sama da kassa za ta nade , ba zan sauka da ga kan kujerar nan ba , ita ce burina a duniyar nan , tun da na taso da son zama saman wannan kujerar na taso , yanzu kuma da na hau ta shi ne za ka ce na sauka ? no , hakan ba zai taba yiyu ba " ya fada cike da bacin rai da allamun fasuwar rai ta kama shi

duk mutanan wajen sai da su ka yi salati su na sauraron abun da Aymane ke fadi , bacin rai ya sa ya tonawa kan shi asiri da kan shi

shiru Malik ya yi ya na sauraron abun da Aymane ke fadi , dole ya yi mishi ta wayo dan ya samu ya sauka da ga kan kujerar nan , Idan ya ce zai ta karfi , ba zai yi nassara ba , dole shi ma ya yi tunani kamar na su na mugaye , dole ya meda kwakwolwar shi irin tasu kafin ya samu Aymane ya sauka da ga kujerar nan , dama an ce mugu shi ya san makwontar mugu , cuta ce za ta dau cuta

a hankali Malik ya sauke ajiyar zuciya , cike da nitsuwa ya ce "as the heir of Malik HICHAM bin JAABAR I have the right to claim the throne of my late father, but since you do not want to give in passively okay, Aymane Abdoul Mujeeb Me Nawfel HICHAM bin JAABAR I provoke you in a duel, the winner will ascend the throne of Saudiya and the loser will pay with his life "

a dubu dari Rafik da Diya su ka kalli Malik su na zaro idanu , har su na hada baki wajen cewa " ka na jin abun da ke fada kuwa , hakan na nufin idan ka fadi kashe ka zai yi "

cikin kwarin guyiwa Malik ya ce " Eh , na ji abun da na fada "

ya na gama fadar haka Aymane ya bushe da wata shegiyar dariya har da tapi ya dafe ciki
shiru kowa ya yi ya kallon shi kamar wani zarrare
sai da ya tsagaita dariyar shi sannan ya dago ya kalli Malik ya ce " kai a ganin za ka iya kashe ni ? , ko ka kashe ni kamar ka kashe maciji ba ka cire kai ba , Okay na yarda , wane irin duel ka ke so mu yi ? "

" Sword Duel " ya fada a takaice ya na kallon Aymane

sake bushewa da dariya Aymane ya yi ya fadin " okay , na yarda , in dai ta haka ne kawai zan zauna saman wannan kujerar , na yarda , kai kuma ka shirya tarda tsohon mahaifinka , dan har yanzu ba a yi wanda zai ga bayan Aymane bin Abdoul Mujeeb , ko mutuwa tsorona na ke , bare kai ragon banza "

" All right , tun da ka yarda fine , yau ranar monday , za mu yi shi a ranar Friday , amma kafin nan , da ga kai har wadanan mutanan fadar taka , ba ku da izinin shigowa fada da sunnan aiki , har sai mun kammala duel din mu , sannan da ga yanzu ka fita da ga Malik Aymane , ka koma Aymane , har zuwa lokacin da za mu kammala , a nada wanda ya yi nassara a matsayin sabon Malik "

" okay " Aymane ya fada a takaice kafin ya sa hannu ya cire Alkyabar Malik da ke jikin shi ya ajiye saman chair din bayan shi , ya cire Rawanin kan shi ya ajiye saman Alkyabar , sannan ya juyo ya fara takawa ya karaso gaban Malik ya tsaya

sai da ya kalle shi cikin ido sannan ya ce " mu zuba mu gani , shege ka fassa , Nawfel Hicham Bin Jaabar tun yanzu ka sa a shirya kabarin ka , da ni ne kai zan ce a yi shi nesa da na mahaifina dan kar ya ga wane irin lusarin yaron da ya haifa " ya kai karshen ya sakin wata yar karamar dariya ya raba ta geffen shi ya wuce

ya na fita Malik ya saki wata yar karamar sheet da ya rike a hannun shi a baya
nan take wajen ya fara zubar da jini
a dubu dari Rafik ya riko hannun nashi ya na fadin " Inallillahi , ranka shi dade , why za ka ji wa kanka haka ? "

a hankali Malkk ya sauke ajiyar zuciya ya na fadin " dole na yi hakan , if not zuciya za ta debeni , na buge shi "

ya na gama fadar haka ya dago kai ya kalli mutanan fadar Aymane , wani mugun kallo ya wurga musu nan take su ka sha jinin jikin su
cikin ba da umarni ya ce musu " idan ku ka yi one minute a cikin wajen nan , ka tabbatar gawarku ce za su fita "

bai gama rufe bakin shi ba su ka tashi daya bayan daya da gudu su ka fice fadar , ta rage da ga Diya sai Malik sai Rafik

su na fita Shi ma Malik ya juya ya fice fadar , ya na tafiya kamar zai tashi sama hannun shi na zubar da jini , ga idanun shi duk sun yi ja da allamun ya na cikin bacin rai

kai tsaye part MALIKAT HOUDA ya nufa , babu ko sallama a bakin shi ya shigo parlourn
nan ya tardo su duk su na zaune ban da Inaya da mama da su ka shiga Bedroom
duk su na ganin shi kowane ya saki wani kyawatencen murmushi , MALIKAT INAS har da hawaye

har sun tashi za su nufe shi , su ka ga Diya ya fado mishi a baya ya rungume shi ya na fadin " ni dama na san za ka dawo , tabbas za ka dawo , ai dama damuna a lokacin da a ka fi bukatar ta ta ke samuwa , kamar wata ka ke a sararin samaniya haskenka ya na mamaye duk duniya , na ji dadin ganin ka abokina , I have really missed you "

ya na gama rufe bakin shi , Malik ya kai hannu cikin zafin nama ya medo Diya gaban shi , ya dunkule hannu ya kai mishi wani mugun bugu a face har sai da ya fadi kassa

a tare duk mutanan wajen su ka razana , Nesrine har da sakin kara , lokaci guda babyn ta ya saki kuka kamar ya san abun da ke faruwa
Chapter 3 · 0% Book details