← Book details Exiled Prince Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 23

Sashe 16

Exiled Prince Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

sai da ya shiga sannan ya su ka juyo su ka kalli junan su baki sake su na zaro idanu , wata yar karamar kara su ka saki da dariya a tare kafin Adel ya ce " sai da na ce muku Malik ne amma ba ku yarda ba "

wani dan karamin murmushin geffen fuska Malik ya saki dan ya jiyo abun da ya ce , da ga haka ya ci gaba da tafiyar shi har ya iso part din MALIKAT HOUDA

bakin shi da sallama ya shigo parlourn MALIKAT HOUDA , nan ya tardo ta zaune tare da MALIKAT AL'UMU da mama da Nesrine , MALIKAT AL'UMU na rike da Nailah , MALIKAT HOUDA kuma ta na rike da Junior ( 🤣🤣🤣✌ gaskiya sai dai mu kira shi da Junior dan ni mutum guda na bawa wannan sunnan wato MALIK NAWFEL HICHAM BIN JAABAR , MY NUMBER ONE 🤣✌ ) MALIKAT INAS kuma ta na rike da Nayel

bai ce musu komai ba ya nufi corridor ya shige , kai tsaye bedroom din da Inaya ke ciki ya nufa dan dama ita ya zo nema

ya na shiga ya gan ta konce tsakiyar gado , ta dunkule waje guda , idanunta na bude
da sauri ya nufi gadon dan a nashi tunanin wani abu ya same ta , ya na isa ya zauna a baki ya na fadin " my Cutie , me ya faru ? ciwo ki ke ? "

a hankali ta dawo da kallon ta gare shi , ta saki wani dan karamin murmushi ta ce " yanzu fa na tashi da ga barci , ko one minute ba a yi ba da na bude ido "

a hankali ya sauke ajiyar zuciya kafin ya ce " to me ya faru ? ko wani abu ki ke so ? fada min zan je na kawo miki "

girgiza mishi kai ta yi ta na fadin " yaya Zayd ba na bukatar komai a yanzu , kawai ina son na huta , jikina duk a mace ya ke "

a hankali ya sunkuyar da kai ya manna mata kiss saman forehead ya na fadin " okay my Cutie , konta ki huta , dama na zo na fada miki ran Friday za mu tafi Makkah , da ga nan mu koma gidanmu na US "

wani dan karamin murmushi ta saki murya a sanyaye ta ce " da gaske yaya Zayd , za mu tafi Makkah ? "

gyada mata kai ya yi a hankali ya na cewa " har Madina sai mun biya , da ga nan mu tafi Dubaï mu yi shopping sannan mu komawar US "

har ta saki wani dan murmushi sai ta marairaice fuska ta na fadin " baby , please tell me , baby nawa na haifa ? don Allah ka fada min , wlh hankalina duk ya ki konciya , da na lumshe idanu sai na dinga jiyo Muryar shi "

wata yar karamar ajiyar zuciya ya sauke , a sanyaye ya ce mata " Cutie , me ki ke so na ce miki yanzu ? "

a hankali ta mike zaune , ta jingina bayanta a jikin forehead din gadon , ta riko hannunshi ta na fadin " ka fada min gaskiya mana , zan fi jin dadin ka fada min gaskiya ko me zai faru hakan zai sa na ji sanyi a zuciya ta , ko dai babyn bai zo da rai ba ? " ta fada ta na dan marairaice fuska

sai da ya dauki lokaci kafin ya ce mata " i'm sorry my Cutie , na yi tunanin in na boye miki hakan ba za ki ji zafin rashin ba , amma gaskiya ne Triplets mu ka samu , sai dai namijin na biyu bai zo da rai ba , I'm sorry "

wata nanauyar ajiyar zuciya ta sauke kafin ta lumshe idanunta , ta fara zubar da hawaye
da sauri ya fara goge hawayen ya na fadin " kin gani ko , shi ya sa na ki fada miki , ga shi yanzu ki na kuka "

a hankali ta girgiza mishi kai ta na fadin " ba komai baby , Allah zai ba mu wani , ko ba komai yanzu zan daina wannan tunanin , amma please ina son na ga Nayab , ina so na ga in ya na kama da Nayel din mu " ta kai karshen ta na ware idanunta a sanyaye

girgiza mata kai ya yi a hankali kafin ya ce " i'm sorry my Cutie , amma tun ranar a ka yi jana'izar shi , bayan ni da doctor da nurse biyu sai mama ba wanda ya san wannan maganar , ko je dan kin matsa ne na fada miki , ki yi hakuri don Allah "

a hankali ta sakin mishi kuka ta na fadin " yanzu ka hana ni ganin babyna , why za ka yi haka , da ka bar ni na gan shi mana "

" i'm sorry my Cutie , wlh ban yi hakan dan na cutar da ke , please ki daina kukan nan wlh b....... "

bai kai karshen maganar shi ba kawai ya ga ta koma Aswad lokaci guda ta na daga mishi da karfi ta ce " ka daina ce min na yi shiru , babyna ne ba nata ba , why za ka ce a yi jana'izar shi ba tare da na gan shi ba " ta fada har wani sama gashin ta ya yi kamar a na hura shi da iska

ba karamar razana Malik ya yi ba , har sai da ya mike tsaye ya na karanto kalmar shahada
wasu yawu ma su daci ya hadiye kafin ya ce " please my Cutie, calm down , please , i'm sorry "

ya na gama fadar haka kawai ya ga ta saki kuka , wasu bakaken hawaye na zubo mata , ta na fadin " ka kawo min babyna na gan shi , ka kawo min shi na gani " ta fada a sanyaye kafin ta lumshe idanunta a hankali , nan take jelar gashinta ta zubo saman shoulder din ta

wata nanauyar ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ware idanunta a hankali
shi ma nanauyar ajiyar zuciya ya sauke ganin idanunta sun dawo dai'dai
a hankali ya zube saman guyiwowinshi ya riko kunnuwan shi , ya na fadin " i'm so sorry my Cutie , just na yi tunanin in na boye miki hakan ba za ki ji zafin mutuwar Nayab ba , ban yi tunanin hakan zai cutar da ke ba , i'm sorry , please forgive me , please "

( in na gane wani abu 🤔🤔🤔 Nayel shi ya dauko Abyad , Nayab kuma ya dauko Aswad , yanzu da babu Nayab Aswad za ta koma jikin Nailah1 ko kuwa ? )

wani dan karamin murmushi ta sakin mishi kafin ta mika mishi hannu
a hankali ya mike tsaye ya riko hannunta , ya zauna bakin gadon
" babu komai , na gode baby , na san duk abun da ka yi ka yi shi because you love me , kuma ba ka son abun da zai cutar da ni , ko ba komai na so na ga Nayab , amma tunda kai ka gan shi , ni ma kamar na gan shi ne , so it's okay now " ta kai karshen ta na sakin mishi wani dan karamin murmushi

murmushi shi ma ya sakin mata kafin ya kai hannu ya fara goge mata bakaken hawayen Aswad ya na fadin " kin sani , ya na kama sosai da Prince , kamar an tsaga kara , ba abun da ya baban ta su "

murmushi kawai ta yi mishi kafin ta koma ta konta ta na fadin " ni yanzu barci na ke ji baby , kuma in na tashi ina son ka shirya min diner da kanka "

" duk abun da ki ke so sarauniyata "

a hankali ta lumshe idanunta ta na sakin murmushi , ta na a haka ta ji saukar lips din shi saman kumatunta ya manna mata kiss sannan ya mike ya na fadin zai dawo zuwa anjima
gyada mishi kai kawai ta yi ba tare da ta ce komai ba
da ga haka ya sa kai ya baro bedroom din
har zai fita parlourn MALIKAT HOUDA ta yi saurin ce mishi " da ka tafi da ita ma zai fi , ka zo ka wuce mutane ko sannu babu "

slowly ya juyo ya kalle ta ya ce " ke dai tsohuwar nan kin shiga rayuwata wlh , sai na yi maganin ki nan gama , kar ki damu ki na gani zan zo na dauke ta na tafi da ita ai dama tawa ce ba taki ba , ci gaba da shiga harkata sai na rataye ki , tsohuwa kawai " ya kai karshen ya na juyawa ya fice abun shi

baki sake MALIKAT HOUDA ke kallon shi , har sai da ya fita sannan ta dawo da kallonta kan MALIKAT AL'UMU da ke rike da jikanta ta ce " kin dai ji abun da yaron ki ya ce ko ? kuma ba ki ce mishi komai ba ?

wata yar karamar dariya MALIKAT AL'UMU ta yi ta na fadin " to mamie ya zan yi ? na isa na shiga tsakanin mata da mijinta , um um ku yi dramar ku cen nawa ni dai kallo kawai "

a tare duk mutanan wajen su ka yi dariya har ita MALIKAT HOUDA , ba karya tun lokacin da Malik ke karami ya saba sosai da MALIKAT HOUDA , dan bayan ita babu wanda ya ke yi wa wassan kaka da jika , ita ma bayan shi ba wanda ta ke yi wa irin wannan wassan , jinin su ne ya hadu tamkar ita ce kakar shi ta gaskiya bayan ba shi da hadi da ita

❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤

( LOVE MEETS POWER ) 👑🔥

( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )

STORY & WRITTEN BY : MEERAH ⚘🕊

【THE ROYALTY LOVE ❤🌹】

【 BOOK ________ 4📚✍❤ 】

_______________________🕊✍🕊✍🕊✍🕊✍🕊✍🕊✍🕊______________________
Chapter 16 · 0% Book details